Bidiyo: Yarinyar da aka ceto bayan kwana 3 a ƙarƙashin gini a Turkiyya

An wallafa

Ku latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon:

An ciro wata yarinya ƴar shekara uku daga ƙarƙashin ɓaraguzan gini da ranta, wadda ta shafe kusan kwana uku a ciki.

Tawagogin masu bincike a birnin Izmir da ke kusa da tashar jiragen ruwa na ci gaba da neman waɗanda ake sa ran suna raye bayan ƙaƙƙarfar girgizar ƙasar da aka yi ranar Juma'a.