Bidiyo: Matan Afirka da Trump ya juya wa baya kan hana su maganin hana ɗaukar ciki

An wallafa

Ku latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon:

A bayyane yake ƙarara cewa Shugaba Trump na Amurka ba abin da ya sha masa kai da harkar Afirka, musamman ganin yadda ya janye tallafin kasuwanci da na lafiya.

Sannan bai taɓa ziyartar nahiyar ba tun da ya hau mulki.

Janye tallafin na Amurka ya jefa mutane da dama musamman mata cikin halin ni ƴasu, ta fannin janye tallafin da ya shafi lafiya.

BBC ta yi nazari kan hakan.