Bidiyo: 'Bala'in da muka gani a zuwan sojoji wajen zanga-zangar EndSars'

An wallafa

Ku latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon:

Rahotanni sun ce an harbe mutane da dama tare da jikkata wasu a yayin zanga-zangar EndSars a Legas.

Wasu shaidu sun cewa BBC ji suka yi kamar yaƙi ake yi a yayin a sojoji suka far musu da nufin kashe su suna tsaka da zanga-zangar tasu ''ta lumana''.

Rundunar sojin Najeriya dai ta yi watsi da hannu cikin lamarin.

An ɓoye sunayen shaidun da suka yi magana da BBC saboda tsaro.