Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
WAEC: Bidiyon ranar farko ta fara jarrabawar kammala sakandare a Najeriya
An wallafa
Ku latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon:
A yau Litinin ɗaliban ajin ƙarshe na sakandare a faɗin Najeriya ke soma rubuta jarrabawarsu ta kammala karatu bayan da aka samu jinkiri na watanni saboda annobar cutar korona.
Ɗalibai fiye da miliyan ɗaya da dubu ɗari biyar ne ake sa ran za su ɗauki tsawon makwanni suna rubuta jarrabawar da ake kira WAEC wadda kuma a kan yi a wasu ƙasashen yammacin Afirka.
Ɗaliban sun fara ne da jarrabawar Lissafi.