Cutar Hepatitis: Abubuwan da ba ku sani ba game da ciwon hanta

An wallafa

Latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon:

Binciken lafiya ya nuna cewa cutar hanta wato Hepatitis B ta zamo cutar da ke kisa a boye.

Masana harkar lafiya sun ce cutar ta fi kisa fiye da cutar Malaria a shekara.

Binciken ya ce kimanin mutane miliyan 257 ne ke fama da cutar samfurin 'B' a duniya, kuma Najeriya na daga cikin kasashe biyar da ke da kashi 60% na masu fama da wannan cutar.

An ware ranar 28 ga watan Yulin kowace shekara a matsayin ranar ciwon hanta ta Hepatitis. Akan haka ne BBC ta yi nazari na musamman a wannan bidiyon kan mece ce cutar da kuma yadda za a kare kai daga kamuwa da ita.

Bidiyo: Bashir Idris

Tsarawa: Usman Minjibir

Karin labaran da za ku so ku karanta