Bidiyon hada-hada a babbar kasuwar Kano bayan bude ta

An wallafa

Latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon:

A ranar Laraba ne sausaucin dokar fita da gwamnati Kano ta yi na bai wa ‘yan kasuwa damar fita domin ci gaba da harkokin cinikinsu.

Gwamnatin jihar ta ce an bude kasuwar ne bayan cimma matsaya da wakilan 'yan kasuwar wajen samar da matakan da za a a dauka a wajen ganin ba a sami yaduwar cutar ba.

Ranakun Laraba da Juma’a da Lahadi ne ranakun da gwamnatin ta amince da a bude wuraren ibadu da kuma kasuwani a jihar.

A wannan bidiyon abokin aikinmu a Kano Khalifa Shehu Dokaji ya dauko mana yadda Kasuwar Sabon Gari ta kasance a ranar farko ta bude ta.