Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Ko Haaland zai kara taka rawar gani a 2023/24

Wannan shafi ne da ke kawo muku labarai da rahotanni kai tsaye kan cefanen 'yan kwallo da labarin wasanni.

Rahoto kai-tsaye

Ibrahim Yusuf Mohammed

  1. Chelsea ta dauko golan Brighton kan fam miliyan 25

    Chelsea ta amince ta siyan golan Brighton Robert Sanchez kan kudi fam miliyan 25.

    Kungiyar dai na neman kara mai tsaron gida a kungiyar bayan sayar da Edouard Mendy ga Al-Ahli ta kasar Saudiyya.

    Sanchez, mai shekara 25, zai kalubalanci Kepa Arrizabalaga wurin neman matsayi na daya a kungiyar.

    Dan wasan na kasar Sifaniya ya na da alaka da masu horar da kungiyar a Chelsea yayin da kocin msui tsaron gida Ben Roberts ya yi aiki tare da shi lokacin da yake Brighton.

    Sanchez ya kasance tare da Brighton tun yana da shekaru 15, bayan ya koma sashen matasansu daga Levante a 2013.

    Ya buga wasansa na farko na Brighton a watan Nuwamba 2020 kuma ya yi kusan shekara biyu yana matsayin mai tsaron gida na daya a kungiyar.

    Haka kuma kasar Sifaniya ta kira shi a shekarar 2021 kuma yana cikin tawagar ta a gasar cin kofin kasashen Turai da aka jinkirta da kuma gasar cin kofin duniya ta 2022, duk da cewa ya buga wasanni biyu ne kacal..

  2. Zaroury ya tsawaita yarjejeniya a Burnley

    Dan wasan kasar Morocco Anass Zaroury ya sanya hannu kan kwantiragin shekaru biyar da Burnley.

    Dan wasan ya koma kungiyar a bazarar da ta gabata kuma ya ci kwallo 11 a wasanni 39 da ya buga. inda ya taimaka wa Burnley ta lashe gasar Championship a bara kuma ya sami shiga tawagar 'yan wasan kasar Morocco zuwa gasar cin kofin duniya.

    Zaroury ya bayyana kakar wasan bara a matsayin wadda ta fi muhimmanci a rayuwarsa na dan wasa, kuma yana sa ran taimakawa kungiyar ta Burnley a inda za ta fafata a gasar Firimiyar bana.

  3. Yunus Musah ya koma AC Milan

    Dan wasan tsakiyar Amurka Yunus Musah ya koma AC Milan kan kwantiragin shekaru biyar bayan da aka kammala cinikinsa daga Valencia.

    An sami labarin cewa A ranar Juma'a ne Musah ya isa birnin Milan bayan cimma yarjejeniya tsakanin kungiyoyin kuma Valencia ta tabbatar a cikin sanarwar ta cewa Musah ya koma kan farashin Yuro miliyan 20.

    Musah ya zama dan wasan Amurka na biyu da ya koma Milan a bazara bayan Christian Pulisic ya koma daga Chelsea.

    Milan ta sanar da cewa Musah zai sanya riga mai lamba 80 a San Siro.

    Dan wasan wanda haifaffen dan New York ne yana rike da fasfo din Italiya, duk da cewa ya cancanci bugawa Italiya ko Ingila ko Ghana, Musah ya fara buga wa Amurka wasa a shekarar 2020.

    Ya bugawa Valenci wasanni 37 a kakar wasan da ta gabata kuma ya taimakawa kungiyar ta kaucewa fadawa rukunin gajiyayyu.

  4. Ramadani ya koma Lecce daga Aberdeen

    Dan wasan Albania Ylber Ramadani ya bar Aberdeen ya koma Lecce ta Seria A kan kudin da ba a bayyana ba.

    Dan wasan mai shekaru 27 ya koma Aberdeen a watan Yunin da ya gabata daga kungiyar MTK Budapest ta kasar Hungary kuma ya taka rawar gani yayin da Dons suka zo na uku a gasar Firimiyar kasara Scotland.

    Ya buga wasanni 44, inda ya zura kwallo daya, yayin da Aberdeen ya samu gurbin shiga gasar cin kofin Turai.

    Aberdeen ta dauko 'yan wasa da damam a yunkurinta na taka rawar gani a kakar wasa mai zuwa.

    'Yan wasan da kungiyar ta dauko sun hada da Slobodan Rubezic da Ester Sokler da Nicky Devlin, da Ross Doohan da kuma Or Dadia kafin fara sabon kakar wasa a ranar Asabar da kuma kammala yarjejeniyar dindindin na Graeme Shinnie da Leighton Clarkson.

  5. Chelsea da Man City na zawarcin Olise

    Chelsea da Manchester City sun kara kaimi a yunkurinsu na daukar dan wasan gaban Crystal Palace Michael Olise.

    Rahotanni sun bayyana cewa dan wasan na kasar faransa na daya daga cikin 'yan wasan da kungiyoyin biyu ke sha'awar dauka amma akwai dan rudani a kan sharuddan kwantairagin dan wasan.

    Roy Hodgson ya bayyana cewa Palace na da aiki a gabanta don ci gaba da rike dan wasan mai shekaru 21, wanda ya lashe kyautar gwarzon dan wasan kungiyar. Olise ya ba da taimako hudu a gasar Firimiya a bara kuma farashinsa ba zai zama matsala ga Chelsea ko City ba.

    Manyan 'yan wasa sun bar Etihad wannan bazaran inda aka tabbatar da ficewar Riyad Mahrez zuwa Saudiyya cikin kwanakin nan, haka ya bar City a da gurbi cikin 'yan wasan gefe kuma yanzu ana samun jita-jita game da yiwuwar ficewar Bernardo Silva.

    Ya zuwa yanzu dai city ta dauko Mateo Kovacic ne kawai kuma ana sa ran za a kara yawan ‘yan wasan kafin a rufe kasuwar cinikin ‘yan wasa.

    Ita kuma Chelsea ta ci gaba da taka rawar gani a kasuwar inda take ta siye da sayar da 'yan wasa a Stamford Bridge yayin da Mauricio Pochettino ke inganta tawagar 'yan wasansa.

  6. Ajax ta dauko Borges daga Man City kan fam miliyan 17.3

    Ajax ta sayi dan wasan gaban Portugal Carlos Borges daga Manchester City a kan kudi kusan Yuro miliyan 20 (£17.3m).

    A kakar wasan da ta wuce, dan wasan mai shekaru 19 ya kare dan wasan da ya fi zura kwallaye a gasar Premier 2 - matakin farko na kwallon kafa - da kwallaye 21 a wasanni 24.

    Borges ya bar City ba tare da ya taba yin babban wasa a kungiyar farko ba, bayan shiga bangaren marasan kungiyar a 2014.

    City ta ta makala sharadin karban kashi 20% cikin kudin da za a sayar da dan wasan nan gaba.

  7. Brighton ba ta da niyyan sayar Caicedo a wannan bazarar

    Brighton na sa ran cewa Moises Caicedo zai ci gaba da kasancewa a kungiyar idan aka rufe kasuwar cinikin 'yan wasa a ranar 1 ga Satumba.

    Dan wasan dai ya kasance kan gaba cikin 'yan wasan da suka yi zawarci a bazaran nan bayan Arsenal ta nuna sha'awarta a watan Janairu.

    Babu kungiyar da ta taya dan wasan kan farashin da Brighton ta kayyade kawo yanzu kuma ba sa tsammanin wannan yanayin zai canza a wannan bazarar.

    Brighton ta dage kan cewa ba sa son sayar da dan wasan na kasar Ecuador mai shekara 21, kuma ba su da bukatan yin hakan bayan ficewar Alexis Mac Allister zuwa Liverpool.

    An sanar da Caicedo game da wannan matsayin kuma Brighton ba ta yi tunanin haka zai zama matsala ba.

    Dan wasan ya nemi barin kungiyar a watan Janairu sakamakon zawarcin Arsenal.

    Brighton ta ki amincewa da haka, sai Caicedo ya sanya hannu kan sabuwar kwangila a cikin watan Maris wanda zai gudana zuwa 2027.

  8. Livramento ya koma Newcastle daga Southampton

    Newcastle United ta kammala cinikin dan wasan baya na Southampton Tino Livramento kan fam miliyan 40.

    Dan wasan mai shekaru 20 ya koma Southampton daga Chelsea a shekarar 2021 kan fam miliyan 5.

    Tafiyar Livramento na zuwa ne bayan da Southampton ta fice daga gasar Premier a bara.

    DAn wasan bayan na Ingila 'yan kasa da shekara 21 ya buga wasanni biyu kacal a karshen kakar wasan da ta wuce bayan ya samu rauni a watan Afrilun 2022.

    Livramento ya buga wasanni 32 a kakar wasa ta 2021-22, 28 daga cikinsu a gasar Firimiya.

  9. Chelsea ta sayi Disasi kan kwantiragin shekaru shida daga Monaco

    Dan wasan baya na kasar Faransa Axel Disasi ya koma Chelsea daga Monaco kan kwantiragin shekaru shida akan Yuro miliyan 45 (£38.57m).

    Disasi, mai shekaru 25, ya koma kungiyar ta Stamford Bridge bayan Wesley Fofana ya samu mummunan rauni a gwiwa.

    Ya buga dukkan wasanni 38 a gasar Ligue 1 ta Monaco a kakar wasan da ta wuce.

    Disasi ya buga wa Faransa wasa sau hudu, ciki har da wanda ya shigo daga baya a wasan karshe na cin kofin duniya na 2022 da Faramnsa ta fafata da Argentina, kuma ya buga wa Monaco wasanni 129 bayan ya koma daga Stade de Reims a watan Agustan 2020.

    Dan wasan ya zama dan wasa na shida da Chelsea ta saya a bazara bayan sayen Christopher Nkunku da Nicolas Jackson da Lesley Ugochukwu da Angelo Gabriel da kuma Diego Moreira, yayin da sabon koci Mauricio Pochettino ke ci gaba da sanya tambarinsa a kan kungiyar.

    A halin da ake ciki, Blues ta amince da farashin mai tsaron gida Robert Sanchez da Brighton, yayin da Brighton ta cigaba da kin amincewa da tayin da Chelsea ke yi kan dan wasan tsakiya Moises Caicedo.