Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Ma'aikatar lafiya a Gaza ta ce an kashe ƙarin Falasɗinawa 193 daga Juma'a

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Rahoto kai-tsaye

Umar Mikail and Buhari Muhammad Fagge

  1. Ban-kwana

    Nan muka kawo ƙarshen labarai da rahotannin namu na yau sai kuma gobe....

  2. Isra'ila ta kashe wani fitaccen masanin kimiyya a Gaza

    Ma'aikatar ilimi ta Falasdinu a Gaza ta ce an kashe wani fitaccen masanin kimiya da iyalansa a hare-haren sama da Isra'ila ke kai wa a birnin Gaza.

    Mutumin mai suna Sufyan Tayeh shi ne shugaban jami'ar musulunci ta Gaza kuma ke jagorantar sashin bincike a physics da lissafi.

    Ma'aikatar lafiyar Hamas ta ce mutane sama da 190 aka kashe tun bayan kawo karshen yarjejeniyar tsagaita wutar mako guda ta wucin gadi

  3. Rasha na ƙara dakarunta a yaƙi da Ukraine mai samun goyon bayan Nato

    Shugaban Rasha Vladimir Putin ya sanya hannu kan wata doka da za ta bayar da damar ƙara yawan dokarun Rasha da kashi 15.

    Za a kai akalla sojoji 170,000 kari a kan wadanda suke fafatawa a filin daga a wurare daban daban, wanda hakan zai kai adadin yawan dakarun sojin Rasha 1,320,000 a Ukraine.

    Ma'aikatar tsaron Rasha ta ce wannan wani mataki ne ga barazanar da take kara fuskanta, ciki har da fadada ayyukan NATO.

    An yi amannar Rasha ta yi rashin nasara a yakin da aka kwashe kusan shekara ɗya da rabi ana fafatawa a hannun Ukraine, ko da yake ba ta bayyana hakan ba a hukumance.

  4. Masu kare muhalli sun nuna damuwa a taron COP 28

    A yayin taron sauyin yanayi na Majalisar Ɗinkin Duniya da ke gudana a Dubai, ƙasashe da kamfanoni da dama sun ɗauki alƙawarin aiki tuƙuri domin rage ɗumamar yanayi a duniya.

    Ƙasashen 100 ne suka yi alƙawarin ninka yadda suke amfani da makamashi maras gurbata muhalli sau uku nan da 2030.Kamfanonin mai da na gas 50 ne ciki har da Aramco na Saudiyya suka yi alƙawarin daina amfani da gas ɗin da yake ƙara dumamar yanayi nan da 2050.

    Sai dai wannan alƙawari ya shafi hayakin kabon ne kawai, ba sauran da ake samu ba lokacin aikin man fetur.

    Masu kare muhalli sun nuna damuwa kan yadda ake ci gaba da samun yawan sinadaran da ke cutae da muhalli.

  5. Mun kama gonar tabar wiwi a jihar Sokoto - NDLEA

    Hukumar hana sha da fataucin miyaguin kwayoyi ta Najeriya NDLEA ta ce ta gano gonar tabar wiwi a jihar Sokoto da ke arewacin Najeriya.

    Kwamandan hukumar a jihar Malam Adamu Iro Muhammad ya ce sun samu labarain gonar ne sannan suka kai mata sumamye domin tabbatar da labarin da suka samu.

    "Ba mu taba ganin irin wannan abu ba a jihar Sokoto, wani mutum ne ya yi noman wiwi a gonarsa tare da masara, na kusan eka uku.

    "Mun je mun kama mutumin da ake zargi muka yi masa hotuna a cikin gonar." in ji Malam Adamu Iro.

    A cewar Malam Adamu ta'ammali da miyagun kwayoyi a jihar na ƙaruwa.

    "Ban da tabar wiwi akwai wasu kwayoyi da suke damunmu a nan wadanda matasa ke sha, akwai wata kwaya da ake kira MET, wacce ta zama ruwan dare a nan Sokoto.

    "Muna iya ƙoƙrinmu iya kokarinmu amma abin na cin tura," kamar yadda Kwamandan ya fada.

    Ya yi kira ga al'ummar jihar da su zama masu bai wa jami'ai haɗin kai wajen gudanar da ayyukansu ta hanyar ba su bayanan sirri na masu aikata laifukan da ke laɓewa a cikin mutane.

  6. Cikin hotuna yadda hare-haren Isra'ila suka lalata yankin kudancin Gaza

    Kudancin Isra'ila na ci gaba da fama da hare-haren Isra'ila tun bayan ƙarewar yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin Isra'ila da Hamas.

    Gwamman Falasɗinawa ne ake gani a zaune a wajen gidajensu a garain Hamad, yankin da Qatar ke ɗaukar nauyi da ke kusa da Khan Younis, bayan dakarun Isra'ila sun yi wa garin ruwan bama-bamai.

    Majiyoyi da dama sun ce an yi wa mazauna yankin gargaɗi gabanin fara kai hare-haren.

  7. Shugaban Faransa zai je Qatar don tattaunawa rikicin Falasɗinawa da Isra'ila

    Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya ce zai je Qatar domin tattaunawa kan sabuwar yarjejeniyar tsagaita wuta a yaƙin da ake yi tsakanin Hamas da Isra'ila.

    Macron ya bayyana haka ne a yayin taron sauyin yanayi na Majalisar Ɗinkin Duniya da ake kira "Cup28" wanda yake gudana a Dubai.

    A jiya Isra'ila ta ci gaba da kai hare harenta a Zirin Gaza bayan tsagaita wuta da aka yi ta kwanaki 7.

    Ma'aikatar lafiya a Gaza ta ce an kashe ƙarin Falasɗinawa 193 tun lokacin da Isra'ila ta ci gaba da kai hare-hare a Zirin Gaza ranar Juma'a.

    Ta ce an kuma raunata wasu mutum 652 tun bayan ƙarewar wa'adin tsagaita wuta na kwana bakwai.

    A cewar hukumomin lafiya na Hamas, adadin mutanen da aka kashe a Gaza ya zarce 150,000 kuma kashi 70 daga cikinsu mata ne da ƙananan yara.

  8. Dakarun juyinjuya halin Iran sun ce harin Isra'ila a Syria ya kashe mambobinsu

    Wani hari da Isra'ila ta kai Syria ya rutsa da wasu mambobin dakarun rundunar juyin juya hali na Iran, kamar yadda kafafen yaɗa labarai na Iran ɗin suka ruwaito.

    Da take sanar da mutuwar IRGC ta ce Mohammed li Ateai da Panah Taghizadeh aka kashe yayin da suke wani aiki a Syria.

    Dakarun Iran suna taimakawa gwamnatin Syria na tsawon shekaru wadda shugaba Bashar Al-Assad ke jagoranta

    Tehran na cikin manyan masu goyon bayan Hamas da kuma ƙungiyar Hezbollah mai ƙarfin fada a ji, wadda ke musayar wuta da Isra'ila a kan iyakar Lebanon tun ranar 7 ga watan Oktoba.

  9. Amurka ba za ta taɓa yarda da korar Falasɗinawa daga Gaza ba - Kamala Harris

    Mataimakiyar Shugaban Amurka Kamala Harris ta ce ƙasar "ba za ta taɓa yarda a fitar da Falasɗinawa daga Gaza ba, ko Gaɓar Yamma da Kogin Jordan, ko datse Gaza, ko kuma sauya iyakar zirin na Gaza".

    Kalaman nata na zuwa ne yayin ganawarta da Shugaban Masar Abdul Fattah al-Sisi, inda ta gode masa bisa rawar da yake takawa wajen kwashe 'yan Amurka daga Gaza.

    Yayin tattaunawar tasu a Dubai, a gefen taron COP28, Harris ta ce za a cimma abin da aka saka a gaba ne kawai "idan aka bi su ta hanyar lumana a fayyace wajen sama wa Falasɗinawa ƙasarsu ta kansu ƙarƙashin Hukumar Falasɗinawa [Palestinian Authority]".

    Harris ta kuma bayyana ƙarara cewa Hamas ba za ta sake mulkin Gaza ba kuma Amurka za ta "dage wajen ganin an sako dukkan mutanen da Hamas ɗin ke garkuwa da su a Gaza".

  10. Labarai da dumi-dumi, An umarci jami'an Isra'ila su bar Ƙatar bayan tattaunawa ta tsaya cak

    An umarci jami'an leƙen asiri na Isra'ila su bar Ƙatar bayan tattaunawa kan ƙulla yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza ta ci "tura", a cewar hukumar Mossad mai leƙen asiri ta Isra'ila.

    Cikin wata sanarwa da ofishin firaministan Isra'ila ya fitar, Mossad ta ce shugabanta David Barnea "ya bai wa mutanensa a Doha umarnin su koma Isra'ila" bayan Firaminista Benjamin Netanyahu ya nemi su yi hakan.

    "Ƙungiyar Hamas ba ta cika alƙawari ba, wanda ya tanadi za ta saki dukkan yara da matan da ke hannunta kamar yadda Isra'ila ta ba ta jerin snayensu kuma ita ma ta amince," in ji sanarwar.

    Ƙatar ce ta yi ta shiga tsakani don ƙulla yarjejeniyar tsakanin Isra'ila da Hamas tun bayan ɓarkewar yaƙin, inda ta taka muhimmiyar rawa wajen tsawaita kwanakin tsagaita wutar har zuwa kwana bakwai da kuma sakin mutanen.

  11. Rukunin farko na motocin agaji sun shiga Gaza bayan cigaba da faɗa

    Ƙungiyar agaji ta Palestinian Red Crescent ta ce rukunin farko na motocin agaji sun shiga Gaza tun bayan ƙarewar wa'adin tsagaita wuta a ranar Juma'a tsakanin Isra'ila da Hamas.

    An ruwaito cewa motoci kusan 50 ne suka shiga ta mashigar Rafah. Ƙungiyoyin agaji na cewa har yanzu akwai ƙarancin kayayyaki.

    Motocin na kan hanyarsu ta zuwa mashigar Awja don bincka su kafin a bari su ƙarasa cikin Zirin Gaza, kamar yadda majiyoyin daga Masar da Red Crescent suka shaida wa Reuters.

    Kafin fara yaƙin, ƙungiyoyin agaji sun ce ana buƙatar motoci kamar 100 na kayayyaki kullum don cigaba da rayuwa lami lafiya a Gaza.

  12. Labarai da dumi-dumi, Ma'aikatar lafiya a Gaza ta ce an kashe ƙarin Falasɗinawa 193 daga Juma'a

    Ma'aikatar lafiya a Gaza ta ce an kashe ƙarin Falasɗinawa 193 tun lokacin da Isra'ila ta ci gaba da kai hare-hare a Zirin Gaza ranar Juma'a.

    Ta ce an kuma raunata wasu mutum 652 tun bayan ƙarewar wa'adin tsagaita wuta na kwana bakwai.

    A cewar sanarwar da ta fitar, jimillar Falasɗinawan da aka kashe a Gaza sun zarta 15,000 tare da raunata sama da 40,000 - kashi 70 cikin 100 na mutanen mata da ƙananan yara.

  13. Abin da ke jawo toshewar jijiyoyin jini ga masu ciki

    Shirin Lafiya Zinariya na wannan makon ya duba abin da ke jawo cutar toshewar jijiyoyin jini ga mata masu ciki.

  14. Babu kayan agajin da suka shiga Gaza tun bayan ƙarewar wa'adin tsagaita wuta - MDD

    Hukumar MDD mai agaza wa Falasɗinawa ta UNRWA ta ce babu wasu kayan agaji da suka shiga Zirin Gaza tun bayan ƙarewar yarjejeniyar tsagaita wuta ta ɗan lokaci a ranar Juma'a.

    Juliette Touma, mai magana da yawun UNRWA, ta faɗa wa BBC cewa: "Abin da muke fargaba shi ne za mu koma inda muke a farkon wannna rikici, lokacin da aka hana shiga da koma Zirin Gaza - wanda har yanzu ake ci gaba da jin raɗaɗinsa."

    Ta ce akwai ƙoƙarin da ake yi na ci gaba da kai kayan agajin, kuma ta yi kiran a tsagaita wuta.

    "Yanzu muna dab da afkawa cikin bala'in da ɗan'adam ya ƙiƙira a Gaza," a cewar Touma.

  15. Idan lokaci ya yi za mu saki Mohamed Bazoum - Firaministan Nijar Lamine Zeine

    Filin Gane Mini Hanya na wannan makon ya tattauna da Firaministan Nijar da sojoji suka naɗa, Ali Lamine Zeine.

    Mista Zeine ya mayar da martani game da kalaman Ministan Harkokin Wajen Najeriya Yusuf Tuggar kan takunkuman da Ecowas ta ƙaƙaba wa Nijar ɗin bayan juyin mulki.

  16. MDD ta amince ta zare hannunta daga sasanta rikicin Sudan

    Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya (MDD) ya kaɗa ƙuri'ar kawo ƙarshen kudirinsa na taimaka wa Sudan dawowa kan turbar dimokraɗiyya daga ranar Lahadi.

    Gwamnatin mulkin sojin ƙasar ce ta bukaci hakan a watan da ya wuce.

    Sudan ta fada cikin yakin basasa tsawon watanni bakwai, inda ake fada tsakanin sojojin gwamnati da kuma na dakarun RSF.

    Dangantaka tsakanin gwamnatin Sudan da MDD na kara tsami sannan kuma kwamitin tsaron na aiki a kasa ne tare da amincewarta.

    Wakiliyar BBC ta ce kungiyoyin agaji sun bukaci MDD ta lalubo hanyar da za a kare fararen hula da kuma tabbatar da daƙile ayyukan cin zarafin su.

  17. Kasafin kuɗin Najeriya na 2024 ya tsallake karatu na biyu a majalisun ƙasar

    Majalisar Dattawan Najeriya da ta Wakilai sun yi wa kasafin kuɗin ƙasar na 2024 karatu na biyu ranar Juma'a kwana biyu bayan Shugaba Bola Tinubu ya gabatar musu da shi.

    A ranar Laraba ne Tinubu ya je majalisar tare da gabatar da naira tiriliyan 27.5 a matsayin kasafin abin da gwamnatinsa za ta kashe a 2024, kuma ya nemi 'yan majalisar su gaggauta amincewa da shi.

    Sai dai shugaban bai bayyana adadin abin da kowace ma'aikata da hukumomin gwamnati za su samu ba a lokacin da ya yi gabatarwar, abin da ya jawo cecekuce da muhawara a ƙasar.

    Jaridar Daily Trust ta ruwaito 'yan majalisar na kokawa yayin muhawarar da suka yi ranar Juma'a game da ƙarancin bayanai kan kasafin, wanda suka ce ya sa sun mayar da hankali ne kawai kan abubuwan da Tinubu ya faɗa a jawabinsa.

    Jam'iyyun adawa sun soki kasafin da cewa "na yaudara ne", yayin da Shugaba Tinubu ya yi masa laƙabi da "kasafin sabunta fata".

    • Fankon kundin kasafin kuɗi Tinubu ya ba mu — Ƴan Majalisa
    • 'Kasafin kuɗin da Tinubu ya gabatar cike yake da bashi da yaudara'
  18. Ɓarnar da Isra'ila ta yi a Gaza bayan ƙarewar yarjejeniyar tsagaita wuta ranar Juma'a

  19. Isra'ila ta hana jami'ar MDD shiga Gaza da yankunan Falasɗinawa

    Isra'ila ta ce ba za ta sabunta takardun izinin shiga Gaza da kuma Gaɓar Yamma da Kogin Jordan ba na babbar jami'ar ayyukan agaji ta Majalisar Dinkin Duniya (MDD) a yankunan Falasɗinawa da Isra'ila ta mamaye.

    A watan da ya gabata ne ma'aikatar harkokin wajen Isra'ila ta zargi Lynn Hastings da nuna son-kai tsakanin Isra'ilar da Falasinawa, zargin daMDD ta yi watsi da shi.

    Mai magana da yawun MDD, Stephane Dujarric, ya ce Babban Sakatare Antonio Guteres na da cikakken kwarin gwiwa a kan Ms Hastings kan abin da ya kira "duk wani kalubalen aiki".

    Ya ce akwai barazanar da aka dinga yi mata wanda kuma ba za a amince da ita ba.

  20. Isra'ila ta hari wurare 400 a Gaza bayan ƙarewar tsagaita wuta ranar Juma'a

    Tun bayan ƙarewar gajeriyar yarjejeniyar tsagaita wuta ranar Juma'a, Isra'ila ta kai hare-hare kan wurare har 400 a Zirin Gaza, a cewar rundunar sojin ƙasar.

    Ta ce ta kai hare-haren ne ta sama, da ruwa, da ƙasa, ciki har da wasu yankuna a kudancin Gaza.

    "Jiragen yaƙi sun kai hari kan sama da wurare 50 a munanan hare-hare kan unguwar Khan Younis," in ji ta cikin wata sanarwa.

    Sanarwar ta ƙara da cewa jirage sun kai wa wani masallaci hari a arewacin Gaza, tana mai iƙirarin cewa mayaƙan Islamic Jihad ne ke amfani da shi a matsayin cibiyar yaƙi. BBC ba za ta iya tabbatar da gaskiyar wannan iƙirari ba.

    Bayan umarnin da sojojin Isra'ila suka bai wa mazauna Gaza na barin gidajensu daga arewaci zuwa kudanci, dubun dubatar mutane ne ke samun mafaka a Khan Younis - akasari cikin tantuna da kuma wuraren da Majalisar Ɗinkin Duniya (MDD) ta samar.