Mu kwana lafiya
Nan za mu rufe wannan shafi na labarai kai-tsaye.
Mu haɗu da ku gobe don samun wasu labaran da suka shafi rayuwarku.
Umar Mikail ke muku fatan alheri.
Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najieriya da sauran sassan duniya.
Abdullahi Bello Diginza and Umar Mikail
Nan za mu rufe wannan shafi na labarai kai-tsaye.
Mu haɗu da ku gobe don samun wasu labaran da suka shafi rayuwarku.
Umar Mikail ke muku fatan alheri.
Gwamnonin yankin arewa maso yammacin Najeriya sun gana da shugaban Bankin Raya Afirka (Africa Development Bank - AfDB), inda suka nemi tallafin bankin wajen haɓaka harkokin noma.
Wata sanarwa daga fadar gwamnatin jihar Zamfara ta ce gwamnan jihar, Dauda Lawal. ya nemi bankin ya kafa wata da'irar harkokin noma da masana'antu da zimmar sarrafa amfanin da aka noma a cikin gida.
"Yayin tattaunawar da gwamnonin Zamfara, da Kebbi, da katsina, da Jigawa, da Kano, da Kaduna suka yi da shugaban AfDB Akinwumi Adesina, sun faɗa masa yankunan da suka fi buƙatar tallafi," in ji sanarwar.
Gwamnonin sun nemi agajin bankin ne don ya tallafa musu wajen daƙile ƙalubalen da suka haɗa da tsaro, da inganta rayuwa, da kuma noma, kamar yadda sanarwar ta bayyana.
Ta ƙara da cewa bankin ya nuna sha'awarsa ta tallafa wa jihohin, inda "shugaban bankin ya jinjina wa gwamnonin game da fifita walwalar al'ummarsu".
An daɗe ana nuna fargaba game da ayyukan 'yan fashin daji da ke hanawa tare da ƙwace wa manoma amfanin gonarsu a waɗannan jihohi, abin da ka iya jawo ƙarancin abinci a yankin da Najeriya baki ɗaya.
Abin da ya sa za mu soke rajistar kamfanoni 30,000 a Najeriya - CACMintuna 45 da suka wuce
Hukumar da ke yi wa kamfanoni rijista a Najeriya ta Corporate Affairs Commission ta ce za ta rufe kamfanonin da ba su biyan kuɗin shekara-shekara.
Sabon shugaban hukumar ta CAC, Hussaini Ishaq Magaji (SAN), ya faɗa wa BBC Hausa cewa adadin kamfanonin da lamarin zai shafa ya kai 30,000.
A cewarsa, za su soke rajistar ne daga ranar 31 ga watan Disamba mai kamawa.
Kamfanoni da sana’o'in da matakin zai fi shafa su ne na shirya tafiye-tafiye, da ‘yan canji, da na haƙar ma’adanai da kuma lauyoyi.
Ɗaruruwan Falasɗinawa ne suka fice daga farfajiyar Asibitin Al-Shifa a yau Asabar, bayan kwanaki da sojojin Isra'ila suka shafe suna dudduba abin da suka kira "cibiyar yaƙi ta Hamas" a ƙarƙashinsa.
Zuwa yanzu ba ta gabatar da wata hujjar kirki ba da ke nuna hakan, bayan wasu bindigogi da kuma wani rami da ta ce ita ce hanyar shiga cibiyar ta Hamas.
Ɗazun nan muka bayar da rahoton harin da aka kai wa wata makarantar MDD a sansanin Jabalia da ke arewacin Gaza, wanda ma'aikatar lafiya a Gaza ta ce ya kashe mutum 50.
Tun daga lokacin ne kuma rundunar sojin Isra'ila ta fara bayyana yadda "za ta faɗaɗa hare-haren da take kaiwa" a sassan zirin na Falasɗinawa.
Rundunar da ake yi wa laƙabi da IDF ta ce a cikin awa 24 da suka wuce "ta kai hare-hare a Zaytun da sansanin Jabalia, inda suka yi arangama da 'yan ta'adda da suka kai mata hari daga gidajen farar hula da makaman harbe tanka da bama-bamai".
Ta ƙara da cewa dakarunta sun "kashe" adadi mai yawa na mayaƙan Hamas, "kuma ta hari gine-ginen 'yan ta'adda da dama".
Kafin yanzu, mai magana da yawun IDF, Laftanar Kanar Peter Lerner, ya faɗa wa BBC cewa suna bincike kan harin.
Rahotonni na cewa an kai wa wata makarantar Majalisar Ɗinkin Duniya (MDD) hari a arewacin Birnin Gaza, inda aka kashe mutane da dama tare da jikkata wasu.
Ma'aikatar lafiya da ke Zirin Gaza ta faɗa wa kamfanin labarai na AFP cewa an kashe aƙalla mutum 50 sakamakon harin da Isra'ila ta kai kan makarantar ta Al-Fakhoura da ke cikin sansanin Jabalia.
Sai dai rundunar sojin Isra'ila ta ce tana bincike kan lamarin.
BBC ba ta iya tabbatar da abin da ya faru ba, amma mun ga wani sahihin bidiyo da ke nuna mutane da yawa da aka ji wa rauni a wurin.
Kamfanin dillancin labarai na AFP ya fitar da wasu hotuna da ke nuna jerin gwanon Falasɗinawa na barin Asibitin Al-Shifa a ƙafa.
Rahotonni sun ce ɗaruruwan mutane ne suka fice daga asibitin, wanda dakarun Isra'ila suka mamaye tsawon kwanaki.
Hotunan sun nuna maza, da mata, da yara na tafiya a kan titin da ɓaraguzai suka shafe yayin da wata motar rusau ta sojoji ke wucewa a bayansu.
Wakilin AFP ya ce daga cikin mutanen akwai marasa lafiya da waɗanda suka ji rauni yayin da suka kama hanyar zuwa kudancin Birnin Gaza daga arewaci.
Tun da fari, ma'aikatar lafiyar Gaza ta ce akwai marasa lafiya 120 da kuma wasu jarirai bakwaini da ba a san adadinsu ba da suka rage a asibitin.
Shugaban asibitin ya zargi Isra'ila da tilasta kwashe marasa lafiyar, amma dakarun sojan ƙasar na cewa wai sun taimaka ne wajen biyan buƙatar da shugaban ya nema.
Mun bayar da rahoton cewa yara kusan 15 ne da ke buƙatar kulawar gaggawa suka isa Haɗaɗɗiyar Daular Laraba (UAE) bayan kwashe su daga Zirin Gaza ta mashigar Rafah.
Kalli lokacin da suka isa filin jirgin sama na Abu Dhabi da kuma lokacin da ake zuba su cikin motocin jinya:
Hukumar agajin Falasdinawa ta Majalisar Dinkin Duniya, UNRWA, ta ce ta karɓi man fetur da aka shigar Gaza, to sai dai ta ce ana buƙatar ƙarin man, domin ci gaba da gudanar da ayyukan jin ƙai.
A jiya ne Majalisar yaƙi ta Isra'ila ta ce za a bar tankokin man fetur biyu su shiga Gaza a kowace rana.
To sai dai UNRWA cikin sanarar da ta fitar, ta ce motoci man fetur biyu rabi ne na bann da ake buƙata don gudanar da ayyukan jin ƙai a kowace rana.
Ana buƙatar man fetur domin zuba wa motocin ɗaukar marasa lafiya, da kwasar bahaya da asibitoci da kuma injunan kamfanonin sadarwa.
Jirgin farko ɗauke da ƙananan yaran Falasɗinawan da suka jikkata daga Gaza, waɗanda ke buƙatar yi musu aiki sun isa birnin Abu Dhabi na ƙasar Haɗaddiyar Daular Larabawa.
Jirgin na ɗauke da ƙananan yara kusan 15 da iyayensu, waɗanda suka taso daga ƙasar Masar bayan da suka fita daga Gaza ta mashigar Rafa.
Ƙasar Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa na fatan ɗaukar mata da ƙananan yara kimanin 1,000 daga Gaza domin yi musu magani a asibitocinta cikin makonni masu zuwa.
Kungiyar Agajin UAE ta Red Crescent na shirin gina asibitin wucin-gadi a yankin Masar a kusa da kan iyakar Rafah ga waɗanda jinyarsu ba za ta bari su iya yin doguwar tafiya ba.
Asibitocin Gaza na fuskantar kalubale masu yawa sakamakon mamayar Isra'ila, wada ta haddasa rashin wutar lantarki, da ruwan sha da sauran manyan abubuwan buƙatu.
Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya taya gwamnati da al'umar Laberiya murna kan samun nasarar kammala zaɓen shugaban ƙasar cikin kwanciyar hankali.
Cikin wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban ƙasar, Ajuri Ngelale, ya fitar, shugaba Tinubu ya taya sabon zaɓaɓɓen shugaban ƙasar Joseph Boakai,murnar lashe zaɓen, tare da yin kira a gare shi da ya haɗa kan 'yan ƙasar wajen gudanar mulki don samar wa ƙasar ci gaba.
Haka kuma shugaban na Najeriya ya jinjina wa shugaban Laberiya, George Weah, bisa nuna abinda ya kira "tattakun shugabanci da ba kasafai ake nuna irinsa ba'' ta hanyar karɓar faɗuwa domin kauce wa rikici a ƙasar.
"Abin da shugaba Weah ya yi babban abin misali ne a tsarin dimokradiyya a wannan lokaci musamman a yankin Afirka ta Yamma, inda dimokradiyya ke fuskantar barazanar masu ƙwace wa mutane abin da suka zaɓa", in ji Tinubu
"Haƙiƙa na jinjina wa shugaba George Weah bisa halin kima da dattaku da ya nuna. Ya nuna cewa bai kamata sakamakon zaɓen ya zama silar tashin hargitsi a ƙasar ba," in ji shugaban na Najeriya.
Yarda da faɗuwa tare da taya abokin hamayya murnar lashe zaɓe, ba abu ne da aka saba gani ba a nahiyar Afirka, inda galibi waɗanda suka sha kaye kan garzaya kotu don neman haƙƙinsu, bisa zargin aikata maguɗi a zaɓukan da suka sha kayen.
Hukumar da ke yaƙi da cin hanci da yi wa tattalin arzikin Najeriya zagon ƙasa ta EFCC ta bayyana takaicinta kan yadda ta ce wasu jami'an sojin saman ƙasar suka kutsa ofishinta da ke Kaduna domin ƙwato 'yan uwansu da hukumar ta tsare bisa zargin 'karya dokar aikin tsaro'.
Cikin wata sanarwa da hukumar ta fitar, mai ɗauke da sa hannun jami'ain hulɗa da jama'a na hukumar, Dele Oyewale, ta ce a ranar Litinin 13 ga watan Nuwamba jami'in EFCC sun kama wasu mutum biyar da hukumar ke zargi da aikata laifukan da suka shafi zambar kuɗi ta intanet a unguwar Barnawa da ke birnin Kaduna
Hukumar ta ce ta kama mutanen ne ba tare da wani tashin hankali ba, daga nan ne kuma wasu mutum shida - da suka haɗar da sojoji huɗu da ɗaliban cibiyar fasahar aikin sojin sama biyu - waɗanda ke wurin a lokaci da aka kama waɗanda ake zargin, suka yi wa ofishin EFCC da ke Kaduna ƙawanya da nufin tilasta sakin mutanen.
''Daga nan ne kuma aka kama su tare da tsare su a ofishin hukumar, bisa zargin karya dokar aiki tsaro", kamar yadda sanarwar ta yi bayani.
A yayin da ake tare da mutanen hukumar EFCC ta ce ta tuntuɓi rundunar sojin sama ta ƙasa inda hukumomin biyu ke tattanawa domin warware lamarin.
Dele Oyewale ya ce a ranar Juma'a wasu jami'an sojin sama sun dirar wa ofishin EFCCn da ke Kaduna a cikin shirin faɗa, don tilasta sakin abokan aikin nasu.
"Hukumar EFCC ta yi aiki cikin nutsuwa, inda ta ci gaba da tattaunawa da jagororin rundunar sojin saman, kuma daga ƙarshe aka cimma matsayar sakin sojojin bayan an ɗauki bayanansu", kamar yadda mai magana da yawun EFCCn ya bayyana.
Sojojin Isra'ila sun ce za su ''ƙara yawan motocin agajin'' da za su shigar da tallafi zuwa Gaza, tana mai cewa a yanzu ''babu iyakancewa'' na yawan motocin da za a bari su shiga yankin.
Cikin wata sanarwar da Kanar Elad Goren na rundunar soji Isra'ila ya fitar, ya ce Isra'ila za ta "ƙara yawan motocin kayan agajin matuƙar ana buƙatarsu".
Ya ƙara da cewa "Duk motocin da Majalisar Dinkin Duniya ta buƙaci a shigar, za mu bari su shiga'' bayan an tantance su.
"Don haka a yanzu ya rage wa MDD ta ba mu adadin da ake buƙata, idan ana buƙatar mota 400, a goben nan za mu bari su shiga, a yanzu babu iyakancewa," in ji shi.
Isra'ila ta tsananta ƙayyade adadin kayan agajin da ke shiga Gaza tun bayan harin 7 ga watan oktoba da Hamas ta kai cikin ƙasarta.
ƙungiyoyin bayar da agaji a baya sun sha faɗin cewa mafi ƙarancin manyan motocin agajin da ake bukata don wadatar da mutanen Gaza shi ne mota 100 a kowace rana.
Sai dai alƙaluma daga hukumar agajin Masar ta Red Crescent da hukumar jin-ƙan Falasɗinawa ta UNRWA sun ce babu wata motar agaji da ta shiga yankin Zirin Gaza cikin kwanaki uku da suka gabata sakamakon ƙarancin man fetur.
Fadar White House ta Amurka da Majalisar Dinkin Duniya sun ce matakin Isra'ila na ɗage takunkuminta da bayar da damar shigar da man fetur sau biyu a kullum a Gaza, ya yi kaɗan kuma ba zai wadatar wajen gamsar da buƙatar agajin da ake ciki ba.
Isra'ila da ke fuskantar matsin lambar diflomasiyya, ta ce ta ɗaga ƙafa ne domin taimakawa don magance matsalolin da ake ciki na rashin wutar lantarki domin a samar da ruwa, da amfanin bahaya da layukan sadarwa.
A ranar Juma'a manyan kamfanonin sadarwa biyu na Gaza suka ce an ɗan dawo da layukan wayoyi na wucin-gadi bayan samun fetur.
Isra'ila dai na cigaba da luguden bama-bamai a yankin.
Ko a yau Asabar kafar yaɗa labaran Falasɗinawa ta ce an kashe mutum 26 a hare-haren sama.
Shugaban Liberia, George Weah, ya amince da shan kaye a zaɓen shugaban ƙasa zagaye na biyu da aka gudanar a makon da ya gabata.
Mista Weah ya shaida wa 'yan ƙasar a wani jawabi da ya gabatar a kafar rediyon ƙasar cewa jam'iyyarsa ta fadi zaɓe, sai dai kuma Liberia ta yi nasara.
Bayan kammala ƙidaya kusan dukkanin ƙuri'un da aka kaɗa, jagoran 'yan adawa Joseph Boakai ke kan gaba da 'yar tazara kaɗan na kashi 51 cikin 100.
Zarge-zarge rashawa na daga cikin batutuwan da suka dabaibaye Mulkin shugaba Weah, amma kuma amincewa da shan kaye ya kafa tarihi a karo na biyu na miƙa mulkin dimokuradiya a cikin shekaru shida.
Kuma wannan shi ne zaɓe na farko tun bayan da Majalisar Dinkin Duniya ta kawo ƙarshen ayyukanta na wanzar da zaman lafiya shekara biyar da suka gabata sakamakon yaƙin basasa a ƙasar.
Masu bin shafin BBC Hausa Kai-tsaye barkanmu da hutun ƙarshen mako.
Abdullahi Bello Diginza ke fatan sake kasancewa da ku a wannan safiya domin kawo muku irin wainar da ake toyawa a fadin duniya.
Ku ziyarci shafukanmu na sada zumunta domin tafka muhara kan labaran da muke wallafawa.