Ma'aikatan asibiti sun tsunduma yajin aiki a Amurka
Sama da ma'aikata dubu saba'in da biyar ne da ke aiki a daya daga cikin manyan ma'aikatan kiwon lafiya na Amurka sun fara yajin aikin kwanaki uku.
Yajin aikin ya hada da ma'aikatan agaji, da masu share-share da masu fasaha, da maiakatan bangaren magunguna da masu aikin lafiyar ido wadanda ke aiki da maiakatar kiwon lafiya ta Kaiser Permanente.
Yawancin a jihar California suke, amma da wasu da ke jihohin Oregon da Colorado.
Hakan na zuwa ne bayan babbar kungiyar kula da lafiya mai zaman kanta da kungiyoyin kwadago sun kasa cimma matsaya bayan shafe watanni ana tattaunawa kan albashi, da kuma karancin ma’aikata.
Likitoci da ma'aikatan jinya da yawa da ke aiki da Kaiser Permanente ba su shiga yajin aikin ba.