Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Zulum ya nuna damuwa kan yadda ya ga asibitin Gwoza

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Abdullahi Bello Diginza and Ahmad Tijjani Bawage

  1. Rufewa

    Mun zo karshen rahotanni a wannan shafi na kai-tsaye.

    Sai kuma gobe Litinin idan Allah ya kai mu - za mu dawo muku da sabbin labarai.

    Ahmad Bawage ke cewa mu kwana lafiya.

  2. An ceto ƴan cirani 80 a Libya

    Jami’an tsaro a iyakokin kasar Libiya sun yi nasarar ceto ƴan cirani da dama bayan ƴan sandan Tunisiya sun jibge su iyakar ƙasar da Libiya.

    An samu akalla mutane 80 da suka haɗa da mata da yara ƙanana cikin tsananin yanayin zafin da ya kai maki 40 na ma`aunin celsius da kuma rashin ruwan sha.

    A farkon wannan wata wani mutum guda ya rasa ransa a lokacin rikici a birnin Sfax na kasar ta Tuniya.

    Jami`an tsaron Tunisiya dai na kamen ƴan cirani sannan su jibge su a iyakokin Libiya da Aljeriya ba tare da kulawa ba.

  3. Ba za mu lamunci cin zarafin ƴan Afrika da ake yi ba - Tinubu

    Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya ce Afirka ba za ta iya samun haɗin-kai da wadata ba yayin da ‘yan nahiyar ke ci gaba da shiga kunci.

    A cikin jawabinsa na farko a taron tsakiyar shekara na kungiyar haɗin kan Afrika karo na biyar a Kenya a yau Lahadi, Tinubu ya tabbatar da buƙatar samun hadin kai a Afirka da watsi yiwuwar faɗa wa sabon rikici ga nahiyar.

    Tinubu ya kuma yi gargaɗin cewa ba za su lamunci cin zarafin ƴan nahiyar da ake yi ba kamar kuma yadda ya faru a baya.

    “Ba za mu iya haɗa kan Afirka ba kuma mu sami wadatar da muke nema yayin da ’yan’uwanmu ke cikin kangin wahala da baƙin ciki. Dole ne mu ci gaba a matsayin nahiya guda da samar da zaman lafiya da wadata,” in ji shugaban, a cewar wata sanarwa da kakakinsa, Dele Alake ya fitar.

    Ya kuma bayyana shirin karfafa rundunar haɗin gwiwa ta kungiyar raya tattalin arzikin ƙasashen yammacin Afrika domin dakile juyin mulki da yaki da ta'addanci a yankin.

    Shugaban na Najeriya, wanda shi ne shugaban kungiyar Ecowas, ya bayyana irin ci gaban da kungiyar ta samu a ɓangarori daban-daban da suka haɗa da kasuwanci da zirga-zirgar jama'a da inganta zuba jari da samar da ababen more rayuwa da tsaro da sauransu.

  4. Ina da kwarin gwiwar cewa za mu sayi Harry Kane - Ollie Hoyness

    Shugaban kungiyar Bayern Munich Uli Hoeness ya ce yana da kwarin gwiwar cewa za su sayi kyaftin ɗin Ingila Harry Kane a bazara.

    An ruwaito cewa zakarun na Jamus sun yi tayin fam miliyan 70 don siyan ɗan wasan gaban na Tottenham.

    Shugaban kungiyar kwallon kafa ta Tottenham Daniel Levy ya gana da jami’an Bayern Munich a ranar Alhamis kan yiwuwar siyar da shi, inda kuma suka tattauna da mashawartan ɗan wasan.

    Hoeness ya shaida wa Sport1 cewa "Kane ya nuna karara a duk tattaunawar da ya yi cewa shawararsa ta tsaya - kuma idan ta tsaya, to za mu same shi."

    "Yana son taka leda a Turai kuma sa'a a gare mu Tottenham ba za ta buga gasar zakarun Turai ba a shekara mai zuwa. Yanzu yana da wata dama ta zuwa babbar kungiya a Turai."

    Kane, wanda kwantiraginsa a Spurs zai kare a watan Yuni mai zuwa, ya zura kwallaye 30 a gasar Premier a bara.

  5. Ƴan sandan Iran za su dawo kama matan da suka karya dokar rufe gashin kansu

    Ƴan sandan Iran sun fara samame domin sanya ido kan matan da ke karya dokar rufe gashin kansu.

    Kafofin yaɗa labaran ƙasar ta ce 'yan sandan na ci gaba da sintiri domin kamo mata da ke bijirewa dokar rufe gashin kansu a bainar jama'a.

    A bara ne zanga-zangar ta ɓark e a faɗin ƙasar ta Iran bayan mutuwar Mahsa Amini.

    Bayan zanga-zangar, gwamnatin Iran ta yanke shawarar soke 'yan sandan ɗa'a'. Aikin ’yan sandan ɗa’a shi ne tabbatar da ka’idojin shigar da tufafin Musulunci a ƙasar.

    Yanzu haka dai an samu labarin cewa 'yan sanda za su sake fara sintiri a motoci da kuma kafa domin kamo waɗanda suka karya dokar. Bayan haka kuma za a gurfanar da su a gaban kotu.

  6. An kashe mutum 11 a wani hari a Kongo

    Akalla mutane 11 ne suka mutu sakamakon wani harin ramuwar gayya da ƴan tawaye suka kai gabashin Jamhuriyyar Dimokuraɗiyyar Kongo.

    Mazauna yankin arewacin birnin Goma, na zargin kungiyar M23 da kai harin. Ɗaruruwan iyalai ne ke kauracewa yankin yayin da ‘yan tawayen ke kwace kauyuka a ‘yan kwanakin nan.

    Kwararru na Majalisar Ɗinkin Duniya da gwamnatin Kongo da kuma wasu ƙasashen yammacin Turai na zargin Rwanda da goyon bayan kungiyar M23 - abin da ta musanta.

    Wani shugaban kungiyoyin fararen hula a gabashin Kongo ya ce tun da farko an yi artabu tsakanin 'yan tawayen M23 da mayakan sa-kai, inda bayan sa'o'i mutane suka gano gawawwakin.

    Ya ce waɗanda harin ya rutsa da su fararen hula ne da ƴan tawayen suka tilasta musu ɗaukar kaya kafin a kashe su a garin Bukombo.

    Akwai kungiyoyi da dama masu ɗauke da makamai da ke fafutukar neman mulki da wani yanki na arzikin ma'adinai na gabashin Kongo, inda M23 ke ɗaya daga cikinsu mafiya karfi.

    Ko da yake Kigali ta musanta hakan, akwai kwararan hujjoji da ke tabbatar da cewa Rwanda na goyon bayan kungiyar.

    Tana so ta yi amfani da kungiyar Tutsi M23 da suka fi yawa domin tinkarar duk wata barazana daga 'yan tawayen Hutu da ke da sansani a lardin Kivu ta Arewa.

  7. 'Yan Arsenal da za su buga wasannin sada zumunta a Amurka

  8. Ambaliya ta hallaka mutum 37 a Koriya ta Kudu

    Masu aikin ceto da ke kokarin kai wa ga motocin da suka maƙale a wani rami da aka yi ambaliya da ke kusa da birnin Cheongiu na Koriya ta Kudu sun ce sun gano gawawwaki tara kawo yanzu.

    Ambaliyar da aka samu sakamakon mamakon ruwan sama da aka kwashe kwanaki ana tafkawa a cikin mashigar karkashin kasa, ta sanya fasinjoji da direbobi maƙale wa a cikin motocinsu.

    Akalla mutane 37 ne suka mutu bayan ambaliyar, inda aka kuma samu zaftarewar kasa da kuma katsewar wutar lantarki a yawancin sassan ƙasar. Har yanzu ba a ga mutane tara ba.

    Har yanzu dai ba a san adadin mutane nawa ne suka maƙale a cikin rami mai tsawon mita 685 a garin Osong ba, amma ana tunanin motoci 15 ne suka nutse.

    An tsinto gawawwaki da dama daga cikin wata motar safa da ceto mutane tara a ranar Asabar.

  9. Mawakiya Jane Birkin ta mutu tana da shekara 76

    Jane Birkin wadda ta kasance mawakiyar kuma 'yar wasan kwaikwayo, ta rasu a yau tana da shekaru 76.

    Ta kasance ƴar asalin Birtaniya kuma ta yi yawancin ayyukanta ne a Faransa.

    An fi saninta ne ta don ƙwararriyar dangantakarta sirri tare da mawaƙin Serge Gainsbourg kuma an ɗauke ta a matsayin mashahuri abin koyi a shekarun 1960 da 1970.

    Kafofin yaɗa labaran Faransa sun ruwaito cewa an tsinci gawarta ne a gidanta da ke birnin Paris.

    Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya kira ta da "Mawaƙiyar Faransa" wadda ta rera mafi kyawun kalmomin harshen ƙasar.

    Ga waɗannan hotuna ne na wani bangare na rayuwarta.

  10. NDLEA ta kama ɗalibin da ya yi yunƙurin fita da ƙwaya zuwa Turai

    Jami'an Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Najeriya NDLEA sun kama wani ɗalibi a filin jirgin saman Abuja bisa zargin yunƙurin fita da kwayar da nauyinta ya kai kilogiram 7.2 zuwa Turai inda yake karatu.

    Dalibin mai suna Benjamin Nnamani Daberechi ya ɗaure kwayar Methamphetamine din da busashen kifi a cikin wani buhu.

    An kama ɗalibin ne a lokacin da ake binciken kayan matafiya a lokacin da yake dab da hawa jirgi.

    Yayin da jami'an hukumar ke masa tambayoyi a kafin kama shin, Daberechi ya yi ikirarin cewa shi ɗalibi ne da ke karatu a ƙasar Cyrus, to amma da suka fara bincika kayansa sai suka gano kwayar a cikin wani buhu da ya ɗaure busasshen kifi.

    Mai magana da yawun NDLEA Femi Babafemi cikin wata sanarwa da ya fitar, ya ce binciken farko ya nuna cewa ƙwayar Methamphetamine ce.

    • Abu bakwai game da yaƙin da NDLEA ke yi da shaye-shaye a Najeriya
    • NDLEA ta kama kasurgumin mai safarar kwayoyin da ake zargi da alaka da Abba Kyari
  11. Messi zai buga wasan farko a Inter Miami cikin watan Yuli

  12. An fara gudanar da taron kungiyar AU a Kenya

    Shugabannin ƙasashen Afirka na gudanar da taron tsakiyar shekara na gamayyar ƙungiyoyi ƙasashen Nahiyar.

    Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu na daga cikin shugannin da suka halarci taron a matsayinsa na shugaban kungiyar ECOWAS.

  13. Zulum ya nuna damuwa kan yadda ya ga asibitin Gwoza

    Gwamnan jihar Borno Babagana Umara Zulum, ya nuna damuwarsa kan rashin wutar lantarki da sauran yanayin da ya samu babban asibitin garin Gwoza

    Gwamnan ya bayyana ɓacin ransa a lokacin da ya kai wa asibitin ziyarar ba-zata da tsakar daren ranar Asabar.

    Cikin wata sanarwa da gwamnan ya wallafa shafinsa na Twitter, ya ce ya kwana a garin wanda shi ne shalkwatar karamar hukumar Gwoza da ke kudancin jihar.

    A ziyarar Zulum ya kewaya sassan asibitin domin duba irin kayayyaki da yadda asibitin ke aiki.

    A lokacin ziyarar gwamnan ya nuna damuwarsa kan yadda ya samu asibitin.

    Ya ce ''Abin takaici ne halin da babban asibitin garin Gwoza ke ciki, babu manyan abubuwan buƙata a asibitin kamar wutar lantarki. Hakiƙa hakan zai kawo cikas da cutarwa ga marasa lafiyar da ke kwance a asibitin, tare da durƙusar da shirinmu na inganta asibitoncin jiharmu''.

    Gwamnan ya kuma nuna ɓacin ransa kan rashin sanar da shi halin da asibitin ke ciki.

    ''Ba zan iya wanke kai na ko ƙaramar hukuma daga wannan laifi ba, dukanmu mun gaza samar da abin da ake buƙata''.

    Zulum ya kuma tabbatar wa da marasa lafiyar da ke kwance a asibitin cewa za a magance matsalolin da asibitin ke fuskanta, inda nan take ya bayar da umarnin fara gyara wuraren da suka lalace ciki har da wutar lantarkin asibitin.

    Haka kuma gwamnan ya yaba wa ma'aikatan asibitin, waɗanda duk da rashin hali mai kyau da asibitin ke ciki ya same su a bakin aikisu, inda ya alƙawarta saka mu da alkairi kan sadaukarwar da ya ce suna yi duk kuwa da tarin kalubalen da suke fuskanta.

    Gwamna Zulum ya saba kai irin wannan ziyara ta ba-zata zuwa makarantu a asibitoci a fadin jihar, a wani yunƙurin na sanin haƙiƙanin halin da suke ciki.

  14. Taɓa Kiɗi Taɓa Karatu 16/07/23

    Shirin Taɓa Kiɗi Taɓa Karatu tare da Haruna Shehu Tangaza da Aisha Sherif Bappa

  15. Majalisar Wakilan Najeriya za ta bai wa sarakunan gargajiya matsayi a tsarin mulkin ƙasar

    Kakakin Majalisar Wakilan Najeriya Hon. Tajedeen Abbas ya ce majalisar za ta yi ƙoƙari don ganin sarakunan gargajiya sun samu matsayin a tsarin mulkin ƙasar.

    Tajedeen ya ce ya zama wajibi a sama wa sarakunan gargajiyar matsayin a kundin tsarin mulkin ƙasar ganin irin rawar da suke takawa a cikin al'umma.

    Kakakin Majalisar Wakilan na wannan jawabi ne a lokacin wata ziyara da ya kai fadar Mai Martaba Sarkin Zazzau Alh. Dakta Nuhu Bamalli.

    Hon Tajedeen wanda ke da matsayin sarautar Iyan Zazzau, na wakiltar mazaɓar zariya a Majalisar Wakilan ƙasar.

    A lokacin ziyarar ya bayyana irin kima da martabar da sarautar gargajiya ke da shi, a don haka ne ya yi kira da a samar wa sarakunan gargajiya matsayi a kundin tsarin mulkin kasar.

    “Na tuna lokacin da muka saurarin ra'ayoyin jama'a kan yi wa kundi tsari mulkin gyaran fuska a shiyoyin ƙasar nan daban-dabn shekara uku da suka gabata, kun gabatar da buƙatar samar wa sarakunan gargajiya matsayi cikin kundin tsarin mulki''.

    ''To ina mai tabbatar muku cewa a yanzu kuna da damar samun haka. A matsayina na ɗa gareku kuma nake jagorantar Majalisar Wakilai, za mu duba wannan ƙuduri domin samar wa sarakunanmu matsayi cikin kundin tsarin mulkin ƙasarmu'', kamar yadda mataimaki na musamman ga kakakin majalisar Musa Krishi, ya bayyana cikin sanarwar da ya fitar.

    Daga ƙarshe ya kiran samun haɗin kan sarakun gargajiya musamman na yankin arewacin Najeriya domin tabbatar da wannan yunƙuri, tare da neman shawarar sarakunan gargajiyar don samun nasarar sauke nauyin da ke rataye a wuyansa na jagorancin majalisa.

    A nasa ɓangare sarkin Zazzau ya ce, da yawa daga cikin 'yan siyasar ƙasar, da zarar sun ci zaɓe sukan manta da sarakunan gargajiya.

    • Gamayyar ‘yan majalisar wakilai na adawa a Najeriya azarɓaɓi ne- Masana
    • Yadda masu son muƙamin shugaban majalisa ke sayen ƙuri'un sanatoci - Ndume
  16. Amsoshin Takardunku

  17. NCAA ta gargaɗi masu jiragen kan gurɓacewar man jirgi

    Hukumar Kula da sufurin Jiragen Sama ta Najeriya ta gargaɗi masu kamfanonin jiragen sama kan gurɓacewar man jirgin a tasoshin shan man jiragen.

    Gargaɗin na zuwa ne bayan da aka gano ruwa mai yawa cikin tankin man ɗaya daga cikin jiragen kamfanin Max Air, wanda ya mallaki Boeing 737 da aka dakatar da tashinsa cikin makon da ya gabata.

    Rahotonni sun ambato Darakta Janar na hukumar sufurin jiragen saman ta Najeriya Kaftin Musa Nuhu na cewa hukumar na gudanar da bincike kan wasu kamfanonin da ke samar da man jirgin, domin gano yadda man ya haɗu da ruwan.

    Ya kara da cewa ''muna bincike game da komai, mun gano cewa wannan jirgin ya sha mai a tasoshin jiragen Legas da Kano da kuma Abuja. Dan haka muna sa ran samun rahoton bincike game da wadannan tasoshin shan man, kuma duk tashar da muka samu da laifin za mu dakatar da ita har sai an magance matsalar''.

    ''Daya daga cikin manyan matakan kariya a hukumarmu shi ne tabbatar da ingancin man jirgi tare da bin matakan tsaftace shi'', in ji shi.

    Daraktan ya ƙara da cewa a baya an samu hatsarin jirage sakamakon gurɓacewar man da suke amfani da shi, wanda ke yin lahani ga injin jirgin, kuma ruwa na daga cikin manyan abubuwan da ke gurɓata man jirgi.

    Haka kuma hukumar ta yi kira ga ma'aikatanta da ke tasoshin man jiragen da su riƙa auna man tare da gwada ingancinsa kafin su bari jiragen su sha man.

    • Fasahar 5G: Abin da zai sa sabbin wayoyinku su iya kawo cikas ga jiragen sama
    • Yadda fasinja ya fitsare wata mata a jirgin sama
  18. Azerbaijan ta zargi Rasha da Armeniya da gaza cika alkawari

    Kasar Azabaijan ta zargi Rasha da Armeniya da gaza cika wajibcin da suka rataya a wuyansu karkashin yarjeniyar tsagaita bude wuta da aka cimma a 2022 da ta kawo karshen yakin da aka kwashe makonni shida ana gwabzawa a yankin Nagorno-Karabakh.

    Ma'aikatar harkokin wajen kasar a Baku ta ce Rasha ba ta yin wani abu da zai hana 'yan gudun hijirar Armeniya kai wa dakarun 'yan awaren yankın han.

    Rasha, wadda ta taimaka wajen tsagaita wutar ya kamata a ce tana da dakarun wanzar da zaman lafiya a mashigar hanyar samar da kayayyaki tsakanin Nagorno-Karabakh da Armeniya, yayin da ita kuma Armeniya dole ne ta amince da ficewa daga sassan Azarbaijan da ta mamaye kusan shekaru talatin

    Armeniya ta mika wa Azarbaijan ikon yankuna uku, biyo bayan fadan da aka shafe makonnishida ana gwabzawa, inda Azarbaijan ta samu nasarar soji a Nagorno Karabakh.

  19. Ana ci gaba da ceto mutanen da ruwa ya tafi da su a Koriya ta Kudu

    Masu aikin ceto a Koriya ta Kudu sun shafe sa'o'i ashirin da budu da suka wuce suna, neman mutanen da suka makale a cikin motoci a wani rami da ambaliyar ruwa to mamaye a tsakiyar yankin Chungcheong.

    Mutum shida ne suka mutu ciki har da wasu mutane biyar da ke cikin wata motar bas da ta nutse, yayin da aka ceto mutum tara.

    Ruwan sama kamar da bakin kwarya a cikin kwanaki hudun da suka gabata ya yi sanadiyarmutuwar mutane akalla 26.

    Tuni aka kwashe dubban mutane daga gidajensu tare da mayar da su matsugunan wucin gadi

  20. Marabanku

    Masu bin mu a wannan shafi barkan mu da hutun ƙarshen mako.

    Abdullahi Bello Diginza ke fatan sake kasancewa da ku a daidai wannan lokaci, domin ci gaba da kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

    Kuna iya tafka muhawara kan labaran da muke wallafawa a shafukanmu na sada zumunta da muhawara

    Ku biyo mu...