Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

An zaɓi Tinubu shugaban ƙungiyar Ecowas

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Abdullahi Bello Diginza and Umar Mikail

  1. Mu kwana lafiya

    Mun kawo ƙarshen rahotannin a wannan shafi.

    Kuna iya tarawa gobe da safe don samun wasu sababbi.

    Umar Mikail ne ke fatan mu kwana lafiya.

  2. Ambaliyar ruwa ta kashe mutum 14 a Indiya

    Ruwan sama kamar da bakin-ƙwarya a arewacin Indiya ya haifar da ambaliya da zabtarewar ƙasa tare da yin awon gaba da gadoji da gine-gine.

    Rahotanni sun bayyana mutuwar aƙalla mutum 14.

    Wuraren da ambaliyar ta fi yin ɓarna sun ƙunshi jihohin Himachal Pradesh da Uttarakhand da Jammu da kuma Kashmir.

    Wakilin BBC ya ce an soke tafiye-tafiyen jiragen ƙasa da dama. Delhi babban birnin ƙasar ya samu saukar ruwan da ba a yi irinsa ba cikin shekara 40.

    Wani bidiyo da ya karaɗe shafukan sada zumunta ya nuna yadda madatsun ruwa suka ɓalle tare da yin awon gaba da motoci a tsaunin Manali.

  3. An zaɓi Tinubu shugaban ƙungiyar Ecowas

    Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya zama shugaban ƙungiyar Economic Community of West African States (Ecowas) ta ƙasashen Afirka ta Yamma.

    Tinubu ya maye gurbin Shugaba Umaro Embalo na Guinea Bissau yayin taron da ƙasarsa ke karɓar baƙunci a yau Lahadi karo na 63.

    "Za mu ɗauki dimokuraɗiyya da muhimmanci. Tana da wuya amma ita ce tsarin gwamnati mafi dacewa," a cewar Tinubu bayan an zaɓe shi a matsayin shugaban ƙungiyar.

    Wannan ne taro na biyu da shugaban na Najeriya ke halarta a ƙasashen waje tun bayan da ya hau mulki a watan Mayu biyo bayan nasarar da ya yi a zaɓen watan Fabrairu.

    Baya ga alwashin jagoranci na gari da ya ci, Tinubu ya bayyana damuwa kan yadda "matsalar tsaro da ta'addanci ke mayar da yankin Afirka ta Yamma baya".

  4. Kotu ta hana 'yan adawa taron kamfe a Zimbabwe

    Wata kotu a Zimbabwe ta jaddada hukuncin hana jam'iyyar adawa shirya gangamin siyasa da zimmar fara kamfe a zaɓen da za a gudanar a wata mai zuwa.

    Tun da farko 'yan sanda sun ce ba za a bari jam'iyyar Citizens Coalition for Change ta shirya taron ba saboda akwai matsala tattare da wurin da suka zaɓa.

    Wakilin BBC ya ce 'yan sandan sun bayyana cewa babban filin da jam'iyyar ta zaɓa a garin Bindura bai dace ba - musamman saboda ba shi da banɗakuna.

    Dalilin haka ne ta hana taron kuma ita ma kotun majistire ta amince da matakin.

    Jami'iyyar CCC ta ce tun daga farkon shekarar da ta gabata, an tarwatsa ko kuma hana tarukanta fiye da 90.

  5. An gano farfesan Najeriya Dipo Fasina da ya ɓata a Turkiyya

    Cikin sa'a, hukumomin Najeriya tare da haɗin gwiwar na Turkiyya sun yi nasarar gano Farfesa Dipo Fasina, wanda ya ɓata kwana takwas da suka wuce.

    Dattijon mai shekara 76 kuma tsohon shugaban ƙungiyar malaman jami'a a Najeriya, ASUU, ya ɓata ne a birnin Istanbul yayin da yake kan hanyar zuwa ƙasar Aljeriya ranar 1 ga watan Yuli.

    Rahotanni sun ce farfesan ya ɓata ne bayan ya gaza samun hawa jirgin da zai wuce da shi Aljeriyan, inda kuma aka rasa inda ya shiga.

    "Hukumar 'Yan Najeriya Mazauna Ƙasashen Waje da haɗin gwiwar ofishin jakadancin Najeriya a Turkiyya sun yi nasarar gano inda Farfesa Fasina yake, wanda ya ɓata tsawon kwanaki a filin jirgi na Istanbul," a cewar wata sanarwa da NiDCOM ta wallafa a Twitter.

    Ana yi wa farfesan, wanda shahararre ne a Najeriya, laƙabi da Jingo.

  6. PSG ta dauki Lucas Hernandez daga Bayern Munich

  7. Ba saboda ƙin amsa wayar Tinubu muka gayyaci Abdulaziz Yari ba - DSS

    Hukumar 'yan sandan farin kaya a Najeriya ta DSS ta tabbatar da gayyatar tsohon Gwamnan Zamfara Abdulaziz Yari zuwa ofishinta.

    Sai dai hukumar ba ta faɗi dalilin da ya sa ta gayyace shi ba, tana mai musanta "jita-jitar" da ake yaɗawa cewa an tsare shi ne saboda ya ƙi amsa wayar Shugaban Ƙasa Bola Tinubu.

    A ranar Asabar ne wasu rahotanni da aka wallafa a shafukan intanet suka ce DSS ta kama tsohon gwamnan ne saboda ya ƙi sauraron shugaban ƙasar game da zaɓen shugaban Majalisar Dattawa da aka yi a watan da ya gabata.

    DSS ta bayyana labarin a matsayin "na ƙarya" kuma "abin dariya".

    "Abu ne maras amfani ko kuma na dariya....Wannan shi ake kira shashanci a rahoto. Yari ya san dalilin da ya sa aka gayyace shi," a cewar sanarwar da DSS ta wallafa a shafinta na Twitter.

    • Akpabio da Tajuddeen sun zama shugabannin majalisa ta goma a Najeriya
  8. Shugaban Amurka Biden zai isa Turai a yau Lahadi

    Shugaban Amurka Joe Biden na kan hanyar zuwa Turai gabanin taron ƙungiyar ƙawancen tsaro ta Nato bayan ƙawayen ƙasarsa da dama sun soki matakin bai wa Ukraine bam mai 'ya'ya da yake shirin yi.

    Birtaniya da Kanada na cikin ƙasashen da suka bayyana adawarsu da miƙa bam ɗin a yaƙin da Ukraine take yi da Rasha saboda haɗarin da yake da shi ga fararen hula.

    Amurka ta ce ana buƙatarsu ne saboda rumbun makaman Ukraine na ƙarewa.

    Mista Biden zai isa Birtaniya da farko a yammacin Lahadi, kafin ya ƙarasa Lithuania don halartar taron na Nato na wannan shekarar.

    Zai gana da Firaminista Rishi Sunak ranar Litinin don tattauna batutuwa da dama, ciki har da yaƙin na Ukraine. Zai kuma gana da Sarki Charles a Litinin ɗin - karon farko ke nan da za su haɗu da sarkin bayan hawansa karagar mulki.

  9. Sri Lanka ta kama masintan Indiya 15 kan zargin kamun kifi a gabar ruwan ƙasar

    Rundunar sojin ruwan Sri Lanka ta kama wasu Indiyawa 15 da ke kamun kifi bisa zarginsu da yin sun a gaɓar ruwan Sri Lanka.

    Kamfanin dillancin labarai na PTI, ya ruwaito rundunar sojin ruwan Sri Lankar na cewa ''ranar 8 ga watan Yuli jami'an da ke gadin tekun Srilanka sun kama wasu Indiyawa bisa zarginsu da yi su a gaɓar ruwan Sri Lankan'' a wani samame da suka kai.

    Cikin sanarwar da rundunar sojin ruwan ta fitar, ta ce Masintan Indiya 15 aka kama a lokacin samamen.

    Ko a watan da ya gabata ma dai sojojin ruwan Sri Lankan sun kama wasu masintan Indiya 22 'yan asalin yankin Tamil Nadu, da ke gudanar da sana'ar tasu a gabar ruwan Sri Lankar.

    Kawo yanzu Sri Lanka ta kama masintan Indiya 74 bisa zargin yin su a gaɓara ruwan ƙasar cikin wannan shekara.

  10. Amsoshin Takardunku

  11. NDLEA ta kama kilogiram 4,560 na tabar wiwi a wasu jihohin Najeriya

    Hukumar da ke Yaki da Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Najeriya NDLEA ta ce jami'anta sun kwace tabar wiwi da nauyinta ya kai kilogiram 4,560 a jihohin Legas da Adamawa da Osun.

    Cikin wata sanarwa da jami'in hulda da jama'a na hukumar Femi Babafemi ya fitar, ya ce jam'ian hukumar sun kuma kai samame wata masana'antar da ake sayar da tabar a jihar Ogun tare da kama mutu hudu da ake zargi da hannu a cinikin tabar ciki har da jami'an wata coci.

    Haka kuma sanarwar ta ci gaba da cewa jami'an NDLEA sun kama wata mace bisa zargin safarar ƙwayar fentanyl a birnin Warri, na jihar Delta.

    NDLEA ta kuma ce a ranar 5 ga watan Yuli, jami'anta sun kama wata mota ƙirar Hilux ɗauke da tabar wiwi mai yawan gaske da nauyinta ya kai kilogiram 408 a kan hanyar Ngurore zuwa Mayo Belwa a jihar Adamawa, wadda aka yi niyyar safararta zuwa garuruwan Yola da Mubi da kuma Gombe.

    Sanarwar ta kuma ce ranar 1 ga watan Yuli jami'an hukumar sun kama buhu 89 na tabar da nauyita ya kai kilogiram 3,842 a jihar Legas da ke kudu maso yammacin kasar.

  12. Mutum hudu sun jikkata a wasan hawan kaho a Sifaniya

    Dubban masu yawon bude-ido ne suka halarci bikin da ake ake gudanarwa shekara-shekara a kasar Sifaniya.

    Kungiyoyin masu kare hakkin dabbobi sun daɗe suna sukar wannan bikin, inda suke kallon bikin a matsayin cin zarafin dabobi.

  13. Hukumar 'yan sandan Najeriya ta kori jami'ai bakwai kan rashin ɗa'ar aiki

    Hukumar kula da aikin 'yan sanda ta Najeriya ta amince da korar wasu jami'anta bakwai bisa laifin amfani da aiki ta hanyar da ba ta dace ba.

    Cikin wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar Ikechukwu Ani ya fitar, ya ce hukumar ta dauki matakin ne a zamanta na 21 karkashin jagorancin Justice Clara Ogunbiyi a madadin shugaban hukumar, Solomon Arase.

    Sanarwar ta kuma ce baya ga korar jami'an bakwai an kuma ladabtar da wasu jami'an tara ta hanyar rage musu girman muƙami.

  14. Gwamnan Sokoto ya kafa kwamiti don binkicen gwamnatin Tambuwal

    Gwamnatin jihar Sokoto ta kafa wani kwamiti da zai vincike batun mallakar filaye da yadda aka sayar da ko a ka yi gwamjon kadadrorin gwamnati a zamanin mulkin tsohon gwamnan jihar Sanata Aminu waziri Tambuwal.

    Cikin wata sanarwa da sakataren yaɗa labaran gwamnan jihar Abubakar Bawa ya fitar, ya ce kwamitin mai mutane biyar ƙarƙashin jagorancin Justice M.A. Pindiga zai kuma duba asusun gwamnatin jihar domin gano adadin kuɗaɗen da aka samau sakamakon sayar da kadarorin.

    Sanarwar ta kara da cewa kwamitin zai kuma duba batun filayen da sabuwar gwamnatin ta ke zargin gwamnatin da ta shuɗen ta rabar ciki har da gidajen gwamnatin jihar da aka yi yi gwanjonsu.

    Haka kuma akwai batun motocin gwamnatin jihar da na kananan hukumomi.

    Sauran mambobin kwamitin sun haɗar da Barrister Nasiru Muhammed Binji a matsayin sakatare, sai Chief Jacob E. Ochidi, SAN, da Alhaji Usman Abubakar da kuma Barrister Lema Sambo Wali a matsayin mambobi.

    An bai wa kwamitin watanni biyu domin gabatar da rahoton sakamkon bicikensa.

  15. Taɓa Kiɗi Taɓa Karatu

    Haruna Shehu Tangaza tare da Aisha Sheriff Bappa ne suka gabatar da shirin na wannan makon.

  16. Tinubu ya ziyarci dakarun Najeriya da ke Guinea-Bissau

    Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya ziyarci dakarun sojin ƙasar da ke aikin wanzar da zaman lafiya a Guinea-Bissau gabanin fara taron shugabannin ƙungiyar ƙasashen ECOWAS karo na 63.

    Dakarun waɗanda ke aiki ƙarƙashin shirin wanzar da zaman lafiya na ƙasashen ƙungiyar ECOWAS sun yi wa shugaban faretin ban girma.

    Shugaban na tare da babban kwamadan dakarun wanzar da zaman lafiya na ƙasashen ECOWA Burgediya Janar Al-hassan Grema, da mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro Mallam Nuhu Ribadu da babban sakatare a ma'aikatar harkokin kasashen waje Ambassador Adamu Lamuwa.

    Sauran 'yan tawagar shugaban ƙasar sun haɗar da tsoffin gwamnonin jihohin Jigawa da Kebbi da Kano.

  17. Tsoffin kwamandojin sojin Ukraine sun koma gida daga Turkiyya

    Rasha ta yi Allah-wadai da mayar da wasu tsaffin kwamandojin sojin Ukraine gida daga Turkiyya.

    Fadar Kremlin ta ce Ukraine da Turkiyya sun ƙarya ƙa'idojin yarjejeniyar musayar fursunoni.

    An kama sojojin biyar ne a masana'antar sarrafa ƙarafar nan ta Azofstal, inda suka tsaya suka fuskanci Rasha.

    Shugaban Ukraine Volodmyr Zelensky ya ce a yau, rana ta 500 da fara wannan yaƙi, mun dawo wa ƙasarmu da 'mazajenta biyu basawan ƙarshe' da suka tsaya kai da fata wajen kare Azovstal da Marioupul.

    Tun farko Rasha ta nemi a rike su ne a Turkiyya har zuwa lokacin da za a kammala yaƙin, kamar yadda yake ƙunshe cikin yarjejeniyar da aka cimma da sa idon Turkiyya

  18. An gano gawar wani ɗan jarida kwana hudu bayan ɓacewarsa a Mexico

    An gano gawar wani ɗan jarida a Mexico da ya ɓace tun ranar Laraba a wani auye a jihar Nayarit da ke yammacın kasar.

    Luis Martin Sanchez, mai shekaru 59, wakilin ɗaya daga cikin manyan jaridun Mexico, ne da ake kira La Jornada.

    An tarar da gawarsa nannade a leda, sannan an samu wata wasiƙa da aka ɗaura a a ƙirjinsa.

    Tun farko matarsa ce ta bada rahoton cewa wasu da ba a san ko su wane ne ba, sun kutsa har gidansu, tare da yin awon gaba da shi.

    Mexico, na ɗaya daga cikin ƙasashen da suka fi hadari ga 'yan jarida a duniya, musamman masu ba da rahoto kan fataucin miyagun ƙwayoyi da cin hancı da rashawa

  19. 'An samu kyautatuwar alaka tsakanin Amurka da China'

    Ministar kudi ta Amurka Janet Yellen ta ce an samu kyaututuwar dangantaka tsakanin ƙasarta da China a cikin ‘yan kwanakin da suka gabata.

    Ta bayyana hakan ne da safiyar Lahadi a birnin Beijing, a karshen ziyararta ta kwana huɗu a Chinar.

    A jiya Asabar, Yellen ta shafe sa’o’i da dama tana tattaunawa da sabon babban mataimakin firimiyan ƙasar a kan harkokin kuɗi He Li-Feng.

    Idan aka yi la’akari da yadda danganataka take tsakanin ƙasashen Amurka da China to ko ba komai za a iya cewa alla san barka game da waɗannan kalamai.

    A don haka ne ma ganin irin yadda alakar take tsakanin ƙasashen biyu a baya, sakatariyar ta tunatar da cewa ‘’ba wata ziyara daya da za ta iya magance kalubalen da ke tsakaninsu, dare daya’’

    To amma ta ce wannan ziyara za ta taimaka wajen ginawa da samar da wata managarciyar hanyar sadarwa da sabbin masu rike da akalar harkokin tattalin arzikin China.

    A jiya Asabar ne Misis Yellen ta yi ganawarta ta farko keke da keke da mataimakin Firimiya He Lifeng, zaman da aka ce ya dauke su sa’a shida.

  20. Sallama

    Masu bin mu a wannan shafi na Kai-tseye barkanmu da hutun ƙarshen mako.

    Abdullahi Bello Diginza ke fatan kasancewa da ku a daidai wannan lokacin domin kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

    Kuna iya lekawa shafukanmu na sada zumunta domin tafka muhawara kan labaran da muke wallafawa.