Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Shugaba Tinubu ya taya Musulmai Barka da Sallah

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Ibrahim Yusuf Mohammed and Umar Mikail

  1. 'Yan Najeriya miliyan huɗu ne mai yiwuwa suka ƙara shiga talauci bana - Bankin Duniya

    Ƙarin 'yan Najeriya kimanin miliyan hudu ne suka sake auka wa ƙangin talauci a cikin wata biyar na farkon wannan shekara saboda tsadar rayuwa.

    Babban masanin tattalin arziƙin Bankin Duniya a Najeriya, Alex Sienaert ne ya bayyana haka lokacin da yake jawabi a Abuja yayin wani nazari kan tattalin arziƙin Najeriya a cikin rabin shekara.

    Katafariyar cibiyar hada-hadar kuɗin ta yaba da sauye-sauyen da Najeriya ke yi ciki har da cire tallafin man fetur da dunƙule kasuwannin canji da shugaba Bola Tinubu ya yi a baya-bayan nan, wanda ta ce zai iya alkintawa ƙasar kuɗi kimanin naira tiriliyan 3.9 ($5bn) a bana kaɗai.

    Babban Bankin ya ce sauye-sauyen tattalin arziƙin na da muhimmanci wajen sake farfado da tattalin arzikin Najeriya wanda tuni ya galabaita, ko da yake matakan na iya gigita al'amura cikin gaggawa ta hanyar haddasa ƙarin hauhawar farashi da tsadar rayuwa.

    A cewar Hukumar ƙididdiga ta ƙasar, sama da ‘yan Najeriya miliyan 130 ne wato fiye da rabin al’ummar ƙasar ke fama da talauci a halin yanzu.

    Babban daraktan Bankin Duniya a Najeriya, Dr Subham Chadhuri, ya ba da shawarar daukar matakan da za su rage tasirin sauye-sauyen tattalin arziki ga jama'a, ya ƙara da cewa ribar da za a iya samu sauye-sauyen ana sa ran za ta kai sama da naira tiriliyan 21 ($27bn) daga 2023 zuwa 2025.

    Najeriya, a matsayinta na ƙasa mafi girman tattalin arziki a Afirka a halin yanzu tana fama da hauhawar farashi na sama da kashi 22% da tsadar rayuwa da raguwar kuɗaɗen shiga ga gwamnati baya ga ƙaruwar rashin aikin yi da taɓarɓarewar tsaro a yawancin sassan ƙasar.

  2. 'Iyalai na buƙatar dalar Zimbabwe miliyan ɗaya don sayen abinci a wata'

    Tsohon maƙiyin Zimbabwe - hauhawar farashi mai tsanani ya sake komawa ƙasar, bayan alƙaluman tsadar haja na shekara-shekara ya ninka zuwa kusan kashi 176% a watan Yuni.

    Kungiyoyin kare haƙkin masu saye sun ce matsakaicin iyali, na bukatar kusan dalar Zimbabwe miliyan ɗaya don sayen abinci kaɗai a kowanne wata, yayin da farashin ke daɗa tashi kusan kullum.

    Yawancin mutane suna kokawa da sayen kayan abinci, sannan wasu suna fashin cin abinci a cewar ƙungiyar Action Aid.

    Gwamnatin Zimbabwe ta ɗora alhakin karyewar darajar dalar Zimbabwe a kan 'yan canji masu sayen kuɗi don cin riba a gaba - kuɗin ƙasar dai ya yi asarar sama da kashi 90% na darajarsa tun a watan Janairu.

    Dalar Amurka ita ma takadar kuɗi ce a Zimbabwe, kuma yawancin mutane sun fi son cinikayya da ita, abin da ya kuɗin ƙasar ya yi rasa darajarsa.

    A baya-bayan nan, gwamnatin Zimbabwe ta umurci hukumomi su sanya biyan wadansu nau'o'in haraje-haraje da kuɗin ƙasar da fatan za a samu ƙarin masu neman dalar Zimbabwe wadda ke darajarta ta yi matuƙar shan wahala.

  3. An kai wasu 'yan Kenya kotu a kan safarar tururuwa

    An gurfanar da wasu ‘yan ƙasar Kenya uku a gaban kotu bisa tuhumar yunƙurin safarar tururuwa zuwa ƙasashen China da Faransa.

    Ana zargin mutanen uku, ciki har da wani mai mata da matar tasa ​​da kuma wani ma’aikacin gidan waya da yunƙurin fasa-ƙwauri na wani nau’in tururuwa mai suna Messor Cephalotes zuwa ƙasashen waje.

    Hukumomi sun ce mutanen na ƙoƙarin aikata haka ne ba tare da sun nemi izini daga hukumar kula da namun daji ta Kenya ba.

    Sai dai sun musanta zargin, amma an ba da belinsu.

    Ba a dai bayyana dalilin da ya sa ake sayar da tururuwa da aka ce kuɗinsa ya kai shilling 300,000 ($2,135) ba.

    Wani mai gabatar da kara ya bukaci kotun ta gaggauta shari’ar domin rayuwar tururuwar da aka gabatar a kotu na cikin hatsari.

  4. Malamar da aka kora a kan ƙin zuwa aiki tsawon shekara 20, ta ce tana da hanzari

    Wata malamar makaranta da aka kora a kan rashin zuwa aiki tsawon shekara 20 a birnin Venice na ƙasar Italiya ta ci alwashin bayar da nata bahasi kan abin da ya faru.

    An kori Cinzia Paolina De Lio daga aiki a 2017, bayan nan sai ta koma tsawon wata huɗu, sai ta shigar da ƙara.

    Kotun kolin Italiya ta tabbatar da korar da aka yi mata, bayan an gwabza shari'a, tana mai cewa ƙauracewa aikin ya nuna tsananin rashin ƙwarewa na dindindin.

    Misis De Lio ta yi Allah-wadai da hukuncin tare da lasar takobin "sake fayyace bayani kan gaskiyar abin da ya faru".

    Malamar makarantar sakandiren, wadda ta ƙware a fannin tarihi da falsafa, ta ce tana da takardu da za su tabbatar da bahasinta kamar yarda ta shaida wa jaridar Repubblica.

    "Zan sake fayyace bayani a kan gaskiyar abin da ya faru." in ji ta, ta ƙara da cewa, "Ba na amsa tambayoyin 'yan jarida da ba za su yi adalci a kan gaskiyar labarina ba."

    A shekarar 2018 ne aka mayar da Misis De Lio bakin aiki bayan wani alƙali a Venice ya yanke hukunci, amma sai ma'aikatar ilimi ta ɗaukaka ƙara, inda kotun ƙolin ƙasar ta soke hukuncin ƙaramar kotun Venice a makon jiya.

    Ma’aikatar ta ce malamar ta daina shiga aji tsawon shekara 20 cikin shekara 24 na aikin da ta yi. A cikin shekara 10 na farko ba ta zuwa koyarwa gaba ɗaya, sai dai an danganta rashin zuwanta aiki a sauran shekara 14 da rashin lafiya, ko matsalolin iyali.

    Kotun ta saurari bayanin cewa a cikin wata huɗu na 2015 lokacin da ta yi koyarwa a Chioggia, kusa da Venice, ɗalibanta sun koka da rashin shiryawa abin da take yi, da rashin shiga aji da kawo littattafan karatu."

    Binciken da aka yi mata ya nuna cewa "ba ta shiryawa kafin ta shiga aji koyarwa" kuma "ba ta da mai da hankali", sannan ɗalibai ba sa son shiga ajinta saboda kullum tana riƙe da waya, abin da kan ɗauke mata hankali.

  5. Shugaba Tinubu ya yi wa Musulman Najeriya Barka da Sallah

    Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya yi kira ga al'ummar Musulmi su yi koyi da dabi'un Annabi Ibrahim, musamman cikakken miƙa wuya ga Allah da juriya da haƙuri da rashin son kai da soyayya da kuma tausayawa.

    Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da shugaban ya fitar a wani ɓangare na murnar bikin Babbar Sallah bana.

    Yayin da yake amincewa da ƙalubalen da Najeriya ke fuskanta, Shugaba Tinubu ya bai wa 'yan Najeriya tabbacin samar da hanyoyin magance matsalolin rayuwa.

    Sanarwar ta ce "Dole ne mu gode wa Allah Madaukakin Sarki da ya ba mu damar halartar wata Sallar Idi".

    "Yayin da muka shagala da farin ciki na wannan lokaci muna murna, kamata ya yi kuma mu dage mu tuna da ƴan baya"

    "Ɗaya daga cikin ayyuka mafi girma da aka rubuta a tarihi na misali mai kyau akwai sadaukarwar da Annabi Ibrahim ya yi da ɗansa Ismail ga Allah Mahalicci."

    "Hanya mafi kyawu da za mu iya fito da wannan misali, ita ce yin koyi da wannan darasi a wajen al'ummar ƙasarmu da kuma ayyukanmu."

    "A halin yanzu, ƙasarmu na fama da ƙkalubale iri daban-daban musamman ma taɓarɓarewar tattalin arziƙinmu da kuma taɓarɓarewar tsaro."

    "Mun fara neman hanyar magance matsalolin ta hanyar shawarwarin da muka yanke kawo yanzu, don gyara tattalin arziƙinmu da kuma kawar da duk wani cikas ga bunƙasar Najeriya."

    Shugaban Najeriya ya kuma yi wa al'ummar ƙasar fatan Barka da Sallah.

    • Na san ƙuncin da janye tallafin mai ya jefa ku - Tinubu
    • Muna tattaunawa da Tinubu don shiga gwamnatinsa - Kwankwaso
  6. Shugaba Tinubu ya koma Najeriya bayan ziyarar kwana bakwai

    Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan wata ziyara zuwa ƙasashen Faransa da Ingila ta tsawon mako ɗaya.

    Wata sanarwa da mai bai wa shugaban shawara na musamman kan harkokin sadarwa, Dele Adeleke ya fitar ta ce Bola Tinubu ya samu kyakkyawar tarba daga dandazon 'yan Najeriyan da suka yi masa maraba a birnin Lagos.

    Ta ce Tinubu ya kai ziyara Paris ne inda ya halarci wani taron ƙoli a kan "Sabuwar Yarjejeniyar Duniya kan Harkokin Kuɗi", kafin daga bisani ya kai taƙaitacciyar ziyara ta ƙashin kai zuwa Birnin London.

    Saukarsa a filin jirgin sama na Murtala Mohammed, ita ce ziyararsa ta farko a Lagos tun bayan hawansa kan mulkin Najeriya. Ta ce Shugaba Tinubu zai yi Idin Babbar Sallah ne ranar Laraba a Filin Idi na Obalende da ke Dodan Barracks.

  7. Tsohon shugaban Najeriya ya yi wa Musulmai Barka da Sallah

    Yayin da al’ummar Musulmi ke shirye-shiryen bukukuwan Babbar Sallah a bana, tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari ya yi kira ga yan Najeriya su bai wa gwamnatin Bola Ahmed Tinubu cikakken goyon baya don samun nasara a mulkinsa.

    Ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da Garba Shehu, mai magana da yawunsa ya fitar don taya al'ummar Musulman Najeriya murnar bikin Babbar Sallah.

    Sanarwar ta ce "Shugabancin ƙasa kamar Najeriya na cikin abubuwa mafi wahala a rayuwa, ya kuma bukaci 'yan Najeriya su bai wa gwamnatin Tinubu cikakken goyon baya."

    "shugabanci, aiki ne mai cike da ƙalubale da ke buƙatar sadaukarwa da goyon bayan 'yan kasa," in ji Buhari.

    Tsohon shugaban ya kuma yi wa Musulmai fatan samun nasarar aikin hajjin bana.

    • Sallar Idin Buhari ta ƙarshe a kan mulki
    • Abin da ƴan Najeriya ke cewa kan ƙarin albashin ƴan siyasa
  8. IMF ya amince wa Senegal rancen kusan dala biliyan biyu

    Asusun ba da lamuni na duniya (IMF) ya amince da bai wa Senegal lamuni na dala biliyan daya da miliyan dari takwas don tallafawa farfado da tattalin arzikin ƙasar tare da kare ta daga abubuwa da za su iya tasowa nan gaba.

    A wata sanarwa bayan wani taron kwamitin zartarwa IMF, asusun ya ce tashin farko ƙasar ta Afirka ta Yamma za ta fara karɓar kusan dala miliyan 216.

    Rancen na shekaru uku zai kuma tallafawa ƙoƙarin Senegal na tunkarar illolin sauyin yanayi.

    Asusun ba da lamunin ya ce yaƙin Rasha da Ukraine ya kawo cikas ga farfadowar ƙasar bayan cutar Korona ta illata kasashe abin da ya ƙara yawan karɓar rance da kuma rage kuɗaɗen ajiyar ƙasashe.

  9. Saudiyya za ta mayar da alhazan Najeriya 10,000 sabbin tantuna

    Hukumomi a Saudiyya sun kammala shirin mayar da alhazan Najeriya 10,000 zuwa wani yanki a Mina saboda ƙorafi a kan rashin isassun tantunan maniyyatan.

    A cikin wata sanarwa da ta fitar ranar Talata, Hukumar Alhazai ta Najeriya (NAHCON) ta bayyana cewa, an gudanar da sabon tsarin ne bayan tattaunawa da jami’an Muttawwif, waɗanda ke da alhakin kula da jin dadin alhazan Afirka da ba Larabawa ba a masarautar.

    Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa alhazan Najeriya da ke gudanar da aikin Hajjin bana sun rasa abin yi a Mina, wurin da mahajjata ke zama kafin su wuce Dutsen Arafat.

    Ta ambato jami'in NAHCON, Mousa Ubandawaki, na cewa matakin ya zo ne bayan ƙorafin da aka kai wa Muttawwif wanda ya haɗa da rashin isasshen abinci da kuma jinkirin ciyar da alhazai.

    “Muttawwif yayin da yake ba da haƙuri kan abin da ya faru ga mahajjatan Najeriya, ya yi alkawarin mayar da alhazan zuwa filin wasa na Turkiyya wanda zai iya daukar kimanin mahajjata 10,000 cikin sauki.”

    Ubandawaki ya ce Shugaban Kamfanin Muttawif, Ahmad Sindhi, ya ba da haƙuri kan abin da mahajjatan Najeriya suka fuskanta.

  10. Za a janye wa fitattun mutane 'yan sanda masu ba da kariya a Najeriya

    Hukumomin ‘yan sandan Najeriya sun sanar da shirin janye wasu jami’an ‘yan sandan da ke ba da kariya da kuma rakiya ga manyan mutane a kasar, da nufin sake tura su aiki a kan tsaron kasa.

    Sabon Sufeto-Janar ɗin ‘Yan Sandan Najeriya, Olukayode Egbetokun, ya ce, “Duk da cewa kare martabar manyan mutane ya kasance mafi muhimmanci, amma ya zama wajibi mu daidaita abubuwan da muka sa a gaba don magance matsalar tsaro da ke addabar al’ummar ƙasar baki ɗaya.

    Wadannan jami’an za a maye gurbinsu ne kawai “inda ya cancanta”, a cewar jaridar Premium Times.

    A farkon watan nan ne dai shugaba Bola Tinubu ya yi sauye-sauye a jami'an tsaron Najeriya inda ya nada sabbin kwamandojin jami'an tsaro da suka hada na rundunar sojin ƙasar baki ɗaya.

  11. Lukashenko ya ce Prigozhin ya isa Belarus - kamfanin dillancin labaran ƙasar

    Kamfanin dillancin labaran Belarus wato Belta ya ruwaito Shugaba Alexander Lukashenko na cewa mutumin da ya kafa kamfanin Wagner, Yevgeny Prigozhin ya isa Belarus.

    Kamfanin ya ambato jagoran na Belarus na cewa "an ba da tabbacin tsaro", kamar yadda shugaban Rasha Vladmir Putin ya alƙawarta.

    “Na ga Prigozhin ya taho a cikin jirgin sama - tabbas ya isa Belarus a yau,” kamar yadda aka ambato shi yana cewa.

    Ya ƙara da cewa zai zauna a cikin ƙasar ne kuma kamfaninsa na Wagner shi zai ɗauki nauyinsa.

    A ranar Asabar, bayan janye boren sojojin da ya yi a Rasha, Prigozhin ya amince da wata yarjejeniya wadda za ta ba shi damar komawa zuwa Belarus.

  12. Hotunan Musulmai yayin tsayuwar Arfa

    Ɗumbin al'ummar Musulmi ne daga ƙasashe daban-daban na duniya ke tsayuwar Arfa da tsakar ranar yau. Tsayuwar Arfa, wani muhimmin ɓangare ne na ibadar Aikin Hajji wadda duk ta wajaba a kan Musulmin da ke da iko aƙalla sau ɗaya a rayuwa.

  13. Mayaƙan Wagner za su miƙa wa gwamnatin Rasha makamansu

    Ma'aikatar tsaron Rasha ta ce ana shirye-shiryen yadda dakarun Wagner za su mayar da makaman da ke hannunsu.

    Wannan ya biyo bayan tabbacin da Vladimir Putin ya bayar cewa mayaƙan Wagner, waɗanda ya ce galibinsu 'yan kishin kasa ne wadanda aka yaudare su zuwa aikata laifuka, za su iya zaɓen shiga aikin soja na ƙasar, ko su koma gidajensu, ko kuma su yi hijira zuwa Belarus.

    Haka kuma, an sanar da cewa hukumar tsaro ta FSB ta yi watsi da duk wasu tuhume-tuhume da ake yi wa wadanda ke da hannu a tarzomar da ta taso, wadanda ke fuskantar tuhuma kan tayar da zaune tsaye.

  14. Ƴan adawar Saliyo sun fara kururuwa kan sakamakon zaɓe

    Dan takarar jam'iyyar adawa a zaɓen shugaban ƙasar Saliyo ya bayyana sakamakon da aka fara fitarwa na zaɓen a matsayin "fashi da rana tsaka", yana mai zargin cewa ba a bai wa wakilansa damar lura da yadda ake ƙidayar kuri'un ba.

    Yayin da aka kirga mafi yawan ƙuri’un da aka kaɗa, bisa ga dukkan alamu akwai tazara mai nisa tsakaniin shugaba mai ci Julius Maada Bio da babban abokin hamayyarsa Samura Kamara.

    Wakilin BBC a Freetown, babban birnin kasar, ya ce zai iya yiwuwa a danganta nasarar da Mr Bio ya samu a kan wasu tsare-tsare na ƙawancen siyasa da ya yi a yayin da yake gudanar da yakin neman zabe, ciki har da samun galaba a yankunan 'yan adawa.

    Masu sanya ido kan zabe na Tarayyar Turai sun soki hukumar zaben kasar Saliyo da rashin gaskiya, sannan kuma sun ce an samu tashe-tashen hankula a wasu yankuna a lokacin kaɗa ƙuri'a.

    Hukumar zabe a Saliyo ta ce tana sa ran nan ba da jimawa ba za a fitar da sakamakon karshe na zaben shugaban kasar da aka gudanar a ranar Lahadin da ta gabata .

  15. Abubuwan da suka kamata ku sani kan aikin Hajji

  16. 'Tsadar rayuwa ta sa kuɗina ba za su kai ni Hajji ba a yanzu'

  17. Shugaba Tinubu zai koma Najeriya yau

    Ana sa ran cewa a yau Talata Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu zai koma Najeriya.

    Wata majiya a fadar shugaban kasa ta bayyana cewa shugaba Tinubu wanda ya bar kasar a ranar 20 ga watan Yuni zuwa birnin Paris na da niyyan komawa Najeriya don yin bukin babbar Sallah a gida.

    An shirya cewa Shugaban kasar, zai koma Abuja daga Paris a ranar Asabar da ta gabata, amma daga nan sai ya wuce birnin Landan don gudanar ziyara ta kashin kansa.

  18. An bankaɗo muryar Trump inda yake magana kan wasu takardun sirrin Amurka

    Kafofin yada labaran Amurka sun samu wani faifan murya, wanda a ciki aka ji Donald Trump ke cewa ya amince da ajiye wata takardar sirrin gwamnatin bayan ya bar fadar White House.

    A cikin faifan muryar, tsohon shugaban yana bincika wasu takardu yana cewa: "Wannan ba karamin sirri ba ne."

    CNN ce ta fara samo muryar, amma kafar yaɗa labarai ta CBS ta Amurka, wadda ke haɗin gwiwa da BBC ma ta samu faifan.

    Mista Trump dai ya ƙi amsa laifin da ake tuhumarsa da shi na karkatar da wasu muhimman takardu.

    CNN ce ta farko da ta fara bayyana faifan mai tsawon kusan minti biyu, wanda ta ce ya fito ne daga wani taron da aka gudanar a watan Yulin 2021 a wurin buga wasan golf na Mista Trump da ke yankin Bedminster, a jhar New Jersey tsakaninsa da mutane da yawa da ke aiki kan rubutaccen tarihin tsohon shugaban ma'aikatansa, Mark Meadows.

    Ana jin Mista Trump yana cewa "wadannan ne takardun" kuma yana magana kan wata takarda da ya kira "ta sirri ce sosai".

    "Sojoji ne suka yi wannan kuma suka ba ni," in ji shi. "Kun gani a matsayina na shugaban kasa da zan iya bayyana shi. Yanzu ba zan iya ba, amma wannan har yanzu sirri ne."

    Da alama faifan iri ɗaya ne da wanda masu gabatar da ƙara na tarayya suka ambata a cikin tuhumar da suke yi wa Mista Trump.

    Ba a tabbatar ko masu bincike sun taɓa gano takaddun da mista Trump ke ambata a lokacin ba.

  19. Rundunar RSF ta Sudan ta sanar da tsagaita wuta domin bikin Idi

    A yau ne yarjejeniyar tsagaita wuta da shugaban rundunar dakarun RSF ya sanar za ta fara aiki domin bukukuwan babbar sallar Idi da za a fara ranar Laraba.

    An bayar da sanarwar dakatar da rikicin ne a wani sakon murya da aka watsa a gidan talabijin na Al Arabiya wanda shugaban kungiyar RSF, Muhammad Hamdan Dagalo, ya gabatar.

    Ya ce matakin zai yi aiki ne a ranakun Talata da Laraba.

    Janar Hemedti ya kuma yi Allah-wadai da cin zarafi da ake yi wa fararen hula - ciki har da wadanda sojojinsa ke yi.

    Ana zargin kungiyar ta RSF da aikata laifukan cin zarafin mutane a Darfur.

  20. Muhimman abubuwa da suka kamata ku yi a ranar Arfa