Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Ma'aikatan lafiya a Najeriya sun janye yajin aiki

Wannan shafi ne da ke kawo abubuwan da ke wakana a Najeriya da makwabtanta da kuma sauran sassan duniya kai tsaye

Rahoto kai-tsaye

Abdullahi Bello Diginza

  1. Tattalin arziƙin manyan ƙasashen Afirka na tafiyar hawainiya mafi muni a tarihi

    Wani sabon rahoto da hukumar kula da harkokin tattalin arziki ta McKinsey ta fitar ya nuna cewa, manyan kasashen Afirka da suka fi girman tattalin arziki da suka hada da Afirka ta Kudu da Masar da Najeriya da kuma Aljeriya suna samun ci gaba mafi kankanta a nahiyar.

    "Habakar da aka samu a baya ta samo asali ne ta hanyar albarkatu." A cewar Acha Leke wani babban jami'i a McKinsey.

    Rahoton ya nuna cewa, yadda wadannan kasashe ke gudanar da tattalin arzikinsu, ya jawo koma-baya ga ci gaban nahiyar baki daya.

    "Idan aka yi la'akari da ci gaban da aka samu cikin shekaru 10, an samu karuwa da kashi 3.3% wanda ba shi da armashi idan aka dubi karuwar yawan jama'a. Amma akwai manyan bambance-bambance a cikin Afirka."

    Rahoton ya kara da cewa kasashen da ke kan gaba wajen bunkasar tattalin arzikin nahiyar a ko da yaushe, su ne kasashen gabashin Afirka musamman kasar Rwanda. A baya-bayan nan, wasu kasashe a yammacin Afirka, kamar Ivory Coast, sun sami karuwar ci gaba.

    Sakamakon haka, Mista Leke ya ce nan gaba, ci gaban zai ta'allaka ne kan karfafa kasuwanci tsakanin yankuna, da taimaka wa harkokin kasuwancin Afirka wajen habaka, da kuma inganta ma'aikata.

  2. China za ta sanya na'urori a ɗakunan jarrabawa domin hana yin satar amsa

    Kasar China na ƙoƙarin samar da wani tsarin sanya ido domin hana magudi a jarrabawar shiga jami'a.

    Biranen kasar da dama na shirin kafa tsare-tsaren sa ido domin hana magudi, yayin da dalibai kusan miliyan goma sha uku ke shirin yin jarrabawar shiga jami'a ta bana.

    Za a samar da na’urorin tantance fuska domin hana sojojin haya da ke karbar kudi domin su zauna wa wasu jarabawar na kwanaki uku.

    Har ila yau, za a haramta wa dalibai sanya kaya masu karaffa da suka hada da bel da agogo, don rage yiwuwar wasu daliban su yi amfani da kyamarori da na’urorin saurare a zauren jarrabawan.

    A shekarar 2020, an yanke wa wani dalibi hukuncin daurin shekaru uku a gidan yari bayan ya yi amfani da na'urar sadarwa ta sirri don samun taimako wajen amsa tambayoyin jarrabawa.

  3. Kotu ta dakatar da ƙungiyoyin ƙwadago daga shiga yajin aiki a Najeriya

  4. Ƴan sanda sun kama 'masu satar kaya' a inda ake rusau a Kano

    Rundunar 'yan sanda a jihar Kano sun damke wasu matasa bisa zargin aikata laifin satar kayan 'yan kasuwa wadanda rushe-rushen da ake yi a wasu sassan birnin Kano ya shafa.

    Wata sanarwa da rundunar ta wallafa a shafinta na twitter ta ce 'yan sandan sun yi nasarar kama wadanda ake zargin ne sakamakon rahotonni da suka samu cewa na cewa daruruwan mutane sun taru suna shirin wawashe kadarori da kayan gine-gine a Triumph Plaza da ke karamar hukumar Fagge.

    Sanarwar ta ci gaba da cewa ana kan gudanar da bincike kan wadanda a ke zargin.

  5. Ma'aikatan lafiya a Najeriya sun janye yajin aiki

    Ma'aikatan lafiya na Najeriya sun janye yajin aikinsu na kwana 12 bayan wata ganawa da suka yi da shugaban ƙasar, Bola Ahmed Tinubu a yau Litinin.

    Ƙungiyar ma'aikatan ta JOHESU, wadda ta yi ganawar da shugaba Tinubu, ta ce ta yanke shawarar janye yajin aikin ne domin bai wa gwamnati wa'adin mako uku domin shawo kan matsalolin da suke fuskanta.

    Mataimakin shugaban ƙungiyar na ƙasa, Dr Obinna Ogbonna ya ce "an samu ci gaba" a tattaunawar da suka yi da shugaban ƙasa.

    "Amincewa tamkar abu ne mai haɗari, amma tunda a yanzu muna magana ne da sabon shugaban ƙasa, wanda da kansa ya roƙi mu ba shi lokaci, ya kamata mu ba shi.

    "Bayan kwanakin 21 za mu duba inda ake sannan mu ɗauki mataki na gaba." in ji Dr Obinna a tattaunawarsa da BBC.

    Ma'aikatan lafiyar dai na nema ne a yi watsi da tsarin biyan albashi na bai-ɗaya, da biyansu alawus-alawus ɗin aiki, da sake duba shekarun yin ritaya da dai sauran su.

  6. Hotunan ziyarar da shugaba Tinubu ya kai a ofishin mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan tsaro

    A ranar Litinin ne shugaba Bola Ahmed Tinubu ya kai ziyara a ofishin mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan tsaro, da kuma cibiyar yaƙi da ta'addanci da ke Abuja.

    Tinubu ya wallafa hotunan ziyarar tasa, inda ya karɓi lambar karramawa daga mai bai wa shugaban shawara kan tsaro, Babagana Monguno.

    Tsohon shugaban ƙasar, Muhammadu Buhari ne ya ƙaddamar da sabon ginin gabanin ƙarewar wa'adin mulkinsa.

    A lokacin ziyarar. Tinubu ya ce ya gamsu da sadaukar da kai na ƙwararrun ma'aikatan gwamnatin tarayya.

  7. Tinubu ya roƙi ma'aikatan lafiya su janye yajin aiki

    Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya roƙi ma’aikatan lafiya na ƙasar ƙarƙashin ƙungiyar JOHESU da su janye yajin aikin da suke yi.

    Shugaban ya yi wannan roƙo ne a ranar Litinin lokacin da ya gana da shugabannin ƙungiyar ta gamayyar ma’aikatan lafiya na ƙasa.

    A lokacin ganawar, Tinubu ya ɗauki alƙawarin cewa zai magance matsalolin da ke addabar ɓangaren na lafiya.

    Hakan dai na zuwa ne a daidai lokacin da ƙungiyoyin ƙwadago a Najeriya ke shirye-shiryen tsunduma yajin aiki a ranar Laraba mai zuwa sanadiyyar tsadar man fetur.

    A makon da ya gabata ne mambobin ƙungiyar ma’aikatan lafiyar suka fara yajin aiki domin neman gwamnati ta biya musu wasu buƙatu da suka gabatar.

    A lokacin da ya yi jawabi sa’ilin ziyarar tasu ga sabon shugaban ƙasa, shugaban riƙon ƙwarya na ƙungiyar, Dr Obinna Ogbonna ya buƙaci shugaban ƙasar da ya tabbatar da an zuba jari sosai a ɓangaren na lafiya a Najeriya.

  8. Za mu duba buƙatun ƙungiyar ƙwadago - Tinubu

    Gwamnatin Najeriya ta ce za ta yi nazari kan bukatun kungiyar kwadago ta TUC a kokarin dakile yajin aikin da kungiyoyin kwadago ke barazanar shiga a fadin kasar a ranar Laraba, sakamakon cire tallafin man fetur.

    Daya daga cikin mahimman bukatun shi ne karin mafi karancin albashi.

    Da yake zantawa da manema labarai bayan wani taro da wakilan kungiyar, mai magana da yawun gwamnatin Dele Alake, ya ce tattaunawar ta yi tasiri kuma suna samun ci gaba. Amma kungiyar kwadago ta Najeriya, NLC ba ta cikin tattaunawar.

    Mista Alake ya ce "da yawa daga cikin bukatun ba wasu abubuwan da za a iya yi ba ne" amma dole ne a yi nazari a kansu tukuna.

    Mataki na gaba shi ne tawagarsa ta gabatar da bukatun kungiyar ta TUC ga Shugaba Bola Tinubu kuma daya daga cikin bukatun shi ne daga wa ma'aikata kafa kan haraji.

    A ranar Larabar da ta gabata, masu sayar da man fetur sun kara farashin man fetur zuwa akalla dala 1 ga kowace lita a fadin kasar - karin da ya kai kusan kashi 200%. Hakan ya shafi farashin sufuri da kayan abinci da sauran kayayyaki, yayin da mafi karancin albashi yake kan kimanin dalar Amurka 65.

    Dele Alake ya ce gwamnati ta dauki bukatar kara mafi karancin albashi da muhimmanci. Ya ce babu mamaki shugaban kasa zai kaddamar da wani kwamiti da za ta yi nazarin yiwuwar yin karin albashi.

    Za a ci gaba da taron a ranar Talata domin bangarorin biyu su duba "alfanu da kuma yiwuwar abubuwan da aka gabatar wa gwamnati."

  9. Masu kallon ƙwallon ƙafa 22 sun mutu a hatsarin mota a Malawi

    Akalla ‘yan wasan kwallon kafa 22 da magoya bayan kungiyarsu sun mutu a gundumar Karonga da ke arewacin Malawi, bayan da motar da suke ciki ta kife a lokacin da suke dawowa daga wani wasa.

    Sanarwar da ‘yan sanda suka fitar ta ce motar da ke dauke da mutane kusan 80 ta juye a daren ranar Asabar bayan da direban ya kasa nade kan motar yadda ya kamata, sai ya doki wani shingen da ke gefen hagu na titin.

    An kai wasu fasinjoji da dama asibiti - kuma akalla 12 daga cikinsu sun sami munanan raunuka.

    Shugaban kasar Malawi Lazarus Chakwera ya aike da sakon ta'aziyya ga iyalan wadanda suka mutu tare da yin umurni ga sashen kula da bala'o'i da su bayar da gudunmuwa cikin gaggawa ga dukkan iyalan wadanda abin ya shafa.

  10. Liverpool ta kusan ɗaukar Mac Allister daga Brighton

  11. Ɗan marigayi Muammar Gaddafi na yajin cin abinci

    Daya daga cikin 'ya'yan marigayi tsohon shugaban ƙasar Libya Muammar Gaddafi, na yajin cin abinci a wani mataki na nuna adawa da ci gaba da tsare shi da ake yi a gidan yarin Lebanon, kamar yadda lauyansa Paul Romanos ya bayyana.

    An dai shafe fiye da shekara takwas ana da tsare Hannibal Gaddafi a gidan yarin Lebanon, bayan da 'yan tayar da ƙayar bayan Lebanon suka yi garkuwa da shi daga Siriya, inda yake zaman gudun hijira bayan rusa gwamnatin mahaifinsa.

    Daga nan ne kuma hukumomin Lebanoon suka ƙwace shi, inda suka ci gaba da tsare shi a gidan yarin birnin Beirut ba tare da gurfanar da shi a gaban kotu ba, kamar yadda lauyan nasa ya bayyana.

  12. Zlatan Ibrahimovic ya yi ritaya daga taka leda

  13. Gwamnatin Kwara ta rage kwanakin aikin gwamnati zuwa wuni uku a mako

    Gwamnatin jihar Kwara a Najeriya ta amince da ɗaukar matakin wucin-gadi na rage adadin kwanakin aikin gwamnati a jihar domin rage wa ma'aikata raɗaɗin da janye tallafin man fetur zai haifar.

    Wani saƙo da sakataren yaɗa labaran gwamnan jihar Murtala Atoyebi, ya fitar kuma aka wallafa a shafin gwamnatin jihar na Facebook, ya ambato shugabar ma'aikata a jihar, Mrs Susan Modupe Oluwole na bayyana matakin,

    Mrs Oluwole ta ce gwamnan jihar Abdulrahman Abdulrazaq ne ya bayar da umarnin rage kwanakin aikin gwamnatin na wucin-gadi daga kwana biyar zuwa uku a kowane mako.

    Mrs Oluwole ta umarci shugabannin ma'aikatu da hukumomin gwamnati da ke faɗin jihar su gaggauta tsara wa ma'aikatansu kwanakin da ya kamata su je aiki.

    Shugabar ma'aikatan jihar ta kuma gargaɗi ma'aikatan kada su tozarta wannan karamci da gwamnan jihar ya yi musu, tana cewa za a tsananta lura da kai ziyara ma'aikatu domin tabbatar da cewa ana bin dokar yadda ya kamata.

    Sabon shugaban ƙasar ne dai ya sanar da matakin janye tallafin man fetur faɗin a jawabin da ya gabatar bayan shan rantsuwar kama aiki.

    Matakin da ya haifar da tashin farashin man a fadin kasar, abin kuma ya sa direbobi suka ninka kudin mota a ƙasar, lamarin da masana ke ganin zai haifar da tashin farashin kayayyaki a ƙasar.

    Tuni dai ƙungiyar ƙwadago ta ƙasar NLC tare da wasu ƙungiyoyin suka yi barazanar shiga yajin aiki matuƙar gwamnatin ƙasar ba ta janye matakin cire tallafin man fetur ɗin ba

  14. Real Madrid za ta ɗauki Kane madadin Benzema

  15. Kotu ta yanke wa soja hukuncin shekara biyar kan guduwa daga aiki

    Kotun soji a Rasha ta yanke wa wani sojan ƙasar hukuncin ɗaurin shekara biyar a gidan yari, sakamakon samun sa da laifin barin sansanin soji ba bisa ƙa'ida ba.

    Kotun wadda ke zamanta a sansanin sojin ta samu halartar sojoji fiye 400 da manyan kwamandojinsu.

    Bayan yanke hukuncin, alƙalin kotun ya gabatar da jawabi kan laifukan da suka saɓa wa tsarin sojoji, kamar yadda yake ƙunshe cikin ƙa'idojin aikin sojin ƙasar.

    Wannan dai ba shi ne karo na farko da ake yanke makamancin wannan hukunci a kotun sojin ba.

    Ko a watan Afrilun da ya gabata ma, kotun ta samu wani soja da laifin barin sansanin sojin ba tare da izini ba.

  16. Kenya ta rufe ofishin jakadancinta a Sudan

    Kenya ta rufe ofishin jakadancinta a Khartoum babban birnin Sudan, yayin da faɗa tsakanin sojojin ƙasar da dakarun RSF ke ci gaba da rincaɓewa.

    Ma'aikatar harkokin wajen Kenya ta ce ofishin jakadancin ya yi ƙoƙarin ganin ya taimaka wajen kwashe 'yan ƙasarta daga Sudan.

    To amma a yanzu ya ce ya rufe ofishin ne saboda barazanar da yake fuskanta daga faɗan da ake yi a birnin.

    Kenya dai ta daɗe tana yunƙurin taimakawa wajen kawo ƙarshen rikicin da ake yi tsakanin sojojin ƙasar da dakarun RSF.

  17. Mazauna Enugu sun ƙi bin umarnin Gwamnan jihar sun zauna a gida

    Mazauna birnin Enugu da ke kudu maso gabashin Najeriya sun yi watsi da umarnin da gwamnan jihar ya bayar na bijire wa umarnin ƙungiyar IPOB na zaman gida a ranar Litinin a jihar.

    Rahotonni sun ce tituna da makarantu da bankuna da kasuwanni da sauran wuraren gwamnati ke ci gaba da kasancewa babu mutane.

    A ranar 1 ga watan Yuni ne gwamnan jihar Peter Mbah ya yi iƙirarin cewa daga yanzu ya haramta batun zama a gida da ƙungiyar IPOB ta bayar.

    Yana mai kira ga al'umma da ɗaiɗaikun ƙungiyoyi a faɗin jihar su fita harkokinsu na yau-da-kullum.

    Mista Mbah ya ce gwamnatinsa a shirye take ta tattauna da mutanen da ke da kyayyawar aniyar samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali domin tabbatar da tsaro da zaman lafiyar jihar.

    Kungiyar IPOB ta kwashe watanni tana saka dokar zaman gida a wasu ranaku a yankin kudu maso gabashin Najeriya.

    A wani mataki na neman sakin jagoran ƙungiyar Nnamdi Kanu

    Matakin da masana tsaro ke kallo a matsayin babbar barazana ga tsaron ƙasar.

  18. Libya ta kori dubban 'yan ci-ranin Masar

    Rahotonni daga Libya na cewa ƙasar ta mayar da dubban ci-ranin Masar da ke zaune a ƙasar zuwa gida.

    Jamai'an tsaron Libya sun ce 'yan ci-rani 4,000 ne aka samu a lokacin wani samame kan masu safarar mutane a gabashin Libya.

    Wata majiya daga jami'an tsaron Masar ta ce rabin waɗanda aka kama yayin samamen ne ke zaune a Libya ba bisa ƙa'ida ba, kuma su kaɗai ne aka mayar Masar.

    Hukumomin kula da 'yan ci-rani sun ce akwai 'yan ci-rani kusan 500,000 da ke zaune a Libya, da yawa daga cikin na neman tsallakawa zuwa Turai ta jirgin ruwa, yayin da wasu ke zauen a ƙasar suna ayyukan ƙwadago.

  19. OPEC za ta rage yawan man da Najeriya ke fitarwa da kashi 20

    Ƙungiyar Ƙasashen Masu Arzikin man Fetur ta OPEC tare da ƙawayenta sun amince da rage ganga miliyan 1.393 na man da suke fitarwa zuwa kasuwannin duniya a kowacce rana.

    Matakin da zai tilasta rage adadin man da Najeriya ke fitarwa da kashi 20.7 cikin 100.

    Yarjejeniyar da ƙungiyar ta cimma bayan wani taro da ta gudanar a ƙarshen mako ta tanadi cewa Najeriya wadda ke kan gaba a arzikin man fetur a Afirka za ta rika fitar da ganga miliyan 1.380 a kowacce rana daga watan Janairu zuwa Disambar 2024.

    Ana sa ran Najeriya za ta riƙa fitar da ganga miliyan 1.826 zuwa 1.747 a kowacce rana, daga watan Agusta zuwa Nuwamba masu zuwa.

    Dama dai rahotonni na cewa ƙasar ba ta fitar da adadin man da OPEC ta keɓe mata, lamarin da masana ke ganin ya taimaka wajen rage kudin shigar da take samu daga sayar da man.

    Matakin da OPEC ɗin ta ɗauka na rage adadin man da ƙasashen ke fitarwa zai shafi kuɗin shiga da gwamnatocin ƙasashen ke samu.

    Matakin da masana ke ganin zai shafi kasafin kuɗin ƙasashen da tattalin arzikinsu, musamman Najeriya wadda man fetur ne babbar hanyar samun kuɗin shigarta.

  20. Ana dakon sakamakon zaɓen 'yan majalisa a Guinea-Bissau

    Masu zaɓe na dakon sakamakon zaɓen 'yan majalisun dokoki da aka gudanar a Guinea-Bissau ranar Lahadi.

    Hukumar zaɓen ƙasar ta ce kusan mutum miliyan ɗaya ne daga cikin al'ummar ƙasar miliyan biyu suka yi rajistar zaɓe a ƙasar.

    Kusan mutum 200 ne suka sanya ido kan zaɓen, ciki har da jami'ai 75 daga ƙungiyar ECOWAS.

    Jam'iyyun siyasa 22 ne suka fafata a zaɓen, inda ɗaya daga cikinsu ke fatan samun rinjayen kujeru a majalisar.

    A baya dai jam'iyyar PIAGC ce ta saba samun rinjaye a majalisar, sai dai a yanzu ta koma jam'iyyar hamayya a ƙasar.

    Kundin tsarin mulkin ƙasar ya tanadi cewa duk jam'iyyar da ke da rinjaye a majalisar ita ce za ta kafa gwamnati, sai dai doka ta tanadi cewa shugaban ƙasar na da ikon rusa majalisar idan hali ya yi.

    A shekarar 2020 ne aka zaɓi shugaban ƙasar Umaro Sissoco Embaló ƙarƙashin jam'iyyar Madem-G15 party wadda ta ɓallae daga ƙawancen da ta ƙulla da PAIGC.

    A yanzu jam'iyyar Madem-G15 party ce ta biyu a yawan kujeru a majalisar dokokin ƙasar.

    A shekarar da ta gabata ne shugaban ƙasar ya fuskanci suka bayan da ya rushe majalisar dokokin ƙasar, sannan ya naɗa jami'an gwamnatinsa, watanni uku bayan da ya ce ya tsallake rijiya da baya kan yunƙurin juyin mulki.