Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

'Shanun Buhari sun ragu saboda kyauta'

Wannan shafi ne da ke kawo abubuwan da ke wakana a Najeriya da makwabtanta da kuma sauran sassan duniya kai tsaye

Rahoto kai-tsaye

Abdullahi Bello Diginza and Nabeela Mukhtar Uba

  1. 'Dakarun RSF sun ƙwace cibiyar adana kayan tarihi ta Sudan'

    Rahotanni daga Sudan na cewa mayaƙan ƙungiyar da ke yaƙi da sojojin ƙasar sun ƙwace cibiyar adana kayan tarihi ta ƙasar da ke birnin Khartoum.

    Mataimakin shugaban gidan tarihin mai suna Ikhlas Abdellatif ta ce sojojin RSF sun shiga ginin a ranar Juma'a. Amma ta shawarce su da kare martabar kadarar ƙasar.

    Zuwa yanzu babu tabbaci game da ko an ɓarnata wani abu a cibiyar, wadda ke kusa da babban bankin ƙasar, wurin da aka tafka zazzafan ɓarin wuta tsakanin ɓangarorin biyu.

  2. An rantsar da Erdogan a matsayin Shugaban Turkiyya karo na uku

    An rantsar da Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan a matsayin shugaban ƙasar zango na uku.

    Wakilin BBC ya ce: "Sakamakon rantsuwar da ya sha, Mista Erdogana ya fara sabon wa'adin mulki na shekara biyar, inda 'yan majalisar jam'iyyarsa suka dinga tafa masa."

    An gudanar da bikin rantsuwar ne a Majalisar ƙasar kusan mako ɗaya ke nan bayan nasarar da ya samu kan babban mai adawa Kemal Kilicdaroglu, a zagaye na biyu na zaɓen.

    Mista Erdogan ya mamaye fagen siyasar Turkiyya tsawon shekara 20, a matsayin firaminista da kuma shugaban ƙasa.

    Daga cikin mahalarta bikin akwai shugaban ƙungiyar ƙawance ta Nato, Jens Stoltenberg da Firaministan Armeniya, Nikol Pashinyan.

  3. Firaministan Indiya ya ci alwashin hukunta masu sakaci a haɗarin jiragen ƙasa

    Firaministan Indiya Narendra Modi ya ci alwashin ɗaukar tsattsauran mataki kan waɗanda aka samu da sakaci a hatsarin jirgin da ya afku a Jihar Odisha.

    Jami'an hukumar kula da sufirin jiragen ƙasa sun ce mutum ɗari biyu da tamanin da takwas ne suka mutu kuma wasu kusan 1,000 suka jikkata a hatsarin, wanda ya haɗa da jiragen fasinja biyu.

    Rahotannin farko-farko sun nuna cewa matsalar sadarwa ce ta haddasa hatsarin.

    Shugaba Modi ya bayyana hatsarin a matsayin "mai sosa rai" bayan ya ziyarci wurin da kuma wadanda ke asibiti.

  4. Gwamnan Bauchi ya zama sabon shugaban gwamnonin PDP

    An zaɓi Gwamna Bala Muhammed na jihar Bauchi a matsayin sabon shugaban gwamnonin Jam'iyyar PDP, mai hamayya a Najeriya.

    An kuma zaɓi gwamnan Rivers Siminalayi Fubara a matsayin mataimakinsa.

    An dai zaɓe su ne a wani taro da jam'iyyar ta PDP ta shirya wa zaɓaɓɓun ƴan jam'iyyar da aka yi a Fadar gwamnatin Bauchi yau Asabar.

    Bala Muhammed ya maye gurbin gwamnan Oyo, Seyi Makinde wanda shi ma ya halarci taron na yini ɗaya.

    Muƙaddashin shugaban Jam'iyyar ta PDP, Umar Damagum, a jawabinsa na buɗe taro ya ce "ina son na sake nanata batun majalisar dokoki ta ƙasa, ya kamata mu sani cewa mu ƴan hamayya ne.

    "Idan muna son mu ci gaba da zama masu muhimmanci, dole ne mu yi aiki tare. Ita ce kaɗai hanyar da za ka tabbatar da muhimmancinka." kamar yadda Damagum ya bayyana.

  5. 'Shanun Buhari sun ragu saboda kyauta'

    Tsohon Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari ya miƙa takardar da ya cike da ke ƙunshe da bayanan kadarorin da ya mallaka ga hukumar ɗa'ar ma'aikata CCB bisa tanadin shafi na shida na Kundin tsarin mulkin ƙasa.

    Mai magana da yawun tsohon Shugaban, Garba Shehu cikin saƙon da ya wallafa a shafinsa na Tuwita, ya ce a yau ne hukumar ta CCB ta tabbatar da karɓar fom din tsohon shugaban ƙasar.

    A cewarsa, takardar bayanan ta nuna cewa kadarorinsa da za a iya sauyawa wuri ba su ƙaru ba - a gida da kuma wajen Najeriya.

    Sannan bai buɗe wani sabon asusun banki ba, baya ga wanda yake da shi a bankin Union a Kaduna.

    Garba Shehu ya ƙara da cewa, tsohon Shugaban bai karɓi bashi ba kuma adadin shanunsa sun ragu saboda ya bayar da wasu kyauta cikin shekara huɗu da ta gabata.

  6. Hotunan gine-ginen da gwamnatin jihar Kano ta rusa

    Gwamnatin jihar Kano da ke arewa maso yammacin Najeriya ta fara rushe wasu gine-gine da aka yi a filayen gwamnatin jihar.

  7. Tinubu ya yi azarɓaɓin janye tallafin mai – Atiku Abubakar

    Tsohon mataimakin shugaban Najeriya, Atiku Abubakar ya soki matakin shugaba Bola Tinubu na cire tallafin mai ba tare da samar da hanyoyin sauƙaƙa wa al'umma ba inda ya ce an ɗauki matakin ba tare da yin zuzzurfan nazari ba.

    Atiku Abubakar wanda shi ne ɗan takarar jam'iyyar PDP a zaben shugaban ƙasar da ya gudana, ya yi wannan suka ne a wani taron PDP da aka shirya wa zaɓaɓɓun jami'ai a jihar Bauchi.

    A cewar Atiku, "tsakanin 1999 da 2007, gwamnatin PDP ta ɓullo da batun cire tallafin mai kuma ni na jagoranci kwamitin. Mun cimma ƙudirin ta hanyoyi biyu amma sai bayan samar da kayayyakin rage raɗaɗin matakin ga waɗanda lamarin ya shafa,"

    "Mun ɗanɗana irin wannan a matsayin jam'iyya da ke mulki. Da abin da za mu yi ke nan ba wai kawai sanar da janye tallafi ba, ba tare da tattaunawa da ɓangarorin da abin ya shafa ba." in ji Atiku Abubakar.

    Bola Tinubu dai ya bayyana matakin janye tallafin man a lokacin da yake jawabinsa na farko ga al'ummar Najeriya bayan rantsar da shi a matsayin shugaban ƙasa.

    Kuma tun lokacin ne al'ummar ƙasar suka shiga ruɗani kasancewar farashin mai ya tashi ga kuma hauhawar farashin kayayyaki.

  8. Gwamnatin jihar Kano ta hana manna fasta a jikin bango

    Gwamnatin jihar Kano ta haramta manna fastoci na siyasa da na tallace-tallace a jikin gine-ginen gwamnati da na masu zaman-kansu a faɗin jihar.

    Sakataren yaɗa labaran gwamnan jihar, Sunusi Bature Dawakin Tofa ne ya bayyana haka cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook.

    Gwamnatin jihar ta ce za ta kafa wata hukuma da za ta tabbatar da bin sabuwar dokar a wani mataki na tsaftace bangwaye da sauran gine-gine daga fastocin siyasa a jihar.

    Sanarwar ta kuma buƙaci masu talla da su yi amfani da allunan talla da sauran hanyoyin tallata haja wajen gudanar da tallace-tallacensu.

    Gwamnan jihar ya umarci jami'ai daga ma'aikatar muhalli da hukumar kashe gobara ta jihar da su riƙa zagayawa titunan birnin domin yage fastocin da aka manna na siyasa da na tallace-tallace.

  9. Hotunan hatsarin jiragen ƙasan Indiya

  10. An kashe sojojin Isra'ila uku a kusa da kan iyakar Masar

    Rundunar sojin Isra'ila ta ce dakarun sojin Masar sun halaka sojojinta uku a kusa da kan iyakar ƙasashen biyu.

    An dai tsinci gawarwakin sojojin a kusa da kan iyakar ƙasar da safiyar ranar ranar Asabar, bayan da aka kasa samunsu a waya

    Rundunar sojin Isra'ila ta ce za ta gudanar da bincike tare da haɗin gwiwwar dakarun sojin Masar.

    Sojojin na Isra'ila sun ce an tsinci gawarwarkin sojojin sa'o'i bayan wani farmaki kan masu safarar ƙwaya a kan iyakar ƙasashen.

    Mai magana da yawun rundunar Sojin Isra'ila ya ce an ƙwace miyagun ƙwayoyi da kudinsu ya kai 400,000 daga hannun wani da ya yi yunƙurin tsallaka kan iyakar ƙasar.

    Ya ce suna zargin kisan sojojin na da alaƙa da farmaki kan masu safarar ƙwayar.

    Ana dai yawan samun arangama tsakanin dakarun sojin Isra'ila da masu safarar ƙwayoyi da ke yunƙurin shigar da ƙwaya ta kan iyakar ƙasashen biyu.

  11. Shin kun san abin da ke haifar wa yara matsalar fitsarin kwance

    Matsalar fitsarin kwance matsala ce da ke ci wa yara da iyayensu tuwo a ƙwarya.

    Shirin Lafiya Zinariya na wannan makon - wanda Habiba Adamu ta gabatar - ya duba abin da haifar da matsalar

  12. Ƙungiyar 'Yan jarida ta Najeriya za ta fara yajin aiki kan cire tallafin mai

    Kungiyar 'yan jarida ta Najeriya NUJ ta ce za ta bi sahun ƙungiyar Kwadago ta NLC a ƙasar wajen tsunduma yajin aiki daga ranar Laraba mai zuwa, saboda cire tallafin man fertur.

    Ƙungiyar ta bayyana cikin wata takarda da ta fitar, bayan ganawar da kwamtin gudanarwarta ya yi da safiyar ranar Asabar domin tattauna batun cire tallafin man fetur da gwamnatin ƙasar ta yi da kuma matakin ƙungiyar ƙwadago ta NLC ta ɗauka na shiga yajin aiki a tsakiyar makon da ke tafe.

    Ƙungiyar ta NUJ ta ce a halin da ake ciki tashin farashin man fetur da na sauran kayayyaki sun jefa al'ummar ƙasar cikin mawuyacin hali.

    Haka kuma ƙungiyar ta umarci mambobinta da ke faɗin jihohin ƙasar da su fara yajin aiki tare da fita zanga-zanga daga ranar Laraba 7 ga watan Yuni matuƙar kamfanin mai na ƙasar NNPCL bai janye ƙarin farashin man fetur da ya yi ba.

  13. Gwamnatin Kano ta fara rushe wasu gine-gine da ta ce an yi ba bisa ƙa'ida ba

    Gwamnatin jihar Kano da ke arewa maso yammacin Najeriya ta fara rushe wasu gine-gine da aka yi a filayen gwamnatin jihar.

    A cikin wata sanarwa da daraktan yaɗa labaran gwamnan Sunusi Bature Dawakin Tofa ya fitar, ya ce gwamnan jihar Abba Kabir Yusuf ne bayar da umarnin fara rushe gine-ginen waɗanda ya ce an yi su ba bisa ƙa'ida ba a wasu wurare mallakar gwamnatin jihar.

    Da safiyar ranar Asabar ne aka fara rusa wasu gine-gine a filin sukuwa a birnin domin ƙwato filin gwamnati kamar yadda sanarwar ta bayyana.

    Idan za a iya tunawa a alƙawuran yaƙin neman zaɓe da gwamnan ya yi, ya alƙawarta ƙwato filaye mallakar gwamnati da aka gina ba bisa ƙa'ida ba.

    Gwamnan ya ce za a rusa wuraren da aka gina a filayen makarantu da masallatai da filayen wasanni, da maƙabartu da kasuwanni da asibitoci, domin tabbatar da bin tsarin ginin birnin, tare da ƙawata shi da kuma tsare lafiyar al'ummar jihar.

    Sanarwar ta kuma yi kira ga mazauna jihar da su yi haƙuri, kasancewar sabuwar gwamnatin jihar na son tabbatar da ci gaban jihar.

    Dama dai a jawabin da sabon gwamnan jihar ya yi bayan shan ranstuwar kama aiki ranar Litinin, ya bayar da umarni ga jami'an tsaro a jihar da su ƙwato kadarorin gwamnatin jihar da ya ce tsohuwar gwamnatin Ganduje ta sayar wa wasu mutane a jihar.

    A ranar Juma'a ne gwamnan ya bayar da umarni ga masu gine-gine a filin da ke bayan sansanin alhazai ( Hajj Camp) a jihar da su gaggauta dakatar da ginin nasu, bayan wata ziyara da ya kai wajen.

  14. Tinubu ya jajanta wa Indiya kan hatsarin jiragen ƙasa

    Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya aike da saƙon jaje ga gwamnati da al'ummar Indiya kan hatsarin jiragen ƙasa da ya kashe fiye da mutum 280 a ƙasar.

    A cikin wata sanarwa da mai taimaka wa shugaban ƙasar kan yaɗa labarai Abdulaziz Abdulaziz ya fitar, Tinubu ya bayyana hatsarin da cewa abu ne mai sosa zuciya.

    Sanarwar ta ce ''Ina jajanta wa iyalan mutanen da hatsarin jirgin ƙasa ya rutsa da su a jihar Odisha, muna taya su jimami kan halin da suke ciki.

    ''Ina miƙa sakon jaje da ta'aziyya ga mai girma firaminista Narendra Modi, da mutanen Indiya tare da iyalan waɗanda lamarin ya rutsa da su'', in ji shugaban na Najeriya.

    Hatsarin ya rutsa da jiragen ƙasa guda biyu maƙare da fasinjoji da kayayyaki a birnin Baladsore a jihar Odisha da ke gabashin ƙasar.

    Fiye da mutum 900 ne suka jikkata a hatsarin wanda ya kasance ɗaya daga cikin hatsari mafiya muni a tarihin ƙasar.

  15. Gbajabiamila ya gode wa Tinubu bisa naɗa shi shugaban ma'aikata

    Kakakin majalisar wakilan Najeriya Femi Gbajabiamila ya gode wa shugaban ƙasar Bola Ahmed Tinubu kan naɗa shi muƙamin shugaban ma'aikata na fadar gwamnati.

    A cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Tuwita jim-kaɗan bayan ayyana shi a muƙamin, mista Femi alƙawarta gudanar da aiki tuƙuru idan ya fara aiki ranar 14 ga watan Yuni.

    ''A matsayina na wanda ya shafe shekara 20 a majalisar dokokin Najeriya, a daidai lokacin da na sake samun nasarar wa'adi na na shida a majalisar, na alƙawarta yin aiki tare da shugabana ƙasa wajen aiwatar da tarin ayyukan da ke gabansa domin zaman lafiya da ci gaban Najeriya'', in ji Femi.

    A ranar Juma'a ne shugaban ƙasar Bola Tinubu ya naɗa Mista Gbajabiamila - wanda a yanzu shi ne kakakin majalisar dokokin Najeriya - bayan ganawarsa da gwamnonin jam'iyyar APC mai mulki.

    Haka kuma shugaban ya sanar da naɗin tsohon gwamnan Benue, kuma tsohon ministan ayyuka na musamman a gwamnatin Buhari George Akume a matsayin sakataren gwamnatin tarayya.

  16. Za a rantsar da shugaban Turkiyya wa'adi na uku a kan mulki

    Nan gaba a yau ne za a rantsar da shugaban Turkiyyar Recep Tayyip Erdogan wa'adi na uku a kan karagar mulkin ƙasar.

    A makon da ya gabata ne Mista Erdogan ya samu nasarar lashe zaɓen zagaye na biyu da aka gudanar tsakaninsa da ɗan takarar jam'iyyar adawar ƙasar Kemal Kilicdaroglu

    Recep Tayyip Erdogan ya kankane fagen siyasar Turkiyya cikin shekara 20 da suka gabata inda ya fara da muƙamin firaminista kafin ya zama shugaban ƙasa.

    Tsare-tsarensa na siyasa da zamantakewa waɗanda ake ganin na musulunci ne sun sanya shi zama fitacce a fage siyasar ƙasar.

    To sai dai masu sukarsa na zarginsa da mulkin kama-karya da rashin iya tafiyar da tattalin arzikin ƙasa.

  17. Ya kamata Tinubu ya tunasar da mutane kafin sanar da cire tallafin mai - Shekarau

    Tsohon gwamnan jihar Kano Sanata Ibrahim Shekarau ya ce da ya kamata sabon shugaban ƙasar ya yi wa 'yan ƙasar bayani kafin cire tallafin mai.

    Yana mai cewa ya kamata shugaban ƙasar ya bi matakai kafin sanar da cire tallafin kai-tseye kamar yadda shugaban ya yi a jawabinsa na farko bayan shan ranstuwar kama aiki.

    ''Ya kamata ya sanar da mutane cewa maganar cire tallafin man fetur tun kafin ya zo an yi ta fiye da shekara guda, har ma an cire shi a kasafin kuɗi na shekarar 2023 da muke ciki'', in ji Shekarau

    A cikin shirimu na Gane Mini Hanya na wannan makon Mallam Ibrahim Shekarau ya taɓo batutuwa da dama ciki har da batun siyasar jihar Kano

  18. Cire tallafin mai: Cigaban Najeriya na buƙatar tsauraran matakai - Wike

    Tsohon gwamnan jihar River da ke kudu maso kudancin Najeriya Nyesom Wike ya kare matakin da shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya ɗauka na cire tallafin man fetur, yana mai cewa mulkin ƙasa irin Najeriya ba abu ne mai sauƙi ba.

    Mista Wike ya bayyana haka ne ranar Juma'a a lokacin da yake ganawa da manema labarai a fadar shugaban ƙasar da ke Abuja.

    Rahotonni sun ce Mista Wike tare da gwamnan jihar Oyo Seyi Makinde da tsohon gwamnan jihar Delta James Ibori sun gana da shugaban ƙasar a wata ziyara da suka kai fadar shugaban ƙasar ranar Juma'a.

    Mista Wike ya ce sun je fadar shugaban ne domin mara masa baya kan matakan da yake ɗauka a gwamnatinsa.

    ''Wannan ya nuna cewa sabon shugaban ƙasa a shirye yake wajen gudanar da mulkinsa, kuma babu aibi dangane da matakin cire tallafin man fetur, domin dole sai an ɗauki tsauraran matakai idan ana so ƙasar ta ci gaba'', in ji Wike.

    A watan da ya gabata shugaba Tinubu ya yaba wa tsohon gwamnan na jihar Rivers a wata ziyarar aiki da ya kai jihar, karon farko tun bayan zaɓensa a matsayin shugaban ƙasar.

  19. MDD ta buƙaci Senegal ta kawo ƙarshen rikicin da ya kaure a ƙasar

    Majalisar Dinkin Duniya ta jagoranci kiraye-kirayen da duniya ke yi wa ƙasar Senegal na lafar da ƙurar da ta kaure a ƙasar bayan hukuncin ɗaurin shekara biyu da aka yanke wa magudun ‘yan adawar ƙasar Ousmane Sonko.

    Gomma mutane ne aka bayar da rahoton cewa sun mutu a jiya Juma’a sannan an sanya dokar hana fita a babban birnin ƙasar Dakar, sakamakon wannan rikici.

    Jagoran ‘yan adawar ya ce wannan wani yunƙuri ne kawai na hana shi tsayawa takarar shugabancin ƙasar a zaɓen ƙasar da ke zuwa.

    Sai dai gwamnatin ƙasar ta ce babu batun siyasa a cikin wannan shari’a.

    Ana fargabar cewa yanayin zai sake ƙazancewa idan ‘yan sanda suka yi amfani da ƙarfi wajen tasa ƙeyar Ousmane Sonko daga gidansa.

  20. Jam’iyyun siyasa sun ceto Amurka daga faɗawa matsin tattalin arziki - Biden

    Shugaban Amurka Joe Biden ya ce Amurka ta tsallake gagarumar matsalar tattalin arzikin ƙasa a wannan makon, Sakamakon jajircewar jam’iyyun ƙasar biyu wajen haɗa kai domin aiki tare.

    Mista Biden ya bayyana hakan ne a wani jawabi da ya gabatar wanda aka haska a gidan talbijin kai-tsaye daga ofishinsa.

    Shugaban na Amurka ya ce amincewa da ƙudurin ƙara kuɗaɗen bashi da ƙasar ke ƙarbowa ya nuna cewa jam’iyyun siyasar ƙasar biyu na iya cimma yarjejeniya a fagen tattalin arzikin Amurka.

    Mista Biden ya ce babu wani abu da ya zarta wannan daɗi yanzu haka a fagen siyasar ƙasar, la’akari da yanayi mai tsanani da Amurkawa suka shiga.

    A yau Asabar ne shugaban zai rattaɓa hannu kan ƙudurin domin ya zama doka.

    Kasuwar hannayen jarin ƙasar ta ɗaga bayan cimma yarjejeniyar lamarin da zai iya ceto mista Biden kan wani abu da ke neman zame masa babbar barazana