Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Abba Kabir Yusuf ya gayyaci Muhammadu Sanusi II bikin rantsar da shi a Kano
Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke wakana a Najeriya da makwabtanta da kuma sauran sassan duniya kai tsaye
Rahoto kai-tsaye
Muhammad Annur Muhammad and Haruna Kakangi
Abba Kabir Yusuf ya gayyaci Muhammadu Sanusi II bikin rantsar da shi
Gwamnan Kano mai jiran gado Abba Kabir Yusuf ya gayyaci Muhammadu Sanusi II bikin rantsar da shi a Kano.
Za a yi bikin ne ranar 29 ga Mayu a filin wasa na Sani Abacha a Kano.
“Ina gayyatarka bikin rantsar da ni da mataimakina Kwamred Aminu Abdusslam Gwarzo.”
"Kasancewarka a wajen bikin ba wai zai kayatar ba ne kawai amma zai kasance muhimmin cigaba da goyon baya gare mu,” kamar yadda gwamnan mai jiran gado Abba Kabir Yusuf ya bayyana a cikin takardar gayyata da ke ɗauke da sa hannunsa.
Sunusi Bature Dawakin Tofa, kakakin gwamnan Kano mai jiran gado, ya tabbatar wa BBC cewa ba wai Muhammadu Sanusi II kawai aka gayyata bikin rantsar da sabon gwamnan na Kano ba, an kuma gayyaci Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, jagoran NNPP da Aliko Dangote da Abdul Samad Isyaka Rabiu da wasu manyan mutane na Najeriya da ƙasashen waje.
An zubar da ruwan wani dam saboda neman wayar salula
An dakatar da wani jami’in gwamnatin India bayan ya bayar da umarnin janye ruwan wani dam domin gano wayarsa ta salula.
An shafe kwana uku ana janye miliyoyin lita na ruwan dam ɗin bayan wayar Rajesh Vishwas ta faɗa ciki a lokacin da yake ɗaukar hoto (selfi)
Lokacin da aka gano wayar, ta sha ruwa ba za ta yi aiki ba.
Mista Vishwas ya yi ikirarin cewa wayar na ƙunshe da muhimman bayanai na gwamnati wanda ya zama wajibi a gano ta, amma an zarge shi da yin sakaci.
Wayar jami’in ƙirar Samsung ce da aka bayyana darajarta ta kai dala 1,200, kuma ta faɗa ne dam din Kherkatta a jihar Chhattisgarh da ke tsakiyar India a ranar Lahadi.
Bayan masu ninkaya a yankin sun gaza gano wayar, jami’in ya yi hayar masu amfani da injin domin janye ruwan, kamar yadda ya bayyana a cikin wani bidiyo da kafofin yadda labaran India suka bayyana.
An dakatar da shi yanzu haka, kuma hukumomi sun ce ruwa muhimmin abu ne da bai kamata a yi hasara ba, kamar yadda wata jami’a Priyanka Shukla a yankin Kanker ta shaida wa wata jaridar ƙasar.
Gwamnatin Sudan ta nemi taimakon tsoffin sojoji
Ma'aikatar tsaron Sudan ta yi kira ga tsoffin sojin ƙasar da suka fito su ɗaura ɗamarar yaƙi a yayin da ake ci gaba da gwabza fada da dakarun RSF.
Mazauna Khartoum babban birnin ƙasar sun ce sace-sace da cin zarafin lalata sun ƙaru duk da yarjejeniyar tsagaita wuta ta kwana bakwai da ɓangarorin biyu suka amince.
Rahotanni sun ce ana ci gaba da gwabza faɗa a El Fasher, babban birnin yankin arewacin Darfur.
An ji ƙarar manyan makamai da safe kuma rahotanni sun ce mutum 11 suka jikkata.
Tsofffin ƙungiyoyin ƴan tawaye biyar na Sudan sun sake ɗaukar mayaƙansu zuwa El Fasher domin kawo ƙarshen rikicin.
Gwamnan Kano mai jiran gado ya ayyana kadarorinsa kafin shan rantsuwa
Gwamnan Kano mai jiran gado Abba Kabir Yusuf ya ayyana kadarorin da ya mallaka ga hukumar ɗa’ar ma’aikata.
Sanarwar da ofishin gwamnan mai jiran gado ya fitar a ranar Juma’a ta ce Abba Kabir Yusuf ya gabatar da kansa ga ofishin hukumar ɗa’ar ma’aikata da ke Kano tare da miƙa fom da ya cike na ƙadarorinsa.
“Na cika sharuɗɗan da kundin tsarin mulki ya gindaya na ayyana ƙadarorin da na mallaka kafin rantsar da ni a 29 ga Mayu," in ji sanarwar.
Abba Kabir Yusuf ya kuma sanar da matakin a shafinsa na Twitter
Gwamnan mai jiran gado ya kuma bayyana cewa dukkanin jami’an da za su yi aiki a gwamnatinsa da suka ƙunshi har da muƙaman siyasa sai sun bayyana ƙadarorinsu kamar yadda doka ta tanada.
A ranar Litinin 29 ga Mayu za a rantsar da Abba Kabir Yusuf na jam'iyyar NNPP a matsayin sabon gwamnan Kano.
Abin da Atiku ya ce kan watsi da ƙarar PDP a kotun ƙoli
Ɗan takarar shugaban kasa a Jam'iyyar PDP a zaɓen 2023 kuma tsohon mataimakin shugaban Najeriya ya ce watsi da ƙarar PDP da kotun koli ta yi ba zai karya masu guiwa ba.
Kotun koli ta yi watsi da ƙarar da PDP mai hamayya a Najeriya ta ɗaukaka tana nema soke cancantar takarar Bola Ahmed Tinubu da mataimakinsa na jam'iyyar APC.
A hukuncin da kotun mai alkalai biyar ta sanar yau Juma'a ta ce PDP ba ta da dama a doka ta yi kara a kan lamarin saboda a cewar kotun PDP ba mamba ce ta jam'iyyar APC ba.
Atiku wanda ya zo na biyu a zaɓen da aka ayyana Bola Ahmed Tinubu na jam'iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaɓen shugaban Najeriya da aka gudanar a ranar 25 ga Fabrairun 2023 tuni ya shigar da ƙara kotun sauraren ƙararrakin zaɓe domin ƙalubalantar sakamakon zaɓen.
"Korar ƙarar PDP a kotun ƙoli ba zai karya muna guiwa ba na neman adalci. Lauyoyinmu za su tabbatar da zaɓen ranar 25 ga Fabrairu an yi maguɗi kuma ya saɓawa kundin tsarin mulki da dokokin zaɓe," kamar yadda Atiku ya bayyana a shafinsa na Twitter sa'o'i bayan hukuncin kotun ƙoli.
Yadda Buhari ya zagaya da Tinubu fadar shugaban Najeriya
Shugaban Najeriya mai barin gado, Muhammadu Buhari ya zagaya da shugaba mai jiran gado, Bola Ahmed Tinubu lungu da saƙo na fadar shugaban ƙasa da ke Abuja a ranar Juma'a.
A ranar Litinin ne 29 ga Mayu Mista Tinubu zai sha rantsuwar kama aiki a matsayin sabon shugaban Najeriya, wanda zai kawo ƙarshen mulkin Muhammadu Buhari.
Hotunan jirgin Kamfanin Nigeria Air da ya isa Abuja
Jirgin Kamfanin Nigeria Air ya isa Abuja, babban birnin ƙasa daga birnin Addis Ababa na Habasha.
An dai jima ana ce-ce ku-ce kan kamfanin bayan da aka yi ƙoƙarin ƙaddamar da shi a shekarun baya amma abin ya ci tura.
A baya-bayan nan ne Ministan sufuri na Najeriya, Sanata Hadi Sirika ya bayyana cewa jirgin saman kamfanin Nigeria Air zai isa ƙasar yau, wani lamari da zai kasance babban ci gaba ga shirye-shiryen soma tafiyar da harkokin kamfanin.
A watan Maris, ministan, yayin wani taron masu ruwa da tsaki a ɓangaren sufuri, ya tabbatar da cewa kamfanin Nigeria Air zai soma aiki gadan-gadan kafin ƙarshen gwamnatin Muhammadu Buhari.
Kotunan Ghana sun kasance fayau saboda yajin aiki
Ayyuka sun tsaya cik a kotunan kasar Ghana sakamakon yajin aikin sai-abin-da-hali-ya-yi da ma'aikata suka sanar tun a jiya Alhamis a kan bukatar karin albashi da bashin da suke bi.
Kungiyar ma'aikatan ta umarci dukkanin mambobinta da kada su je aiki, lamarin da ya sa harabobin kotunan kasar da kusan a ko da yaushe suke makil da jama'a, suka kasance fayau.
An shawarci jami'an da ke kula da harkokin rubuce-rubuce na kotunan da kada su bude wata kotu a tsawon lokacin yajin aikin har sai Shugaba Nana Akufo-Addo ya amince da bukatarsu ta karin albashin da kuma biyan bashin da suke bi na kudade tun daga watan Janairu na wannan shekara.
Ana ganin kotunan Ghana na daya daga cikin hukumomin gwamnati da suke cike da kararraki, saboda haka ake ganin yajin aikin zai kara yawan tarin shari'o'in.
Kuma masu lura da al'amura na ganin lamarin zai haifar da nakasu ga kammala shari'o'i.
Ma'aikatan lafiya sun fara yajin aikin sai-baba-ta-gani a Najeriya
Harkokin kula da lafiya sun sake gamuwa da cikas a asibitocin gwamnati a Najeriya, sakamakon yajin aikin da ma'aikatan lafiya suka shiga na sai-abin-da-hali-ya-yi.
Ma'aikatan wadanda ba su kunshi likitoci da jami'an jinya ba wato nas-nas, a karkashin hadaddiyar kungiyar JOHESU, sun dauki wannan mataki ne a fadin kasar saboda batutuwan da suka shafe albashi da kuma kula da jin dadinsu.
Gamayyar kungiyar ta ce ta bai wa gwamnati wa'adin mako biyu domin biya wa ma'aikatan bukatunsu amma kuma ba abin da aka yi.
Ma'aikatan su ne ke kula da bayanan marassa lafiya da dakunan gwaje-gwaje da sauran ayyuka a asibitocin gwamnati a Najeriya.
Yajin aikin ya tilasta wa wasu marassa lafiya tafiya asibitocin ƴan kasuwa, marassa hali kuwa sun rasa na yi, wanda hakan ke jefa rayuwar wasu da dama cikin hadari.
Kari a cikin bukatun ma'aikatan suna son ba tare da bata wani lokaci ba, gwamnati ta amince a rika biyansu da tsarin albashin ma'aikatan lafiya na gaba-daya da biyansu bashin kudaden alawus-alawus da suke ba shi ma nan da nan tare kuma da sake tsarin shekarun yin ritaya daga aiki.
JOHESUN ta shiga wannan yajin aiki ne kwana hudu bayan da kungiyar likitoci masu neman kwarewa ta janye yajin aikinta na gargadi na kwana biyar domin bai wa gwamnati mako biyu ta aiwatar da yarjejeniyar da ke tsakaninsu.
An yaƙe ni saboda hana shigowa da miyagun abubuwa Najeriya - Babagana Monguno
An kama fasinjan da ya buɗe kofar jirgin sama ana tafiya
An kama wani mutum wanda ya bude kofar fitar gaggawa ta wani jirgin sama na kamfanin Asiana Airlines a lokacin da yake shirin sauka a Koriya ta Kudu.
Dukkanin fasinjojin jirgin, wanda ya sauka lafiya a babban filin jirgin sama na Daegu, yau Juma'a, su 194 sun fita lafiya duk da kasancewar kofar a bude.
Rahotanni sun ce aƙalla fasinja shida sun gamu da matsala ta nunfashi inda aka ɗauke su zuwa asibiti.
Jirgin na sauka aka kama mutumin wanda ya bude kofar, ɗan sama da shekara 30
Akwai yara da dama a cikin jirgin da za su je kallon wani wasa da za a yi a ƙarshen mako.
Kuma sun firgita sosai inda suka riƙa kuka da karkarwa a lokacin.
Ƴan sanda sun fara gudanar da bincike a kan lamarin.
Ƴan bindiga sun kashe basarake suka ƙona gawarsa a jihar Imo
Wasu ƴan bindiga sun kashe babban basaraken garin Orsu Obodo da ke karamar hukumar Oguta a jihar Imo, Eze Victor Ijioma da kuma wazirin garin Mgbele shi ma a karamar hukumar.
Rahotanni sun ce maharan sun kashe shugabannin gargajiyar ne a hare daban-daban a jiya Alhamis.
Ƴan bindigar da ba a san ko su wanene ba zuwa yanzu sun hallaka babban basaraken ne a motarsa a garin Izombo kuma suka banka masa.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa wani da ya ga yadda abin ya faru wanda bai yarda a bayyana sunansa ba ya ce maharan sun tare basaraken na al'ummar Orsu Obodo a mahadar Umuamaka a garin Izombe da ke makwabtaka da nasu, inda suka hallaka shi.
Ya kara da cewa domin su tabbatar da ya mutu ne suka sanya wa gawarsa a cikin motar wuta.
Jaridar Punch ta ruwaito cewa kakakin rundunar ƴan sanda a jihar Henry Okoye ya tabbatar mata da labarin kashe-kashen yau Juma'a.
Kuma ya ce Kwamishina ƴan sandan jihar Muhammed Barde ya kaddamar da binciken zakulo maharan.
Kashe-kashe da ƴan bindiga kan yi a jihar ta Imo sun karu tun bayan zabun da aka yi na jihar da kuma na tarayya.
Salah ya yi takaicin rashin samun gurbin gasar zakarun Turai
Za a fara sanya na'ura a cikin ƙwaƙwalwar ɗan'Adam
Wani kamfanin binciken kwakwalwa da Elon Musk ya kafa, ya ce ya samu amincewar hukumomin Amurka don gudanar da binckensa na farko a kan dan'Adam.
Kamfanin na Neuralink ya bayyana binciken a matsayin muhimmin mataki na farko, amma bai yi karin haske a kan binciken nasa ba.
Kamfanin na aiki ne kan yadda za a rinka sa wata na'ura a cikin kwakwalwar mutum domin taimaka wa masu fama da shanyewar jiki da makanta, da kuma taimaka wa, wasu nakasassu kan yadda za su yi aiki da kwamfuta.
Kamfanin ya ce, yana son ya yi amfani da fasahar da za ta zartar da aikin da jikin bil'Adama ke yi.
Kotun Ƙolin Najeriya ta yi fatali da karar PDP a kan Tinubu da Shettima
Kotun Kolin Najeriya ta yi watsi da karar da PDP da dan takararta na shugaban kasa Atiku Abubakar suka daukaka zuwa gabanta ta neman soke cancantar takarar Bola Tinubu da mataimakinsa na jam'iyyar APC.
A hukuncin da kotun mai alkalai biyar ta sanar yau Juma'a ta ce PDP ba ta da dama a doka ta yi kara a kan lamarin saboda a cewar kotun PDP ba mamba ce ta jam'iyyar APC ba.
Masu korafin suna ikirarin cewa zaben Kashim Shettima a matsayin mataimakin dan takarar shugaban kasa, Tinubu ya saba wa sassa na 29(1), 33, 35, da kuma na 84(1)(2) na doka zabe ta kasar ta 2022.
A karar suna cewa Shettima ya saba doka saboda ya yi takarar mataimakin shugaban kasa da kuma kujerar majalisar dattawa ta Borno ta tsakiya a lokaci daya.
A don haka ne wadanda suka shigar da karar suke neman kotun ta soke cancantar APC da Tinubu da Shettima daga takarar wadda suka riga suka yi ta zaben shugaban.
Hukuncin kotun kolin ya kasance daidai da wanda wata babbar kotun tarayya a Abuja ta yi tun da farko.
An kama mutumin da ake zargi da kai harin da ya hallaka mutum huɗu a Japan
Ƴan sanda a Japan sun kama wani mutum da ake zargi da kai harin bindiga da wuka da ya yi sanadin mutuwar mutum hudu, ciki har da ƴan sanda biyu.
An kama mutumin a wata gona da ke kusa da birnin Nakano a tsakiyar Japan, inda aka aikata kisan.
Shaidu sun ce maharin ya caka wa wata mata wuƙa, sannan ya harbe ɗan sanda lokacin da suka iso inda ya aikata kisan farko.
Rahotanni sun ce har yanzu babu wanda ya san dalilin wannan kisa ko hari.
Japan dai ba ta fiya samun masu aikata irin wannan laifi na harbi ba, domin ko a tsawon shekarar da ta gabata bai fi sau hudu aka samu mutane da aikata kisa ta hanyar harbi ba.
Manyan ƙasashen duniya na neman mayar da Afirka filin-daga - AU
Kungiyar Tarayyar Afirka ta yi gargadi cewa nahiyar na cikin barazanar kasancewa wani filin daga, tsakanin manyan kasashen duniya da ke goggaya da juna domin ganin sun yi tasiri a nahiyar.
Shugaban hukumar kungiyar, Moussa Faki Mahamat, ya ce dole Afirka ta jure wa abubuwan da za su biyo baya kan karuwar hamayya tsakanin manyan kasashe a kanta.
Abin da a cewarsa ke barazanar haifar da sabon yaƙin cacar-baka, tsakanin manyan kasashen na duniya.
Kasashe irin su China da Rasha da Amurka a wannan shekara duk sun aika manyan jami'an diflomasiya Afirka.
Yanzu haka akwai ministan harkokin wajen Ukraine da ke rangadi a Afirka, inda ya nemi kasashen nahiyar da su bar matsayin da suka dauka na kasancewa ƴan ba-ruwanmu a kan yakin Ukraine.
Shugaban ya yi gargadin ne yayin da kungiyar ta hadin kan kasashen Afirka ke cika shekara 60 da kafuwa.
Amurka ta sanya takunkumi a kan ɗan Rasha kan yaƙin Mali
Amurka ta sanya takunkumi kan wani dan Rasha wanda ta ce shi ne yake jagorantar mayakan Wagner da ke Mali.
Amurkar ta ce Ivan Maslov, babban jigo ne a harkokin kamfanin sojojin hayar na Wagner a duniya.
Ta ce Wagner babu mamaki suna amfani da zamansu a Mali wajen rubanya kokarin tattara makamai da kayayyakin yaki da Ukraine.
Sannan ta zargi kamfanin na Rasha da shigar da na'urorin kakkabo makami mai linzami ga dakarun RSF a Sudan.
A farkon wannan shekara Amurka ta ayyana Wagner a matsayin kamfanin da ake haya domin aikata manyan laifuka a kasashen duniya.
Kamfanin ya jima yana taimaka wa Mali a yakin da gwamnati ke yi da mayaka masu ikirarin jihadi.
Yau Kotun Ƙolin Najeriya za ta yanke hukunci kan Tinubu da Shettima
A yau Juma'a Kotun kolin Najeriya za ta yanke hukunci a kan kararar da dan takarar shugaban kasa na babbar jam'iyyar hamayya ta Najeriya, PDP, Atiku Abubakar da jam'iyyar tasa suka shigar ta neman soke takarar Bola Tinubu da mataimakinsa Kashim Shettima a zaben da aka yi na 2023.
A karar da suka shigar suna neman kotun ta ayyana cewa takarar Tinubun da Shettima wadanda suka riga suka yi nasara a zaben ranar 25 ga watan Fabarairun 2023, karkashin jam'iyya mai mulki APC, cewa ba ta dace ba.
Masu korafin suna ikirarin cewa zaben Kashim Shettima a matsayin mataimakin dan takarar shugaban kasa, Tinubu ya saba wa sassa na 29(1), 33, 35, da kuma na 84(1)(2) na doka zabe ta kasar ta 2022.
A korafin suna cewa Shettima ya saba doka saboda ya yi takarar mataimakin shugaban kasa da kuma kujerar majalisar dattawa ta Borno ta tsakiya a lokaci daya.
A don haka ne wadanda suka shigar da karar suke neman kotun ta soke cancantar APC da Tinubu da Shettima daga takarar wadda suka riga suka yi ta zaben shugaban.
A hukuncin da alkalin babbar kotun tarayya a Abuja da aka fara kai karar Justice Inyang Ekwo, ya yi, ya yi watsi da ita bisa dalilin cewa PDP ba ta da damar gabatar da korafin.