Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Najeriya na nazari don hana durƙushewar rayuwa idan an cire tallafin mai

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Ahmad Tijjani Bawage

  1. Bankwana

    To yau a nan za mu rufe wannan shafi wanda ke kawo muku labarai da rahotanni kai tsaye. Mun yi farin cikin kasancewa da ku a tsawon wannan rana ta Alhamis.

    Da fatan za ku ci gaba da bibiyar mu a wannan shafi na BBC Hausa.

    Buhari Muhammad Fagge ke cewa mu kwana lafiya!

  2. Japan ta amince da fara amfanin da kwayoyin zubar da ciki

    Ma'aikatar Lafiya ta kasar Japan ta amince da amfanin da kwayoyin zubar da ciki na farko da aka samar a ƙasar.

    A halin yanzu dai, matan da ke neman zubar da ciki ba za su iya yin hakan ba sai ta hanyar tiyata.

    Ƙwayoyin waɗanda wani kamfanin Burtaniya ya sarrafa, za a iya amfani da su wajen zub da cikin da ya kai har makonni tara.

    Sai dai har yanzu maganin na jiran amincewa ta karshe, bayan an gama tattaunawa kan farashi da kuma ka'idojin amfani da shi.

    Ana yi wa wannan matakin kallon wani ci gaba ta fuskar ba mata damar yin zabi wajen haihuwa a Japan.

  3. Wasu batutuwa kan wasan daf da karshe a Champions League

  4. Asibitocin Darfur sun cika da marasa lafiya

    Ƙungiyar Likitocim ta Duniya ta ce dalilin rikicin da ya ɓarke tsakanin sojoji da mayaƙan RSF ya janyo rashin masaka tsinke a 'yan asibitocin da ke aiki a birnin Darfur da ke yankin arewacin Sudan.

    Ƙungiyar bayar da agaji ta likitocin ta ce tawagarta ta mayar da wuraren karɓar haihuwa na kula da waɗanda suka ji rauni saboda cikar da wasu asibitocin suka yi waɗanda ke kusa da inda ake rikicin.

    Ma'aikatan ƙungiyar sun ce "Halin da ake ciki na musifa ne. Sun karɓi mutum 300 da aka raunata, abin takaici kuma shi ne mutum 50 sun mutu ya zuwa yanzu.

    Mafi yawan waɗanda suka ji raunin fararen hula ne waɗanda harsashi ya sama, kuma mafi yawansu yara ne. " Kan dandagaryar asibitocin ma cike yake da mutanen da suka raunata."

    Wakilan Ƙungiyar sun ce yawan mutanen ya fi ƙarfin asibitocin saboda babu inda za ka iya fita da waɗanda suka raunatan saboda an rufe filayen jiragen sama da kan iyakoki.

  5. Erdogan: Nan da shekara mai zuwa za mu kawo ƙarshen hauhawar farashi

    Shugaban Turkiyya ya ce nan da shekara mai zuwa, gwamnatinsa za ta kawo ƙarshen matsalar hauhawar farashi.

    Recep Tayyib Erdoğan ya bayyana haka ne lokacin da yake jawbai a bikin bunƙasa sauya fasalin birni wanda ya gudana a dandalin Gaziosmanpaşa.

    "Da zarar mun kawar da matsalolin da suke gabanmu, za mu shawo kan matsalar hauhawar farashin kaya nan da ƙarshen wannan shekarar, kuma daga nan za mu shawo kan matsalar baki ɗaya," In ji Erdogan.

    Erdogan ya ce za a ci gaba da aiwatar da karɓar kuɗin ruwa kaɗan a kan basuka, matakin da ya ce yana da ƙwarin gwiwa hakan zai rage hauhawar farashi.

    "Matuƙar wannan ɗan'uwan naku yana jan ragamar ƙasarku, babu abin da zai ƙara yawan kuɗin ruwa, maimakon haka, raguwa ma zai ƙara yi.

    "Mun kammala mu'amalarmu da Bankin Lamuni na Duniya a 2013.

    Sun ce kamata ya yi gwamnati ta karɓo bashi daga wurinsu, muka ce musu a'a.

    Na shaida wa shugabar IMF cewa zan iya ci gaba da gudanar da ƙasarmu a haka. Bayan 2013 sai ya zama ba mu da wata hulɗa da IMF.

  6. Raflin da za su busa wasan mako na 32 a Premier League

  7. Hawan Sallah a Kano bayan kammala azumin watan Ramadan

  8. Abin da ya kamata ku sani kan wasan Arsenal da Southampton

  9. Najeriya na nazari don ganin harkokin rayuwa ba su durƙushe ba idan an cire tallafin mai

    Gwamnatin Najeriya ta ce tana nazari a kan hanya mafi dacewa ta cire tallafin man fetur, ba tare da an kawo cikas ga harkokin rayuwa a ƙasar ba.

    Babban sakatare a ma'aikatar albarkatun man fetur, Ambasada Gabriel Aduda ne ya bayyana haka lokacin da yake jawabi ga manema labarai a ƙarshen Taron Ƙoli kan Makamashi na Duniya a Najeriya.

    Ya ce gwamnati tabbas ta duƙufa kan aniyar cire tallafin man fetur, amma ba ta sa ranar yin hakan ba, don kuwa sai ta gama nazarin duk alƙaluma da nufin ganin raɗaɗin da lamarin zai kawo, bai kasance mai tsanani ga masu ƙaramin ƙarfi a Najeriya ba.

    Kamfanin dillancin labarai na Najeriya NAN ya ruwaito Aduda na cewa ko da yake cire tallafin man fetur abu ne da aka mayar da hankali kansa tsawon lokaci, amma Shugaba Buhari kuma ministan albarkatun mai yana ɗaukar lamarin da gaske, kuma yana tuntuɓar kowa da kowa a ɓangaren samar da mai.

    A cewarsa har yanzu, jami'an gwamnati na duban tsanaki kan yadda za a cire tallafin ba tare da al'amuran raryuwa sun hargitse ba.

    Ya ce nauyi ne a kansu a matsayinsu na gwamnati, don haka tabbas sai sun kawo matakan da za su rage raɗaɗi kuma a samar da canjin ƙasashen waje ta yadda 'yan kasuwa za su iya samu cikin sauƙi don shigo da kayan da ake buƙata.

    Gabriel Aduda ya tabbatar da cewa sai sun samar da kuɗaɗen canjin waje na aƙalla wata shida ta yadda ko an samu akasi, rayuwa ba ta tagayyara ba.

  10. Idin 2023: Musulmai a faɗin duniya na bikin kammala azumin watan Ramadan

  11. An kashe mutum goma 'yan gida ɗaya a wani harin bindiga cikin Afirka ta Kudu

    An harbe mutum goma 'yan gida ɗaya bayan wani rukunin mutane sun kutsa kai gidansu a birnin Pietermaritzburg cikin lardin KwaZulu-Natal a Afirka ta Kudu.

    'Yan sanda sun ce 'yan bindigar sun shiga gidan ne inda mata bakwai da maza uku suka taru kuma suka buɗe musu wuta.

    Babu bayanai a fayyace kan abin da harzuƙa kisan kan.

    Ministan 'yan sanda Bheki Cele da sauran manyan jami'ai daga rundunar 'yan sandan Afirka ta Kudu sun kai ziyara gidan da aka kai harin.

    Wannan ne karo na biyu da ake kashe ɗumbin mutane a KwaZulu-Natal a cikin wannan mako bayan an hallaka mutum huɗu ranar Alhamis a wani gida da ke KwaMashu, arewa da birnin Durban mai tashar ruwa.

  12. Ga wasu hotunan Musulmi a lokacin Sallar Idi daga Masallacin Idi na Kubwa a Najeriya

  13. Jirgin yaƙin Rasha ya yi kuskuren luguden wuta a kan wani birnin ƙasar

    Ma'aikatar tsaron Russia ta ce wani jirgin yaƙinta ya buɗe wuta tare da raunata wasu mata biyu da kuma lalata gine-gine da dama a birnin Belgorod bisa kuskure.

    Belgorod dai na kan iyakar Russia da Ukraine.

    Gwamnan jihar Vyacheslav Gladkov ya ce luguden wutar da jirgin ya yi ya tona wani ƙaton rami mai zurfin mita 20 a tsakiyar birnin.

    Sanarwar da ma'aikatar tsaron Russia ta fitar ta nuna cewa jirgin yakinta na Sukhoi Su-34 ya yi kuskuren buɗe wuta da wasu makamai, to amma sanarwar ba ta bayyana irin makaman ba aka harba ɗin ba.

  14. Dakarun RSF sun ba da sanarwar tsagaita wuta

    Dakarun rundunar kai ɗaukin gaggawa ta RSF da ke yaƙi a Sudan sun sanar da tsagaita wuta tsawon kwana 3 domin bada dama ga ayyukan jin ƙai.

    Lokacin ya fara ne daga karfe shida na safiyar Juma'a agogon Sudan.

    Tun da farko kafin wannan sanarwar, babban birnin ƙasar, Khartoum ya sha luguden bama-bamai da tsakar dare.

    Majalisar Ɗinkin Duniya da Amurka da wasu ƙasashen duniya sun buƙaci dukkan ɓangarorin sojin da ke faɗa a Sudan su mayar da wuƙa kube ko don bukukuwan sallah.

    Wakiliyar BBC ta ce.dubban mutane sun maƙale a gidajensu babu abinci, kuma babu ruwa, ala tilas wasu sun tafi Kogin Nilu

    Kawo yanzu sama da mutume 300 ne suka mutu a yaƙin da aka shafe kwana shida ana gwabzawa.

  15. Barkanmu da Sallah

    Mukhtari Adamu Bawa ke muku fatan kun sauko daga Idin Ƙaramar Sallah, da fatan Allah ya mamaita mana.

    Idan kuka kasance da mu a wannan shafi tsawon wannan rana ta Juma'a, za mu kawo muku labarai da rahotanni na abububuwan da ke faruwa a Najeriya da maƙwabtan ƙasashe har ma daga sauran sassan duniya.