Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Buhari ya saka tubalin ginin sabuwar hedikwatar Ecowas

Wannan shafi na kawo maku labaran abubuwan da suke faruwa a Najeriya da wasu sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Abdullahi Bello Diginza and Umar Mikail

  1. Ƙarshen rahotannin ke nan

    Nan muke ƙarƙare rahotanni a wannan shafi na kai-tsaye. Don ganin rahotannin da muka kawo a yau Lahadi, ku duba ƙasan shafin.

    Mu haɗu da ku gobe don samun wasu sabbi daga sassan duniya.

    Umar Mikail ke muku fatan alheri.

  2. Dubban 'yan Congo na zanga-zangar adawa da 'yan tawayen M23

    Dubban mutane ne a Jamhuriyyar Dimokraɗiyyar Congo ne suka shiga zanga-zangar nuna adawa da ƴan tawayen M23.

    Kungiyar M-23 na daga cikin gwamman ƙungiyoyin ƴan tawaye da ke rikici a gabashin ƙasar.

    Cocin Katolika ta ƙasar ce ta yi kira ga mutane da su fita zanga-zanga bayan addu'o'in ranar Lahadi.

    Congo na zargin Rwanda da goyon bayan ƴan tawayen, kodayake Rwandar ta musanta zargin.

    Wakilin BBC ya ce wasu daga cikin shugabannin cocin na kira ga ƙasashen Yamma da su ɗauki tsauraran matakai kan Rwanda sakamakon goyon bayan ƴan tawayen na M23.

    Rikici tsakanin sojojin Congo da mayaƙan tawayen ya ƙara tsanani a 'yan watannin nan, inda lamarin ya yi sanadin raba kusan mutum 400,000 da muhallansu.

  3. Masu zanga-zanga kan tsadar rayuwa sun kashe ɗan sanda a Syria

    Rahotanni daga Syria na cewa an kashe wani ɗan sanda da farar hula bayan gwamman masu zanga-zanga sun afka ofishin gwamna a kudancin birnin Sweida.

    Waɗanda suka shaida lamarin sun ce masu zanga-zangar sun fusata ne sakamakon hauhawar farashin kayayyaki da kuma ƙaruwar cin hanci, wanda hakan ya sa suka cinna wa gidan gwamnan wuta.

    Wakilin BBC ya ce tun da farko kusan masu zanga-zanga 200 ne suka taru a tsakiyar birnin, inda suke kira da shugaban ƙasar Bashar al-Assad ya sauka daga mulki.

  4. Yadda Buhari ya saka tubalin ginin sabuwar hedikwatar Ecowas a Abuja

    Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ƙaddamar da tubalin ginin sabuwar hedikwatar Ƙungiyar Raya Tattalin Arziƙin Ƙasashen Afirka ta Yamma, Ecowas a Abuja babban birnin ƙasar.

    Shugabannin ƙasar Guinea Bissau Umaro Embaló, da na Saliyo Julius Maada Bio, da Shugaban Ecowas Omar Alieu Touray, da Jakadan China a Najeriya Cui Jianchun, su ne suka taya Buhari saka ɗambar ginin a yau Lahadi.

    Ana sa ran kammala sabuwar hedikwatsar a shekara ta 2025.

    Shugaba Muhammadu Buhari ya ayyana cewa hamshaƙin ginin, wanda gwamnatin China ta samar da kuɗin ginawa, zai ƙarfafa zumunci a tsakanin ƙasashen Afirka.

    Ginin zai kuma wakilci al'ummar Afirka ta Yamma mutum miliyan 380 sannan zai kasance matsuguni ga manyan cibiyoyin Ecowas uku, ciki har da ginin hukumar gudanarwar ƙungiyar da Kotun Ecowas, har ma da Majalisar Dokokin Ecowas.

    A gefe guda kuma, shugabanin mambobin ƙungiyar na gudanar da taro karo na 62.

  5. Osinbajo ya isa Vietnam

  6. Ba za mu sauya matakin rage yawan fetur a kasuwar duniya ba - OPEC

    Ƙungiyar ƙasashe masu arzikin man fetur da ƙawayenta ta OPEC+ ta amince da ci gaba da rage yawan gangar mai miliyan biyu daga kasuwar duniya duk rana.

    Ƙungiyar ta sanar da matakin a yau Lahadi bayan kammala taronta karo na 34 ta bidiyo, wanda ministocin ƙasashen suka halarta.

    Matakin na zuwa ne kwana ɗaya bayan ƙasashen ƙungiyar G7 - mafiya girman tattalin arziki a duniya - sun ƙayyade farashin dala 60 kan kowace ganga ɗaya na man Rasha.

    A ganawar da suka yi kafin yanzu, OPEC+ ta amince ta rage yawan man daga kasuwa da ganga miliyan biyu a kullum duk da kiraye-kirayen da Amurka ta dinga yi na kar ta yi hakan.

    Ƙungiyar mai mamba 13 ta ce ba za ta janye matakin ba, "wanda aka ɗauka bayan lura da kasuwar a lokacin don ɗaukar matakin da ya zama dole da zimmar daidaita kasuwar fetur a duniya".

    OPEC ta sha nanata cewa ba za ta ɗauki ɓangare ba a yaƙin da Rasha, wadda mamba ce, take yi da Ukraine tana mai cewa ba ƙungiyar siyasa ba ce.

  7. Neymar zai buga wasan Brazil da Koriya ta Kudu

    Kocin Brazil Tite ya tabbatar da cewa Neymar zai buga wasansu da Koriya ta Kudu a zagaye na biyu na gasar cin kofin duniya da Qatar ke daukar bakunci.

    Dan wasan mai shekaru 30 bai buga wasanni biyu a jere na Brazil ba, saboda raunin da ya ji a wasansu na farko da Serbiya.

    Brazil wacce ake ganin za ta iya lashe gasar ta zama ta farko a rukunin G duk da cewa ta sha kashi a hannun Kamaru a wasansu na karshe na zagayen farko.

    Tite ya ce "Neymar ya yi atisaye a yau kuma zai iya buga wasanmu na ranar Litinin".

    Dan wasan PSG din ya wallafa a shafinsa na Twitter cewa a yanzu ya samu sauki.

  8. Yaƙin Ukraine zai ragu a cikin watannin hunturu - Amurka

    Hukumar tattara bayanan sirri ta Amurka ta ce yaƙin da ake yi a Ukraine na raguwa kuma zai ci gaba da raguwa a watannin hunturu masu zuwa.

    Daraktar hukumar Avril Haines ta ce duka ɓangarorin da ke yaƙi da juna a yanzu sun fara sassautawa.

    Hakan na zuwa ne bayan da Rasha ta ƙaddamar da hare-hare kan tashar lantarkin Ukraine.

    A yanzu yaƙin na cikin wata na tara, a baya-bayan nan kuma Rasha ta rasa iko da wasu yankunan da a baya ke hannunta.

    Misis Haines ta shaida wa ma'aikatar tsaro a California cewa a yanzu an yi fi kai hare-hare a yankunan Bakhmut da Donetsk da ke gabashin Ukraine.

  9. Ambaliyar ruwa ta kashe masu ibada tara a Afirka ta Kudu

    Mutum tara sun mutu yayin da takwas suka ɓace sakamakon ambaliyar da wani kogi ya yi, inda ya tafi da masu bauta a wani coci.

    Shaidu sun ce fiye da masu bauta 30 ne ke tsaye a kan duwatsun da ke kusa da kogin lokacin da ruwan mai gudun gaske ya ratso ta inda suke.

    Shaidar ta ƙara da cewa an tsamo Faston da ke jagorantar ibadar bayan da ya maƙale cikin tarin bishiyoyin da ruwan ya taho da su.

    Masu aikin ceto da suka haɗar da 'yan sanda da jami'an kiyaye aukuwar bala'i na ci gaba da nemo waɗanda ruwan ya tafi da su.

    Robert Mulaudzi mai magana da yawun ma'aikatar bayar da agajin gaggawa ta ƙasar ya ce sun samu gawa biyu ranar Asabar, tare da ceto mtum ɗaya wanda ya ce an kai shi asibiti domin kula da lafiyarsa.

  10. Hikayata 2022: Labarin "Tsoro"

    A wannan makon mu fara kawo muku labarai 12 da alkalan gasar Hikayata suka ce sun cancanci yabo a gasar ta bana.

    Labarin na yau shi ne mai taken ‘Tsoro’ wanda Fatima Abdullahi da ke Layin Sarki gida mai lamba 4 da ke Dibanguba Crescent, Mando Kaduna ta rubuta, kuma Halima Umar Sale ta karanta.

  11. Buhari na ganawa da shugabannin ƙasashen ƙungiyar ECOWAS

    Shugabanin ƙasashe mambobin ƙungiyar tattalin arzikin ƙasashen Afirka ta yamma na gudanar da taron ƙungiyar karo na 62 a Abuja babban birnin Najeriya.

    A wani saƙo da mai taimaka wa shugaban Najeriya kan kafofin sadarwa na zamani Bashir Ahmad ya wallafa a shafinsa Tuwita ta ce shugabannin za su tattauna batutuwan da suka shafi tsaro da siyasa da tattalin arzikin ƙasashen ƙungiyar.

    Tuni dai shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ƙaddamar da aikin ginin sabon sakatariyar ƙungiyar a Abuja babbarn birnin Najeriya

  12. An sake kai hari ofishin INEC a jihar Imo

    Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Najeriya ta tabbatar da kai hari kan ofishinta da ke ƙaramar hukumar Oru ta yamma a jihar Imo da ke kudu maso gabashin ƙasar.

    A wani sako da hukumar ta wallafa a shafinta na Tuwita ta ce an kai harin ne da misalin ƙarfe 4:00 na asubahin ranar Lahadi.

    Hukumar ta ce harin ya shafin babban ɗakin taro na ofishin tare da lalata kujeru da sauran kayyaki a ɗakin taron.

    A 'yan kwanakin nan dai ana samun yawaitar hare-hare kan ofisoshin hukumar a ƙananan hukumomin jihar.

    A ranar Asabar ma dai rundunar 'yan sandan jihar Imo ta ce dakarunta sun samu nasarar daƙile wani hari da wasu 'yan bindiga da ake zargin 'yan kungiyar IPOB ne tare da wata ƙungiya mai ƙawance da ita da ake kira Eastern Security Network, da aka fi sani da ESN suka kai kan ofishin hukumar zaɓe na ƙaramar hukumar Orlu da ke jihar.

    Hukumar ta ce wannan shi ne hari na bakwai kan ofisoshinta a jihohi biyar cikin wata huɗu.

  13. Iran ta aiwatar da hukuncin kisa kan jami'an leƙen asirin Isra'ila

    .

    Iran ta ce ta zartar da hukuncin kisa kan wasu mutum huɗu waɗanda ta zarga da aikin leken asiri ga ƙasar Isra'ila.

    Kafofin yaɗa labaran ƙasar sun ce an aiwatar da hukuncin kisan da safiyar yau Lahadi.

    A watan Mayu, dakarun juyin juya hali na ƙasar suka ce sun kama wasu mutane da suka zarga da sata da garkuwa da mutane da kuma kwace.

    Ƙasashen Isra'ila da Iran sun kasance maƙiyan juna, inda Iran ɗin ke goyon bayan ƙungiyoyin da ke adawa da Isra'ila irin su Hezbollah da Hamas.

  14. 'Yan sanda sun kama matar da ta binne jaririn da ta haifa a Jigawa

    Rundunar 'yan sanda ta jihar Jigawa ta ce jami'anta sun kama wata mata mai suna Balaraba Shehu da ke ƙauyen Tsurma a ƙaramar hukumar Kiyawa bisa zargin binne sabon jaririn da ta haifa a ban ɗaki.

    Yayin da yake tabbatar wa da BBC faruwar lamarin, mai magana da yawun rundunar 'yan sandan jihar DSP Lawan Shiisu Adam ya ce sakamakon bayanan sirrin da rundunarsu ta samu ne ya kai su ga gano matar tare da tono jaririn a ban ɗakin gidan.

    ''Bayan haihuwar ta ne sai ta shiga ban ɗaki ta haƙa rami a kusa da masai ta binne jaririn''

    Ya ce bayan tono jaririn ne aka garzaya da shi babban asibitin Dutse inda likitoci suka tabbatar da cewa ya rasu.

    DSP Shiisu Adam ya ce matar ta sanar da su cewa ta samu cikin ne ba ta hanyar aure ba, ta kuma bayyana wani saurayinta mai suna Ahmadu Sale wanda aka fi sani da 'Dan kwairo' da ta ce shi ne ya yi mata cikin,.

    Kawo yanzu dai matar mai shekara 30 tare da saurayin nata mai shekara 25 suna hannun jami'an 'yan sanda.

    Tuni kwamishinan 'yan sandan jihar ya bayar da umarnin mayar da batun zuwa shalkwatar cibiyar binciken manyan laifuka ta rundunar da ke babban birnin jihar Dutse.

  15. Wane ne tsohon shugaban China Jiang Zemin?

    Shirin na wannan makon wanda Nabeela Muktar Uba ta gabatar, ya amsa tambayar da aka yi kan tarihin tsohon shugaban China Jiang Zemin, da kuma tambaya game da ciwon sanyi

  16. Peter Obi ya bayyana manufofinsa

    Ɗan takarar Shugabancin Najeriya ƙarkashin Jam'iyyar Labour, Peter Obi ya bayyana ƙudurorin da zai mayar da hankali a kansu idan ya samu nasarar lashen zaɓen shugaban ƙasar da ke tafe a shekara mai zuwa.

    Mista Obi ya bayyana ƙudurorin nasa mai shafi 72 a shafinsa na Tuwita ranar Lahadi da safe.

    Wanda ya yi wa take da ''Abu ne mai yiyuwa: Yarjejeniyarmu da 'yan Najeriya'

    Cikin ƙudurorin nasa, tsohon gwamnan na jihar Anambra ya lissafo batutuwa bakwai da ya ce gwamnatinsa za ta mayar da hankali a kan su idan aka zaɓen shi a matsayin shugaban ƙasar a zaɓen 2023.

    Ƙudurorin sun haɗa da kawo ƙarshen ayyukan 'yan fashin daji, da masu tayar da ƙayar baya, sannan da kawo gagarumin sauyi a fannin shari'a ta yadda doka za ta yi aiki a kan kowa.

    Haka kuma daga cikin manufofin nasa mista Obi ya ce zai gina manyan abubuwan more rayuwa na zamani domin samar da wadatacciyar wutar lantarki, sannan kuma ya alƙawarta bunƙasa fannin sufurin jiragen ƙasa da na sama da kuma titunan mota.

    A 'yan kwanakin baya-bayan nan dai ɗan takarar na fuskantar suka kan rashin bayyana manufofin nasa, musamman daga jam'iyyun hamayya.

    A watan Okbota Mista Obi ya nesanta kansa daga wasu manufofi da aka danganta shi da su.

    Inda ya ce zai bayyana manufofin nasa ga al'umma da zarar sun kammala.

  17. An buɗe tsohon babban birnin Saudiyya domin masu yawon buɗe ido

    A yau ne a karon farko ake sake buɗe tsohon babban birnin masarautar Saudiyya na farko wato 'At - Turaif'.

    Za a buɗe tsohon birnin - wanda ke yankin Diriya a wajen Riyadh babban birnin ƙasar na yanzu - domin ziyarar jama'a tun bayan da aka sake raya garin.

    Garin na 'At- Turaif' mai fadoji da masallatai da gidaje na ƙasa, a nan ne aka fara kafa gidan sarautar da ke mulkin Saudiyya a yau, sama da shekara 250.

    Gwamnatin Saudiyyar na fatan sake gyara birnin da ta yi tare da buɗe shi ga jama'a zai bunƙasa mata harkar yawon bude idanu.

    Haka kuma garin na daga cikin wuraren tarihi da Hukumar Raya Al'adu ta Majalisar Ɗinkin Duniya UNESCO ta sanya a matsayin wuraren tarihi na hukumar.

  18. Iran na shirin rushe Rundunar Hizbah ta ƙasar

    Babban lauyan gwamnatin Iran, Mohammad Jafar Montazeri ya ce hukumomin kasar na shirin rushe rundunar 'yan Hisbah ta kasar.

    An samar da jami'an ne domin tabbatar da bin tsarin sanya tufafi na Musulunci.

    Kasar Iran dai na fama da mummunar tarzomr ƙin jinin gwamnati tun bayan da wata matashiya mai shekara 22, Mahsa Amini ta rasu a hannun 'yan sanda.

    An kama ta ne bisa zargin ƙin ɗaura dan kwalinta ko hijabi yadda ya kamata.

    Babban lauyan gwamnatin ƙasar ya kuma ce majalisar dokoki da kuma ɓangaren shari'a na ƙasar suna sake nazarin dokokin sanya tufafin.

    Tun a shekarar 1983 ne dai aka yi dokar tilasta wa mata sanya hijabi a kasar.

  19. Maraba

    Masu bibiyarmu a wannan shafi barkanmu da hutun ƙarshen mako a wannan safiya ta Lahadi.

    Abdullahi Bello Diginza ke fatan kun tashi lafiya.

    Ku ci gaba da kasancewa tare da mu domin kawo muku labarai da rahotonnin abubuwan da ke faruwa a Najeriya da ma sauran sassan duniya.

    Haka kuma kuna iya ziyartar shafukanmu na sada zumunta domin tafka muhawara kan labaran da muke wallafa.