Masana harkokin dfplomasiyya
a Najeriya, sun fara tofa albarkacin bakinsu a kan wani furuci da tsohon
shugaban kasar, Cif Olusegun Obasanjo ya yi cewa tasirin Najeriya a duniya yana
raguwa, musamman ma a kan kasashen nahiyar Afirka.
Wasu masana na
ganin cewa akwai gaskiya a cikin maganar, suna danganta lamarin da rashin ƙwararrun masu ba da shawara
ga shugabanni da kuma rashin aiki da ita idan an ba su.
Tsohon shugaban
Najeriya Cif Olusegun Obasanjo, ya yi wannan furucin ne a wajen wani bikin ƙaddamar da littafi a kansa, musamman ma yadda ya shahara
wajen rubuta wa shugabannin Najeriya wasikar bankada ko tonun silili.
Ya ce tasirin
kasar na fada a ji da kuma dadadden kallon da ake mata na babbar Yaya, kuma
rumfa sha shirgi na ci gaba da raguwa musamman ma a kan kasashen nahiyar
Afirka, sakamakon gazawa ko rashin tabuka abin kirki wajen jagorantar kannen
nata.
Cif Obasanjon
ya buga misali da wata gazawa da ya ce Najeriya ta yi wajen daidaita
tsakanin shugabanni da ƴan tawaye a kasar Chadi - lamarin da sai da ƙasar Qatar
ta dako gari daga nahiyar Asiya ta je ta shiga tsakani.
Tuni dai wasu
masana huldar jakadanci suka fara tofa nasu albarkacin bakin a kan wannan
maganar.
Ambasada Sulaiman
Dahiru, tsohon jakadan Najeriya ne, wanda ya ce duk da cewa Cif Obasanjo kan ji
babu wanda ya yi komai in ba shi ba…a wannan ɓigiren ya fadi gaskiya.
Sai dai na
tambayi Ambasada Sulaiman Dahiru ko da wani abu da Najeriyar za ta yi don mai
da martabar tata ta jagora ga kasashen nahiyar Afirkan?
A shekarun baya,
an yi zamanin da Najeriya ta yi tasiri a kan kasashen Afirka da wasu kasashen
duniya, musamman irin rawar da ta taka wajen yaki da nuna launin fata a kasar
Afirka ta kudu da wasu makwabtanta.
Akwai ma lokacin
da kasa irin Amurka ba ta daukar wani mataki a kan Afirka sai ta nemi shawarar
Najeriya.