Mu kwana lafiya
Nan za mu dakata da kawo rahotannin a wannan shafi a yau Asabar.
Ku duba ƙasa don karanta labaran da muka wallafa, kafin mu ɗora da wasu sababbi gobe da safe.
Umar Mikail ke cewa mu zama lafiya.
Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Wannan shafi na kawo muku labarai kai-tsaye kan abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.
Abdullahi Bello Diginza and Umar Mikail
Nan za mu dakata da kawo rahotannin a wannan shafi a yau Asabar.
Ku duba ƙasa don karanta labaran da muka wallafa, kafin mu ɗora da wasu sababbi gobe da safe.
Umar Mikail ke cewa mu zama lafiya.
Tawagar ƙwallon ƙafa ta Faransa mai riƙe da Kofin Duniya ta zama ta farko da ta samu nasarar zuwa zagaye na gaba a gasar bayan ta lallasa Denmark 2-1.
Tun a jiya Juma'a Qatar mai masaukin baƙi ta zama ƙasa ta farko da aka yi waje da ita daga gasar.
Kylian Mbappe ne ya ci wa Faransa ƙwallayen, inda mai tsaron bayan Denmark Andreas Christensen ya ci wa ƙasarsa ɗaya.
Kazalika, a ɗazu an yi gumurzu tsakanin Saudiyya da Poland inda Poland ɗin ta doke Saudiyya 2-0.
Haka kuma an fafata tsakanin Australiya da Tunisiya a wasan da Australiyar ta yi nasara da 1-0 .
A halin yanzu dai ana karawa ne tsakanin Argentina da Mexico a wasan Rukuni na C.
'Yan bindiga sun kashe mutum biyu masu gadi a yankin Ikare Akoko na Jihar Ondo da ke kudancin Najeriya.
Rahotanni sun ce lamarin ya faru ne da tsakar dare ranar Juma'a a wurare daban-daban da suka haɗa da Kasuwar Mimiko da kuma makarantar NASFAT.
An bayyana cewa an yanki ɗaya daga cikin masu gadin a ka, sannan kuma aka yanki ɗayan a hannu amma ba a ciri wani sassa na jikinsu ba.
Tuni 'yan kasuwa suka ƙaurace wa kasuwar ta Mimiko wadda a nan ne aka ga gawar mutum ɗaya.
'Yan sanda sun kwashe gawarwakin zuwa mutuware, yayin da suka ƙaddamar da bincike kan lamarin.
Shugaba Tsai-Ing-Wen ta Taiwan ta yi murabus daga jagorancin jam'iyyar Democratic People's Party (DPP) mai mulki, tana mai cewa ta ɗauki alhakin rashin taɓuka abin kirki a zaben ƙasar.
Ƙoƙarin da ta yi na neman ƙuri'un jama'a ta hanyar bijire wa ƙarin barazanar da China ke yi wa tsibirin nasu da sojoji bai sa masu kaɗa ƙuri'a sun zaɓi jam'iyyarta ba.
Ofishin harkokin cikin gida na Taiwan ya ce sakamakon zaɓen ya nuna ainahin ra'ayin jama'ar Taiwan, abin da suke so shi ne zaman lafiya da kwanciyar hankali.
Chiang Wan, wanda jikan jika ne ga shugaban Taiwan na farko, shi ne zai zama magajin garin Taipei babban birnin ƙasar.
Tuɓaɓɓen Firaministan Pakistan Imran Khan ya yi wa dubun-dubatar magoya bayansa jawabi a karon farko tun bayan jikkata shi da aka yi da harbin bindiga mako uku da suka wuce.
Dandazon jama' sun taru a birnin Rawalpindi ɗauke da tutoci da kwalaye don yin maci.
Tsohon ɗan wasan kirket ɗin ya buƙaci magoya bayan nasa da su yi rayuwa ta 'yanci "ba tare da fargabar kisa ba".
An kashe mutum ɗaya tare da raunata wasu da dama yayin harin a farkon watan nan daidai lokacin Mista Khan ke jagorantar maci.
An harbi tsohon firaministan a ƙafa kuma aka yi masa tiyata. Ya zargi jami'an gwamnatin da ke ci a ƙasar da yunƙurin kai masa harin a Wazirabad.
Shirin Gane Mini Hanya na wannan makon ya tattauna da Gwamnan Gombe Muhammadu Inuwa Yahaya game da shirinsu na haƙo man fetur a jihohin Bauchi da Gombe.
Yayin da babban zaɓe na 2023 ke ƙaratowa a Najeriya, hukumar zaɓe ta Independent National Electoral Commission (INEC) ta hana 'yan siyasa yaƙin neman zaɓe a masallatai da coci-coci.
Hanin na cikin kundin ƙa'idojin kamfe da INEC ta fitar a ranar Alhamis game da yadda jam'iyyu da 'yan siyasa za su gudanar da yaƙin neman zaɓuka da kuma adadin kuɗin da za su iya kashewa.
"Kar a yi yaƙin neman zaɓe a wuraren ibada, da ofisoshin 'yan sanda da kuma ofisoshin gwamnati," a cewar INEC.
Kazalika, kundin ya ce "kar a yi amfani da kalaman ɓatanci ko kuma kalaman ƙiyayya yayin yaƙin neman zaɓe".
Bugu da ƙari, "kar wani mutum ya ɗauki makami zuwa wurin taron kamfe ko kuma maci".
Shugaban kamfanin sojojin haya na Rasha mai suna Wagner ya ce wani tsohon janar na zaratan sojojin Amurka na aiki da kamfanin a yaƙin da Rasha ke yi da Ukraine.
Yevgeny Prigojin (Prigozhin) ya yi ikirarin cewa tsohon janar ɗin wanda bai bayyana sunansa ba, yana jagorantar wata runduna da ya kira Rundunar Birtaniya (British Battalion).
Ana ganin kamfanin sojin hayar na ɗanɗana kuɗarsu a yaƙin da Rashar ke yi a wasu sassan gabashin Ukraine, musamman ma a kusa da fagen dagar Bakhmut da ke yankin Donetsk.
Mista Prigojin (Prigozhin) ya bayyana wannan labari ne a yayin wata hira da jaridar Helsingin ta kasar Finland.
Asusun kula da ƙananan yara na Majalisar Ɗinkin Duniya ya ce mummunan fari da ba taɓa gani ba cikin gomma shekaru ya jefa miliyoyon yara cikin matsalar rashin abinci da ruwan sha a ƙasar Ethiopia.
A wani saƙo da UNICEF ɗin ya wallafa a shafinsa Tuwita ya ce da yawa daga cikin yaran na cikin hatsarin mutuwa sakamakon cutar cutar Tamowa.
Yankin gabashin Afirka na fama da mummnan farin da ba a taɓa gani ba cikin gwamman shekaru, bayan da aka kwashe damina biyar ba tare da samun girbe amfanin gona ba.
Lamarin da ya shafi mutane da dama tare da asarar dabbobi masu yawa, sakamakon rashin abinci da ruwan sha.
Cutar sanyi ta Candidiasis na ɗaya daga cikin cututtukan da ke janyo kaikayi a al’aurar mata, musamman ma a tsakanin mata masu ciki.
Sai dai rashin tsafta na daga cikin manyan abubuwan da masana a fannin kiwon lafiya suka ce yana janyo cutar sanyin.
Wasu ƙarin dalilan da ke janyo wa mata samun cutar sanyin ta Candida, sun haɗa da ciwon suga da yin amfani da magungunan kashe kwayoyin cuta fiye da kima da wasu magungunan hana ɗaukar ciki da samun juna biyu.
Haka zalika wasu daga cikin alamomin cutar su ne ƙaiƙayin gaba da kuraje da zafi lokacin fitsari da zafi lokacin saduwa da zafi a mara.
Wannan batu shi ne shirinmu na Lafiya Zinaya ya tattauna a wannan makon, sai ku latsa hoton da ke ƙasa domin sauraron cikakken shirin
Ana fargabar mutane da dama sun mutu bayan ruwa yayi awon gaba da gidajensu sakamakon mamakon ruwan sama a tsiburin Ischia na ƙasar Italiya.
An ga ɓaraguzan gine-gine da bishiyoyi da kananan motoci tare da sauran tarkace ruwa na gudu da su cikin kogi a ranar Asabar.
Wata mace mai shekara 25 tare da iyalanta ciki har da sabon jaririnta na daga cikin waɗanda rahotonni ke cewa sun ɓace.
Magajin garin Lacco Ameno ɗaya daga cikin garuruwan da ke tsiburin, ya ce har yanzu ba a san inda gomman iyalai suke ba, yayin gine-gine da dama suka ruguje. Haka kuma rahotonni sun ce mutane da dama na maƙale a cikin wani otal da ke tsiburin.
An dai yi gargaɗin cewa yanki zai fuskanci mamakon ruwan sama haɗe da iska mai ƙarfi har zuwa ranar Lahadi.
Jami'an yankin sun umarci mazauna tsiburin da su zauna a gidajensu, domin kauce wa rashin samun taimakon gaggawa idan buƙatar hakan ta taso.
Likitan tawagar ƙwallon ƙafa ta Brazil ya ce fitaccen ɗan wasan tawagar ƙasar Neymar ba zai buga karawa biyu da suka rage na cikin rukuni ba, sakamakon raunin da ya ji a idon sawu.
An cire ɗan wasan mai shekara 30 a minti na 80 a fafatawar da ƙasar ta ci Serbiya da ci 2-0.
Ɗan wasan ya bayyana raunin da ya ji a matsayin 'ɗaya daga cikin abu mafi wahala a rayuwarsa ta ƙwallon ƙafa'
"Babu abin da ya zo min da sauƙi a rayuwata a kodayaushe ina ƙoƙarin cimma burina na cin ƙwallaye '', kamar yadda ɗan wasan ya rubuta a shafinsa na Instagram.
"Ban taɓa yi wa wani mummunan fata ba, a kullum ina taimakon mai buƙatar taimakona''.
''Na ji rauni, haƙiƙa babu daɗi, to amma ina da tabbacin cewa zan samu sauki domin dawowa fili, zan yi duk mai yiyuwa domin taimaka wa ƙasata, da abokan wasana, da kuma kaina''.
Dan wasan na PSG ya sha fama da jinyar idon sawu a ƙafarsa ta dama a 'yan shekarun da suka gabata.
A shekarar 2019 ma bai buga gasar Copa America ba, bayan da ya ji irin wannan ciwon, haka kuma a shekarar 2021 ma ya kwashe makonni yana fama da irin wannan jinya.
Tsohon sakataren jam'iyyar NEPU Alhaji M.K. Ahmed MFR, Sarkin Yakin Lokoja ya rasu bayan fama da doguwar jinya.
Alhaji M.K. Ahmed ya rasu a kano yana da shekara 90 a duniya.
Marigayin na daga cikin waɗanda aka yi gwagwarmayar kafa jam'iyyar NEPU da su a jamhuriya ta farko, ya kuma yi aiki kurkusa da Mallam Aminu Kano, inda har ya kai matsayin babban sakataren jam'iyyar na ƙasa.
Alhaji M.K. Ahmed shi ne kuma ya samar da ƙungiyar jin daɗi da walwalar alhazai na Najeriya.
Wani direban babbar mota ya kashe jami'an Hukumar Kiyaye Aukuwar Hadura ta Najeriya biyu a kan babbar hanyar Aba da ke kudancin ƙasar.
A wata sanarwa da hukumar ta fitar mai ɗauke da sannun babban jami'in wayar da kan jama'a na hukumar Bisi Kazeem, ya ce muƙaddashin babban shugaban Hukumar Dauda Ali Biu, ya bayyana damuwarsa game da kashe jami'an hukumar biyu, tare da alkawarta gurfanar da waɗanda suka yi sanadiyyar mutuwar jami'an a gaban kotu domin su fuskanci hukunci .
Sanarwa ta ce Mista Biu ya yi Allah wadai da wannan lamari da ya yi sanadiyyar mutuwar jami'an hukumar waɗanda ke bakin aikinsu, sakamakon abin da ya kira 'aikin direbobi masu tukin ganganci waɗanda ke ci gaba da karya dokar tuƙi'
Lamarin ya faru ne sakamakon ƙoƙarin kauce wa rami da direban babbar motar ya yi, yayin da yake tsaka da gudu a kan hanyar, kamar yadda sanarwar ta bayyana.
Jami'an hukumar FRSC dai sun daɗe suna zargin direbobin ƙasar da tukin ganganci tare da gudun wuce kima a kan titunan ƙasar, lamarin da hukumar ke cewa shi ne musabbabin mafi yawancin haduran da ke aukuwa a kan titunan ƙasar.
Hotunan bidiyo da aka yaɗa a shafukan sada zumunta sun nuna yadda sabuwar zanga-zangar adawa da kullen korona ta ɓarke a birnin Urumqi na ƙasar China.
Zanga-zangar ta ɓarke ne bayan da wata gobara da ta tashi a wani gini ranar Alhamsi ta kashe mutum 10 a birnin.
An ga masu zanga-zangar na fuskantar jami'an tsaro, yayin da suke karya shingayen da aka kafa tare da ihun ''a kawo ƙarshen kullen korona''.
To sai dai hukumomin birnin na Urumqi sun musanta zargin cewa dokar kullen ce ta hana mutanen kuɓucewa gobarar.
Birnin wanda ke yammacin ƙasar na cikin dokar kullen korona tun farkon watan Agusta.
Bayan kwashe shekaru da gwamantin Nejeriya ta dakatar da koyar da darasin Tarihi a makarantun firamare da ƙananan makarantun sakandire na ƙasar, gwamnatin ƙasar ta bayar da sanarwar sake dawo da koyar da darasin.
An ware malamai 3700 waɗanda za a bai wa zagayen farko na hararwa ta musamman domin inganta koyar da darasin.
To ko mene ne muhimmancin koyar da darasin tambayar kenan da Abokin aikina Muhammad Annur Muhammad ya yi wa Dakta Aliyu Tilde kwamishinan ilimi na jihar Bauchi.
Latsa hoton da ke ƙasa domin sauraron hirar tasu
Shugaba Rasha Vladimir Putin ya yi alƙwarin cewa Rasha ba za ta taɓa mantawa da sojojinta waɗanda ke filin daga da waɗanda suka mutu ba.
Mista Putin na wannan kalamai ne yayin da yake ganawa da uwayen sojojin da ƙasar da aka tura yakin Ukraine.
Ya gaya wa matan cewa yana jin zafi tare da waɗanda suka rasa ‘ya’yansu a yaƙin.
‘’Ina so ku sani cewa ni da kaina da gwamnatina muna jin zafin wannan rashi tare da ku, kuma mun san cewa ba a bin da zai iya maye gurbin rashin ɗa musamman ma ga uwa’’, in ji mista Putin.
Wannan dai shi ne karon farko da fadar gwamnatin Rasha ke ƙoƙarin nuna cewa shugaban Putin ya damu da sojojin da kuma iyalansu.
A ’yan kwanakin nan mataye da ‘yayansu sun riƙa sanya sakonni na bacin rai cewa an tura mazaje da ‘yayansu fagen daga ba tare da horo ko isassun kayyyakin yaki ba.
Hukumar kare haƙƙin bil adama ta Majalisar Ɗinkin Duniya a Afghaninstan ya ce matakan taƙaita walwala da ‘yancin mata da ‘yan mata da Taliban ke ɗauka ka iya zama laifin muzgunawa, wanda kuma hakan babban laifi ne a kan bil adama.
A wata sanarwa Ƙwararru a kan haƙkin ɗan adam na Majalisar Ɗinkin Duniya suka fitar sun ce sun lura da ƙaruwar abin da suka kira 'gagarumar' ƙaruwar take haƙkin bil adama a 'yan watannin nan inda suke cewa kular da ake bai wa mata tamkar a na mayar da su fursunoni ne.
Sun dai ‘yan Taliban sun ce suna mutunta hakkin mata ne daidai da yadda fahimtarsu take ga dokokin addinin musulunci.
Kasashen yammacin Duniya na son Taliban ta dawo daga rakiyar matakan da suke ɗauka game da haƙkin mata muddin suna so ƙasashen su yaiwaye su tare da amincewa da gwamnatin da suka kafa a Afghanistan.
Masu bibiyarmu a wannan shafi na BBC Hausa barkanmu da wannan safiya ta Asabar, da fatan mun wayi gari lafiya.
Ku kasance da mu a yinin yau domin karanta labarai da rahotanni kai tsaye na wasu abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.
Sunana Abdullahi Bello Diginza, kuma ni zan ja ragamar wannan shafi a daidai wannan lokaci.
Kuna iya ziyartar shafukanmu na sada zumunta domin tafka muhawa kan labaran da muke wallafawa.