Shugaban Hukumar Yaƙi da Cutar Sida (HIV) a Najeriya ya ce mutanen ƙasar 1.619,133 ke shan magungunan rage raɗaɗin cutar.
A lokacin wata tattaunawa da manema labaru ranar Alhamis, a Abuja, Gambo Aliyu ya ce hakan na nuna irin ci gaban da aka samu a ɓangaren yaƙi da cutar, kasancewar mutum 838,020 ne suke shan maganin a shekarar 2017.
Ya kuma ce yawan masu kamuwa da cutar ya ragu daga 103,404 a 2019 zuwa 92,323 a 2021.
Haka nan ya ce an samu ƙaruwar cibiyoyin kula da masu cutar daga 10 a 2017 zuwa 118 a shekara ta 2021, lamarin da ya sanya ya zuwa 2021 ake kula da sama da mutum 221,010.
Bayanan dai na zuwa ne gabanin ranar yaƙi da cuta mai karya garkuwar jiki ta duniya ta shekarar 2022.
Ministan lafiya na Najeriya Osagie Ehanire ya ce taken ranar ta wannan shekarar shi ne samar da dama ga kowa wajen kula da kuma kare yaɗuwar cutar.
Ya ce an fitar da taken ne a matsayin wani sabon yunkuri na taƙaita yaɗuwar cutar.