Mu kwana lafiya
Mun kawo ƙarshen rahotanni a wannan shafi.
Mu haɗe da ku gobe don kawo wasu sabbi daga sassan duniya.
Umar Mikail ke fatan za mu kwana lafiya.
Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Wannan shafin zai kawo muku labarai kai tsaye a kan abubuwan da ke faruwa a Najeriya, da yammacin Afirka da duk ƙasashen duniya.
Umaymah Sani Abdulmumin and Umar Mikail
Mun kawo ƙarshen rahotanni a wannan shafi.
Mu haɗe da ku gobe don kawo wasu sabbi daga sassan duniya.
Umar Mikail ke fatan za mu kwana lafiya.
Mutum aƙalla 13 aka kashe sakamakon harin da 'yan fashin daji suka kai a ƙauyen Karekuka na Jihar Taraba da ke tsakiyar Najeriya da tsakar ranar Juma'a.
Kazalika, an jikkata mutanen da ba a san adadinsu ba a harin waɗanda ke jinya yanzu haka a Cibiyar Lafiya ta Tarayya da ke birnin Jalingo, kamar yadda kakakin 'yan sanda na Taraba ya shaida wa BBC Hausa.
Tuni aka yi jana'izar mutanen a garin da ke cikin Ƙaramar Hukumar Gassol, akasarinsu kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.
'Yan sanda sun ce tun farko mutanen garin ne suka kama ɗaya daga cikin 'yan fashin bayan wani hari da suka kai kuma suka kashe shi, inda su kuma suka kashe mutum 13 a harin ramuwar gayya.
Sai dai wasu rahotanni na cewa 'yan bindigar sun sake yi wa Garin Gidado tsinke a safiyar yau Asabar amma sun tarar ba mutane a garin.
SP Abdullhi Usman ya ce an tura jami'an tsaro yankin don kwashe gawarwakin mutanen bayan harin.
'Yan sanda a Saudiyya sun kama wani mutum da ake zargi da hayaniya cikin jama'a wanda hakan ya ci karo da tarbiyyar al'ummar kasar.
Ministan cikin gida na Saudiyya ya wallafa wani bidiyo da ya karade shafukan sada zumunta, wanda ya nuna mutumin na janyo ayar Al-Ƙur'ani mai tsarki yana wa'azi kan cakuɗuwar mata da maza a wuri guda a kasar.
Wannan lamari dai ya janyo ce-ce-ku-ce a Saudiyya, inda jama'a da yawa ke kokawa kan yadda karatun Ƙur'ani a bainar jama'a ke neman zama wani abu da ya ci karo da al'ada.
A 'yan shekarun nan, maza da mata a Saudiyya na harkokinsu a cakude ba tare da ware wani jinsi ba kamar yadda ake yi a baya.
Shirin Gane Mani Hanya na wannan makon ya tattauna da ɗan takarar gwamna na Jihar Kaduna jam'iyyar PDP, Isa Ashiru.
Wata Babbar Kotun Jihar Akwa Ibom a kudancin Najeriya ta yanke wa wani mai unguwa hukuncin kisa ta hanyar rataya sakamakon samun sa da laifin kisa.
Kotun ta ba da hukuncin ne a ranar Juma'a bayan an tuhumi Chief Essien Matthew Odiong da laifi huɗu a ranar Juma'a, wanda shi ne mai unguwar Efen Ibom da ke Ƙaramar Hukumar Ika ta jihar, a cewar rahotanni.
Mai Shari'a Edem Akpan ya samu basaraken mai mata 12 da 'ya'ya 60 da laifin kisan Udoma Akpan Udo Ubom ta hanyar yi masa allura da wasu sinadarai a watan Afrilun 2017.
'Yan uwan marigayi Ubom ne suka zarge shi da maita kuma suka kai ƙararsa wajen mai unguwar, inda shi kuma ya gurfanar da shi a gaban majalisar mgabata ta unguwar tare da umartarsa da ya rantse cewa shi ba maye ba ne.
An faɗa wa kotun cewa mai unguwar ya gudu daga ƙauyen bayan aika-aikar a 2017 amma ya sake komawa a 2019, inda 'yan sanda suka kama shi.
Kimanin masu aikin ganyen shayi 150,000 ne suka tsunduma yajin aiki a Bangladesh, suna neman a kara musu kudin aikin da suke yi a kullum.
Wakilin BBC ya ce mafi karancin albashin da suke karba a kowacce rana bai fi dalar Amurka daya ba, kimanin naira 680.
Sai dai kungiyoyin ma'aikatan sun ce suna son a yi karin kashi biyu da rabi na albashin, amma masu gonakin da suke yi wa aiki sun ki amincewa da hakan, suna cewa za su kara dai abin da ya samu.
Kafofin yada labaran kasar sun ambato cewa ma'aikatan sun samar da kilo miliyan 96 da ganyen shayi a bara.
'Yan sandan gwamnatin Taliban sun tarwatsa mata masu zanga-zanga a birnin Kabul ranar Asabar.
Mata kusan 40 ne suka hau kan titunan birnin da zimmar neman ƙarin 'yanci ga mata kafin jami'an tsaro su tarwatsa su ta hanyar harbi cikin iska.
Tun bayan ƙwace mulki da Taliban ta yi, ƙungiyar ta rage wa mata 'yanci.
Dandazon mutane sun dinga ihun "burodi da aiki da 'yanci" ɗauke da kwalaye masu rubutun "15 ga watan Agusta baƙar rana ce" - wato ranar da mayaƙan Taliban suka kama birnin Kabul a 2021.
"Wannan karon ba su dake mu sosai ba," kamar yadda wata ta faɗa wa BBC.
Fari da ake ci gaba da fuskanta a kasashen Turai na haifar da cikas ga kamfanoni da dama, yayin da bangaren makamashi na yankin ke kara shiga cikin matsi.
Yanayi na rani ya jawo karfin samar da lantarki ta hanyar amfani da madatsun ruwa ya yi kasa da kashi 20 cikin 100.
A kasashen Italiya da Sifaniya da suka fi shan wahalar raguwar kwararan ruwa a kogunansu, sun rage yadda ake amfani da ruwan daga rafuka wajen sanyaya cibiyoyin sarrafa nukiliya.
A Birtaniya, masana sun ce an samu rauni kan yadda cibiyoyin samar da karfin wutar lantarki masu amfani da gas ke aiki saboda wahalar da ake sha wajen sanyaya na'urori.
Kazalika, su ma farantan samar da karfin wuta ta amfani da hasken rana sun rage abin da suke samarwa.
Hukumomin birnin tarayya, Abuja sun cafke wasu mutane 480 da ake zargin fursunoni ne da suka tsere daga gidan yarin kuje daga gine-ginen da ba a karasa ba da kangwaye a yankunan Maitama da Wuse II.
Shugaban jami'an kar-ta-kwana da ke farautar fursunonin, Mista Bennett Igweh, ya ce fursunoni da galibinsu maza ne sun mayar da kwangaye da gidajen da babu mutane da filaye maboya domin cigaba da aikata muggan laifuka.
Ya kuma kara da cewa jami'an sun kuma kama mutanen dauke da kakin 'yan sanda da wayoyin hannu da bindiga da aduna da wasu irin makamai.
Jami'in ya ce za su cigaba da kai wannan samame a matsugunai 21 na marasa karfi da suka hada da Kabusa da Gishiri da Waru da Wasa da sauransu da ke cikin garin Abuja.
Igweh ya ce sun alkawarta kawo karshen irin wadannan miyagu da ke haifar da barazanar tsaro a Abuja.
Jama'ar wasu manyan garuruwa uku, wadanda suka hada da Danbar-dikko da Danbar-Kwannawa da kuma Buwade, a karamar hukumar Illela ta jihar Sakkwato, na tserewa zuwa wasu garuruwan jihar, da kuma jamhuriyyar Nijar mai makwaftaka.
Sakamakon yawaitar hare-haren 'yan bindiga, wadanda sukan kona gidaje da dukiyoyi, kuma su sace mutane da dabbobi.
Honarabul Bello Isa Ambarura, mai wakiltar mazabar Illelar a majalisar dokokin jihar Sakkwato, ya yi wa BBC karin haske kan wannan matsala ta rashin tsaro.
Shugaban ƙasar Saliyo Julius Maada Bio ya ce boren kin jinin gwamnati da aka yi a ƙasar cikin wannan mako wani yunkuri ne na hamɓarar da gwamnatinsa.
Lokacin da ya ke jawabi a kafar talabijin ta kasar, ya ce gwamnati ta yi kokari sosai wajen yaki da tsadar rayuwa.
'Yansanda shidda da wasu fararen hula ne aka kashe lokacin zanga-zangar a ranar Laraba a lokacin da jami'an tsaro suka yi amfani da barkono mai sa hawaye da bindiga wajen tarwatsa masu zanga-zangar a Freetown babban birnin kasar.
Sama da mutum 100 ne aka kama tare da sanya dokar hana fita a cikin dare.
Ƙungiyar kwadago ta NLC a Najeriya ta nemi gwamnatin Tarayya ta kara albashin ma'aikata da kashi 50 cikin 100 lura da yanayin tsadar rayuwa.
NLC ta mika wannan bukata ga shugaba Muhammadu Buhari ta wasikar da ke dauke da sa hannun shugabanta Ayuba Wabba.
Wasikar ta yi tuni da cewa gwamnonin su suka karfafa batun janye tallafin mai, da kawo batun ritayan ma'aikatan gwamnati a shekara 50, da kuma rage kudaden da ake bai wa majaliasa domin aikin mazabu.
Ƙungiyar ta caccaki gwamnoni kan wadannan shawarwari, su na mai cewa duk wanda ya goyi bayan ra'ayinsu to ba shi da maraba da makiyin gwamnati.
NLC ta ce batun karin albashi ne abin da ya kamata a mayar da hankali a kai, domin a wannan lokaci shi ne mai muhimmanci.
Masu fafutikar dai na ganin akwai bukatar gwamnati take amfani da yanayin kasa da abubuwan da ke faruwa wajen fayyace albashi da samawa 'yan kasar sauki.
Mashahuran 'yan siyasa da marubuta a fadin duniya sun soki harin da aka kai wa Salman Rushdie - da yawan su suka ce wannan tamkar hari ne a kan fadin albarkacin baki.
Mai bayar da shawara kan tsaro na Amurka, Jake Sullivan ya ce abu ne maras dadi.
Firaministan Burtaniya Boris Johnson ya ce an far wa Salman ne a kan kudurinsa na aiwatar da 'yancinsa wanda kuma ya cancanci a ba shi kariya - shi ma shugaban Faransa Emmanuel Macron na da irin wannan ra'ayi.
Wani marubuci dan asalin Burtaniya Ian MacEwan ya ce harin tamkar an kai shi ne a kan 'yancin yin tunani da fadin albarkacin baki.
Ɗan takarar gwamnan jihar Kano a inuwar jam'iyyar PDP, Mohammed Abacha ya nemi babbar kotun Tarayya a Kano ta tilastawa hukumar zaɓe ta INEC tabbatar ma sa da takararsa.
Abacha ya kalubalanci hukuncin da ya tabbatar da cewa Sadiq Wali ne sahihin ɗan takarar PDP a Kano.
Mohammed Abacha ya ce shi ne ya lashe zaben fitar da gwamni da aka gudanar a ranar 25 ga watan Mayu wanda ya ce INEC ta tura wakilai domin sa ido, amma sai kuma aka musanya sunansa da Sadiq Wali.
Mai neman takarar na son kotu ta hana PDP da shugaban jam'iyyar na Kano gabatar da Wali a babban zaben da ke tafe a 2021.
Akwai dai rarabuwar kawuna tsakanin 'ya'yan jam'iyyar PDP da ke da tsagi biyu a Kano.
Wannan dalilin ne ya sa bangarorin da ke rikici da juna kowa ya gabatar da na shi zaben fitar da gwanin.
Abin da ya kai ga PDP ta samu 'yan takara biyu kafin daga bisani aka tabbatar wa da Sadiq Wali kujerar takara.
Sai dai Mohammed Abacha tun daga wannan lokaci ya ke kalubalantar matsayar jam'iyyar da maka batun a gaban kotu.
A cikin watan Satumba za a cigaba da sauraron karar.
Sanannen marubucin nan na Burtaniya Salman Rushdie na can a wani asibiti da ke Amurka an makala masa na'urar taimako wajen numfashi, bayan ya samu raunuka sanadiyyar harin da aka kai masa da wuka a birnin New York.
Wakiliyar BBC ta ce wakilin Sir Salman, Andrew Wylie ya ce Salman ya samu rauni a hantarsa, ba zai iya magana ba, kuma akwai yiwuwar zai rasa idonsa daya, yayin da kuma aka yi masa mummunar yanka a wani bangare na hannunsa.
Wani mutum ne dai ya rinka sossoka masa wuka a daidai lokacin da ya hau dandamali domin yin jawabi kan 'yancin fasaha a wata cibiyar zane-zane.
Salman Rushdie dai ya rinka fuskantar barazana ga rayuwarsa daga wadanda ake ma kallon masu tsattsaurar akidar musulunci tun a shekarar 1989, lokacin da tsohon jagoran Iran, marigayi Ayatollah Khomeini ya bayar da fatawar yin Allah-wadai da littafin da ya rubuta mai taken 'Satanic Verses', wanda ake ma kallon wani mummunan sabo.
'Yansanda sun ce sunan wanda ya kai wa Salman wannan hari Hadi Matar, daga jihar New Jersey.
Gwamnan Filato, Simon Lalong ya nemi afuwan mabiyan cocin Katolika kan kalamansa da suka jawo ce-ce-ku-ce lokacin da ya ke kare matsayar nadin da jam'iyyarsa ta APC ta yi ma sa.
Tun a ranar Talata aka soma wata takaddama tsakanin Gwamnan jihar Filato Simon Lalong da Mabiya addinin Kirista ‘yan darikar Katolika.
Hakan ya biyo bayan kalaman da gwamnan ya yi cewa Fafaroma Francis bai ga laifin karbar mukamin darakta-janar na kamfe din ɗan takarar shugaban kasa a APC, Bola Tinubu, da mataimakinsa Kashim Shettima, ba duk da cewa dukkansu Musulmai ne.
Kalaman sun fusata kiristoci mabiya katolika wadanda suka bayyana ambato sunan Fafaroma a zaman raini ga jagoran nasu.
Abin da ya kai ga sun bukaci a gaggauta dakatar da Lalong daga harkokin cocin.
Sai dai a wata wasika da ya aike wa cocin, Lalong ya amsa cewa ya yi kuskure don haka ya nemi a yafe ma sa, da alkawarta ci gaba da ayyukansa ta hanya mafi dacewa.
Gwamna Lalong ya ce bai yi wadannan kalamai ba domin muzanta kiristocin kasar.
Bayanai game da binciken da FBI ta gudanar a gidan tsohon shugaban Amurka Donald Trump ranar Litinin a Florida sun nuna cewa hukumar ta gano wasu takardu har kashi 11, wasunsu kuma dauke da bayanan tsantsar sirri na kasar.
Bayanan sun ce makasudin samamen na FBI shi ne kan zargin da ake wa Trump din da karya dokokin leken asiri na Amurka, wanda ya shafi ajiye takardu masu matukar muhimmanci ga kasa.
Wadanda ya kamata su kasance a wata ma'ajiya da ke karkashin gwamnati ita kadai.
Wakiliyar BBC ta ce FBI ta je Mar a Logo gidan tsohon shugaba Donald Trump, inda ta bincike dakuna kwana 58, da ban-daki 33.
Wani alkalin Amurka ne ya fallasa bayanan da ke kunshe a takardar, bayan da tsohon shugaban kasar ya ce ba zai hana a fitar da bayanan ba.
A martaninsa ta shafinsa na sada zumunta, Donald Trump ya ce, ya ajiye takardun ne a wata ma'ajiya mai tsaro, kuma a cewarsa zai iya mika su ga hukumar inda sun bukata cikin lalama, ba sai sun sanya siyasa cikin lamarin ta hanyar kai samame a gidansa ba.
Rundunar 'yan sandan Najeriya, reshen Jihar Legas, ta sallami wani jami'inta, Kofur Opeyemi Kadiri, saboda binciken wayar wani matafiyi.
Sanarwar da rundunar ta fitar ta ce an sallami kofur ɗin ne bayan na'urar daukar bidiyo ta nuna shi yana binciken wayar mutumin a gefen hanya wanda kuma hakan ya saba wa umarnin da Sufeto Janar na 'Yan Sanda Usman Alkali Baba ya bayar.
A cikin bidiyon, an jiyo matafiyin na kokawa da nuna rashin amincewa kan bukatar da dan sandan ya yi na binciken wayarsa, inda ya ce sufeton 'yan sandan kasar ya hana yin hakan, amma jami'in ya ki saurara masa.
Kofur Kadiri na aiki ne da rundunar 'yan sandan jihar Legas ta shiyyar Dolphin.
Hukumar 'yan sandan Najeriyar, ta gargadi jami'anta da cewa su tabbatar sun nuna kwarewa da kuma yin abin da doka ta tanada yayin gudanar da ayyukansu, sannan ta kira jama'a su dinga bai wa 'yan sandan hadin kai yayin gudanar da aikinsu.
Umayma Sani ce za ta kasance da ku a wannan shafi na rahotanni kai-tsaye na abubuwan da ke faruwa daga sassan duniya.
Amma za mu fi mayar da hankali kan Najeriya da Nijar da maƙwabtansu.
Barkanmu da hantsin Asabar, da fatan an fara hutun ƙarshen mako - ga masu yin sa.