Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Gwamnatin Buhari ta ci tarar Trust TV N5m

Wannan shafi ya na kawo muku rahotanni kai-tsaye daga Najeriya da makwabtanta da sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Bello Habeeb Galadanchi

  1. Amurka da Iran za su koma tattaunawa kan nukiliya

    Wakilan Amurka da Iran na kan hanyar zuwa Vinenna, domin tattaunawa ba ta kai tsaye ba kan hanyoyin da za a bi domin farfado da yarjejeniyar nukiliyar 2015. tsaikon da aka samu na watanni.

    Jagoran wakilan Amurka Rob Malley, ya ce ba shi da dogon buri kan makomar zaman da za su yi, sai dai kasarsa ta shirya da kyakkyawan fatan za a cimma kwakkwarar matsaya.

    Iran ta ce a shirye babban mai shiga tsakani na bangarenta Ali Bagheri-Kani yake domin tattauna shawarwarin da bangarorin suka gabatar.

    A makon da ya gabata babban jam’in diflomasiyya na Tarayyar Turai Josep Borrell wanda kuma ke tsara tattaunawar ya ce zai gabatar da sabon daftari domin kokarin kawo karshen kiki-kakan da ake yi.

    Shugaban hukumar kula da harkokin nukiliya na duniya Rafael Grossi ya ce Iran na cike da buri kan shirinta na nukiliya.

  2. Kamfanonin mai na cin kazamar riba a kan talakawa - MDD

    Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya ce bai dace ba sam-sam kamfanonin mai da iskar su rika cin kazamar riba a kan mutanen da suka fi talauci a duniya kuma suna matukar gurbata yanayi.

    Da yake gabatar da rahoto a kan matsalar karancin makamashi da ake fama da ita a duniya, Mista Guterres ya bukaci dukkanin gwamnatoci su rika tatsar kamfanoni haraji mai yawan gaske, sannan su yi amfani da kudin wajen taimaka wa mafiya rauni a cikin al'umma.

    Ya ce manyan kamfanoni sun ci riba jumulla wadda ta kai kusan ta dala biliyan dari daya a watanni uku na farkon shekarar nan.

    Mista Guterres ya zargi kamfanonin man da masu ba su kudaden gudanarwa da tsabar hadamar da ke muzguna wa talakawa, suna kuma lalata muhalli.

    Haka kuma ya yi kira ga kasashe da su dauki matakan rage amfani da makamashi mai gurbata yanayi, a madadinsa su hanzarta sauyawa zuwa ga makamashi maras illa ga muhalli.

  3. Masana sun gano hanyar farfado da sassan jikin aladen da ya mutu

    Kwararru a Jami'ar Yale ta Amurka sun yi wata gagarumar nasara ta farfado da wasu sassan jikin aladu, sa'a daya bayan kashe dabbobin.

    Masu binciken sun ce wannan nasara da suka samu za ta iya taimaka wa wajen samar da karin sassan jiki da za a iya amfani da su wajen dashe ga marassa lafiyar da wani sashe nasu ya daina aiki.

    Masana kimiyyar sun kirkiri jini ne da ya yada iska (oxygen) a jikin aladun ; sannan kuma jinin yana dauke da wasu sinadarai da suka farfado da wasu daga ayyukan sassan jikin da a lokacin suke mutuwa.

    Ana fatan za a yi amfani da wannan fasaha nan gaba a kan sassan jikin mutum, kuma a yi amfani da ita wajen adana sassan jikin su dade kafin a dasa su.

    Wata hanyar da ake gani za a iya amfani da wannan fasaha kuma idan ta tabbata ita ce ta yadda za a iya farfado da mutanen da suka rasa iskar shaka bayan ruwa ya ci su ko kuma sun gamu da cutar bugun-zuciya.

  4. An cire shingen hana taba Ka'abah

    Hukumomin Saudiyya sun cire shingen da suka sanya don hana alhazai tabawa da kuma sumbatar Al-Hajar Al-Aswad da kuma Kaʿabah.

    An cire kariyar ne wadda ta kewaye Ka'abah wadda aka sa a lokacin annobar korona domin hana mutane, yayin da aka fara aikin Umrah.

    Ana ta yada hotunan masu ibadah da suke ta kokarin taba Al-Hajar Al-Aswad din.

    A farkon shekarar nan hukumomin kasar ta Saudi Arabia suka janye yawancin matakan kariyar da suka sanya na kokarin dakile annobar korona.

    Aikin Hajjin da aka kammala a watan da ya gabata ya kasance kusan yadda ake yi a shekarun baya kafin daukar matakan kariya na korona, bayan shekara biyu da ta tsauraran matakai da aka dauka na rage yawan mahajjata.

  5. Yadda aka kai wa Mataimakin Babban Sufeton 'yan sanda hari a hanyar Abuja

    Mataimakin Babban Sufeton 'yan-sandan Najeriya da ke shugabantar sashe na 12 da ke Bauchi, Audu Madaki, ya tsira da ranshi amma ya samu raunuka daga harsashi a lokacin da wasu da ake zargin 'yan ta'adda ne suka kai wa motarsa hari a kusa da garin Kwoi da ke Jihar Kaduna.

    An kai wannan hari ne jiya Talata a lokacin da AIG din yake kan hanyarsa ta zuwa Abuja daga Bauchi, tare da ma'aikatansa ba tare da motocin masu tsaronshi ba, kamar yadda jaridar Daily Nigerian ta ruwaito.

    Wasu majiyoyin tsaro wadanda ba su yarda a bayyana sunayensu ba sun gaya wa jaridar cewa maharan sun je ne a cikin mota kirar Sharon baksuwaja (Volksvagen), suka bude wa motarsa wuta.

    Majiyoyin sun kara da cewa Mr. Madaki ya samu raunuka biyu na harsashi a kafarsa, shi kuwa mai tsaron lafiyarshi ya rasa ransa.

    Daya daga cikin majiyoyin ya bayyana cewa AIG din ya yi kuskure da ya bi wannan hanya mai hadari ba tare da jerin motocin masu tsaronshi ba.

    "Daga shi sai direbanshi sai mai tsaron lafiyarshi da dogarinshi, amma ba da ban jarumtakar mai tsaron lafiyar tashi ba wanda shi ma ya bude wuta, da lamarin ya fi haka muni."

    Ya zuwa yanzu hukumar 'yan sanda ba ta ce komai game da lamarin ba.

  6. Gwamnatin Buhari ta ci tarar Trust TV N5m

    Hukumar da ke sa ido kan kafafen watsa labarai ta Najeriya, ta ci tarar Trust Television Network (Trust TV) naira miliyan biyar saboda labarin da suka wallafa kan hare-haren da ake kai wa a jihar Zamfara mai taken "Nigeria's Banditry: The Inside Story".

    Wata sanarwa da kamfanin Media Trust ya fitar ta ce hukumar, a wata takarda dauke da sa hannun darakta janar dinta Balarabe Shehu Illela, ta ce ta ci tarar Trust TV ne "saboda ta watsa rahoto na musamman da ya saba ka'idojin wasu sassan ayoyin dokar hukumar."

    Sai dai kamfanin Media Trsut ya ce a "Yayin da muke ci gaba da nazari kan matakin hukumar da kuma duba zabukan da muke da su, muna sanar da cewa a matsayinmu na gidan talbijin, mun yi amannar cewa muna aiki ne domin al'umma ta hanyar karin haske kan batun garkuwa da mutane mai sarkakiya da kuma yadda yake shafar miliyoyin jama'ar kasarmu."

    Sanarwar ta kara da cewa rahoton ya bi salsalar zaman dar-dar a tsakanin al'umma da kuma abubuwan da suka sanya rikicin da ya sa wasu ke daukar makamai da ke jefa mutane cikin gagarumin halin kaka-na-ka-yi.

    Ta ce rahoton ya fito da matsalolin rashin adalci da kabilanci da rashin iya gudanar da mulki wadanda su ne ke haddasa irin wannan rikici.

    Kazalika ya bayar da shawara kan yadda za a magance matsalolin ta hanyar tattaunawa da masana da masu ruwa da tsaki, ciki har da Ministan Yada Labarai, Alhaji Lai Mohammed, da Sanata Saidu Mohammed Dansadau, da Farfesa Abubakar Saddique na Jami'ar Ahmadu Bello, da sauransu. A makon jiya ne gwamnatin Najeriya ta yi tur da matakin da BBC da kuma Trust TV suka dauka na watsa rahoton na musamman, tana mai cewa za ta dauki mataki a kansu.

  7. An rantsar da sababbin alkalan Kotun Shari'a 21 a Jihar Borno

    Alkalin alkalan jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya, Mai Shari'a Kashim Zannah, ya rantsar da alkalan Shari'ar Musulunci 21 a jihar.

    Da yake magana a taron rantsarwar ranar Talatan nan a birnin Maiduguri, Mai Shari'a Zannah ya bukaci sababbin alkalan da su jajirce wajen gudanar da aikinsu kamar yadda suka dauki rantsuwar kama aiki.

    Ya kuma yi kira da su gudanar da shari'o'in da za a gabatar musu bisa turbar doka da rantsuwar da suka dauka.

    Ya ce "Kowannenku ya zo ne saboda cancanta ba don wani iko ba ko hanya, saboda haka ba za ku wahala wajen fahimtar mu da muke cewa ba za mu amince da cin hanci da rashawa ba. Babu yadda za a yi mu amince da cin hanci da rashawa.

    "Za mu hukunta duk mutumin da aka samu da cin hanci ta korarsa daga aiki da tozarta shi. Wannan shi ne kadai hukuncin, ba rage matsayi ba ko sauyin wajen aiki. Babu wata mafita a wannan lamari, kamar yadda ba mu da mafita wajen zaben ku wannan aiki saboda kun ci jarrabawa.'

  8. Birtaniya ta bai wa likitoci 'yan Najeriya 266 lasisi cikin wata biyu

    Babbar kungiyar kiwon lafiya da ke bayar da lasisi ta jajirce cewa rijistar likitoci a Birtaniya ta bada lasisi ga likitoci 'yan Najeriya 266 a watan Yuni da Yuli na 2022, a cewar rahoton jaridar Punch.

    Tasirin haka shi ne akalla likitoci 'yan Najeriya uku ake bai wa lasisi a kowace rana duk da yunkurin gamnati na dakile ficewar likitoci da jami'an kiwon lafiya daga kasar.

    A halin yanzu akwai likitoci da suka samu horo a Najeriya 9,976 da ke aiki a Birtaniya.

    Wannan adadi bai kunshi wasu likitoci ba wadanda 'yan Najeriya ne amma ba su samu horo a Najeriyar ba, a cewar rahoton.

    Yanzu haka Najeriya ce kasa ta uku da ta fi kowace yawan likitoci da ke aiki a Birtaniya - bayan Indiya da Pakistan.

    Sai dai duk da haka kasar na fama da karancin likitoci.

    Kungiyar likitoci ta Najeriya ta ce akwai likitoci 100,000 da suka yi rijista da ita.

  9. Ina shan wahala saboda tsadar dizel - Obasanjo

    Tsohon shugaban Najeriya, Olusegun Obasanjo ya yi korafi a kan tsadar dizel, da farashin abincin dabbobi da kuma farashin canji da yadda hakan ke shafar kiwon kifi a Najeriya.

    Obasanjo, wanda mai kiwon kifi ne, ya ce yana cikin tasku saboda tsadar dizel, lamarin da ke kawo tsaiko ga kiwon kifinsa.

    Obasanjo ya yi wannan magana ce a jiya Talata a Abeokuta da ke jihar Ogun, a lokacin taron kungiar masu kiwon kifi na yankin kudu maso yammacin Najeria a cikin dakin karatun littafi na Obasanjo (OOPL).

    Obasanjo ya bayyana cewa cigaba da tashin farashin dizel da kuma cigaba da karuwar farashin abincin kifi zai hana masu kiwon yin aikinsu, sai dai idan har sun hada kai su amince da farashi da za su cigaba da barin su suna sana'ar.

    Ya yi bayani yana cewa a halin yanzu farashin dizel 800 ne lita daya, sannan samar da kilo daya na kifi naira 1,400 ne, kuma ya kara da cewa, idan har suna son samun riba, to ba za su iya sayar da kifi kasa da 1500, lamarin da ya su duk wani abu da ya yi kasa da haka zai jawo faduwa ne da asara.

    Obasanjo ya ce: "Farashin dizel ya yi sama saboda yadda ake tafiyar da kasar nan ba yadda ya dace ba ne.

    "Saboda haka idan haka ta faru, wasu daga cikin mu da muke bukatar amfani da dizel domin noman kifi zamu yi asarar ne baki daya, kuma a lokacin da hakan zai faru, 'yan Najeriya za su ci gaba da bukatar cin kifi."

    "Noman kifi zai gagara, sannan manoman da ke wajen Najeriya zasu ringa kawo wa nan.

    "Za ka rasa aikin yi, ka talauce. Saboda haka me ya kamata mu yi? Mu hada kai mu cigaba da raya noman kifi domin kula da bukatun wadanda su ke cin kifi da kuma masu noman kifin," a cewarsa

  10. Mutum hudu sun mutu a zanga-zanga a Iran kan tsadar rayuwa a watan Mayu

    Ƙungiyar kare haƙƙin bil'adama ta Amnesty International ta tabbatar da mutuwar aƙalla mutum huɗu a zanga-zangar da aka yi a watan Mayu a ƙasar Iran a kan tsadar rayuwa da kuma rugujewar wani gini da ya kashe mutane da yawa.

    Ƙungiyar ta ce jami'an tsaron Iran sun yi ta harba harsashai kuma sun yi harbi daga sama don tarwatsa zanga-zangar da aka yi a yankin Kudu maso yammar ƙasar.

    Ƙungiyar ta ce wasu daga cikin masu zanga-zangar sun fara ƙone-ƙone da ɓarna amma jami'an tsaron sun amsa laifunsu na amfani da ƙarfin da ya wuce gona da iri.

  11. Rashin dala ya sa matafiyan Najeriya sun rasa na yi

    'Yan Najeriya na ci gaba da fuskantar matsala da shan wahala wajen canza dalar Amurka a babban bankin kasar (CBN) a kan farashin gwamnati.

    Wadanda wannan lamari ya fi shafa su ne matafiya kasar waje wadanda yake daukar su lokaci kafin su samu canjin yin kasuwanci (BTA) da canjin kashewa (PTA) a sanjin gwamnati mai sauki domin zuwa asibiti ko karatu ko harkar kasuwanci.

    Wannan rashi ya shafi iyaye saboda wahalar samun dala domin biyan kudaden makaratun yaransu da ba su kudin kashewa.

    Bincike ya nuna cewa akwai matuƙar wahala wajen samun dala saboda bukatarta ta fi adadin da ake da ita, lamarin da ya tursasa wa bankuna ƙara tsawon lokutan samar da PTA/BTA daga makonni biyu zuwa takwas.

    Amma wasu masana sun bayyana cewa CBN ta tsananta hanyar samun dalar ne saboda wasu marasa kishin kasa na amfani da tsarin ba yadda ya dace ba.

    Sakamakon bincike da babban bankin ya yi ya nuna cewa akwai mutane da yawa da ba su da niyyar tafiyar kasar waje, ko amfani da kudaden a kasar waje don amfani da su akan ƙa'ida.

    Amma sai su hada takardun bogi sannan su nemi banki ya ba su kudaden waje don kawai su tara, ko su sayar a kasuwannin bayan fage.

  12. An kama mutum shida kan zambar mutane a shafin masu auren jinsi daya a Najeriya

    Ƴan sandan jihar Nasarawa a arewa ta tsakiyar Najeriya sun kama mutum shida da ake zargin suna amfani da wani shafin intanet suna zambar mutanen da suke auren jinsi ɗaya.

    An ce waɗanda ake zargin suna amfani da shafin ne don neman amincewar mutane kafin daga bisani su zambe su.

    Kamen ya zo ne bayan wani da abun ya shafa ya ce an ɗauki hotunan tsiraicinsa, kuma an yi masa barazanar yaɗa hotunan idan bai ba da kuɗi ba

    An ce lamarin ya faru ne a unguwar Masaka, a ƙaramar hukumar Karu da ke da iyaka da birnin tarayya Abuja.

    Kakakin ƴan sandan jihar, Ramhan Nansel ya gaya wa BBC cewa wanda ake zargin, maza huɗu da mata biyu, sun yaɗa hotunan masu neman auren jinsi ɗaya, kuma sun gayyaci masu sha'awar yin haka don shirya ranakun da za su haɗu.

    Sannan kuma sai su zambaci mutanen ko su ƙwace musu ƙadarorinsu kuma su yi musu barazanar ɓata musu suna don rufe bakinsu.

    Ƴan sandan sun ce za a yanke wa waɗanɗa ake zargin hukunci bayan kammala bincike.

    Gwamnatin Najeriya ta hana auren jinsi ɗaya, ta kuma saka dokar ɗaure mutum har na shekaru 14 idan an kama masu aikata laifin.

  13. An kaɗa ƙuri'ar kan batun zubar da ciki a Jihar Kansas ta Amurka

    Masu jefa kuri'a sun yi gagarumar nasara inda suka bayyana cew ba sa son yin garanbawul ga ƙundun tsarin mulkin jihar wanda yace babu 'yancin zubar da ciki.

    Wannan shi ne gwajin farko na kuri'a akan lamarin tun lokacin da kotun kolin Amurka ta amince da jihohi akan su haramta zubar da ciki.

    Da kuri'ar da aka jefa ya haramta zubar da ciki, 'yan majalisu za su iya hana zubarwa a jihar.

    Tambayar da aka saka akan takardar kuri'ar ta jawo muhawarori masu zafi tun bayan da kotun kolin Amurka watanni biyu da suka wuce, da ya soke dokar Roe v Wade ta 1973 wanda ya hallasta zubar da ciki a duk fadin kasar.

    A lokacin da aka soke Roe v Wade, shugaba Biden ya ce 'yancin zubar da ciki zai kasance batu mai muhimmanci ga masu jefa kuri'a. Abun da ya faru a Kansas ya kasance shaidar abun da ake tunani.

    Donald Trump yayi nasara a Kansas da maki 15 shekaru 2 da suka wuce, amma yanzu ya jefa kuri'ar amincewa a kare 'yancin zub da ciki, lamarin da ake gani a matsayin babbar nasara.

    A yanzu wata kariya ce, sannan za a tabbatar da sakamakon a hukumance a cikin mako daa.

    Amma ga 'yan Democrats da masu kungiyoyin da ke goyon bayan zub da ciki, wannan alama ce da ke nuna cewa Amurkawa na matukar bakin ciki da soke 'yancin zub da ciki da aka yi - kuma suna ganin hukuncin koton kolin ya sha ban-ban da abunda jama'a su ke so.

  14. Fyade na karuwa a Sudan ta Kudu a lokacin da yaki ke raguwa

    Tarzomar jinsi da fyade masu alaƙa da rigingimu na ƙaruwa a Sudan ta Kudu, yayin da faɗa ke raguwa a ƙasar, bisa rahoton ofishin Majalisar Dinkin Duniya a kasar (Unmiss).

    A cikin rahoton, ofishin ya ce akwai ƙaruwar kashi 218% a fyaɗe da fyaɗen taron dangi tsakanin watan Afrilu da Yuni.

    "Wannan tashin goron zabo na fyade da tarzomar jinsi ba za a amince da shi ba, kuma ya fi shafar mata da yara mata sosai," a cewar Nicholas Haysom, shugaban Unmiss.

    Fadace-fadace tsakanin kananan al-ummomi na ci gaba da shafar fararen hula, biyo bayan arangama da aka sha yi tsakanin mayaƙan sa kai da dakarun gwamnati.

    Fitowar rahoton ya zo a lokaci daya da isar ƙwararru uku daga hukumar 'yancin kai ta Majalisar Dinkin Duniya a Sudan ta Kudu.

    Za su hadu da jami'an gwamnati da wakilan kungiyoyin farafen hula da jami'an diflomasiyya dangane da sakamakon rahoton.

  15. Ƴan sanda na bincike kan budurwar 'da ta rataye kanta' a Kano

    Rundunar ƴan sandan jihar Kano a arewacin Najeriya tana ci gaba da bincike kan abin da ya sa wata budurwa mai shekara 17 ta rataye kanta a ƙauyen Garin Dau da ke yankin karmar hukumar Warawa.

    Mafi akasarin mazauna ƙauyen dai sun yi zargin cewar budurwar ta rataye kan nata ne bisa auren dole da iyayenta ke shirin yi mata.

    Sai dai iyayen nata sun musanta wannan zargi inda suka ce ba ta kammala makarantar sakandare ba, balle a yi maganar aurar da ita.

    Faruwar wannan lamari dai ya ya zowa mazauna yankin da mamakin sakamakon yadda da dama daga cikin mutanen kauyen ke bayyana budurwar da kyawawan ɗabi'u.

    A yau ne aka shiga yini na biyu na rasuwar Safiya mai shekaru 17 da ke aji biyu a makarantar sakandare, wadda aka tarar da gawarta a rataye kuma ana zargin ita ta rataye kanta.

    SP Abdullahi Haruna Kiyawa shi ne mai magana da yawun rudunar ƴan sanda a Kano, ya shaida wa BBC cewa sun sami labarin faruwar lamarin, kuma suna bincike kan lamarin don gano shin budurwar ce ta rataye kan nata ko kuwa.

    Wannan dai shi ne rahoton rataye kai na baya-bayan nan da aka samu a Kano, sabanin a watanin baya da suka gabata, biyo bayan kiraye-kiraye da wayar da kan al’umma da hukumomin jihar suka dauka.

    A mafi akasarin lokuta ƙwararru a fannin sanin halayyar dan adam na alaƙanta ɗabi’ar mutum ya rataye kansa, sakamakon ciwon damuwa da yake fama da shi, ko wata larura da ta shafi kwakwalwa.​

  16. Amurka ta ce akwai yiwuwar harin ramuwar gayya daga al-Qaeda

    Amurka ta bukaci al'ummarta da su zamo masu taka-tsantsan domin kauce wa hare-haren ramuwar-gayya, bayan harin da ta kai wanda ya hallaka jagoran kungiyar al-Qaeda, Ayman Alzawahiri.

    Ma'aikatar harkokin wajen Amurkar ce ta aika da gargadin ga Amurkawa a fadin duniya, tana mai cewa kisan ka iya tunzura magoya bayan al Qaeda ko 'yayan kungiyoyi masu alaka da ita su yi kokarin kai hari kan al'ummarta ko gine-gine mallakinta.

    Shugaban Amurka Joe Biden ne dai ya tabbatar da kisan Al-zawahiri a wani harin jirgi maras matuki da aka kai a Kabul, babban birnin Afghanistan.

    Amurka na da yakinin cewar wanda aka kashen yana daga cikin wadanda suka kitsa harin da aka kai kan dogayen gine-ginen nan na Amurka a ranar 11 ga watan Satumban shekarar 2001.

  17. Turkiyya za ta binciki jirgin ruwan Ukraine mai dauke da tsaba

    A yau ne ake sa ran jirgin ruwan dakon kayan nan wanda ke dauke da tsaba daga Ukraine zai fuskanci wani gagarumin bincike a kan tekun da ke karkashin ikon kasar Turkiyya.

    Jirgin dakon kayan shi ne na farko da ya baro wata tashar jirgin ruwa da ke karkashin ikon Ukraine tun bayan mamayen da Rasha ta kaddamar a kan kasar.

    Wakilin BBC ya ce jirgin wanda ake wa lakabi da Razoni yana dauke ne da hatsi daga Ukraine tan dubu 26, wanda za a kai Lebanon, kuma wannan kalilan ne daga cikin miliyoyin tan din hatsi da ke jibge a tashoshin ruwan Ukraine.

    Jami'an daga kasashen Rasha, da Ukraine, da Turkiyya da kuma na majalisar dinkin duniya, za su binciki jirgin ne domin tabbatar da cewa ba ya dauke da wasu kaya da aka haramta.

    Ana sa ran dawowar fitar da hatsi daga kasar Ukraine zai taimaka wajen rage matsalar abinci da duniya ke fuskanta, wanda ya kazance sanadiyyar toshe wasu tashoshin jiragen ruwan Ukraine da Rasha ta yi.

  18. Assalamu Alaikum

    Masu bibiyar mu a wannan shafi, barkanku da hantsin Laraba, da fatan kun tashi lafiya.

    Zamu kawo muku rahotanni da labarai kai tsaye na abubuwan da ke faruwa a Najeriya da makwabtanta, da kuma sauran sassan duniya.