Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Gwamnatin Chadi ta hana kananan 'yan mata fita daga kasar

Wannan shafi ne da ke kawo muku labarai da rahotonnin abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Abdullahi Bello Diginza and Muhammad Annur Muhammad

  1. Rikicin Hausawa da kabilar Berti ya ci sama da mutum 100 a Sudan

    Hukumomin jihar Blue Nile da ke kudu maso gabashin Sudan sun ce mutum 105 ne aka tabbatar sun rasa ransu a rikici kan filaye da aka shafe kwanaki ana yi.

    Ministan lafiya na jihar ya gaya wa kamfanin dillancin labarai na Faransa cewa, yanzu hankali ya kwanta amma yadda za a yi da mutanen da rikicin ya raba da gidajensu ita ce matsalar.

    Majalisar Dinkin Duniya ta ce mutum dubu 15 ne suka tsere daga muhallansu a jihar ta Blue Nile, kuma da yawa daga cikinsu sun samu mafaka ne a makarantu.

    Rahotonni sun ce rikici tsakanin Hausawa mazauna ƙasar da kuma 'yan ƙabilar Berti ya faro ne ranar Litinin kan rikicin mallakar filaye.

    Sai dai kuma wasu na cewa fadan ya tashi ne a sanadiyyar nadin sarautar gargajiya da aka yi wa Hausawa.

    Majalisar ta ce a fadin kasar ta Sudan sama da mutum miliyan 14 ne ke bukatar taimakon gaggawa, amma kuma tana matukar karancin kayan taimakon.

    Rikicin na Blue Nile ya haddasa zanga-zanga a tituna a biranen kasar ta Sudan, inda har aka sanya dokar hana fita a biyu daga cikinsu a farkon makon nan.

  2. Gwamnatin Chadi ta hana kananan 'yan mata fita daga kasar

    Gwamnatin Chadi ta hana kananan 'yan mata barin kasar ba tare da izinin iyayensu ba, matakin da kungiyoyin kare hakkin mata suka koka da shi tare da neman hukuma ta sauya shawara.

    Minisatn tsaro Janar Idriss Dokony Adiker wanda ya bayyana dokar, ya ce ana samun tarin 'yan mata da ke tururuwar ficewa daga kasar, suna zuwa inda ake ci da guminsu.

    Samnarwar ta hana kamfanonin shirya jigilar jiragen sama da motoci daukar kananan 'yan mata zuwa kasashen waje.

    Sai dai kuma sanarwar ministan ba ta fayyace iya shekarun 'yan matan da dokar ta shafa ba, ko kuma wanda takamaimai zai bayar da izinin fitar tasu ba.

    Gamayyar kungiyoyin kare 'yancin mata na Chadi ta soki matakin da cewa ya saba wa 'yancin 'yan mata da kuma dan-Adam.

    Gawamayyar ta ce dokar ta nuna wariya, domin yara maza kanana suma ana safararsu, inda ake ci da guminsu.

    Wani rahoto na yaki da laifuka a tsakanin kasashe ya nuna cewa matsalar safarar mutane ta karu a Chadi a shekarun nan.

    Haka kuma rahoton ya ce an samu karuwar yawan mata 'yan Chadi da ke zuwa karuwanci a kasashe makwabta a 2021.

  3. Turai za ta ƙara ƙaƙaba wa Rasha takunkumi kan Ukraine

    Jakadun ƙasashen tarayyar Turai sun amince da sabbin takunkmai kan Rasha bisa yaƙin da take yi a Ukraine.

    Sun haramta shigar da zinare daga Rasha da kuma toshe kadarorin babban bankin Rasha Sberbank.

    Sannan kuma za su ƙaƙaba takunkumin kan wasu mutane da hukumomin ƙasar ta Rasha.

    Shugabancin EU na Jamhuriyyar Czech ya ce takunkuman za su yi daidai da na ƙasashe bakwai mafiya ƙarfin tattalin arziƙi, wato G7.

    Tun da farko, ministan harkokin wajen Rasha, Sergei Lavrov, ya nuna cewa, manufar Moscow kan Ukraine, ita ce ta ƙara fadada daga burin ƙwace yankin gabashin Donbas.

    Yana mai bayar da misali da wasu yankunan kudanci da yanzu ke ƙarƙashin ikon Rasha.

  4. Shugaban Faransa ya damu kan illar gobarar daji

    Shugaban Faransa, Emmanuel Macron, ya ce ƙaruwar hatsarin da ke tattare da gobarar daji da sauyin yanayi ke haifarwa za ta buƙaci ɗaukar mataki don kare gaba.

    Yana magana ne a wata ziyara da ya kai yankin Gironde da ke kudu maso yammacin Faransa, inda wutar dajin ta laƙume fiye da murabba'in kilomita dari biyu.

    Mista Macron ya ce sauyin ba wai Faransa kawai ya shafa ba - ya shafi baki dayan yankin Bahar Rum.

    Ya yi alƙawarin samar da mataki na farfaɗo da dajin da wuta ta cinye.

    Dukkanin ƙasashen Faransa da Sifaniya sun ce za su ƙara kashe kuɗi wajen yaki da wutar daji.

    Wasu kasashen Turai da dama na tunkarar wutar, ciki har da Portugal bayan yanayin zafi ya ƙara tsananta.

  5. Matar shugaban Ukraine ta roki Amurka karin makamai

    Uwargidan shugaban Ukraine ta roƙi 'yan majalisar dokokin Amurka da su taimaka wa ƙasar da ƙarin makamai.

    Da take jawabi a gaban majalisun biyu, Olena Zelenska ta ce za a yi amfani da makaman ne don kare ƙasa ba don far wa wata ƙasa ba.

    Ms Zelenska ta ce mafita tana a Washington, tana mai roƙo a taimaka a dakatar da abin da ta kira ta'addanci da ake yi wa 'yan Ukraine.

    Ta ce wannan zai kasance babbar nasara da samun ƴancin rayuwa da ƴanci da kuma samun farin ciki.

    Yayin da sojojin Rasha ke ci gaba na nausawa yankin gabashi, Ukraine na neman ƙarin manyan makamai masu cin dogon zango.

  6. Ana zanga-zangar neman saukar shugaban Malawi

    'Yan sanda na dauki-ba-dadi da masu zanga-zanga a babban birnin Malawi Lilongwe, kan neman cire shugaban kasar Lazarus Chakwera.

    Masu zanga-zangar na zargin shugaban kasar da kasa daukar matakan shawo kan matsalar tsadar rayuwa, inda suke neman shugaban ya sauka domin a yi sabon zabe.

    Hotunan bidiyo da ake ta yadawa a shafukan intanet na nuna yadda masu zanga-zangar ke kafa shigayen duwatsu a kan tituna.

    'Yan sanda sun ce sun kama kusan mutum 80, sannan kuma ana samun rahotannin wawashe dukiya da tashin hankali.

    Masu rajin kare hakkin dan-Adam ne suka shirya zanga-zangar.

    Shugaba Chakwera, wanda mai wa'azin Kirista ne da ya juye ya koma siyasa ya hau mulki ne a 2020, inda ya yi alkawarin kawar da abin da ya kira katutun cin hanci da rasahawa.

  7. Mali ta kori kakakin Majalisar Dinkin Duniya

    Gwamnatin mulkin soji ta Mali ta umarci kakakin rundunar wanzar da zaman lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya da ya fice daga kasar cikin sa'o'i 72.

    Ma'aikatar harkokin wajen kasar ta zarge Olivier Salgado da sanya wasu jerin bayanai da ke nakasu ga huldar diflomasiyyar kasar a shafukan intanet.

    Gwamnatin ta ce ya yi kalaman da ba haka suke ba, da cewa an sanar da hukumomin kasar game da zuwan sojoji 49 na kasar Ivory Coast.

    Majalisar Dinikin Duniya ta ce sojojin sun je Mali ne domin tallafa wa dakarunta na zaman lafiya, amma kuma gwamnatin kasar ta ce ba ta san da zuwansu ba.

    Saboda haka ta kama su a matsayin sojojin haya, ta kuma tsare su, da niyyar gudanar da binciken sharia'a a kansu.

  8. Shugaban Kenya ya zaftare farashin masara domin saukaka wa talakawa

    Shugaban Kenya Uhuru Kenyatta ya bayar da umarnin rage kudin garin masara da sama da rabi domin saukaka wa 'yan kasar tsadar rayuwa.

    A yanzu za a rika sayar da jaka mai nauyin kilogram 2 na garin a kan sulai (shillings) 100, maimakon sulai (shillings) 205 da ake sayarwa a da.

    Shugaban ya bayar da umarnin ne bayan wata ganawa da ya yi da 'yan kasuwa da sauran masu hada-hadar masarar a fadar gwamnatin kasar da ke Nairobi.

    Shugaba Kenyatta ya ce daukar matakin ya zama wajibi saboda halin matsi da 'yan kasar ke ciki sakamakon fari da aka samu da kuma wasu dalilai na waje.

    Mista Kenyatta ya caccaki 'yan siyasa da ya zarga da amfani da tashin farashin garin masarar da yarfen siyasa a yayin da kasar ke tunkarar zabe a ranar 9 ga watan Agusta mai zuwa.

    A sanarwar da fadar gwamnatin ta fitar an dakatar da karbar harajin tashar jirgin kasa da kuma kudin fito na shigar da masara kasar ta gabashin Afirka.

  9. Dakarun Rasha na ci gaba da luguden wuta a Ukraine

    Dakarun Rasha na ci gaba da luguden wuta a biranen Ukraine. A arewa maso gabashi, gwamnan lardin ya ce an kashe mutum uku, da suka ƙunshi har da wani ƙaramin yaro.

    An kuma bayar da rahoton mutuwar mutum biyu da raunata wasu da dama a Ikopol, arewacin yankin Crimea da Rasha ta ƙwace.

    Amma hukumomin da Rasha ta naɗa a yankin Kherson sun ce suna takaita zirga zirga a gadar da ta ratsa kogin Dnieper, da ke fskantar hare-haren rokoki daga Ukraine.

  10. Babu wanda zan kyale a yaki da cin hanci da rashawa - Raila Odinga

    Shugaban babbar jam’iyyar adawa a Kenya Raila Odinga ya ce babu wanda za a kyale a yaki da cin hanci da rashawa, da ya yi alkawarin aiwatarwa idan aka zabe shi a matsayın shugaban kasa a zaben watan gobe.

    Wannan dai shi ne karo na biyar da Mista Odinga ke neman takarar shugabancin kasar.

    Tsohon firaministan mai shekara 77, ya ce a shekarunsa ba shi da ra’ayin sake yin takara, amma yana da abubuwa da dama da yake son aiwatarwa ko da kuwa ba a zabe shi ba.

    Ya ce “Na janye jikina daga harkokin siyasa, to amma nadin da kungiyar tarayyar Afirka ta yi min a matsayin babban jakada kan harkokin gine-gine, ne ya kara tsumani''

    Mista Odinga ya kara da cewa ce idan ya ci zaben, zai mayar da hankali kan yaki da cin hanci da rashawa, inda ya ce kasar na hasarar dala milliyan 16 a kullum sakamakon cin hanci da rashawa.

    “Babu wanda zai tsallake yakin da zan yi da cin hanci da rashawa, ko da kuwa ni ne aka gano ina cin hanci da rashawaa a hukunta ni,” in ji shi.

  11. Gwamnatin Benin za ta yi gwanjon kadarorin jagoran adawa na kasar

    Gwmnatin kasar Benin za ta yi gwanjon manyan kadarori masu alfarma na babban jagoran adawar kasar kuma hamshakin dan kasuwa Sébastien Ajavon

    Daga cikin kadarorin har da wata motar alfarma ta Rolls Royce, wacce kamfanin dillancin labarai na AFP ya ruwaito kimar darajarta ta kai dala 122,339.

    Akwai kuma karin wasu manyan kadarori kusan 140 da za a saka su a kasuwa domin sayar da su.

    Mista Ajavon wanda ke gudun hijira a birnin Paris, bayan da aka yanke masa hukuncin daurin shekarar 20 saboda zargin ta'ammali da miyagun kwayoyi.

    To sai dai kotun kare hakkin bil-adama ta Afirka, ta ce hukuncin da aka yanke masa ya saba wa doka,

    To amma rahotonni na cewa gwamnatin Benin ta kafe cewa hukuncin na farko yana nan daram.

    A zaben 2016 dai, ya tsaya takarar shugabancin kasar, sai dai daga baya ya mara wa shugaban kasar na yanzu Patrice Talon baya.

    To sai dai daga baya dangantaka ta yi tsami tsakanin mutanen biyu

  12. Fusatattun matasa sun jefi dan majalisa a Ghana.

    Wasu fusatattun matasa a yankin Suame na kasar Ghana sun kori wani dan majalisa, inda suka rika yi masa ihu, da zagi, tare da jifansa da ledojin Fiya-wata.

    Dan majalisar mai suna Osei Kyei Mensah-Bonsu wanda shi ne shugaban masu rinjaye a majalisar, ya je yankin ne domin nuna damuwarsa game da matsalolin da mutanen yankin nasa ke fuskanta wadanda suka hada da rashin kyawawan hanyoyi.

    A makon da ya gabata ne dai, mazauna yankin suka gudanar da wata zanga-zanga tare da toshe hanyoyi sakamakon halin da titunan yankin ke ciki

    Lokacin da matasan suka sami labarin cewa dan majalisar yana yankin sai suka nufi inda yake domin su kore shi.

    daga baya dai 'yan sanda sun hallara a wajen domin daidaita al'amura.

    Matasan sun ce sun kori dan majalisar ne, saboda tun da yake wakiltarsu a majalisar bai taba cika alkawuran da ya dauka musu ba.

    Mista Mensah-Bonsu ya ce ko kadan bai damu da abin da matasan suka yi masa ba, saboda a cewarsa, matasan za su iya yi wa kowanne jami'in gwamnati haka, ba iya shi kadai ba.

  13. An sake gano wata 'yar Chibok a Borno

    Dakarun soji na rundunar Hadin kai, da ke yaki da Boko Haram a Najeriya, sun tabbatar da sake gano wata 'yar makarantar Chibok mai suna Ruth Bitrus, wacce ta kubuta daga hannun mayakan Boko Haram tare da danta.

    Jaridar Daily Trust a Najeriya ta ruwaito babban kwamandan dakarun rundunar, Manjor janar GC Musa na bayyana hakan ranar Laraba.

    A lokacin da yake mika wasu magunguna da hukumar raya yankin arewa maso gabas ta bai wa sojojin da ke aiki a yankin.

    Kwamandan ya ce ''Idan za ku iya tunawa makonni da suka gabata, mun kubutar da 'yan matan Chibok biyu, to yanzu ma mun sake kubutar da wata guda daya''

    A 'yan kwanakin baya ne dai, dakarun suka kubutar da 'yan mata biyu a karamar hukumar Gazuwa.

  14. An umarci kasashen Turai su rage amfani da gas

    Hukumar gudanarwar tarayyar Turai ta umarci mambobinta da su rage amfani da gas da kashi 15 cikin 100 nan da watan Maris, saboda fargabar janye shigar da gas da Rasha ke yi zuwa kasashen.

    Hukumar ta ce a halin yanzu matakin na radin kai ne, amma kuma zai zame wa kasashen tilas idan Rasha ta daina tura gas din nata cikin kasashen.

    Cikin makonni biyu da suka gabata ne dai Rasha ta rufe wani bututun da ke kai wa Jamus gas, tana mai cewa wasu gyaye-gyare za ta yi masa, ta kuma alkawarta dawo da aikinsa ranar Alhamis mai zuwa.

    To sai dai akwai fargaba game da cika wannan alkawari.

    A shekarar da ta gabata Rasha ta fitar da kashi 40 cikin 100 na gas zuwa Turai, Inda kasashen Jamus da Italiya suka fi kowa sayen da gas din a shekarar 2020.

    Tun lokacin da Rasha ta fara mamayar Ukraine ta daina sayar da gas dinta ga kasashen da suka ki yadda su biya ta da kudin roubles

  15. Najeriya na cikin shirin ko-ta-kwana game da cutar Marburg

    Hukumar da ke yaki da cutuka masu saurin yaduwa ta Najeriya, ta ce tana cikin shirin ko-ta-kwana, bayan da aka samu bullar cutar Marburg a kasar Ghana.

    A wata sanarwa da hukumar ta NCDC ta fitar ta ce Najeriya ta tanadi abubuwan gwaje-gwajen gano cutar da kuma yadda za su magance ta idan ta bulla a kasar..

    Ta kara da cewa likitocin kasar sun shirya wa cutar ta Marburg mai alaka da Ebola, an kuma tsaurara matakan sa-ido kan cutar.

    Kawo yanzu dai ba a samu rahoton bullar cutar a kasar ba, wacce ta fi kowacce kasa yawan al'umma a nahiyar Afirka.

    A farkon makon nan ne dai,hukumomin lafiya a Ghana suka tabbatar da bullar cutar a kasar, inda mutum biyu da aka tabbatar na dauke da cutar suka mutu, yayin da aka killace gomman mutane.

  16. Morocco ta yanke wa 'yan ci-rani hukuncin daurin wata 11

    Wata kotu a Morocco ta yanke wa wasu 'yan ci-rani 33 hukuncin daurin wata 11 saboda shiga kasar ba bisa ka'ida ba.

    A watan da ya gabata ne dai wani kwale-kwale ya kife a tekun kasar makare da 'yan ci-rani, a kokarinsu na shiga Turai, abin da ya yi sanadiyyar mutuwar da dama daga cikinsu.

    Majalisar Dinkin Duniya, da kungiyar tarayyar Airka da kuma wasu kungiyoyin kare hakkin dan adam sun sha yin Allah-wadai saboda yadda jami'an tsaron Morocco da na Sifaniya ke amfani da karfin da ya wuce kima kan 'yan ci-ranin.

  17. An kama wasu 'yan majalisar dokokin Amurka kan 'yancin zubar da ciki

    Akalla 'yan majalisar dokokin Amurka 17 ne aka kama a birnin Washington DC, saboda zanga-zangar adawa da soke 'yancin zubar da ciki.

    Cikin 'yan majalisar da aka kama sun hadar da Alexandria Ocasio-Cortez, da Rashida Tlaib da Ilhan Omar

    An ga 'yan majalisar na rera wakokin da ke cewa ''A bar mu, mu sakata, mu wala'' tare da toshe wasu titunan birnin kafin 'yan-sanda su yi awon-gaba da su .

    A kwanakin baya ne dai Kotun Kolin Amurka ta haramta dokar 'yancin zubar da ciki a fadin kasar.

  18. Wata mata za ta sha daurin shekara 30 saboda satar kananan yara

    Wata kotu a birnin Beira na kasar Mozambican ta yanke wa wata mata hukuncin daurin shekara 30 a gidan yari, da kuma biyan tarar dala 3,100, sakamakon samunta da laifin sace wasu kananan yara guda biyu domin neman kudin fansa.

    A watan Oktoban bara ne matar mai shekara 37, ta sace wani yaro mai shekarar 14, inda ta nemi kudin fansa kusan dala 313.

    Haka kuma ta kara sace wani yaron a watan Disamba, inda ta nemi kudin fansa dala 390.

    Alkalin kotun ya ce ''Abu guda daya da za a yi domin kawar da aikata irin wannan laifi, shi ne zartar da hukuncin da doka ta tanada a kan duk wanda ya aikata makamancinsa''.

  19. Cikin kwana biyu za a iya kawo karshen yajin aiki ba sai mako biyu ba - Shugaban ASUU

    Shugaban kungiyar malaman Jami'o'i ta Najeriya ASUU ya ce wa'adin mako biyu da shugaban kasar ya bayar domin kawo karshen yajin aikin ya yi yawa.

    A wata hira da gidan talabijin na Channels Tv, shugaban na ASUU Farfesa Emmanuel Osodeke ya ce a bangarensu na malaman jami'a, cikin kwanaki biyu za a iya warware wannan matsala.

    Ya kara da cewa ''mako biyu ya yi yawa, an riga an kammala tataunawa domin cimma matsaya, kawai zuwa za ku yi ku ce mana kun amince, wannan kuma ba zai wuce kwana biyu ba''

    Farfesa Emmanuel Osodeke ya ce ''A kowacce shekara 'yan Najeriya na kashe kusan biliyan 200 wajen biyan kudin makaranta a jami'o'in kasar Ghana''

    ''Ya kamata gwamnati ta bai wa bangare ilimi fifiko a kasar nan, saboda dukkanmu mun je makaranta'' in ji Shugaban

    Tun a ranar Litinin 14 ga watan Fabrairu ne kungiyar ASUU, ta tsunduma yajin aikin gargadi ga gwamanatin Najeriya na tsawon wata guda sai dai daga baya ƙungiyar ta mayar da yajin aikin na Illa Masha Allahu.

  20. Barkanmu da warhaka

    Abdullahi Bello Diginza ne ke muku barka da safiyar Laraba, 20 ga watan Yulin 2022. A yau ma za mu ci gaba da kawo muku labarai da rahotanni kai-tsaye kan abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

    Za ku iya ziyartar shafinmu naFacebookkoTwitterko kuma naInstagramdomin bayyana ra'ayoyinku kan irin labaran da muke wallafawa ko kuma tafka muhawara a kai.