Sai da safenku
Mun kawo ƙarshen rahotanni a wannan shafin.
Mu haɗu da ku gobe idan Allah ya kai mu. Ni ne Umar Mikail ke cewa mu kwana lafiya.
Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Wannan shafi ne d ake kawo muku labarai da rahotanni na abubuwan da ke faruwa a Najeriya da wasu sassan duniya.
Awwal Ahmad Janyau and Umar Mikail
Mun kawo ƙarshen rahotanni a wannan shafin.
Mu haɗu da ku gobe idan Allah ya kai mu. Ni ne Umar Mikail ke cewa mu kwana lafiya.
Jam'iyyar Labour a Australia ta lashe babban zaben kasar karon farko cikin shekara 10.
Shugaban Jam'iyar, Anthony Albanese, ya shaida wa magoya bayansa ya yi farin ciki da damar da suka ba shi ta zama firaministan kasar.
Albanese ya ce: "Kun girmama ni da wannan damar da kuka ba ni ta zama Firaministan Australia na 31 a tahiri."
Ya ce yana so a rantsar da shi a ranar Litinin domin ya samu halartar taron da za a yi a Tokyo da shugabannin Amurka da Japan da kuma Indiya.
A yayin bayaninsa, ya bayyana yadda ya fito daga gidan masu karamin karfi, yana cewa yana fatan nasararsa "ta zaburar da masu tasowa su kai ga matsayinsa a nan gaba".
Shugaban gasar La Liga ta Spaniya, Javier Tebas, ya caccaki PSG da mamallakin ƙungiyar ɗan ƙasar Qatar, Nasser Al-Khelaifi, game da sabon kwantaragin da suka ba wa Kylian Mbappe na miliyoyin kuɗi.
Cikin wani saƙon Twitter, Tebas ya ce: "Abin da PSG ke son yi da ba wa Mbappe wannan maƙudan kuɗin bayan ta sanar da asarar miliyan yuro 700 a 'yan shekarun nan kuma tana da ƙunshin albashi [da take biya] na yuro miliyan 600, cin fuska ne ga ƙwallon ƙafa."
Rahotanni sun tabbatar da cewa Mbappae zai sanya hannu kan yarjejeniya mai gwaɓi ta tsawon shekara uku a PSG.
An sha alaƙanta ɗan wasan mai shekara 23 da ya lashe Kofin Duniya a 2018 da komawa Real Madrid, amma yanzu ya amince ya tsawaita zamansa a birnin Paris tare da zakarun Ligue 1.
A cewar wani rahoto da wata hukumar Ligue ta wallafa a watannan mai suna Ligue de Football Professionel (LFP), PSG ta yi asarar yuro miliyan 224.3 a kakar 2020-21.
Hakan ta faru ne bayan asarar yuro miliyan 124.2 a kakar 2019-20 sakamakon annobar korona bayan an katse gasar ta Ligue 1 a watan Maris na 2020.
Shugaban Turkiyya Rajib Tayyib Erdogan ya tattauna da shugabannin Sweeden da Finland ta wayar tarho.
Yayin tattaunawar tasu, Erdogan ya buaci su dauki matakin da ya dace na kawo karshen goyon bayan da suke bai wa abin da ya kira kungiyoyin " 'yan ta'adda".
A wannan makon ne kasashen biyu suka nemi su shiga kungiyar ƙawancen tsaro ta Nato.
Sai dai Turkiyya wadda ita ma mamba ce a kungiyar, ta yi barazanar kawo tsaiko ga bukatar tasu, wadda ke neman amincewar duka mambobin kungiyar.
Erdogan ya zargi kasashen biyu da goyon bayan mayakan Ƙurdawa, da kuma kungiyar 'yan aware ta PKK.
Albarkacin cikar BBC Hausa shekara 65 da kafuwa ranar 13 ga watan Maris na 2022, muna kawo muku hirarraki da tsofaffin ma'aikatanmu.
Mun fara fitar da jerin hirarrakin ranar Talata 1 ga watan Maris na shekarar 2022.
Tsoffafin ma'aikatan sun yi bayanai ne a kan yadda suka samu aikin BBC da yadda ya kasance musu, da rayuwa bayan sun bar aikin da dai wasu abubuwan da suka shafe su.
A yau za mu gabatar muku da hira ne da tsohon abokin aikinmu Idris Muhammad Amin.
Rundunar sojan Najeriya ta ce ta kashe wasu 'yan ƙungiyar IPOB biyu da take nema tare da lalata sansanin ƙungiyar a Jihar Imo da ke kudancin ƙasar.
Kakakin sojin Najeriya Birgediya Janar Onyema Nwachuku ya ce dakarunsu tare da haɗin gwiwar 'yan sandan DSS sun afka wa sansanin IPOB ranar Juma'a a Ƙaramar Hukumar Orlu.
"Dakaru sun lalata sansanin ba da horo bayan musayar wuta da su, inda aka kashe ƙasurguman miyagu biyu na ƙungiyar da ke cikin jerin mutanen da jami'an tsaro suka fi nema waɗanda suka addabi mazauna yankunan Orlu, da Orsu, da Njaba," in ji sanarwar.
"Haka nan dakaru sun lalata wani wurin bauta da 'yan ƙungiyar ke amfani da shi wajen yin addu'o'i, da kuma wani wurin haɗa makamai."
Sanarwar ta ƙara da cewa sojoji sun ƙwace bindigar harba-ruga uku da ƙaramar bindiga ƙirar gida da kuma layu da sauran makamai.
Rundunar haɗin gwiwa ta Multinational Joint Task Force (MNJTF) mai yaƙi da Boko Haram a yankin Tafkin Chadi ta ce ta tarwatsa sansanin ƙungiyar 10 a arewa maso gabashin Najeriya.
Dakarun rundunar da suka ƙunshi sojojin Nijar da na Najeriya, da kuma dakarun rundunar Operation Hadin Kai ta Najeriya, sun fara aikin ne ranar Talata da ta wuce.
Wata sanarwa daga kakakin MNJTF, Kanar Kamarudeen Adegoke, ta ce dakarunsu sun gudanar da aikin fatattakar 'yan Boko Haram a garuruwan Grada, da Kwatan Maishayi, da Daban Karfe, da Daban Gajere, da Tumbun Buhari da kuma Tunbun Abuja.
Sai dai sanarwar ta ce dakaru ba su fafata da "ƴan ta'addan" ba saboda sun gudu daga sansanonin nasu a lokacin sharar.
Ya ƙara da cewa sojoji sun yi nasarar ɗebe makamai daga wuraren, ciki har da katan-katan na kifi, da hatsi, da kuma babur.
Matsalar tsaro na cikin manyan matsalolin da ke ci wa al`ummar Najeriya tuwo a kwarya.
Gwamnatoci na ikirarin cewa suna bakin kokarinsu, amma za a iya cewa har yanzu hakar ba ta cimma ruwa ba.
Batun tsaron ne ya mamaye alkawuran da masu neman shugabancin kasar suke yi wa jama`a.
Manjo Hamza Almustapha, tsohon babban dogarin tsohon shugaban Najeriya, marigayi janar Sani Abacha da ke neman takara a jam`iyyar Action Alliance ya yi alkawari irin wannan, kuma a filin Gane Mini Hanya na wannan makon ya tattauna da Ibrahim Isa a kan aniyarsa ta share wa `yan Najeriya hawaye a cikin kankanin lokaci. Sai dai ya fara ne da bayani a kan dalilin da ya sa ba ji duriyarsa ba tsawon wani lokaci
An tura shugabannin gamayyar kungiyoyinadawa na Wakit Tamma a Chadi zuwa gidan yari da da ke tsakiyar kasar.
A cikin rahoton da ta bayar, jaridar Alwihda mai goyon bayan gwamnati ta ce: "An sauya wurin da ake tsare da Wakit Tamma da shugabannin kungiyoyin fararen hula da suka halarci zanga-zangar adawa da manufofin Faransa a Chadi a ranar 14 ga Mayu.”
Ta ƙara da cewa: "A ranar 20 ga Mayu aka mayar da su cibiyar Klessoum da hukumar leken asiri ke tsare mutane, kafin aka sauya su zuwa Moussoro da ke lardin Barh El Gazel tsakiyar Chadi.
Duk da cewa ba a bayyana dalilan da suka sa aka mika su ba, amma majiyar da jridar ta ruwaito ta ce hakan ya faru ne saboda matsalar tsaro.
Daga cikin wadanda aka sauya wa wuri sun hada da mai magana da yawun Wakit Tamma, Max Loalngar da Hissein Massar Hissein shugaban gamayyar kungiyoyin farar hula da Youssouf Korom, babban sakataren kungiyar 'yan kasuwa na kasar Chadi.
Zanga-zangar da kawancen Wakit Tamma suka shirya a ranar 14 ga watan Mayu don nuna adawa da Faransa ta rikide zuwa tarzoma inda aka kama wasu jagororin adawa da dama.
Shugaban Amurka Joe Biden ya ce a shirye yake ya yi gaba da gaba da shugaban Koriya ta Arewa Kim Jong-Un.
Biden wanda ke ziyara a Koriya Ta Kudu ya ce zai yi tattaunawar ne kawai idan Mista Kim ya tabbatar da gaskiya kuma da gaske yake.
Shugaban na Amurka da takwaransa na Koriya Ta Kudu a Seoul, Yoon Suk-yeol sun tattauna yiyuwar karo jiragen yakin Amurka, da makamai masu linzami a Koriya Ta Kudu.
Tsohon shugaba Donald Trump shi ne shugaban Amurka na farko da kai ziyara Koriya Ta Arewa. Ya gana da Kim sau uku.
A Najeriya yayin da aka samu bullar cutar kyandar biri, masana a fannin kiwon lafiya sun bayyana wasu hanyoyi na kaucewa kamuwa daga cutar, musamman a tsakanin kananan yara.
Cutar wadda asalinta ana kamuwa da ita ne daga dabbobin daji, amma tana bazuwa a tsakanin mutane, kuma tafi tsanani a tsakanin yara.
Sai dai kamar sauran cutar virus, ita cutar kyandar biri bata da magani.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar Bauchi, CP Umar Mamman Sanda, ya bayar da umarnin gudanar da bincike kan rikicin da ya barke a karamar hukumar Warji a jihar Bauchi, sakamakon ɓatanci ga addinin Islama da ake zargin wata mata ta yi a yankin Katangan.
Rundunar ƴan sandan jigar ta ce an samu jikkatar mutane da dama kuma an ƙona gidaje shida da shaguna bakwai sakamakon wani saƙon ɓatanci ga addinin Musulunci na wata mata mai suna Rhoda Jatau mai shekara 40 ma’aikatar lafiya a ƙaramar hukumar da aka wallafa a kafofin sada zumunta.
Wannan na zuwa bayan kisan wata ɗaliba Kirista a Sokoto da aka zarga ta zagi Annabi SAW a WhatsaApp
Rundunar ƴan sandan Bauchi ta ce jami’anta sun ƙoƙarin shawo kan rikicin kuma ƙura ta lafa yayin da suke ci gaba da aikin wanzar da zaman lafiya.
Mata msu gabatar da labarai a talabijin sun fito ba tare da rufe fuska ba, suna masu bijerewa dokar Taliban da ta ba matan Afghanistan umarnin rufe fuska a bainar jama'a domin dacewa da tsarin addinin Islama
Tun da farko tsohon shugaban Afghanistan Hamid Karzai a wata hira da Kristin Amanpour a gidansa a Kabul ya yi kira ga matan masu gabatar da labarai su bijerewa dokar, yana mai cewa "wannan bai shafi hijabi kuma ba ya da nasaba da al'adun Afghanistan."
Ya kuma yi kira ga Taliban su janye matakin yana mai cewa mataki ne da zai shafi martabar Afghanistan a idon duniya.
A ranar Alhamis ne Taliban ta umarci mata masu gabatar da labarai a kafofin talabijin na Afghanistan su rufe fuskokinsu, amma kuma yawancinsu da ke gabatar da labarai kamar Tolo News da Ariana da Channel One da Shamshad dukkaninsu sun bijerewa umarnin.
Hukumar leƙen asirin Birtaniya MI5 ta ce ta gano kusan ƴan ƙasar 10,000 da wasu masu leƙen asiri na ƙasashen waje ke bibiya ta hanyar amfani da shafukan bogi a Facebook da LinkedIn.
Masu leƙen asirin na bibiyar mutane a muhimman hukumomin gwamnati a kafofin sada zumunta suna tambayarsu wasu muhimman bayanai.
Wata sabuwar manhaja ta gwamnatin Birtaniya da ake kira The Think Before You Link na taimakawa mutane gano maso leƙen asiri na ƙasashen waje da ke fakewa a shafukan jabu a kafofin sadarwa na intanet.
An samar da manhajar ne ga jami'an gwamnati da kuma waɗanda ke aiki a wasu muhimman wurare, amma kuma kowa na iya sauke manhajar.
Manajan kungiyar kwallon kafa ta Ingila, Newcastle United, ya ce ba shi da iko kan daya daga cikin tufafin da kungiyar ke son amfani da su a kakar mai kamawa – wanda da alama ya yi kama da irin na ƴan wasan Saudiyya.
Eddie Howe ya shaida wa manema labarai cewa yana sane da sukar tsarin tufafin.
Hotunan da aka fitar na samfurin tufafin ƙungiyar a kaka mai zuwa a makon da ya gabata ya janyo suka daga ƙungiyoyin kare haƙƙin bil'adama.
Amnesty International ta ce bisa ga dukkan alamu wata hujja ce da ke nuna cewa gwamnatin Saudiyya na son yin amfani da Newcastle wajen kawar da kai daga ayyukanta na keta haƙƙin dan Adam.
A watan Oktoba ne wani kamfani da ke samun goyon bayan Masarautar Saudiyya ya karɓi ragamar Newcastle.
Wata kotu a birnin Lagos a Najeriya ta yankewa wani dan kasar Denmark hukuncin kisa.
Babbar kotun ta Legas ta kama mutumin mai shekara 53 da laifin kisan matarsa Zainab 'yar Najeriya, da 'yarsu mai shekara uku da ake kira Petra a wani rikicin iyali.
Shekaru hudu kenan ana ta fadi tashigaban shari'a kafin yanke masa hukuncin kisa ta hanyar rataya a ranar Juma’a.
Gwamnatin Legas ce ta shigar da ƙara tana zargin Peter Nielsen da laifin kisan matarsa da ƴarsa kuma Mai Shari’a Bolanle Okikiolu-Ighile ta yanke masa hukuncin kisa ta hanyar rataya.
Sai dai ba kasafai ake aiwatar da hukuncin kisa a Najeriya ba saboda matsalolin kare haƙƙin bil'adama, kuma duk da cewa har yanzu kotuna na yanke hukuncin yawanci mutum kan kare rayuwarsa ne a tsare.
Ma'aikatar lafiya a Falasdinu ta ce sojojin Isra'ila sun harbe wani matashi a wani samame da suka kai wani sansanin 'yan gudun hijira da ke gabar yammacin kogin Jordan.
Haka kuma sun ce wani matashi dan shekara sha takwas ya ji mummunan rauni.
Sansanin 'yan gudun hijira na Jenin wuri ne da ake yawan samun rikici tsakanin sojojin Isra'ila da Falasdinawa.
A makon da ya gabata ne aka harbe wata yar jaridar Aljazeera Shireen Abu Akleh a wajen, lokacin da take ba da labarin wani hari da Isra’ila ta kai sansanin.
Rasha ta rufe hanyar shigar da iskar gas zuwa Finland, kamar yadda kamfanin samar da iskar gas na Finland ya tabbatar..
Katafaren kamfanin makamashi na Rashar Gazprom, ya ce kasar Finland ta ki cika umarnin Rasha na biyan kudin man da ta ke saya da kuɗin Rubble na Rasha, maimakon duro da dala.
Kasashen turai na na adawa da matakin na Rasha inda ta dage sai sun biya ta da kudin ƙasarta don kaucewa kawo cikas ga tasirin takunkuman da tuni aka ƙaƙabawa Rasha.
Ƙasashen Bulgaria da Poland sun fuskanci hukunci irin wannan daga gwamnatin Moscow,saboda sun bijirewa biyan kudin na Rasha.
Sama da mutum 80 ne aka tabbatar sun kamu da cutar kyandar biri a kasashe akalla 12 na Turai.
Hukumar Lafiya ta Duniya ta ce ana binciken wasu mutane 50 da ake zargi sun kamuwa da cutar - ba tare da bayyana sunayen kasashe ba - kuma ta yi gargadin cewa akwai yiwuwar a samukaruwar adadin.
An tabbatar daɓullar cutar a ƙasashen Turai 9, da kuma Amurka, Canada da Australia.
Cutar Kyandar biri ta fi yawa a a Tsakiya da Yammacin Afirka.
Cuta ce da ba kasafai ake kamuwa da ita ba kuma yawancin mutane suna murmurewa cikin 'yan makonni, a cewar Ma'aikatar Lafiya ta Burtaniya.
Cutar ba yaduwa sosai tsakanin mutane kuma barazanar yaduwarta ga al’umma ba ya da yawa.
Babu wata allurar rigakafi ta Kyandar biri, amma rigakafin kyanda na samar da kariya da kashi 85, saboda yanayin cutukan kusan iri ɗaya ne.
Maraba da kasancewa da mu a wannan shafin da muke kawo labarai da rahotanni kan abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya