Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

An sace mutane 'da dama' a hanyar Kaduna zuwa Abuja

Wannan shafi ne d ake kawo muku labarai da rahotanni na abubuwan da ke faruwa a Najeriya da wasu sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Awwal Ahmad Janyau and Mustapha Musa Kaita

  1. Umar Sulaiman Akko: Abubuwan da ba zan manta da su ba a lokacin da na yi aiki da BBC

  2. Amurka na shirin cire wa Venezuela takunkumi

    Amurka na shirin cire takunkumin da ta saka wa gwamnatin Venezuela a matsayin wata hanya ta bayar da ƙarfin gwiwa a tattauna da ƴan adawa.

    Amurka da kusan akasarin ƙasashen Turai na zargin Shugaba Nicolas Maduro da tauye dimokraɗiyya da kuma ƙin amincewa da shugaban adawa na ƙasar wato Juan Guaido a matsayin zaɓaɓɓen shugaban Venezuela.

    Amurka ta ce dukansu suna son a ci gaba da wannan tattaunawa a Mexico inda a bara ne aka dakatar da wannan tattaunawar.

    Sakamakon wannan takunkumin, an haramta wa kamfanonin Amurka da Amurkawan cinikayya da jama'a da kuma kamfanonin da ke da alaƙa da gwamnatin Mista Maduro.

  3. Mutum bakwai sun mutu a India sakamakon ambaliya

    Ambaliyar ruwa tare da zaftarewar kasa a jihar Assam da ke India, sun janyo mutuwar mutum bakwai.

    Haka kuma rahotanni sun ce wasu fiye da dubu 30 kuma suka bar muhallansu sannan gadoji da hanyoyi duk sun lalace sakamakon ambaliyar ruwan.

    An dai soke zirga-zirgar jiragen kasa a yankin. Hukumar kula da yanayi ta kasar ta yi hasashen cewa za a samu ruwan sama kamar da bakin kwarya a kwanaki masu zuwa.

    Ana dai yawan samun ambaliyar ruwa a Assam a lokutan da damuna ta kankama abin da kwararru suka ce sauyin yanayin da ake samu ne ke janyo hakan.

  4. An sace mutane 'da dama' a hanyar Kaduna zuwa Abuja

    Rahotanni daga Najeriya na cewa masu garkuwa da mutane sun sace mutane da dama a kan hanyar Kaduna zuwa Abuja a ranar Talata.

    Wani wanda ya shaida lamarin ya bayyana wa BBC cewa lamarin ya faru ne a garin Katari da misalin 4:30 na yammaci.

    Ya bayyana cewa akwai motoci da dama waɗanda suna ajiye a kan ɓangaren zuwa Kaduna da ɓangaren dawowa da aka yi awon gaba da masu motocin.

    Ya kuma ce bayan faruwar lamarin jami'an tsaro masu ɗumbin yawa sun isa wurin domin kai ɗauki.

    Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na Jihar Kaduna Samuel Aruwan ya tabbatar da faruwar lamarin inda ya ce jami'an tsaro sun yi musayar wuta da yan bindigar amma babu ƙididdiga ta mutanen da aka sace.

  5. Gwamnatin Najeriya ta ja kunnen kamfanin Facebook

    Ministan watsa labarai da al'adu na Najeriya Alhaji Lai Mohammed ya buƙaci shafin Facebook da sauran shafukan sada zumunta da su daina barin ƴan ƙungiyar IPOB da ke fafutikar kafa ƙasar Biafra su rinƙa amfani da shafin wurin neman tayar da zaune tsaye ko kuma haɗa rikicin ƙabilanci.

    Ministan ya bayyana haka ne a Abuja a ranar Talata bayan wata tattaunawa da ya yi tare da wakilan kamfanin Facebook.

    Lai Mohammed ya bayyana cewa tun da gwamnatin tarayya ta ayyana IPOB a matsayin ƴan ta'adda, Facebook ba shi da hurumin ba yan IPOB damar bayyana ra'ayinsu.

    Ministan ya bayyana cewa duk da an dade ana ta ƙorafi ga Facebook kan ayyukan ƴan IPOB, amma kamfanin bai yi komai ba da zai dakatar da su.

    Ya ce a yanzu gwamnatin Najeriya za ta ci gaba da sa ido kan Facebok da sauran shafukan sada zumunta a ƴan kwanakin nan domin tabbatar da cewa sun bi ƙa'idoji.

  6. An tura ƴan majalisa a Tunisia gidan yari saboda cin mutuncin ƴan sanda

    Wata kotun soja a Tunisia ta yanke wa wasu ƴan majalisar dokokin ƙasar huɗu hukuncin zaman gidan yari sakamakon samunsu da laifin cin mutuncin ƴan sanda.

    Waɗanda aka tura gidan yarin sun haɗa da Saif Eddine Maklouf wanda ke jagorantar Jam'iyyar Karama a rusassar majalisar ƙasar.

    An tura ɗaya daga cikin manyan masu caccakar Shugaba Kais Saeid na ƙasar zaman gidan yari na wata huɗu haka su ma sauran ƴan jam'iyyar sun samu irin wannan hukuncin.

  7. Yadda Ukraine ke kwashe sojojinta da suka makale a Azovstal

    Ukraine ta tabbatar da kwashe daruruwan sojojinta da suka shafe fiye da wata biyu makale a kamfanin sarrafa karafa na Azovstal da ke birnin Mariuopol.

    Mataimakiyar ministar tsaron kasar Hanna Maliar ta ce an kwashe sojoji 53 da suka ji munanan raunuka zuwa garin Novoazovsk da mayaka masu samun goyon bayan Rasha suke rike da shi.

  8. Harim makamai masu linzami ya kashe mutum 8 a Ukraine

    Hukumar agajin gagawa a Ukraine ta ce an kashe akalla mutum takwas, yayin da wasu 12 kuma suka samu raunuka, bayan wasu makamai masu linzami da Rasha ta harba sun fada kan wasu jerin gidajea garin Desna da ke arewacin Kyiv.

    A kusa da gidajen akwai wani sansani da ake horar da sojoji.

    Lamarin ya faru ne da safiyar yau, inda wani shugaba a yankin yammacin Lviv ya ce harin makami mai linzamin ya lalata wasu kayayyaki a tashar jirgin kasan da ke yankin.

    Rasha na ta kai hare hare kan wuraren sufuri da kuma depo depo din man fetir a kusa da Lviv.

  9. PDP ta sake ɗage ranakun tsayar da ƴan takara

    Jam'iyyar PDP mai hamayya a Najeriya ta sanar da sake ɗage ranakun tsayar da ƴan takararta a zaɓen 2023.

    Jam'iyyar ta wallafa takardar da ta aika wa hukumar Inec da ke bayyana sabbin ranakun da ta tsayar na zaɓen fitar da ƴan takarar ƴan majalisar jiha da na tarayya da na gwamnoni.

  10. Taliban ta ce ta kusan buɗe makarantun mata a Afghanistan

    Gwamnatin Taliban ta ce ba da daɗewa ba za ta buɗe makarantun mata, kamar yadda kamfanin dillacin labarai na Ariana News ya ruwaito.

    Kakakin gwanatin Taliban Zabihullah Mujahid, ya ce an samu ci gaba a tattaunawa da malaman addini kan bude makarantun mata, yana mai cewa ba da dacewa ba za a bude makarantun.

    Makarantun mata sun kasance a rufe a Afghanistan tun lokacin da Taliban ta kwace mulki a watan agustan bara. Taliban ta ce sai ta ɗauki mataki kan kayan makarantan mata wanda ya dace da shari’a da kuma al’adun Afghanistan.

  11. An cika shekara 25 da faɗuwar gwamnatin Mobutu a DR Congo

    An cika shekara 25 da faɗuwar gwamnatin kama-karya ta Mobutu Sese Seko a Jamhuriyyar Dimokuradiyyar Congo

    Mista Mobutu ya mulki DR Congo, da a lokacin ake kira Zaire, sama da shekara 30 amma a tsere daga Kinshasa, a daren da 17 ga Mayun 1997 yayin da ƴan tawaye suka doshi babban birnin ƙasar.

    Jagoran ƴan tawaye a lokacin, Laurent Kabila, ya kwaci mulki kuma ya sauya sunan ƙasar zuwa Jamhuriyyar Dimokuradiyyar Congo.

    Mobutu ya mutu bayan shekara ɗaya bayan ya gudu zuwa Morocco inda aka binne shi.

    A 2013 shugaba Joseph Kabila ya ce gwamnati za ta karɓo gawar amma daga baya babu wani mataki bayan sanarwar.

    Masu adawa da Mabutu na zarginsa a matsayin marar tausayi kuma mai rashawa wanda ya wawushe arzikin ƙasar.

    17 ga Mayu, rana ce ta hutu a Jamhuriyyar Congo. Inda ake gudanar da faretin soja a Kinshasa.

  12. Kotu ta tsawaita wa'adin rusa tagwayen bene hawa 40 a Indiya

    Kotun ƙoli a Indiya ta bayar da wa'adin wata uku a rusa tagwayen bene hawa 40 na Supertech a Noida, yankin Utter Pradesh.

    Hukumar da ke rusa dogayen bene ta nemi ƙarin lokaci a kotun. Ya kamata a rusa tagwayen benen a ranar 22 ga Mayu, amma yanzu kotu ta ce sai zuwa 28 ga Agusta.

    Tagwayen benen na Supertech, an gina su ne ba bisa ka'ida ba, inda kotu ta bayar da umarnin a rusa.

    Tsawon benen ya kai mita 103, kuma wannan ne karon farko da za a rusa wani dogon bene a Indiya.

  13. Wani bincike ya ce sauro ya fi cizon mutane da rana

    Wani bincike kan halayyar cizon sauro da ke sa zazzaɓin malariya a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya ya gano cewa kusan kashi daya bisa uku na cizon sauro na faruwa ne cikin gida da rana.

    Binciken da aka gudanar a baya - bisa hasashen cewa sauro ya fi cizon mutane da dare - ya mayar da hankali wajen ɗaukar matakan yaƙi da zazzabin cizon sauro kan gidan sauro da aka yi wa magani.

    Sabon binciken ya nuna cewa ya kamata a faɗaɗa matakan yaƙi da zazzabin cizon sauro ba a gida kawai ba – har zuwa makarantu da wuraren aiki da shaguna.

    Masu bincike sun dogara ne kan binciken da aka kwashe shekara guda ana yi kan sauro da aka tattara bayan cizon abubuwa a Bangui babban birnin Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya.

    Malariya na kashe dubban daruruwan mutane a kowace shekara, wadanda yawancinsu kananan yara ne a Afirka.

  14. Taliban ta rusa hukumar kare haƙƙin ɗan adam da majalisa a Afghanistan

    Taliban ta rusa wasu manyan hukumomi guda biyar na tsohuwar gwamnatin Afghanistan da ke samun goyon Amurka inda ta bayyana su marar amfani.

    Hukumomin sun haɗa da hukumar kare haƙƙin ɗan adam da majalisun dokoki.

    Kakakin Taliban ya ce hukumomin ba su cikin kasafin kuɗin ƙasar na shekara.

    Tun da Taliban ta ƙwace mulki a Afghanistan a watan Agusta, hukumar kare haƙƙin ɗan adam ba ta yi aikinta ba a Afghanistan

  15. Gwamnatin sojin Mali ta ce ta murƙushe yunƙurin juyin mulki

    Gwamnatin Sojin Mali ta ce ta murƙushe wani yunƙurin juyin mulki a makon da ya gabata da wasu sojoji suka jagoranta da suka samu goyon bayan ƙasashen yammaci da ba a bayyana.

    A jawabin da aka bayyana a kafar talabijin, “wasu tsiraru jami’an sojin Mali sun yi yunƙurin kai hari a ranar 11 a 12 ga watan Mayun 2022.”

    “Wadannan ƙasashen sun samu goyon bayan ƙasashen yammaci. An murƙushe yunƙurin saboda ƙwarewar hukumomin tsaro.

    Sai dai sanarwar ba ta yi cikakken bayani ba game da al’amarin.

    Sanarwar ta ƙara da cewa waɗanda aka kama za a gurfanar da su, amma ba tare bayyana sunayensu ba.

    Wasu majiyoyi sun ce kusan mutum 10 aka kama ake tsare da su.

  16. Zaki ya tsere bayan ya kai wa mai tsaron gandun daji mummunan hari

    Wani mutum mai shekara 40 ya tsallake rijiya da baya bayan da zaki ya kai masa hari a lardin Gaza a kudancin Mozambique.

    Mutumin ya samu mummunan hari kuma yanzu haka yana jinya a asibiti.

    Wani jami'i ya ce zakin da ya kai wa mutumin hari ya kuma tsere daga gandun dajin Limpopo.

    Ya ce masu kula da andun daji da hukumomin yankin za su dauki matakan da suka dace kan lamarin da kuma kawar da fargaba ga mutane.

    Rikici tsakanin namun daji da mutane ba sabon abu ba ne a mozambique.

    A farkon shekarar nan, an kashe wani zaki bayan ya kai wa wasu mutum uku hari kusa da wani gandun daji a lardin Niassa.

    Namun dajin da suka fi barazana sun hada da zaki da kada da gwaggon biri da giwaye da kuma kura.

  17. Korona na ƙara bazuwa a Koriya ta Arewa

    Koriya ta Arewa ta sanar da cewa ƙarin mutun 170,000 sun kamu da cutar korona.

    Yanzu haka an killace mutum 650,000 a fadin kasar.

    Babban birnin kasar Pyongyang ne ya fi fuskantar bala'in annobar, inda yanzu haka sojoji ke taimakawa jami'an lafiya raba magani.

    Haka ma malaman makaranta da dalibai likitoci na taimakawa wurin gano wadanda suka yi hulda da masu ɗauke da cutar.

    Koriya ta Kudu mai makwabtaka ta ce har yanzu tana jiran amsa daga makwaciyartakan shirinta na taimakawa.

  18. ‘Yaran da ke fama da yunwa na ci gaba da karuwa’

    Majalisar Dinkin Duniya ta ce adadin yaran da ke fama da tamowa na kara karuwa a fadin duniya.

    Majalisar Dinkin Duniya tace ba komi ya kawo haka ba illa zuwan annobar korona, da sauyin yanayi da kuma rikice-rikice a kasashe.

    Kazalika majalisar ta ce kasashen Gabashin Afrika da Afghanistan ne lamarin yafi kamari.

    A Afghanistan kadai sama da yara miliyan daya ne ake saran za su fuskancimatsananciyar tamowa, yayin da ake sa ran a samu yara miliyan biyu cikin wannan yanayi a kasashen gabashin Afrikar.

    Babbar daraktar UNICEF Catherine Russell kenan take cewa ko wane daga cikin yaran nan na bukatar agajin lafiya da gaggawa kafin su kai matakin da ake gudu.

  19. Maraba

    Muna maku maraba da kasancewa da mu a wannan shafin da muke kawo labarai da rahotanni kan abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya