Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Ganduje ya zaɓi mataimakinsa Nasiru Gawuna don ya gaje shi

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da Afirka da sauran sassan duniya musamman batutuwan da suka shafi Sallah karama.

Rahoto kai-tsaye

Awwal Ahmad Janyau and Umar Mikail

  1. Said a safenku

    Mun zo ƙarshen rahotannin a wannan shafi na rahotanni kai-tsaye.

    Kafin mu sake haɗuwa da ku gobe don samun wasu sabbi, ku duba ƙasa don karanta waɗanda muka kawo a yau Asabar.

    Umar Mikail ke muku fatan alheri.

  2. Dalilin da ya sa kamfanonin sufurin jirgi a Najeriya suka janye yajin aiki

    Ƙungiyar kamfanonin sufurin jiragen sama a Najeriya ta ce ta bayyana dalilin da ya sa ta fasa shiga yajin aikin da ta tsara daga Litinin mai zuwa.

    Shugaban ƙungiyar Airline Operators of Nigeria (AON), Abdulmunaf Yunusa Sarina, ya faɗ wa BBC Hausa gwamnatin Najeriya ta ba su tabbacin cewa za ta shiga tsakaninsu da kamfanonin da ke samar da man fetur da jirgi ke amfani da shi.

    Ya ce sun ba wa gwamnatin wa'adin awa 48 don ta lalubo hanyoyin sauƙaƙa musu wajen samun man jirgi mai rahusa.

    Tun farko ƙungiyar ta ce za ta dakatar da aiki ne saboda tsadar man fetur da jirgi ke amfani da shi, Jet A1, wanda ake sayarwa kan N700 a kowace lita.

    Da ma rahotanni sun ambato wasu kamfanonin na cewa ba za su shiga yajin aikin ba kamar yadda ƙungiyar tasu ta nema. Kamfanonin Ibom da Dana na cikin waɗanda aka ambato na cewa za su ci gaba da aiki.

    A jiya Asabar, gwamnatin Najeriya ta roƙi kamfanonin da kada su dakatar da ayyuka "saboda zai shafi tattalin arzikin ƙasa".

  3. Gwamna Ganduje ya zaɓi mataimakinsa Nasiru Gawuna don ya gaje shi

    Gwamnan Jihar Kano da ke arewacin Najeriya, Abdullahi Umar Ganduje, ya zaɓi mataimakinsa Nasiru Yusuf Gawuna a matsayin wanda zai gaje shi a babban zaɓe na 2023.

    Wasu majiyoyi a Fadar Gwamnatin Kano sun shaida wa BBC Hausa an cimma matsayar ce yayin wani taron masu ruwa da tsaki na jam'iyyar APC mai mulkin Kano da aka gudanar a yau Asabar.

    Sai dai wata majiya da ta nemi a ɓoye sunanta ta faɗa wa BBC Hausa cewa har yanzu ba a kai ga daddale wannan zaɓi ba a hukumance.

    Kazalika, an ruwaito cewa taron ya amince Kwamashinan Ƙananan Hukumomi da Harkokin Masarautu Murtala Sule Garo ya zama mataimakin Gawuna a takarar tasu.

    Ana kallon matakin a matsayin wani sauyi daga goyon bayan da Murtala Garo ke samu na wasu jiga-jigan gwamnatin, ciki har da matar gwamna Hajiya Hafsat Ganduje, a matsayin wanda zai maye gurbin Ganduje.

    Matakin na zuwa ne kwana biyu bayan Kotun Ƙoli ta tabbatar wa ɓangaren Ganduje shugabancin APC a Kano sakamakon rikicin da ya biyo bayan zaɓukan shugabanci a watan Oktoba tsakaninsa da ɓangaren tsohon Gwamna Sanata Ibrahim Shekarau.

    • Kotun Koli ta bai wa bangaren Ganduje nasara a kan zabukan shugabancin APC a KanIbrahim
    • Shekarau: Rashin iya jagorancin Ganduje ne silar rikicin APC a Kano
  4. Hukumar NDLEA ta kama mata biyu masu ciki da zargin safarar miyagun ƙwayoyi

    Hukumar yaƙi da shan miyagun ƙwayoyi a Najeriya (NDLEA) ta ce ta kama wasu mata biyu masu ciki a filin jirgin sama na Murtala Muhammed suna shirin safarar haramtattun ƙwayoyi.

    Wata sanarwa da hukumar ta fitar ta ce a ranar Laraba, 4 ga watan Mayu an kama wasu katan-katan na kwalaben giya da ake zargin suna ƙunshe da haramtattun ƙwayoyi, inda nan take aka kama wadda ta kai kayan don aikawa da su Dubai mai suna Shola Ogunrinde.

    Ci gaban bincike ya sa aka kama wata mace mai ciki mai suna Seun Babatunde, waddda ke gudanar da harkokin sayar da kayan maye a Iyana da ke Legas, in ji NDLEA.

    Kakakin NDLEA, Femi Babafemi, ya ce an kama mai ciki ta biyun ne mai suna Gloria Asibor ranar Alhamis, 5 ga watan na Mayu lokacin da take ƙoƙarin shiga jirgin Turkish Airlines zuwa Bolonia na Spaniya ɗauke da ƙwayar Tramadol 300 mai nauyin 200 da 225 giram.

    A gefe guda kuma, an kama wani mai suna Nworie Phillip Chikwendu bayan ya dawo daga Brazil ranar Talata, 3 ga watan Mayu a jirgin Qatar Airways.

    Sanarwar ta ƙara da cewa binciken da jami'ai suka gudanar ya sa suka gano fakitin hodar ibilis biyu a jakarsa ta baya ƙunshe cikin takalman silifa. Bayan an matsa da bincike ne kuma aka sake gano wasu fakiti biyu na koken ɗin.

  5. Labarai da dumi-dumi, Kamfanonin sufurin jirgin sama a Najeriya sun dakatar da yajin aiki

    Ƙungiyar kamfanonin sufurin jiragen sama a Najeriya ta ce ta fasa dakatar da zirga-zirgar jiragen da ta yi niyyar yi daga Litinin.

    Shugaban ƙungiyar Airline Operators of Nigeria (AON) Abdulmunaf Yunusa Sarina ne ya tabbatar wa BBC Hausa a yau Lahadi cewa sun jingine matakin nasu.

    Tun farko ƙungiyar ta ce za ta dakatar da aiki ne saboda tsadar man jirgi da ake sayarwa kan N700 a kowace lita.

    Da ma rahotanni sun ambato wasu kamfanonin na cewa ba za su shiga yajin aikin ba kamar yadda ƙungiyar tasu ta nema. Kamfanonin Ibom da Dana na cikin waɗanda aka ambato na cewa za su ci gaba da aiki.

    A jiya Asabar, gwamnatin Najeriya ta roƙi kamfanonin da kada su dakatar da ayyuka "saboda zai shafi tattalin arzikin ƙasa".

    Za mu kawo ƙarin bayani da zarar mun samu...

  6. Arsenal ta yi kane-kane a mataki na hudu a teburin Premier League

    Arsenal ta jaddada matsayinta na shiga gasar Zakarun Turai ta Champions League a kakar badi.

    Gunners din ta yi nasarar doke Leeds United da ci 2-1 a wasan mako na 36 da suka fafata a Emirates ranar Lahadi.

    Eddie Nketiah ne ya fara ci wa Gunners kwallo minti biyar da fara wasa, sannan minti biyar tsakani ya kara na biyu.

    Leeds United ta farke daya ta hannun Diego Llorente, amma ta karasa karawar da 'yan wasa 10 a cikin fili, bayan da aka bai wa Luke Ayling jan kati tun a minti na 27 da fara tamaula.

    Da wannan sakamakon Arsenal ta ci gaba da zama a mataki na hudu a teburin Premier League da maki 66 da tazarar maki hudu tsakaninta da Tottenham, wadda ke mataki biyar.

  7. Matar shugaban Amurka ta kai ziyarar ba-zata a Ukraine

    Matar shugaban Amurka Jill Biden ta kai ziyarar ba-zata a Ukraine yayin balaguron da take yi zuwa Romania da Slovakia, inda take jaddada goyon bayan Amurka ga ƙawayenta na Nato.

    Mrs Biden ta gana da matar shugaban Ukraine Olena Zelenska a wata makaranta da ke garin Uzhhorod, wanda yanzu ake amfani da shi a matsayin wurin ɓuya ga fararen hula.

    Uwar gidan Biden ɗin ta ce ta so ne ta nuna cewa "Amurkawa na tare da jama'ar Ukraine", inda ta ƙara da cewa yaƙin wanda yanzu ya shiga wata na uku "na rashin imani ne" kuma dole a dakatar da shi.

    Mrs Zelenska ta ce abu ne "na bajinta" mutum ya ziyarci Ukraine.

    "Mun fahimci irin haɗarin da mai ɗakin Biden ta saka kanta a ziyarar da ta kawo Ukraine, lokacin da ake ta ɓarin wuta a kowace rana, ake kunna jiniya kowace rana, har a yau," in ji ta.

  8. Shugaban Zimbabwe ya hana bankuna bayar da bashi a ƙasar

    Shugaba Emmerson Mnangagwa na Zimbabwe ya umarci bankunan ƙasar su daina ba da rancen kudade, kuma dokar ta soma aiki nan take.

    An ɗauki matakin ne domin rage yawan yaɗuwa kudaden kasar da zimmar shawo kan karayewar da darajarsa ke yi.

    Dalar Zimbabwe ta rage daraja da kusan kashi 50 cikin 100 a wannan shekara, yanayin da ya sa ta kasance kudin da a yanzu a Afirka ya fi fuskantar koma-baya.

    A wani jawabi ta kafar talabijin ɗin kasar, Shugaba Mnangagwa ya sanar da wasu matakai, ciki har da kara kudin haraji kan hada-hadar kudaden ketare tsakanin bankuna, da karbar takardar kudi a banki.

  9. Ƴan bindiga sun saki fursunoni a gidan yarin Burkina Faso

    Rahotanni sun ce aƙalla fursunoni 60 suka tsere daga gidan yarin Burkina Faso bayan harin ƴan bindiga.

    Rahotannin sun ce mahara ne ɗauke da manyan makamai suka abka gidan yarin Nouna a Kossi da ke lardin Boucle du Mouhoun arewa maso yammacin Burkina Faso suka saki fursunoni.

    Sai dai hukumomin Burkina Faso ba su tabbatar da al’amarin ba.

    Harin na zuwa bayan kashe aƙalla mutum 14 da suka kunshi ƴan sa-kai a wani harin kwanton ɓauna da aka kai wa ayarin kayan abinci a lardin Seno.

  10. “Yara miliyan shida na bukatar taimako a Syria”

    Hukumar kula da kananan yara ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce yara miliyan shida da rabi ne ke bukatar taimako a Syria - adadi mafi girma tun bayan barkewar rikici a kasar fiye da shekaru 10.

    UNICEF ta ce a cikin watanni uku na farkon wannan shekara, an kashe ko an raunata yara 213. Hukumar ta ce rikicin Syria ya yi nisa – amma kudaden da ake kashewa wajen gudanar da ayyukan jin kai na raguwa cikin sauri.

    Ta ce ta samu kasa da rabin kudaden da take bukata na wannan shekarar.

  11. Buhari na kan hanyar zuwa Ivory Coast

    Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari na kan hanyar zuwa Abidjan babban birnin Ivory Coast domin halartar taron Majalisar Ɗinkin Duniya kan kare kare muhalli musamman yadda za a magance kwararowar hamada.

    Sanarwar da fadar shugaban ta fitar ta ce Buhari zai bar Abuja a ranar Lahadi zuwa Abidjan, domin halartar taron na kwana biyu da za a soma a ranar Litinin.

    Taron ya shafi yadda za a magance kwararowar hamada da fari da zabtarwar ƙasa da sauran matsalolin muhalli, zai ƙunshi shugabannin ƙasashe da sauran masu ruwa da tsaki.

    Buhari zai tafi tare da rakiyar maƙaraban gwamnatinsa da suka ƙunshi ministan harakokin waje Geoffrey Onyeama da na muhalli Mohammed H. Abdullahi da ministan noma Dr Mahmoud Mohammed da kuma na ruwa Inginiya Suleiman H. Adamu.

  12. Masar ta saki wasu ƴan TikTok da ta kulle kan yaɗa bidiyon tsadar rayuwa

    Rahotanni sun ce hukumomin Masar sun ba da umarnin sakin wasu mutane uku da suka yaɗa wasu bidiyo na barkwanci a TikTok suna sukar hauhawar farashin kayayyaki a kasar.

    Kafar yada labaran Dostor mai zaman kanta ne ta bayar da rahoton matakin tare da ambatar lauyan kare hakkin dan adam Islam Salama.

    Mutanen ukun, da sukek iran kansu Zurafaa al-Ghalaba, masu nishadantar da mutane.

    An kama su ne a watan Afrilu kuma masu gabatar da kara sun tuhume su da " yada labaran karya" tare da tsare su na tsawon kwanaki 15 kafin a gudanar da bincike.

    Suna da mabiya sama da 140,000 aTikTok. A daya daga cikin bidiyonsu, wanda aka kalla sau miliyan 12.2, sun nuna cikin raha cewa yanzu cin kaji wani jin dadi ne a Masar.

    Tashin gwauron zabi na kayayyakin masarufi a Masar, wanda ake zargin yakin Rasha a Ukraine ya haifar ,ya sa mutane da dama na wallafa bidiyo kan halin tsadar rayuwa tare da gargadin yunwa.

  13. Kakakin majalisar Ivory Coast Amadou Soumahoro ya rasu

    Shugaban Majalisar Ivory Coast, Amadou Soumahoro, ya rasu yana da shekara 68, kamar yadda shugaban ƙasar Alassane Ouattara ya sanar.

    Mr Soumahoro wanda ya rasu a ranar Asabar, ya kasance babban mai goyon bayan shugaba Ouattara. Yana cikin waɗanda suka kafa jam'iyyar Rassemblement des Républicains (RDR), ta Mista Ouattara, a 1994.

    Tsohon ministan cinikayya Amadou Soumahoro, ya zama shugaban majalisa ne a 2019 National Assembly, inda ya maye gurbin tsohon Firaminista kuma shugaban ƴan tawaye Guillaume Soro.

    Ya kwashe watanni yana jinya a ƙasar waje. A bara ɗaya daga cikin mataimakan shugaban majalisa Adama Bictogo ya ci gaba da jagorancin majalisar.

  14. Na damu da dokar Taliban kan matan Afghanistan - Antonio Guterres

    Sakatare Janar na Majalisar Ɗinkin Duniya Antonio Guterres ya bayyana damuwa kan sabuwar dokar Taliban da ta tilasta wa mata rufe fuska a Afghanistan.

    "Na kaɗu da da sanarwar da Taliban ta fitar na cewa dole ne mata su rufe fuskokinsu a bainar jama'a kuma lalura kawai za ta fitar da su daga gida," kamar yadda ya wallafa a Twitter.

    Guterres ya yi kira ga Taliban su cika alƙawalin da suka ɗauka ga matan Afghanistan da kuma haƙƙin da ya rataya a wuyansu ƙarƙashin dokokin ƙasa da ƙasa na kare haƙƙin ɗan adam.

  15. An kwantar da Sarki Salman na Saudiyya a asibiti

    An kwantar da Sarki Salman bin Abdulaziz na Saudiyya a asibiti a birnin Jeddah domin duba lafiyarsa.

    Kamfanin dillancin labaran Saudiyya ya bayar da ɗan takaitaccen bayani daga Masarautar inda ta ce sarkin ya tafi asibitin ƙwararru na Sarki Faisal a ranar Asabar.

    Sarkin mai shekara 86 an taɓa masa aiki a 2020.

    An yi imanin cewa Yarima mai jiran gado Mohammed bin Salman ne ke riƙe da madafun iko na Saudiyya tun bayan da aka naɗa shi a shekarar 2017.

  16. Harin bom a makaranta a Ukraine ana fargabar ya kashe mutane da dama

    Mutum kusan 60 ake fargabar sun mutu bayan wani bam ya tashi a wata makaranta a gabashin Ukraine, inda dakarun gwamnati ke fafatawa da sojojin Rasha da ƴan aware.

    Gwamnan yankin Luhansk, Serhiy Gaidai, ya tabbatar da mutuwar mutane biyu, yana mai cewa mutum 60 ne ake fargabar sun mutu a ƙarƙashin ɓaraguzan makarantar da ke Bilohorivka.

    Ya kara da cewa, kimanin mutane 90 ne ke zaune a cikin ginin kuma an ceto 30, bakwai daga cikinsu sun samu raunuka.

    Mista Gaidai ya ce wani jirgin Rasha ne ya jefa bam a ranar Asabar.

    Ba a iya tantance zargin nasa kai tsaye ba kuma babu wani martani da Rasha ta mayar.

    Luhansk ya kasance yanki na fagen yaƙi yayin da sojojin Rasha ƴan aware ke neman yi wa dakarun gwamnatin Ukraine ƙawanya dakarun gwamnati, tsawon watanni biyu da fara mamayar Rasha.

  17. Birtaniya za ta sake ba Ukraine tallfi

    Birtaniya ta ce za ta bai wa Ukraine ƙarin taimakon na tallafin dala biliyan 1.6.

    Wannan ya ruɓanya taimakon da Birtaniya ta baUkraine sau uku, tun soma mamayar Rasha.

    Mista Boris ya ce abin da Putin ya yi a wurare kamar Buka laifukan yaki ne kuma hakan ya lalata kimarsa da ta gwamnatinsa.

    Mista Boris zai halarci taron shugabannin kasashen G7 a ranar Lahadi da za a tattauna da Shugaba Zelensky kan wasu karin taimakon da Ukraine ke bukata.

  18. Maraba

    Muna maku maraba da kasancewa da mu a wannan shafin da muke kawo maku labarai da rahotanni kan abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya