Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Al-Shabab ta yi iƙirarin kashe sojojin AU 170

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da Afirka da sauran sassan duniya musamman batutuwan da suka shafi Sallah karama.

Rahoto kai-tsaye

Nasidi Adamu Yahaya

  1. Rufewa

    Masu bibiyarmu a wannan shafin a nan muka zo ƙarshen kawo muku labarai da rahotanni kai tsaye, sai kuma gobe Laraba idan Allah Ya kai mu za mu ci gaba da kawo muku wasu labaran.

    Za ku iya ziyartar shafinmu na Facebook ko Twitter ko kuma na Instagram domin bayyana ra'ayoyinku kan irin labaran da muke wallafawa ko kuma tafka muhawara a kai.

  2. Ana zargin sojojin hayar Rasha da kashe mutum 12 a Jamhuriyyar Tsakiyar Afrika

    Ana zargin sojojin hayar Rasha da kashewa da azabtarwa da kuma dukan farar hula a Jamhuriyyar Tsakiyar Afrika.

    Shaidu sun shaida wa ƙungiyar Human Rights Watch cewa a wani lamari da ya faru a Yulin bara, mayaƙa masu magana da harshen Rasha sun harbe aƙalla mutum 12 waɗanda ba su ɗauke da makamai a wani shingen bincike.

    Akasarin waɗanda aka kashe an tona rami mara zurfi inda aka rufe su a kusa da Bossangoa.

    Jamhuriyyar Tsakiyar Afrika ta musanta ɗauko sojojin haya na kamfanin Wagner na ƙasar Rasha domin yaƙar ƴan tawaye.

  3. Sojojin Rasha na ci gaba da zafafa hare-hare

    Sojojin Rasha na ci gaba da zafafa hare-hare a masana'antar nan ta sarrafa karafa da ke Ukraine bayan rukunin farko na farar hular da aka kwashe daga wajen sun samu tsira.

    Majalisar dinkin Duniya ta ce an kwashi mutane fiye da dari daga masana'antar da ke birnin Mariupol inda suka shafe makwanni suna samun mafaka a ginin karkashin kasa.

    A yanzu, an kwashe akasarin mutanen zuwa birnin Zaporizhzhia yayin da sauran kuma ke can Mariupol.

    Magajin garin Mariupol ya ce kusan farar hula dari biyu ne har yanzu suke makale a masana'antar.

  4. Biden ya buƙaci a kare hukuncin kotu da ya halasta zubar da ciki

    Shugaba Joe Biden ya yi kira da a kare hukuncin kotu da ya halasta zubar da ciki a sassan Amurka bayan ɓullar wata takarda da ta nuna Kotun Koli na iya soke hukuncin.

    Mista Biden ya ce yin adalci ya bukaci kada a soke karar.

    Babban alkali a kotun, Mai Shari'a John Roberts ya tabbatar babu wani kuskure a daftarin ra'ayin amma ya jaddada cewa ba shi ne hukunci na ƙarshe ba.

    A cewar wakiliyar BBC, galibin yan majalisa daga jam'iyyar Conservative sun bayyana daftarin ra'ayin a matsayin gagarumin ci gaba, sun kuma nuna damuwa game da cin amanar da ta kai ga bullar takardar.

    Idan har aka soke hukuncin jihohin Amurka za su zama suna da yancin tsara dokokinsu da suka shafi zubar da ciki kuma tsarin zubar da ciki zai haramta a fiye da jihohi 20.

  5. Putin ya bayyana hanyoyin da za a bi a kawo ƙarshen yaƙin Ukraine

    Shugaban Rasha Vladimir Putin ya ce ƙasashen yamma za su iya taimakawa a kawo ƙarshen yaƙin Ukraine ta hanyar matsa wa Shugaba Volodymyr Zelensky lamba da kuma dakatar da ba dakarunsa makamai.

    Mista Putin ya bayyana haka ne a wayar tarho ta farko a sama da wata guda da ya yi da Shugaban Faransa Emmanuel Macron.

    Kamar yadda shafin intanet na Shugaban Rasha ya bayyana, Mista Putin ya bayyana cewa mambobin Ƙungiyar Tarayyar Turai suna nuna halin ko-in-kula da laifukan yaƙin da sojojin Ukraine ke aikatawa.

    Mista Macron ya shaida wa Mista Putin cewa akwai buƙatar Rasha ta shigo da batun yarjejeniyar tsagaita wuta domin bayar da dama ga ƙarin farar hula su bar maƙerar Azovstal da ke Mariupol.

    Ya ce a shirye yake domin ya yi aiki da ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa domin taimakawa a ɗage takunkumin da aka saka wa Rasha na fitar da abicnin Ukraine ta tekun Black Sea.

  6. Al-Shabab ta yi iƙirarin kashe sojojin AU 170

    Ƙungiyar da ke iƙirarin Jihadi a Somalia ta al-Shabab ta ce ta kashe sama da sojojin Burundi 170 waɗanda suka je Somalia gudanar da ayyukan Ƙungiyar Tarayyar Afrika wato AU.

    Al-Shabab ɗin kuma ta ce ta ƙwace iko da sansanin ƙungiyar ta AU inda a nan ne aka ajiye sojojin na Burundi kuma sansanin yana da nisan sama da kilomita 100 daga Mogadishu babban birnin ƙasar.

    Ba dai a tabbatar da iƙirarin ƙungiyar ba amma akwai rahotannin da aka samu da ke nuna cewa an yi musayar wuta sosai bayan harin da suka kai da asuba kuma shaidu sun bayyana cewa sun ga ana ta harbi daga saman jirgi mai saukar angulu.

    Masu iƙirarin jihadi na yawan kai hare-hare da kuma tayar da bama-bamai a yaƙin da suke yi da gwamnatin ƙasar Somalia.

  7. Hotunan Shugaban Majalisar Ɗinkin Duniya a Maiduguri

  8. Tsohon kocin Najeriya Gernot Rohr na son zama kocin Mali

    Tsohon kocin tawagar Najeriya Gernot Rohr ya tabbatar da cewa ya tattauna da hukumomin Mali domin zaman kocin kungiyar kwallon kafar kasar.

    Kungiyar kwallon kafar kasar tana neman mutumin da zai cike gurbin da aka bari bayan korar kocin tawagar kasar Mohamed Magassouba bayan fitar da kungiyar daga rukunin 'yan 16 a gasar cin Kofin Afrika na bana da kuma shan kashi a wasan neman cancantar shiga gasar cin Kofin Duniya.

    Hukumar kwallon kafar Mali ta yaba da rawar da Rohr ya taka a nahiyar Afirka, musamman a Najeriya inda yake neman a biya shi dala miliyan daya saboda korarsa daga aiki ba bisa ka'ida ba.

    Rohr ya shaida wa BBC Sport Africa cewa "Tattaunawar da muka yi da Mali mai armashi ce kuma tana cike da martaba.

    "Mun kwashe wasu kwanaki muna tattaunawa amma ba mu kammala ba. Mali tana da tawaga karama mai kwazo."

    A baya dai, Rohr ya horas da tawagogin Jamhuriyar Nijar, Gabon da Burkina Faso, kuma an kore shi daga aiki a Najeriya a watan Disamba, mako hudu kafin soma gasar cin Kofin Nahiyar Afirka a Kamaru.

  9. Shugaban Zimbabwe ya bukaci Birtaniya ta shiga taitayinta

    Shugaban kasar Zimbabwe Emmerson Mnangagwa ya gaya wa gwamnatin Birtaniya ta daina yin katsalandan cikin sha'anin kasarsa, kamar yadda jaridar gwamnatin kasar Herald ta ambato kakakin shugaban yana fada.

    Hakan ya biyo bayan sukar wani kudirin doka, wanda masu suka ke cewa zai bai wa gwamnatin karin damar juya kungiyoyin masu zaman kansu.

    Gwamnatin ta ce kudirin dokar zai kawo kawo karshen halasta kudin haramun da kuma kungiyoyin kasashe waje da ke daukar nauyin harkokin siyasar, sai dai masu rajin kare hakkin dan adam sun ce hakan zai bai wa hukumomi damar yin katsalandan a harkokin kungiyoyi masu zaman kansu.

    Za a zartar da kudirin dokar duk da sukar da ake yi masa, kamar yadda aka ambato Shugaba Mnangagwa yana cewa.

  10. Mutum takwas sun mutu bayan sun sha burkutu a Iran

    Mutum takwas ne suka mutu bayan sun sha burkutu a birnin Bandar Abbas na kasar Iran, a cewar kafafen watsa labaran kasar.

    Kazalika an kwantar da mutum 51 a asibiti sakamakon shan burkutun, kamar yadda wata jami'iar lafiya a birnin Dr Fatemeh Nowruzian ta shaida wa taron manema labarai.

    Mutum 17 daga cikinsu suna halin rai-kwakwai-mutu-kwakwai, yayin da aka yi wa mutum 30 wankin-koda, in ji likitar.

    'Yan-sanda sun ce sun kama mutum takwas bisa zargin yin burkutun da kuma raba ta ga jama'a.

    Kasar Iran ta haramta yin barasa da sayar da ita da kuma shan ta, ko da yake ana barin wasu da ba Msulmai ba su sha.

    Ana yi wa dukkan Musulmin da aka samu da lafin shan barasa bulala 80.

  11. Fafaroma ya nemi ganawa da Vladimir Putin

    Fafaroma Francis ya ce ya nemi tafiya Moscow domin ganawa da shugaban Rasha Vladimir Putin kan rikicin kasarsa da Ukraine, amma har yanzu ba a ba shi amsa ba.

    Fafaroma ya shaida wa jaridar Italiya Corriere della Sera cewa ya aike da sako zuwa fadar Kremlin kwanaki 20 bayan soma farmakin da Rasha ke kai wa Ukraine, ta hanyar wani babban jami'an difilomasiyyar Vatican.

    Wannan ne karon farko da Fafaroma ya ambaci Rasha a bayyanar jama'a da kuma fadar sunan Putin tun da kasar ta kaddamar da yaki da Ukraine fiye da watanni biyu da suka gabata.

    Fafaroma ya kuma ne kwanan baya ya kwashe minti 40 yana tattaunawa ta manhajar zoom da shugaban Cocin Orthodox ta Rasha.

    Ya gaya wa jaridar cewa Patriarch Kirill yana goyon bayan yakin, kuma ya kwashe minti 20 yana yi masa bayani kan dalilansu na shiga yakin.

  12. 'Yan a-waren Kamaru sun sace wata Sanata ta jam'iyya mai mulki

    Kamfanonin dillancin labarai sun rawaito cewa an sace wata 'yar majalisar dattawan Kamaru ta jam'iyyar da ke mulki a yankin da ake magana da turancin Ingilishi, inda 'yan a-ware suka yi ikirarin ballewa daga kasar.

    An sace Elizabeth Regina Mundi ranar Asabar tare da direbanta a garin Bamenda da ke arewa maso yammacin kasar, kamar yadda aka ambato jami'an yankin suna cewa.

    Wani jami'i ya shaida wa kamfanin dillancin labaria na AFP cewa bangarori biyu na 'yan a-waren Ambazonian Defence Forces (ADF) sun yi ikirarin sace 'yar majalisar dattawan.

    Wani bidiyo da aka watsa a shafukan sada zumunta ya nuna sanatar tana karanta wata sanarwa da ke kira a bayar da 'yancin kai ga Jamhuriyar Ambazonia.

    Masu fafutikar kafa kasar Ambazonia da ke yankin da ake magana da turancin Ingilishi sun yi zargin cewa yankin da ake magana da Faransanci ya danne su.

  13. Tayoyin jirgin Dana sun kama da wuta a Fatakwal

    An ceto dukkan fasinjoji 50 da ke cikin jirgin saman kamfanin Dana bayan tayoyinsa sun kama da wuta a Fatakwal babban birnin Ribas a Kudu maso kudancin Najeriya.

    Lamarin ya faru ne ranar Litinin.

    Gidan talbijin na Channels TV ya ambato kakakin kamfanin jirgin Kingsley Ezenwa yana tabbatar da aukuwar lamarin a wata sanarwa da ya fitar ranar Talata, yana mai cewa ba a samu asarar rayuka ba kuma babu wanda ya jikkata.

    Ya kara da cewa jirgin mai lamba 5N JOY yana shirin tashi daga Fatakwal zuwa Lagos lokacin da lamarin ya faru.

    Ezenwa ya kara da cewa direban jirgin ya lura da wutar da ta kama a jikin tayoyin kafin ya tashi daga nan ya sanar da masu lura da filin jirgin.

    Ya kara da cewa birkin jirgin ne ya yi tasiri kan tayoyin lamarin da ya haddasa tashin wutar.

  14. 'Yan bindiga sun kashe dan-sanda da wasu mutane a Anambra

    Wasu 'yan bindiga sun kashe mutum hudu, cikinsu har da wani dan-sanda a kauyuka biyu na jihar Anambra da ke Kudu maso gabashin Najeriya.

    Jaridar PREMIUM TIMES ta rawaito cewa an kashe biyu daga cikinsu ne, wadanda 'yan uwa ne, a kauyen Ukpor da ke karamar hukumar Nnewi South.

    An bayyana sunayensu da Godwin Ikechukwu Modobi da Nnajiofor Modobi da ke zaune a kauyen Umuhu.

    Kazalika an kashe sauran mutanen biyu a kusa da wani coci a kauyen Ozubulu da ke karamar hukumar Ekwusigo.

    Kakakin rundunar 'yan-sandan jihar, Ikenga Tochukwu, wanda ya tabbatar da kashe-kashen, ya ce Ikechukwu dan-sanda ne da ke aiki a jihar.

    Wadannan kashe-kashe na zuwa ne kwanaki kadan bayan kisan mutum biyar a gidan sayar da barasa das ke kauyen Osumenyi na karamar hukumar Nnewi South.

  15. An kama mutanen da suka tayar da tarzoma yayin karamar Sallah a Ethiopia

    Jami'an tsaron Ethiopia sun ce sun sun tsare mutum 76 bisa zargin tayar da tarzoma ranar Litinin yayin da Musulmai suka taru domin gudanar da sallar Idi a Addis Ababa, babban birnin kasar.

    'Yan sanda sun yi amfani da barkonon-tsohuwa wajen tarwatsa taron jama'a lokacin da lamarin ya faru ko da yake babu rahoton rasa rai.

    Dubban mutane ne suke halartar sallar Idi da aka gudanar a babban filin wasan kasar yayin da tarzomar ta barke.

    Lamarin ya faru ne kwanaki kadan bayan da aka tayar da jijiyoyin wuya tsakanin Musulmai da Kiristoci a sassan kasar bayan an kashe Musulmai 20 da ke halartar jana'iza a makon jiya a arewacin Ethiopia.

    Bayan aukuwar lamarin a birnin Gondar, an gudanar da jerin zanga-zanga a wurare da dama da kuma tarzoma ciki har da kona akalla coci uku a kudancin kasar.

  16. Shugaban Majalisar Dinkin Duniya ya nemi a taimaka wa Jamhuriyar Nijar

    Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya yi kira ga kasashen duniya su taimaka wa sojojin Jamhuriyar Nijar domin yaki da masu tayar da kayar baya da suke yawan kai hare-hare a kasar.

    A yayin da jawabi lokacin wata ziyara da ya kai Niamey, babban birnin kasar, babban jami'in na Majalisar Dinkin Duniya ya ce rikicin da ke faruwa a yankin Sahel ya zama babbar barazana ga duniya.

    Antonio Guterres ya kara da cewa Jamhuriyar Nijar ba za ta iya tunkarar matsalar masu ikirarin jihadi ita kadai ba kuma ya yi kira ga wasu kasashe su taimaka mata da horaswa da kuma kayan yaki.

    Faransa da Amurka suna da sansanonin soja a Jamhuriyar Nijar.

    Jamhuriyar Nijar mamba ce ta kasashen G5 Sahel da ke yaki da masu tayar da kayar-baya da suka hada da Mauritania, Mali, Burkina Faso da kuma Chadi.

  17. Muna aiki domin ceto mutanen da aka sace daga jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna - Buhari

    Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya tabbatar wa iyalai da 'yan uwan mutanen da aka sace daga jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna cewa za a dawo da 'yan uwansu gida ba tare da matsala ba.

    Ya bayyana haka ne a yayin da wasu al'ummar Abuja suka kai masa gaisuwar Sallah ranar Litinin a fadarsa ta Aso Villa.

    Wata sanarwa da Femi Adesina, mai magana da yawun Shugaba Buhari ya fitar ta ambato shugaban kasar yana cewa 'yan bindigar suna amfani da mutanen da suka kama ne a matsayin wata garkuwa.

    "A yayin da muke murnar wannan lokacina farin-ciki a tsakanin abokai da iyalai, muna sane cewa iyalai da dama a kasarmu suna cikin yanayi na tsoro da zaman dar-dar sakamakon sace 'yan uwansu da 'yan ta'adda suka yi, cikinsu har wadanda aka sace bayan an sanya bam a jirgin kasan Abuja - Kaduna.

    "Na bai wa jami'an tsaro umarni su yi gaggawar kubutar da su daga hannu masu satar mutane cikin koshin lafiya," in ji Buhari.

  18. Barkanmu da warhaka

    Nasidi Adamu Yahaya ne yake yi muku barka da wannan safiya. Da fatan ana ci gaba da shagulgulan Sallah lafiya.

    Ku kasance tare da ni a wannan safiya domin sanin halin da duniya ke ciki, musamman batutuwan da suka shafi shagulgulan na Sallah.