A yi Sallah lafiya
Ƙarshen rahotannin kenan a wannan shafi na kai-tsaye. Mu haɗu da ku gobe idan Allah ya kai mu don kawo sabbin rahotannin.
Umar Mikail ke cewa Barka da Sallah tare da fatan Allah ya maimaita mana.
Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da Afirka da sauran sassan duniya musamman Ukraine da Rasha.
Awwal Ahmad Janyau and Umar Mikail
Ƙarshen rahotannin kenan a wannan shafi na kai-tsaye. Mu haɗu da ku gobe idan Allah ya kai mu don kawo sabbin rahotannin.
Umar Mikail ke cewa Barka da Sallah tare da fatan Allah ya maimaita mana.
Gwamnan Jihar Edo da ke kudancin Najeriya, Godwin Obaseki, ya ƙara albashi mafi ƙaranci a jihar zuwa N40,000 sama da N30,000 da gwamnatin tarayya ta saka wa ma'aikatanta.
Obaseki ya sanar da ƙarin a yau Lahadi yayin da ake bikin Ranar Ma'aikata ta Duniya. Kazalika wasu rahotanni na cewa tsoffin ma'aikatan jihar sun gudanar da zanga-zangar neman a biya su garatutinsu a yau ɗin.
"Kamar yadda muka sani, mafi ƙarancin albashi na N30,000 da ƙyar zai iya riƙe iyali, rashin ɗa'a ne da tausayi mu ci gaba da basarwa cewa ba mu san halin ƙunci da ma'aikatanmu ke ciki ba," a cewar Mista Obaseki.
"Gwamnatin Edo ta yanke shawarar sake duba albashi mafi ƙaranci daga N30,000 zuwa N40,000 kowane wata, ba wata tantama Edo ce jiha ta farko tun bayan shigowar annoba (korona) da ta ɗauki wannan matakin."
'Yan Najeriya na ci gaba da fama da hauhawar farashin kayayyaki yayin da hukumar ƙididdiga ta NBS ta ce hauhawar farashi a watan Maris ta kai kashi 15.9 cikin 100.
A Afrika ta Kudu, ma'aikata sun tayar da bore a filin da Shugaba Cyrill Ramaphosa ya gabatar da jawabin bikin Ranar Ma'aikata ta Duniya, suna neman a kara musu albashi.
Hakan ya tilasta masa ficewa daga dandalin bikin.
Ma'aikatan da ke aiki a wuraren hakar ma'adanai na kasar na fama da yajin aiki tun watannin baya.
Sun yi ta ihu suna cewa "dole Cyrill ya bar mukaminsa", suna masu cewa suna bukatar a kara musu albashi.
Shugaba Ramaphosa ya yi kokarin yi musu bayani amma suka dinga yi masa ihu.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce za su "tabbatar ba a samu ƙarancin kuɗi ba" a gwamnatinsa wajen samar da tsaro a faɗin ƙasar kuma "saura ƙiris a samu nasara a yaƙi da 'yan ta'addan Boko Haram masu fakewa da Musulunci".
Shugaban ya bayyana hakan ne yayin da yake taya al'ummar Musulmi murnar bikin Ƙaramar Sallah a yau Lahadi, yana mai cewa "muna da dalilin da ya sa za mu yi bikin (Sallah) cikin ƙwarin gwiwa".
"Yaƙin da ake yi da 'yan ta'adda da suke fakewa da Musulunci ya kusa zuwa ƙarshe," in ji shi cikin wata sanarwa da kakakinsa Garba Shehu ya fitar. "Yaƙin ya ɗauki lokaci kuma da wuya. An kusa cimma nasara."
Buhari ya yaba wa aikin hukumar NDLEA mai yaƙi da miyagun ƙwayoyi, yana mai cewa ta ƙwace fiye da kilogiram miliyan 3.4 na miyagun ƙwayoyi da suka kai darajar naira biliyan 130 a 2021, da kuma kama manyan masu safarar ƙwayoyin a farkon 2022.
"Domin ƙarfafa wa hukumar da lamarin ya shafa gwiwa, Shugaban Ƙasa ya ba da umarnin a ƙara wa jami'an tsaro 3,500 girma, da kawo kayan aiki da kuma ba da horo," a cewar Garba.
"Haka nan Shugaban Ƙasa ya ba da umarnin haɗa kai da aiki tare tsakanin jami'an tsaro, yana mai cewa an kawo ƙarshen tsarin rashin aiki tare tsakanin hukumomi da kuma tabbatar da cewa ba a samu ƙarancin kuɗi ba wajen samar da tsaro ga 'yan ƙasa."
Wasu al'ummar Musulmi sun gurdanar da Sallar Idi a jihohin Sokoto da Kebbi da ke arewa maso yammacin Najeriya.
A jihar Sokoto, Sheikh Musa Lukwa ne ya jagoranci Idi da mabiyansa a ranar Lahadi.
Haka ma a garin Jega na jihar Kebbi sun gudanar da Sallarsu ta Idi.
Sarkin Musulmi Mai Alfarma Muhammad Sa’ad Abubakar ya ayyana ranar Litinin a matsayin ranar Sallah bayan kasa ganin watan Shawwal a ranar Asabar.
Samun irin wannan saɓani ba sabon abu ba ne a Najeriya, inda a shekarar da ta gabata ma fitaccen malamin Taijjaniyya Sheikh Ɗahiru Bauchi ya gudanar da Idi ba tare da bin umarnin sarkin Musulmin ba.
Shugabar Majalisar Wakilai ta Amurka Nancy Pelosi ta jagoranci tawagar 'yan majalisar zuwa Kyiv babban birnin Ukraine, kan kuɗirin Amurka na goyon bayan ƙasar a yaƙin da take yi da Rasha.
Ms Pelosi ta shaida wa shugaba Volodymyr Zelensky cewa Ukraine na fafutuka ne na neman ƴanci ga kowa - kuma Amurka za ta mara mata baya har sai an samu nasara.
Da take magana a Poland, ta ce Majalisar za ta hanzarta aiwatar da dokar da ta amince da bukatar Shugaba Biden na dala biliyan talatin da uku ga Ukraine.
Dan majalisa Jason Crow wanda tsohon soja ne ya ce a fili take cewaƴan Ukraine za su iya yin nasara a yaƙin idan aka ba su makaman da suke bukata.
Shugaban Kenya Uhuru Kenyatta ya sanar da ƙara yawan mafi ƙarancin albashi a yau Lahadi da kashi 12 cikin 100 yayin da gwamnatinsa ke yaƙar tsadar rayuwa a ƙasar.
Hauhawar farashi ta kai matakin da ba ta taɓa kaiwa ba cikin wata bakwai a watan Afrilu, akasari saboda tashin farashin mai da kayayyakin abinci, in ji hukumomi.
"A matsayinmu na gwamnati mai tausayi, muin lura cewa akwai buƙatar ƙara albashi mai ƙarfi don kare ma'aikatanmu daga shiga wani ƙuncin," a cewar Kenyatta yayin jawabin Ranar Ma'aikata.
Ya ce ƙarin albashin zai fara aiki ne daga ranar 1 ga watan Mayu, inda zai tashi daga kuɗin Kenya shilling 13,500 duk wata (dala 116 kenan) zuwa 15,120 (dala 130.5).
Sai dai kuma ƙarin bai kai abin da ƙungiyar ƙwadago ta Central Organisation of Trade Unions-Kenya (COTU) ta nema ba na kashi 24 cikin 100.
Hukumar Hisbah a Jigawa ta yi gargaɗi ga masu shirin shirya casu a lokacin bikin Sallah.
Hukumar ta ce za ta yi dirar mikiya ga duk wanda ya shirya casu ko alfasha a lokacin bikin Sallha kamar yadda shugabanta Ibrahim Dahiru ya bayyana wa kamfanin dillacin labarai na Najeriya NAN a Dutse.
“Muna amfani da wannan dama domin yin gargaɗi cewa jami’ansu za su kama duk wanda ya aikata aikata alfasha da sauran munanan dabi’u irin kidan DJ da rawa da sayarwa ko amfani da kayan wasan wuta,” in ji shugaban na Hisbah na Jigawa.
Shugaban Taliban a Afghanistan ya bayyana nasarorin da ƙungiyar ta samu tun karɓe ikon mulkin ƙasar.
Shugaban na Taliban Hebatullah Khondzadeh ya fito bainar jama'a da ba saba gani ba cikin tsauraran matakan tsaro, ya ce Afghanistan ta samu nasara a "ƴanci da kuma tsaro."
A hudubarsa ta Idi a Kandahar, shugaban bai bayyana hare-haren da aka kai ba lokacin azumin Ramadan a ƙasar.
Wannan ne karo na biyu da Khundzadeh ya fito bainar jama'a tun lokacin da Taliban ta ƙwaci mulki a Afghanistan
Gwamnan jihar Nasara Abdullahi Alhaji Sule ya ce kammala ayyukan da ya fara su ne mafi muhimmanci a gabansa fiye da neman wa’adi na biyu na mulkin jihar.
Gwamna Abdullahi Sule ya ce ba ya cikin gwamnonin Najeriya da suka damu da sake samun dama karo na biyu don su kammala wasu ayyuka.
A wannan hira ta musamman da abokin aikinmu Yusuf Ibrahim Yakasai, gwamna A A sule ya bayyana matsayarsa kan zaben da aka yi wa Sanata Abdullahi Adamu a matsayin shugaban jam’iyyar APC.
Amma Yusuf din ya fara da tambayarsa kan alkwarin da ya yi gabanin zaben 2019 kan cewa zai nemo masu zuba jari da za su samar da ayyukan yi ga matasan jihar ta Nasarawa.
A kowacce ranar 1 ga watan Mayu ake yin bikin Ranar Ma'aikata Ta Duniya
Wannan rana na da dumbin tarihi a cikin rayuwar 'yan kwadago a kasashe daban-daban.
Ƙungiyoyin kwadago a kasashen duniya kan gudanar da manya -manya taruka kuma su fito su bayyana ire-iren abubuwan da ke ci masu tuwo a ƙwarya game da lamarin rayuwar ma'aikata.
A Abuja babban birnin Najeriya, ma’aikata sun yi gangami a dandalin Eagle Square.
Hotunan bikin ranar ma'aikata a Abuja.
Al'ummar musulmi a Jamhuriyar Nijar sun yi idin Sallah bayan sanar da ganin watan Shawwal a ƙasar, abin da ya kawo ƙarshen azumin watan Ramadana a Nijar.
A daren Asabar al'umma ƙasar a ɓangrori daban-daban suka tabbatar da ganin jinjirin watan Shawwal abinda hukumar ƙolin ƙasar ta musulunci da ma gwamnati suka tabbatar bayan cikakken bincike.
Sai dai a wasu ƙasashe da dama ba a yi Sallah ba sai Litinin saboda rashin ganin watan na Sallah.
Jagoran Iran ya yi afuwa ko sassauta hukuncin ɗauri ga fursunoni 1,542 da aka yanke wa hukunci a wani mataki na murnar bikin Sallah da ke nuna kawo ƙarshen azumin watan Ramadan, kamar yadda shafinsa ya bayyana a ranar Asabar.
Ayatollah Ali Khamenei ya ce “ya amince da yin afuwa ko sassauta hukuncin da aka yanke wa masu laifi 1,542."
Jagoran na Iran yakan yi afuwa ga masu laifi a manyan bukukuwan addini, tare da sa hannun shugaban ɓangaren shari’ar ƙasar
A ranar Litinin ne za a yi bikin Sallah a Iran.
Dubban ƴan Bangladesh ne suka garzaya zuwa babbar tashar jirgin kasa ta Dhaka da tashohin jiragen ruwa domin komawa garuruwansu na asali don bukukuwan Sallah.
Bayan shekaru biyu na matakan korona, ƴan ƙasar na farin cikin dawo da sufuri wanda zai ba su damar zuwa gida cikin sauƙi. A bara an dakatar da zirga-zirgar ababen hawa don hana mutane ketare iyakokin jihohi saboda tsoron yaɗuwar korona.
Ɗaruruwan ƴan ƙasar ne ke ficewa Dhaka babban birnin Bangladesh a motoci da jirgin ruwa da na ƙasa zuwa ƙauyukansa domin bikin Sallah.
Shugaban soja na Guinea, Kanal Mamady Doumbouya, ya ce ya zaɓi watanni 39 na rikon kwarya kafin a shirya zaɓe ya mayar da mulkin kasar hannun hannun farar hula.
A lokacin da yake jawabi ta kafar Talabijin ɗin kasar, Mista Doumbouyaya ce kwamitin rikon-kwarya a yanzu zai gabatar da daftarinsa zuwa ga majalisa.
Sanarwar na zuwa ne, adaidai lokacin da kungiyar ECOWAS - da ke ta nanata neman mulki ya koma hannun farar hula - ta tsayar da ranar Litinin a matsayin wa'adin karshe don fitar da tsare-tsaren komawar mulkin dimokuradiyya.
Sojoji karkashin jagoranci Kanal Mamady Doumbouya ne suka kifar da gwamnatin zababben shugaba Alpha Conde a Satumban 2021, bayan ganin irin wannan juyin-mulkina Mali.
Sannan ita ma wata mamba a Ecowas Burkina Faso ta fuskanci irin wannan juyin-mulkin a watan Janairu.
Shugaba Volodymyr Zelensky na Ukraine ya yi gargaɗin cewa Rasha na sake girke ƙarin dakaru domin kai sabbin hare-hare gabashin kasar.
Ya ce gwamnatin Rasha ta ƙara tura wasu dakaru yankin Kharkiv da ke arewa maso gabashi a ƙoƙarin sake matsa kaimi a Donbass.
A ranar Asabar dakarun Ukraine suka ce sun kai hari kan wani sansanin Rasha da ke kusa da Kharkiv, da sake karɓe ikon wasu yankunan.
Sai dai sun ce Rasha na c igaba da mayar da hankali wajen sake gina ƙarin sojoji kusa da iyaka da kuma garin Izium.
Jami'an a yankin Luhansk sun ce luguden wutar Rasha na ƙaruwa a kullum.
Rahotanni na cewa hare-haren Rasha a gabashi na tsanani yayin da Shugaban yankin Luhansk ya ce yana tunanin Rasha na shirin kai hari mafi girma a ranar 9 ga watan Mayu - ranar da bisa al'ada ta saba bikin murnar nasarar da ta samu galabar Jamus a yankin duniya na Biyu.
Muna maku maraba da kasance da mu a wannan shafin da muke kawo maku labarai da rahotanni kan abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya