Rufewa
Masu bibiyarmu a wannan shafin a nan muka zo ƙarshen kawo muku labarai da rahotanni kai tsaye, sai kuma gobe Talata idan Allah Ya kai mu za mu ci gaba da kawo muku wasu labaran.
Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da Afirka da sauran sassan duniya musamman batutuwan da suka shafi Sallah karama.
Nasidi Adamu Yahaya and Mustapha Musa Kaita
Masu bibiyarmu a wannan shafin a nan muka zo ƙarshen kawo muku labarai da rahotanni kai tsaye, sai kuma gobe Talata idan Allah Ya kai mu za mu ci gaba da kawo muku wasu labaran.
Jami'ai a Ukraine sun ce wani makami mai linzami mallakin Rasha ya sauka a tashar jirgin ruwa ta birnin Odesa lamarin da ya halaka mutane tare da jikkata wasu da dama.
Hukomomi a birnin sun ce harin ya shafi gine-ginen farar hula sannan ginin wata majami'a ya sauka.
Birnin na Odesa dai ya tsira daga yakin tsawon wata biyu da aka rika gwabzawa sakamakon mamayar da Rasha ta yi a Ukraine haka kuma harin da Rasha ta kai ranar Asabar ya lalata hanyar jirgin sama a tashar jirgin birnin
Shugaban ƙasar Kenya Uhuru Kenyatta ya buƙaci mataimakinsa, William Ruto da ya yi murabus a daidai lokacin da dangantakar da ke tsakanin mutum biyun ke ƙara tsami gabannin zaɓen ƙasar da ke tafe a watan Agusta.
Mista Kenyatta na zargin Mista Ruto da rashin mayar da hankali wajen taimaka wa ƙasar ta farfaɗo daga matsin tattalin arziƙi inda ya ce bai kamata Mista Ruto ɗin ya rinƙa caccakar gwamnatinsu ba.
Sai dai a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Twitter, Mista Ruto ya yi iƙirarin an shafe sama da shekara biyu majalisar zartarwa ta tarayyar ƙasar ba ta yi zama ba.
Rashin jituwar da ke tsakaninsu ta fito fili ƙarara a yayin jana'izar tsohon shugaban ƙasar Mwai Kibaki da aka gudanar a ranar Juma'a inda Shugaba Kenyatta ya ƙi yarda ya sha hannu da Mista Ruto.
Ma'aikatan agaji a Burkina Faso na ci gaba da kokarin kai wa ga masu hakar ma'adanai takwas da suka makale a karkashin kasa tsawon sama da mako biyu.
Ambaliyar ruwa sakamakon mamakon ruwan sama a watan da ya gabata ta lalata mahakar ma'adinan ta sinadarin zinc a Perkoa wadda wani kamfani na kasar Canada, Trevali ke tafiyar da harkokinta.
Har yanzu masu hakon ma'adinai shida ne daga Burkina Faso sai wani daga Zambia da kuma wani dan Tanzania suka yi batan dabo.
Wani dan uwan mutanen ya shaida wa kamfanin dillancin Labarai na Faransa cewa ba a fada masa komai ba game da yiwuwar gano su da ransu.
Firaminista Albert Ouedraogo, a wata ziyara da ya kai a karshen makon da ya gabata, ya zargi shugabannin mahakar inda ya ce an yi amfani da abin fashewa wanda ya lalata ginin.
Hukumar kare hakkin bil adama a Habasha ta ce tana gudanar da bincike kan wani hoton bidiyo da ya nuna wasu mayaka suna cin zarafin wani matashi da suke zargi ya fito ne daga yankin Tigray.
A cikin bidiyon da aka yi ta yadawa, an ga yaron cikin jini ana dukansa da kafa ana kuma jifansa da duwatsu kafin daga baya a ɗirka masa harsashi a ciki.
Kawo yanzu, babu tabbaci kan ko ya rayu. An dai ga tambarin sojin Habasha a jikin kakin akasarin mutanen da aka gani a bidiyon.
Zai yi wuya a iya tantance lokacin da aka naɗi bidiyon.
A watan Maris ne hukumar ta ce dukkan bangarorin da ke rikici a arewacin Habasha sun take hakkokin bil adama wanda ka iya zama laifukan yaki.
Mai Martaba Sarkin Zazzau Malam Ahmed Nuhu Bamalli ya dakatar da hakimai huɗu na Masarautar Zazzau daga muƙamansu.
A wata sanarwa da mai magana da yawun Fadar Zazzau, Abdullahi Aliyu Kwarbai ya fitar jim kaɗan bayan sauka daga hawa a yau, an dakatar da hakiman ne bisa saɓa dokokin da aka gindaya na Hawan Sallah.
Hakiman da aka dakatar sun haɗa da Ubangarin Zazzau Alhaji Bashir Shehu Idris da Wakilin Birnin Zazzau Alhaji Suleiman Ibrahim Dabo da Sarkin Dajin Zazzau Alhaji Shehu Umar da kuma Garkuwan Kudun Zazzau Alhaji Muhammadu Sani Uwais.
Ana zargin hakiman da saɓa doka ta uku da ke cikin kundin laifukka da hukunce-hukuncen hawa a Masarautar Zazzau wadda ta haramta wa kowane hakimi yin hawa da ƴan tauri riƙe da makamai.
Ana ci gaba da fuskantar kalubale a kokarin da hukumomin Ukraine ke yi na ganin an kwashe farar hular da suka makale a birnin Mariupol da aka daidaita.
Ma'aikatar tsaron kasar a Kyiv ta ce sojojin Rasha na toshe hanyoyin jin kai da ke kusa da masana'antar sarrafa karafa - bangaren Mariupol na karshe da ke karkashin ikon Ukraine.
A wani birnin kuwa, farar hula da dama sun shafe sa'oi suna dakon motocin da aka tsara za su kwashe su. Ana dai ci gaba da jiran jerin gwanon motoci daga Mariupol.
Ma'aikatan agaji da likitoci na jiran ko ta kwana. Haka kuma ana samun rahotannin cewa jerin gwanon motocin na fuskantar tsaiko don haka ba tabbacin ko yaushe za su iso.
Nan gaba ne kuma ake sa ran za su isa birnin Zaporizhzhia amma har yanzu akwai daruruwan mutane da ke makale a masa'antar.
Shugaban kasar Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa ya bar wurin taron Ranar Ma'aikata ta duniya bayan wasu ma'aikata sun far wa dandamalin da yake jawabi.
Sun rika yi masa ihu suna cewa "Dole ne Cyril ya sauka daga mulki," suna dauke da kwalayen da ke dauke da bukatar karin albashi a filin wasan da ke birnin Rustenburg na arewa maso yammacin kasar.
Ma'aikatan, wadanda suke aiki a wata ma'aikatar hakar ma'adinai, sun kwashe makonni suna yajin-aiki.
Shugaba Ramaphosa ya yi kokarin yin tsokaci kan bukatun ma'aikatan amma an rika yi masa ihu.
Ma'aikatan suna bukatar karin albashi da rand 1,000 ($63; £50) - bukatar da Shugaba Ramaphosa ya amince da ita kai-tsaye.
Rundunar sojin Rasha ta ce ta lalata jirgin yakin Ukraine samfurin MiG-29 lokacin wata fafatawa a sama a lardin Donetsk da ke gabashin kasar.
A wani taron manema labarai, kakakin rundunar sojan, Igor Konashenkov, ya ce dakarunsu sun kuma lalata makamai masu-linzamin Ukraine biyu samfurin Tochka-U a Luhansk, da kuma wasu makaman masu-linzami samfurin Smerch a Donetsk.
Ya kara da cewa sun lalata jirage marasa matuka goma na Ukraine.
A cewarsa, dakarun Rasha sun kuma hari wurare 38 da sojan suke, ciki har da wuraren ajiye makamai.
Dukkan bangarorin biyu sun sha yin ikirarin yi wa juna halani, ko da yake BBC ba ta iya tantance hakikanin ikirarinsu ba.
Shugaban Tunisia Kaïs Saïed ya sanar da shirinsa na sake rubuta kundin tsarin mulkin kasar.
A jawabin da ya yi na ranar karamar sallah ta gidan taldijin na kasar, Mr Saïed, wanda ya rusa gwamnati da majalisar dokokin kasar, ya ce za a kafa kwamitin da zai sake rubuta daftarin tsarin mulkin kasar kuma za a kammala shi nan da 'yan kwanaki.
Bai bayyana karara sauye-sauyen da za a yi wa tsarin mukin ba, amma ya ce zai samar da abin da ya kira Sabuwar Jamhuriya.
Masu hamayya sun soke shi suna masu zarginsa da rike kusan daukacin madafun iko tun lokacin da ya kwace mulki watanni tara da suka wuce.
Jami'an tsaro a Addis Ababa, babban birnin Ethiopia, sun fesa barkokon-tsohuwa kan wasu Musulmai da suka taru domin gudanar da sallar Idi.
Dubban Musulmai ne suka taru a babban filin wasan birnin inda kuma a nan ake sallar Idi amma rikici ya barke. Ba a samu rahoton mutuwa ba.
Lamarin ya faru ne kwanaki kadan bayan da aka tayar da jijiyoyin wuya tsakanin Musulmai da Kiristoci a sassan kasar bayan an kashe Musulmai 20 da ke halartar jana'iza a makon jiya a arewacin Ethiopia.
Bayan aukuwar lamarin a birnin Gondar, an gudanar da jerin zanga-zanga a wurare da dama da kuma tarzoma ciki har da kona akalla coci uku a kudancin kasar.
Matakin da jami'an tsaro suka dauka na fesa barkonon-tsohuwa kan Musulman zai iya dagula lamura.
An ga hotunan mutane suna tserewa yayin da ake wurga musu barkonon-tsohuwa da kuma mata da ke neman 'ya'yansu cikin kaduwa.
Rundunar 'yan sandan Addis Ababa ta dora alhakin lamarin kan "wasu tsirarun mutane" kuma ta ce an lalata wurare da dama.
Shugaban Ukraine Zelensky ya yi gagardi cewa rikicin da ake yi a kasar zai iya haddasa matsalar karancin abinci a duniya.
Da yake magana da wani shirin labarai na Australia mai taken 60 Minutes, Zelensky ya ce kasarsa za ta yin asarar miliyoyin tan na hatsi saboda Rasha ta rufe tashar jiragen ruwa da ke isa Bahar Aswad.
Ukraine na daya daga cikin kasashen duniya da ke fitar da hatsi da sauran kayan abinci.
"Rasha tana ta durkusar da tattalin arzikin kasarmu baki daya," Zelensky.
Ministan tattalin arzikin Jamus ya ce kawunan kasashen Turai sun rabu game da neman daina sayen fetur da iskar gas daga Rasha.
Ministocin Tarayyar Turai sun tattaunawa game da sanya takunkumi kan man fetur na Rasha, sai dai kasar Hungary ta bayyana karara cewa ba za ta amince a daina sayen albarkatun mai daga Rasha ba.
Jamus ta ce ba ta shirya daina sayen gas daga Rasha ba amma za ta bari a sanya takunkuman daina sayen fetur na kasar.
An gudanar da bukukuwan Sallah, da suka hada da hawan dawaki, a karom farko cikin shekaru uku a birnin Katsina da ke arewacin Najeriya.
Akalla mutum takwas ne aka tabbatar sun mutu bayan wani gini mai hawa uku ya rushe a yankin Ebutte Meta da ke binrin Lagos na Najeriya.
Lamarin ya faru ne ranar Lahadi da daddare.
Wata mata da jirirnta na cikin wadanda suka mutu, a cewar Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Najeriya, NEMA.
Babban jami'in hukumar a yankin Kudu maso Yammacin Najeriya, Ibrahim Farinloye, wanda ya tabbatar da aukuwar lamarin, ya kara da cewa an ceto mutum 23 daga cikin ginin.
Wannan shi ne karo na biyu a wata kusan uku Tda gini ya rushe a yankin na Yaba-Ebutte Meta inda ya kashe mutane.
Shugaban sojojin Ukraine ya ce makamansu masu-linzami sun lalata jiragen ruwan Rasha guda biyu da ke sintiri a Bahar Aswad.
"Mun lalata jiragen ruwan Rasha biyu samufurin Raptor-class da safiyar nan kusa da Tsibirin Zmiinyi (Snake)," a cewar babban jami'in rundunar sojan Ukraine Valeriy Zaluzhniy.
Wasu bidiyo da rundunar sojin Ukraine ta fitar da ba a tantance su ba sun suna wasu abubuwa da ake tsammani makamai masu-linzami ne sun fada kan jiragen ruwan biyu a yayin da suke sintiri a kusa da Bahar Aswad
Kawo yanzu Moscow ba ta ce komai a kan batun ba.
A yau Litinin ne ake bikin Sallah karama a fadin Najeriya da wasu sassan duniya bayan an kwashe kwanaki talatin ana azumin watan Ramadan.
Musulmai daga jihohi daban-daban sun caba kwalliya inda suka tafi masallatai domin gudanar da Sallar Idi.
Gabanin nan, a cikin sakonsa na sallah, Shugaba Muhammadu Buhari na kasar, ya ce za su "tabbatar ba a samu ƙarancin kuɗi ba" a gwamnatinsa wajen samar da tsaro a faɗin ƙasar kuma "saura ƙiris a samu nasara a yaƙi da 'yan ta'addan Boko Haram masu fakewa da Musulunci".
Sanarwar da mai magana da yawun Shugaban, Garba Shehu ya fitar, ya ce "Muna da dalilin da ya sa za mu yi bikin (Sallah) cikin ƙwarin gwiwa".
"Yaƙin da ake yi da 'yan ta'adda da suke fakewa da Musulunci ya kusa zuwa ƙarshe," in ji shi. "Yaƙin ya ɗauki lokaci kuma da wuya. An kusa cimma nasara."
Nasidi Adamu Yahaya ne yake yi muku barka da Sallah. Da fatan an kammala azumin watan Ramadan lafiya.
Ku kasance tare da ni a wannan safiya domin sanin halin da duniya ke ciki, musamman batutuwan da suka shafi shagulgulan Sallah.