Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Wace ce farkar Putin da ake kira 'Secret First Lady'?

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da Afirka da sauran sassan duniya musamman Ukraine da Rasha.

Rahoto kai-tsaye

Sani Aliyu and Badariyya Tijjani Kalarawi

  1. Mayakan Tigray sun fice daga yankin Afar - TPLF

    Daukacin mayakan Tigray sun fice baki daya daga yankin Afar na kasar Habasha, kamar yadda kakakin kungiyar TPLF Getachew Reda ya wallafa a shafinsa na Tiwita.

    “Sako ga al'ummar kasashen waje, da 'yan kasarmu da suka damu da halin da muke ciki, don haka mu na shaida muku cewa babu mayakin Tigray ko daya a yankin Afar, sun fice baki daya,” in ji sakon da ya wallafa..

    Mr Getachew, ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Reuters ranar Litinin, cewa ya na fatan wannan matakin zai sanya a kai kayan agaji musamman na abinci ga wadanda ke tsananin bukatar taimako a yankin da ke fama da matsanancin fari.

    Tun bayan barkewar yaki tsakanin gwamnatin Habasha da 'yan tawayen Tigray, kasar ke cikin tsaka mai wuya.

    Ya yin da yarjejeniyar dakatar da bude wutar da aka cimma a watan jiya, ta bada damar kai manyan motocin kayan abinci 144 kacal zuwa yankin, kamar yadda shirin samar da abinci na Majalisar Dinkin Duniya ya bayyana. Yayin da Majalisar Dinkin Duniya ke cewa akalla motocin abinci 100 ya kamata a dinga kai wa yankin a kowacce rana.

    A ranar Litinin, ayarin motocin kayan abinci 70, karkashin sa idon MDD suka shiga Tigray. Shugaban shirin wanzar da zaman lafiya na gwamnati a yankin Afar, Ibrahim Hamed Mohammed ya shaidawa BBC cewa mayakan Tigray sun janye daga yawancin wurare, amma har yanzu akwai da dama daga cikinsu da ba su fice ba.

    "Ba dukansu ne suka janye ba. Har yanzu akwai sojojin Tigray a gundumar Araju, da Hida da kuma Magal. Su na nan kusa da iyakokinmu, tafiyar ba ta wuce ta kilo mita 15 ba,'' in ji shi.

  2. Sojan Najeriya ya kashe kansa bayan ya shiga hannu kan tuhumar taimakawa ISWAP

    Rahotanni daga yankin arewa maso gabashin Najeriya na cewa wani sojan kasar ya kashe kansa bayan da aka kama shi bisa tuhumar cewa yana aiki tare da mayaka masu ikirari jihadi na kungiyar ISWAP.

    Wakilin BBC ya ce wata majiya mai kusanci da rundunar sojojin Najeriya ta sanar da shi cewa lallai sojan na da hannu a wasu hare-hare da aka kai kan wasu al'umomin jihar Yobe a cikin makonni da suka gabata.

    Manyan hafsoshin sojin kasar sun fara sa ido kan sojan ne bayan da aka kai wasu hare-hare biyu a garuruwan Geidam da Gashua na jihar ta Yobe, kuma daga nan suka fara bibiyar wuraren da yake zuwa cikin sirri.

    An kuma kama shi yayin da yake kokarin tserewa, bayan da ya gane cewa dubunsa ta cika.

    Sai dai sojan - wanda kwararre ne wajen sarrafa makamai - ya kwace wata bindiga a hannun daya daga cikin sojojin da ke rakiyarsa kuma ya kashe kansa duk da cewa an saka masa ankwa a hannu.

    A makon jiya wasu wadanda ake kyautata zaton mayakan ISWAP ne suka kai wani hari kuma suka kashe akalla mutum goma, ciki har da mata.

    Wannan harin ya biyo bayan wani harin na daban da aka dasa wani bam wanda ya halaka mutum shida baya ga raunata wasu mutum 19 a jihar Taraba, harin da kungiyar ISWAP ta dauki alhakin kai shi.

  3. Wata mata cikin fasinjojin jirgin kasan Abuja - Kaduna ta haihu a hannun masu garkuwa da ita

    Daya daga cikin fasinjojin da 'yan fashin daji suka sace daga jirgin kasan da ya tashi daga Abuja zuwa Kaduna ranar 28 ga watan Maris ta haihu a hannun masu garkuwa da ita.

    Tashar talabijin ta AriseTV wadda ta wallafa wannan labarin ta kuma ce wani dan uwan matar ne ya sanar da su haka.

    Dan uwa nata ya sanar cewa an kai wani likita wurin da ake rike da ita wanda ya taimaka mata wajen haihuwa.

    "Matar na da tsohon ciki wanda ya kai wata takwas yayin da aka sace ta da sauran gomman fasinjoji, kuma ta haihu ne bayan da 'yan ta'addan suka gayyaci likitoci su karbi haihuwar. Sai dai ba mu san halin da abin da ta haifa yake ba," inji dan uwan matar.

    A farkon wannan makon ne dai masu garkuwa da mutanen suka wallafa hotunan fasinjojin da kawo yanzu suka shafe wata guda cur a hannunsu.

  4. Budewa

    Barkanmu da wayewar gari wannan rana ta Alhamis!

    A yau ma BBC hausa za ta ci gaba da ayyukan sanar da ku da ilmantar da ku abubuwan da ke wakana a sassan duniya.

    Sani Aliyu ne ke tare da ku a wannan rana, kuma ni ne zan jagoranci sada ku da labarai da rahotannin da ke tafe.

    Sai ku ci gaba da kasancewa da BBC Hausa,

  5. Rufewa

    A nan muka kawo karshen labarai da rahotanni na kai tsaye, da muke ba ku a wannan shafi.

    Sai ku tare mu gobe domin samun sabbin labarai da rahotanni daga sassa daban-daban na Duniya.

    Badriyya Tijjani Kalarawi ke sallama da ku, mu kwana lafiya.

  6. An fara allurar riga-kafin cutar Ebola a Kongo

    Hukumar Lafiya ta Duniya ta ce an fara yin riga-kafin cutar Ebola a wasu yankunan Jamhuriyar Dimukradiyyar Kongo, inda aka samu sake barkewar cutar da ta hallaka mutum biyu.

    Kawo yanzu, allurai 200 sun isa birnin Mbandaka, sannan jami'an lafiya za su fara da yi wa mutanen da suka yi mu'amala da wadanda suka kamu da cutar kafin rasuwarsu.

    Hukumar Lafiya ta Duniya ta ce, su ma jami'an lafiya za su kasance a sahun gaba wajen yin riga-kafin. Ta kara da cewa gwajin da aka yi a cibiyar gwaji da ke Kongo, ya nuna tabbas an samu wani sabon nau'in cutar ta Ebola.

    Ana ci gaba da gudanar da binciken kimiyya domin gano ko ita ma tana da alaka da dabbobi.

  7. Malamai: An kashe musulmai 20 a Habasha

    Rahotanni na cewa an kai hari kan wasu musulmai 20 kuma duka sun mutu a yankin Amhara na kasar Habasha, a lokacin suna kan hanyar zuwa jana'iza.

    Tashin hankalin ba shi da alaka da fadanda ake yi tsakanin dakarun gwamnati da 'yan tawayen Tigray.

    Shugaban kwamitin addinin musulunci a yankin Amhara ya ce an jefawa masu tafiya jana'izar ababen fashewa, nan take mutane uku suka mutu.

    Ya kara sauran wadanda lamarin ya shafa sun mutu ne sakamakon tarzomar da ta barke lokacin da bata gari suka fara sata a shagunan da ke kusa.

    Makabartar da harin ya faru dai an dade ana takaddama akan ta tsakanin mabiya addinin Musulunci da Kiristoci kibdawa masu rinjaye a kasar Habasha.

  8. Kotu ta dage sauraren karar shugaban IPOB

    Babbar kotu da ke zama a Umuahia, a jihar Abia a kudancin Najeriya, ta dage zaman sauraren karar jagoran kungiyar IPOB mai fafutukar kafa ƙasar Biafra, Mazi Nnamdi Kanu zuwa 12 ga watan Mayu, kan kalubalantar matakin gwamnatin Najeriya na taso keyarsa zuwa gida daga kasar Kenya.

    A ranar 28 ga watan Yuni 2021, aka sato Kanu daga Kenya tare da taso shi gida Najeriya, karkashin jagoirancin tawagar gwamnatin Najeriya kamar yadda lauyansa ya bayyana.

    Lauyan KanuAloy Ejimakor ya shaidawa kotu cewa, hakan ya sabawa 'yancin wanda ya ke karewa, dan haka cikin wadanda ake shari'ar da su har da shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya, da ministan shari'a na kasar.

    A zaman kotun na ranar 25 ga watan Maris, an dage zaman zuwa 27 ga watan Afirilu, amma hakan ba ta samu ba aka kara dagewa zuwa watan gobe.

    Kanu yana fuskantar zarge-zargen da suka shafi cin amanar kasa lamarin da ya sa aka gurfanar da shi a gaban wata babbar kotun tarayya da ke Abuja bisa fafutukar da yake yi wajen ganin an kafa kasar Biafra ta hanyar IPOB.

    Ana zarginsa da "hada kungiyoyi na tayar da zaune-tsaye, yada labaran karya, mallakar makamai ba bisa ka'ida ba da kuma shigowa da haramtattun kaya Najeriya.

  9. Wace ce farkar Putin da ake kira 'Secret First Lady'

    "Dukkan iyalai suna da labarin da za su bada kan yaki, kada mu manta da irin labaran da za mu bai wa manyan gobe."

    Wannan na nufin, Alina Kabaeva, da ake wa lakabi da 'Secret First Lady' ta Rasha, gabannin a fara yaki tsakanin Rasha da Ukraine.

    Dalilin shi ne, Amurka ta kakabawa duk wani makusancin shugaba Vladimir Putin, takunkumi ciki har da 'ya'yansa, amma har yanzu Alina ba ta fuskanci hakan ba.

  10. EU ta zargi Rasha da takalar fada kan sayar da iskar gas da kudin ƙasarta

    Kungiyar Tarayyar Turai ta ce matakin Rasha na dakatar da sayar wa Poland da Bulgaria gas abu ne da ake kallo da takalar fada da ci da ceto, kamar yadda shugabar hukumar gudanarwar Tarayyar Turai Ursula von der Leyen ta bayyana.

    "Za mu tabbatar matakin da kamfanin Gazprom na Rasha ya dauka, ba zai yi kwakkwaran tasiri ga kasashen Turai da suka dogara da shi ba," in ji ta a wajen taron manema labarai ranar Laraba.

    von der Leyen, ta kuma gargadi kamfanonin makamashin Turai da kasa su amince da sharuddan Rasha na sayan hajarta da kudin kasa Rubble, tare da cewa wannan matakin ya sabawa dokokin takunkuman da da Trayyar Turai ta kakabawa Rasha.

    "Biyan kudin gas da Rubble,idan har wasu na ganin ba komai ba ne, to wannan ya sabawa ka'ida kuma yi wa takunkuman da aka sanyawa Rasha hawan kawara ne," in ji ta.

    A karshe ta bayyana cewa kamfanonin da suke mu'amala da Rasha da suke kokarin sayan gas da kudin rubble, su na daukar babbar kasada.

  11. Yariman Saudiyya ya gana da shugaban Chadi

    Yariman Saudiyya mai jiran gado Mohammed bin Salman ya gana da shugaban soji na Chadi Mahamat Idriss Déby a birnin Jeddah.

    Kamfanin dillacin labaran Saudiyya ya ce shugabannin biyu sun tattauna batutuwan da suka shafi fanoni da dama na inganta hulɗar ƙasashen biyu.

    Sai dai babu cikakken bayani kan batutuwan da suka tattauna.

  12. Rasha ta saka wa 'yan majalisar Birtaniya 287 takunkumi

    Ma'akatar harkokin wajen Rasha ta bayyana cewa kasar ta saka wa wasu 'yan majalisar kasar Birtaniya 287 takunkumi, tana tuhumarsu da "tunzura al'umma domin su kyamaci Rasha".

    Wannan matakin na nufin 'yan majalisa 213 daga jam'iyyar Conservative da 74 daga jam'iyyar Labour ba za su sami izinin shiga Rasha ba.

    Ma'aikatar ta kuma ce tana iya daukan "wasu matakan ladabtarwan" - bayan da Birtaniya ta dauki irin wannan matakin a watan Maris.

    Cikin jadawalin da Rasha ta fitar, akwai sunayen wasu 'yan majalisar da ba sa majalisar a halin yanzu.

  13. "Akwai yiwuwar akai hare-haren bam da karamar sallah"

    Hukumar 'yan sandan farin kaya ta DSS ta fitar da wata sanarwa cewa akwai yiwuwar wasu miyagu su kai hare-haren bam kan al'umma yayin karamar sallah mai zuwa wadda ta kawo karshen watan Azumin Ramadan.

    Cikin sanarwar, ta ce an gano wani shirin da wasu kungiyoyi suka kitsa domin kai hare-haren kan wasu mhimman wurare da masallatai da kuma wuraren shakatawa.

    Wannan gargadin na zuwa ne bayan da wasu abubuwa suka fashe a mashaya a jihohin arewa maso gabashin Najeriya biyu - Yobe da taraba - inda mutane da dama suka halaka.

    Wani tsagin kngiyar Boko Haram da aka fi sani da ISWAP ne ta dauki alhakin kai hare-haren.

  14. NDLEA na binciken gidajen Abba Kyari shida tare da rukunin shaguna a Maiduguri

    Hukumar da ke yaki da masu safarar miyagun kwayoyi a Najeriya NDLEA, ta shafa fenti a jikin wasu gidaje shida da wani katafaren gini mai shaguna a Maiduguri mallakin jami'in dan sanda DCP Abba Kyari.

    Fentin alama ce ana binciken gidajen.

    Katafaren ginin bene ne mai hawa biyu mai suna Assurance Plaza da ke kan titin barikin Giwa a Maiduguri kuma yana da shaguna 100.

    Baya ga ginin, hukumar na kuma binciken wasu gidajen zama shida a cikin unguwar masu hannu da shuni ta New GRA Maiduguri.

    Wannan matakin na zuwa ne kasa da kwana biyu da NDLEA ta kama wani babban mai safarar Tramadol wanda darajarsa ta kai Naira biliyan 3, wanda hukumar ta ce yana da alaka da DCP Abba Kyarin.

  15. APC ta bukaci ministocin Buhari da ke son yin takara su ajiye aiki

    Domin kaucewa taka dokar zabe ta Najeriya, jam'iyyar APC mai mulkin kasar ta bayyana ranar karshe da ministoci da masu rike da mukaman gwamnati ya kamata su ajiye ayyukansu a matakan tarayya da na jihohi idan suna son tsayawa takara a zabukan da ke tafe.

    Jami'an gwamnatin na da zuwa ranar Asabar 30 ga watan Afrilu su ajiye mukaman nasu.

    Matakin ya shafi wasu ministocin gwanatin Buhari kamar ministan sufuri Chibuike Rotimi Amaechi da kwadago Chris Nigige, suna ciki jami'an da suka bayana aniyarsu ta tsayawa takara.

    Sashe na 3(i) na dokar jam'iyyar APC kan tsayar da 'yan takara a zaben 2023 na cewa: "Ba a yarda wani jami'in da ke rke da mukami a kowane matakin gwamnati ya zama deleget ko a zabe shi domin fitar da 'yan takara."

    Jadawalin zabe da hukumar zabe mai zaman kanta INEC ta fitar ya tsara cewa jam'iyyun siyasa na da zuwa ranar 3 ga watan Yuni domin su mika ma hukumar mutanen da suka tsayar a zabukan da ke tafe."

  16. Gwamnatin Najeriya ta yi watsi da tattaunawa da kungiyar ASUU - Osodeke

    Daliban jami'a a Najeriya na kokawa kan yadda aka yi watsi da halin da suke ciki.

    Koken na zuwa ne bayan da gwamnatin Najeriya da jami'an kungiyar malaman jami'a ta kasar ASUU suka gaza cimma wata matsaya kan warware rikicin da ya janyo malaman suka tsunduma cikin yajin aiki tun cikin watan Fabrairu.

    Shugaba ASUU Farfesa Victor Emmanuel Osodeke ya shaida wa BBC cewa gwamnati ta yi watsi da batun tattaunawar da bangarorin biyu ke yi.

    Ya kuma ce gwamnatin ta daina nemansu, har ta kai ga ta fara hana su albashinsu na tsawon wata biyu.

    Farfesan ya ce hana su albashinsu ba zai sa gwuiwoyinsu su yi sanyi ba, kuma za su ci gaba da neman hakkokinsu.

    "A bara ma an hana mu albashinmu na wata takwas zuwa tara kuma ba mu mutu ba."

    Kungiyar ASUU ta fada cikin wannan yajin aikin ne domin ta ce gwamnatin Najeriya ta ki biyan 'ya'yan kungiyar wasu hakkokinsu, a karkashin wata yarjejeniya da suka kula tun shekarar 2009.

  17. Rasha ta kulle bututun iskar gas zuwa kasashen Poland da Bulgeriya

    Kamfanin da ke samar da makamashi na Rasha Gazprom ya sanar cewa ya kulle bututun da ke jigilar iskar gas zuwa kasar Poland da Bulgaria bayan da kasashe biyun suka ki biyan kudin kayan da kudin Rasha wato rouble.

    Tun farko kasashen biyu wato Poland da Bulgariya sun ce Rasha ta sanar da su a hukumance cewa za ta kulle bututun.

    Sanarwar kamfanin na Gazprom ya biyo bayan bayanan da ke cewa iskar gas din ta ci gaba da shiga kasar Poland da sanyin safiyar yau Laraba amma daga baya Poland ta sanar cewa gas din ya daina isa kasarta.

    Cikin wata sanarwa, kamfanin makamashi na Poland ya yi tir da matakin na Rasha, yana cewa "matakin ya karya yarjejeniyar da Rasha da Poland suka kulla".

    Bulgariya ma ta tuhumi Rasha da karya yarjejeniyar kasuwanci iskar gas tsakaninsu.

    Sai dai zuwa wannan lokacin da muke hada wannan rahoton, sauran kasashen Turai na ci gaba da samu iskar gas daga Rasha.

  18. Mai son yi wa APC takara na son sauya sunan Najeriya

    Wani dan takarar mukamin shugaban kasa a Najeriya Adamu Garba, yace yana son a sauya sunan kasar zuwa "Tarayyar Nigritia" ko kuma Nigritia.

    Ya ce wannan na cikin matakan da zai dauka idan aka zabe shi shugaban kasa.

    Za a gudanar da zaben shugaban kasa a watan Fabrairun 2023 ne.

    "Me zai hana mu sauya fasalin wannan kasar, ta hanyar mayar da ita tarayya sosai kuma mu sauya sunanta zuwa "Tarayyar Nigritia" ko kuma NIGRITIA. Dama can Nigritia shi ne tsohon sunannmu kafin Lady Lugard ta sauaya shi zuwa Najeriya," inji Adamu Garba cikin wani sako na Twitter da ya wallafa.

    Ya kuma kawo misalan wasu kasashe da suka sauya sunayensu "na mulkin mallaka" kamar Ghana da Kenya da Benin da Togo, bayan da suka sami 'yancin kai.

    Mista Graba ya kuma wallafa wani bidiyo da ke bayyana yadda ya dace a fadi sunan da yake so a sauya.

  19. Mu hada karfi da karfe domin murkushe matsalar rashin tsaro - Buhari

    Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi kira ga dukkan jam'iyyun siyasa a kasar da su ajiye batutuwan zabe a gefe guda kuma su hada hannu da gwamnatinsa a kokarin da take yi na magance matsalar tsaro a kasar.

    Shugaban ya bayyana haka ne yayin da wasu jami'an jam'iyun suke shan ruwa a Fadar Aso Rock tare da wasu manyan 'yan kasuwar kasar, inda ya ce rashin tsaro shi ne babbar matsalar da ke damun kowane dan Najeriya.

    Shugaban ya ce a makon jiya, yayin taron babban kwamitin gudanarwa na jam'iyyarsa ta APC, an fitar da kwakkwarar matsaya cewa jam'iyyar za ta ci gaba da kokarin karfafa turakun dimokradiyya a dukkan matakan mulki na kasar.

    Ya kuma tabo batun saukaka kasuwanci a kasar inda ya shaida wa manyan 'yan kasuwan da ke dakin cewa gwamnatinsa ta taka rawar gani a fagn inganta yanayin kasuwanci a Najeriya, sannan ya bukaci su taimaka ma ta wajen kawar da talauci da samar da ayyukan yi ga matasa:

    "Babu gwamnatin da ta yi aiki mai yawan namu a bangaren samar da daidaitaccen yanayi da renon kasuwanci ga manya da kananan kamfanoni domin su bunkasa.

    Yayin da yake magana a madadin jam'iyyun siyasa da suka halarci shan ruwan, Injiniya Yusuf Yabagi, wanda shi ne shugaban jam'iyyar Action Democratic Party (ADP) ya bayyana shugaba Buhari a matsayin mai yekini gina dimokradiyya na gaske.

    'Yan kasuwan da suka halarci shan ruwan ma sun yi tsokaci, inda Mista Kola Adesina wada shi ne shugaban kamfanin Sahara Group, ya ce tilas shugaban da zai gaji Muhammadu Buhari "ya rungumi salon karfafa gwuiwar jama'ar kan samar da sabuwar najeriya, ba gina kansa ba kawai".

  20. Budewa

    Masu bibiyar wannan shafi na kai-tsaye daga BBC Hausa, Sani Aliyu na yi muku fatan kun wayi gari cikin koshin lafiya.

    A yau Laraba ma akwai labarai da rahotanni daga sassan duniya daban-daban da za mu kawo muku, saboda haka sai ku ci gaba da kasancewa da Sashen Hausa na BBC a intanet da shafuka sada zumunta, har ma a rediyo da talabijin.