Ƙarshen rahotannin kenan a wannan shafi
Mu haɗu da ku gobe don samun wasu sabbin rahotannin.
Kafin nan, Umar Mikail ke muku fatan alheri.
Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da Afirka da sauran sassan duniya musamman Ukraine da Rasha.
Awwal Ahmad Janyau and Umar Mikail
Mu haɗu da ku gobe don samun wasu sabbin rahotannin.
Kafin nan, Umar Mikail ke muku fatan alheri.
Shugaban Majalisar Turai, Charles Michel, ya yi maraba da sakamakon zaɓen kuma ya taya Macron murnar lashe shi bisa hasashen da aka yi.
Cikin wani saƙon Twitter, Mista Michael ya ce ƙungiyarsu ta EU na buƙatar Faransa wadda za ta mayar da hankali manufar ƙungiyar da kuma Turai baki ɗaya.
Ita ma Shugabar Hukumar Turai, Usula von der Leyen, ta yi maraba sannan ta ce tana jiran ci gaba da aiki da shugaban da aka sake zaɓa.
Sowa ta ɓarke a gaban zanƙaleliyar hasumiyar Eiffel Tower da ke birnin Paris daidai lokacin da ake bayyana hasashen cewa Emmanuel Macron ya lashe zaɓen shugaban ƙasa a yammacin yau Lahadi.
Magoya baya sun yi ta ihun "Macron, shugaban ƙasa".
Macron zai ci gaba da jagorancin Faransa cikin shekara biyar masu zuwa.
Sakamakon da ke shigowa a zaɓen shugaban Faransa na nuna cewa Shugaba Emmanuel Macron ya samu nasarar lashe zaɓen.
Shugaban wanda da ma aka yi hasashen zai ci ya samu kashi 58 cikin 100 na ƙuri'un da aka kaɗa.
A gefe guda kuma, Marine Le Pen ta ci kashi 42 cikin 100, a cewar masu hasashen sakamakon.
Tsohon tauraron wasan damben boxing, Myke Tyson, ya nannaushi wani fasinja a cikin jirgi sakamakon abin da ya ce robar ruwa da aka cilla masa.
Wani bidiyo da aka ɗauka a cikin jirgin ya nuna yadda Mista Tyson ya ragargaje mutumin yana kai masa naushi ba ƙaƙƙautawa a ka.
Sai dai kafin faruwar hakan, an ga wani matashi na tsaye ta bayan kujerar da Tyson ke zaune yana maganganu, kodayake ba a jin abin da yake cewa.
A cewar TMZ, Tyson ya amince ya ɗauki hoto da mutumin amma kuma daga baya ya ci gaba da matsa masa duk da cewa ya nemi ya bari.
'Yan sanda sun ce sun saki mutum biyun da suka tsare amma za a ci gaba da bincike.
Ƙungiyar masu iƙirarin jihadi ta ISWAP ta ɗauki alhakin kashe 'yan sandan Najeriya a harin da wasu 'yan bindiga suka kai kan ofishinsu a Jihar Kogi da ke tsakiyar ƙasar ranar Asabar.
Wata sanarwa da ƙungiyar ta fitar a dandalin sadarwa na Telegram ta ce mayaƙanta sun buɗe wa ofishin wuta da mashinga tare da kashe 'yan sanda biyar a Ƙaramar Hukumar Adavi.
Sai dai rundunar 'yan sandan Najeriya ta ce dakarunta uku aka kashe.
Ba a saba ganin 'yan ƙungiyar sun kai hari yankin ba, tana mai cewa ta kai shi ne saboda ɗaukar fansar kashe kwamandojinta da jami'an tsaron Najeriya ke yi a kwanan nan.
Kazalika, ƙungiyar ta ce ita ce ta kai hari kan wata mashaya a Jihar Taraba kwana ɗaya kafin wannan harin na Kogi.
Rahotanni sun ce shugaban Yan adawa a Chadi Dadi Hassan Guero ya koma ƙasar bayan ya gudu zuwa Masar shekaru kusan 20.
Ya sauka ne a N'Djamena a ranar Asabar, inda magoya bayansa suka tarbe shi.
Hukumomin Chadi sun shirya gudanar da taron ƙasa na sasantawa a ranar 10 ga Mayu inda za a tattauna yadda ƙasar za ta koma tubar dimokuradiyya.
A farkon watan Afrilu ƴan tawayen FACT da mayaƙa da dama suka miƙa wa sojojin Chadi makamansu.
Wannan na zuwa bayan soma tattaunawa a Doha, ƙasar Qatar.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya bayyana mummunar fashewar da aka yi a wata matatar mai ta haramtacciyar hanya a matsayin wani bala'i a ƙasa, yana mai cewa ƙasar na cikin "kaɗuwa da tashin hankali".
Jami’ai sun ce aƙalla mutum 109 ne suka mutu sakamakon fashewar wani abu a jihar Imo da yammacin Juma’a.
Buhari ya umarci jami’an tsaro da su ƙara ƙaimi domin rufe haramtattun matatun mai a yankin kudu maso gabashin kasar.
Ana kyautata zaton Najeriya na asarar kusan ganga 2,000 na danyen mai a rana, sakamakon satar mai daga bututuna manyan kamfanonin mai.
Cin hanci da rashawa ya durkusar da yunkurin da ake na dakile satar mai.
Marine Le Pen ta kasance ta farko da ta jefa ƙuri'a a ranar Lahadi.
Ta jefa ƙur'a ne a Hénin-Beaumont a arewacin Faransa.
Daga baya ne, Emmanuel Macron ya jefa ƙuri'arsa a Le Touquet, tare da matar shi Brigitte
Ƴan sanda a Najeriya sun ce suna gudanar da bincike domin gano wanda ke da wata matatar mai ba bisa ka’ida a yankin Neja Delata inda gomman mutane suka mutu.
Sama da mutane 100 suka mutu a gobarar da ta tashi a haramtattun matatun man a jihar Imo da ke kudu maso gabashin Najeriya.
Iyalai na ta tururuwan zuwa neman 'yan uwansu, sai dai gobarar ta kona mutane ta yawa ba a iya ganesu.
Rahotanni na cewa ko mutanen da aka ceto da farko lokacin faruwar al'amari daga bisani sun mutu.
Rashin ayyukan yi da talauci na taka rawa wajen kafuwar irin wadannan haramtattun matatun don kasuwanci, sai dai galibi ba a wanyewa lafiya.
Kwamishinan harkokin mai a Imo ya gargadin 'yan Najeriya kan kaucewa irin wadannan ayyuka, yana mai cewa galibi na rusa rayuwar matasa ko kai wa ga rasa rayuka.
Wata babbar lauyar kare haƙƙin bil'adama ta Birtaniya ta yi zargin cewa an bai wa sojojin Rasha "izni " su yi wa fararen hula fyaɗe a yayin da suke mamaye Ukraine.
Baroness Kennedy of The Shaws, da ke cikinwani kwamitn shari'a da ke taimakawa wajen tattara laifukan yaƙi da aka aikataa Ukraine, ta ce hujjoji zuwa yanzu sun nuna "manyan laifuka" da sojojin Rasha suka aikata.
Da take magana dashirin Sky na Sophy Ridge a ranar Lahadi, ta ce anba sojojin wani nau'in "kariya" saboda basu da wani horo na kiyaye laifuka.
Amma ta ce gurfanar da mutane a kan irin waɗannan laifuka yana da matukar wahala.
Ana zargin Rasha da aikata laifukan yaƙi a yankuna da dama na Ukraine ciki har da Bucha. Fadar Kremlin ta sha musanta cewa dakarunta sun aikata ta'asa.
Musulman Faransa za su yanke hukuncin wanda za su zaɓa sakanin Emmanuel Macron da wasu daga cikinsu ke kallon shugabancinsa ya yi masu illa da kuma Marine Le Pen, wacce jam’iyyarta ta yi ƙaurin suna wajen kyamar Musulmi.
Macron da Le Pen na fafatawa ne zagaye na biyu na zaɓen Faransa a ranar Lahadi, kuma mataki na ƙarshe da zai tantance mutumin da zai mulki Faransa shekaru biyar nan gaba.
Dukkaninsu na farautar ƙuri’un da Jean-Luc Melenchon ɗan takarar da ya zo na uku a zagaye na farko ya samu, wanda aka bayyana cewa kusan kashi 70 na Musulmin Faransa shi suka zaɓa saboda sassaucinsa.
Sai dai ana ganin yawancinsu za su ƙauracewa zaɓen saboda kasa yanke hukunci kan wanda za su zaɓa tsakanin shugaba Emmanuel Macron da Marine Le Pen.
Mafi yawan musulmin Faransa na fushi ne da Macron musamman dokar 2021 da suke Allah wadai da ita da kuma manufar rufe cibiyoyin Musulmi da hukumomi suka ce na ƙara ƙarfafa tsattsauran ra’ayi.
Marine Le Pen kuma mai ƙyamar baƙi ta sha alwashin haramta hijabi da cin tarar duk wadda aka kama sanye da lulluɓi.
Ana zargin wani mutum mai shekara 32 da kashe matarsa mai suna Mercy Samuel a Jos a jihar Filato da ke arewacin Najeriya.
Hukumomin jihar Filato sun tabbatar da faruwar lamarin, inda Kwamishiniyar kula da harakokin mata ta jihar Rebecca Sambo ta shaida wa BBC Pidgin cewa lamarin ya faru ne a daren 17 ga watan Afrilu.
Ta ce mijin ya yaga cikin matarsa misalin ƙarfe biyu na dare ya cire ƴan hanjinta.
Matar ƴar shekara 25 ta mutu bayan an garzaya da ita zuwa asibitin koyarwa na Jami’ar Bingham a Jos domin yi mata tiyata.
Rundunar ƴan sandan Filato ta ce tana kan gudanar da bincike game da al’amarin.
Mercy da mijinta sun yi aure tsawon shekara tara kuma sun haifi ƴaƴa biyu.
Dan uwanta ya ce cikin dare makwabta suka ji tana ihu, ko da aka fito sai ga ƴan hanjin cikinta a hannunta.
Yanzu haka ƴan sanda na farautar mijin wanda ya gudu.
‘Yan bindiga sun yi garkuwa da mambobin kungiyar Makiyaya ta Najeriya (MACBAN) guda 10 tare da sace shanu 300 a jihar Anambra.
An kai wa Fulanin harin ne cikin dare suna bacci a Obene cikin ƙaramar hukumar Ogbaru a jihar Anambra, kamar yadda shugaban Miyetti Allah shiyar kudu maso gabashin Najeriya, Alhaji Gidado Siddiki ya shaida wa jaridar The Nation.
Ƴan bindigar da aka bayyana sun kai 40 ɗauke da manyan makamai sun buƙaci a biya su miliyan hudu a matsayin kuɗin fansa da kuma bindiga daga iyalan wadanda aka kama.
Shugaba Volodymyr Zelensky na Ukraine ya sanar da cewa sakataren harkokin wajen Amurka, Antony Blinken da na harkokin tsaro, Lloyd Austin za su ziyarci birnin Kyiv a yau Lahadi.
Mista Zelensky ya ce yana saran su iso kasarsa da kayayyakin taimako.
Ya ce zai gana da su kuma yana ganin shugaban Amurka ya aikowa Ukraine duk wani abu na taimako da muke ta roko a kai.
Ya kuma sanar da cewa kusan mutane rabin miliyan - da suka hada da yara akalla dubu biyar - an maida su daga yankunan Ukraine da Rasha ta mamaye zuwa yankin Rasha.
Mista Zelensky ya kuma soki ganawar da sakataren janar na Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres, zai yi da Vladimir Putin a Moscow a ranar Talata kafin ya je Kyiv.
Ya ce kamata ya yi Mista Guterres ya soma zuwa Ukraine domin ganin abubuwa da idonsa kafin ya je Rasha.
Mista Zelensky ya shafe sa'o'i uku yana jawabi ga manema labarai daga tashar jirgi ta karkashin kasa a Kyiv.
Birnin Shanghai na China mai hada-hada ya rawaito cewa an samu mutum 39 da suka mutu sakamakon annobar korona a ranar Asabar - adadi mafi yawa da ake samu tun tsaurara dokar kulle makonni hudu da suka gabata.
A ranar Litinin da ta gabata aka bada rahoton mutum na farko da ya mutu tun sake dawowar annobar, da kuma samun dubbai da suka kamu a rana guda.
Birnin Shanghai mai al'umma miliyan 25 yanzu haka na fama da barkewar wannan annoba mafi girma a China kawo yanzu.
Ana c igaba da daukar matakai masu tsauri, da kwashe mutane daga gidajensu domin yi feshi. Sannan a Beijing, jami'ai na gargadi kan barazanar da cutar da ke yaduwa cikin gaggawa ke haifarwa.
Faransawa sun fara kaɗa kuri'a a zaɓen shugaban kasa a yau Lahadi, zagaye na biyu, kuma na karshe da zai tantance mutumin da zai mulki Faransa shekaru biyar nan gaba.
Ana fafatawa tsakanin shugaba mai ci, mai ra'ayin Tarayyar Turai Emmanuel Macron da Marine Le Pen mai ra'ayin rikau, wadda ta alkawarta ganin ta samun mulkin kasar da kalubalantar mahukunta Turai.
Mista Macron ake kallon mutumin da zai yi nasara, amma zaɓen ana ganin zai yi zafi sosai fiye da na wanda aka gani a zabensu shekaru biyar baya.
Akwai Milyoyin masu kada kuri'a da suka kasa yanke hukunci kan mutumin da za su zaɓa ko kuma su haƙura da zaɓen baki ɗaya.
Kuri'ar jin ra'ayi na hasashe za a fuskanci karancin mutune a rumfunan zabe, irinsa na farko tun 1969.
Muna maraba da kasancewa da ku a wannan shafin da muke kawo maku labarai da rahotanni kan abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya.