Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Shekara 52 na mulkin Alafin na Oyo sun ƙayatar ta hanyoyi da yawa - Buhari

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da Afirka da sauran sassan duniya musamman Ukraine da Rasha.

Rahoto kai-tsaye

Awwal Ahmad Janyau and Umar Mikail

  1. Mu kwana lafiya

    Ƙarshen rahotannin kenan a wannan shafin. Sai kuma gobe, inda za mu kawo wasu sabbi.

    Umar Mikail ke cewa mu zama lafiya.

  2. An saki Alpha Conde daga ɗaurin talala

    Gwamnatin mulkin soja a Guinea ta ce tsohon shugaban kasar da aka hamɓare, Alpha Conde, yanzu ya samu 'yanci kuma an ba shi damar ganawa da mutane.

    Mista Conde, mai shekara 84, ya zama zaɓaɓɓen shugaban ƙasa na farko a ƙasar Guinea a shekara ta 2010, amma sojoji suka hamɓarar da shi a shekarar da ta gabata, aka kuma tsare shi a gida.

    Sojojin sun ce Mr Conde zai ci gaba da zama a gidan matarsa da ke babban birnin kasar Conakry.

    Juyin mulkin ya biyo bayan zanga-zangar da jama'a suka yi kan yunkurinsa na neman wa'adi na uku - wanda ƴan adawa suka ce ya saɓawa kundin tsarin mulkin kasar.

  3. Zaɓen Faransa: An fara kaɗa ƙuri'a a ƙasashen waje

    An fara kaɗa kuri'ar zaben shugaban kasar Faransa karo na biyu a wasu yankunan da ke wajen ƙasar, kwana guda kafin a yi zaben a cikin ƙasar.

    An takatar da yakin neman zabe tsakanin 'yan takarar tun a ranar Juma'a.

    Ba za a wallafa wani ra'ayi ba na magoyin bayan 'yan takarar ko kuma a sanya muryar 'yan takarar a kafofin yada labarai a yau.

    Macron dai mutum ne mai matukar goyon bayan bukatun nahiyar Turai kuma yana fafutikar ganin kasashen na hada kai wajen tunkarar lamura.

    Ita kuwa Le Pen wadda ke da shakku kan ra’ayin hada kan kasahen na Turai, tana so a dauki tsauraran matakai kan shige da fice.

  4. Shekara 52 na mulkin Alafin na Oyo sun ƙayatar ta hanyoyi da yawa - Buhari

    Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya jajanta wa gwamnatin Jihar Oyo da al'ummar jihar kan rasuwar sarkin Yarabawa Alafin na Oyo, Lamidi Olayiwola Adeyemi III, ranar Juma'a.

    Buhari ya bayyana shekara 52 da sarkin ya shafe a karagar mulki da "masu ƙayatarwa ta hanyoyi da dama" cikin wata sanarwa da kakakin fadar shugaban ƙasa Femi Adesina ya fitar.

    A yau Asabar aka yi jana'izar sarkin a tsohon garin Oyo, inda aka binne shi a farfajiyar masarautarsa.

    Mai martabar ya rasu ne yana da shekara 83 a wani asibiti da ke Jihar Ekiti bayan ya yi fama da jinya.

    Shugaban ya yi addu'ar Allah ya ji ƙan sa, yana mai cewa "na tuna irin kalaman hikima da ya dinga yi a duk lokacin da ya halarci tarukan ƙasa".

  5. An yi jana'izar Alaafin na Oyo Oba Lamidi Adeyemi

    An yi jana'izar Alaafin na Oyo, Oba Lamidi Adeyemiɗaya, wanda ɗaya ne daga cikin manyan sarakunan Yarabawa a kudancin Najeriya.

    An binne shi a fadarsa da ke tsohon garin Oyo a yau Asabar kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.

    Masarautar Oyo ta ce ya rasu ne a ranar Juma’a yana da shekara 83 bayan ya yi jinya a Asibitin Koyarwa Jami’ar Afe Babalola a Ado Ekiti, babbar birnin jihar Ekiti da ke kudu masu yammacin Najeriya.

    Shi ne sarki mafi daɗewa a kan gadon sarautar.

  6. An kashe mutum biyar bayan harin Rasha, in ji Ukraine

    Aƙalla mutum biyar aka kashe bayan harin da Rasha ta kai a garin Odesa mai tashar jirgin ruwa, a cewar babban jami'i a ofishin shugaban Ukraine.

    Wani jariri ɗan wata uku da haihuwa na cikin waɗanda suka mutu, kamar yadda Andriy Yermak ya wallafa a dandalin Telegram.

    Ya ƙara da cewa wasu 18 sun ji rauni.

    An hari wani gini mai ƙunshe da gidaje yayin luguden wutar.

    "Ba abin da aka raga wa," in ji Yermak. "Rashin imani zai gamu da hukunci."

  7. Ebola ta dawo a Congo

    Hukumomi a Jamhuriyyar Dimokuradiyar Congo sun ce an samu ɓullar Ebola a arewa maso yammacin ƙasar, karon farko bayan wata shida da rabuwa da cutar.

    Hukumomin sun ce cutar ta ɓulla ne a Mbandaka, babban birnin lardin Equateur.

    Sau 13 aka samun ɓullar cutar a congo, haɗi da ɓarkewar cutar a 2018 inda ta kashe sama da 2,000.

  8. Yadda birnin Mariupol da Rasha ta yi wa ƙawanya ya koma

    Wasu hotuna sun nuna girman yadda aka tarwatsa birnin Mariupol wanda dakarun Rasha suka yi wa ƙawanya kusan wata biyu.

  9. Nawa ne kuɗin kujerar hajjin bana?

    Hukumar Alhazzai ta kasa a Najeriya ta ce za ta bayar da fifiko ga wadanda suka riga suka ajiye kudadensu a hannun hukumomin alhazzai na jihohinsu tun ‘yan shekarun baya, wajen rabon kujeru kimanin dubu 43 da hukumomin Saudiyya suka warewa kasar a bana.

    Sai dai hukumar ta yi gargadin cewa kodayake kawo yanzu ba ta tantance ko nawa za a biya kujera a bana ba, maniyyata su kwana cikin shirin biyan karin kudi sosai da zai iya ninka wanda aka biya a baya.

    Hakan kuwa inji ta saboda dalilai kamar na tashin canjin dala da na farashin man jirgin sama da kuma Karin harajin da hukumomin Saudiyya suka yi.

    Wadannan bayanan dai sun fito fili ne a yayin wani taro da hukumar ta yi da shugabannin hukumomin alhazzai na jihohi a makon nan bayan da kasar Saudiyya ta sanar da yawan kujerin da ta kebewa kasar a bana.

    Kan haka ne a filinmu na Gane Mini Hanyana wannan makon Haruna Shehu – Tangaza ya tattauna da Alhaji Abdullahi Harɗawa, kwamishinan aikace-aikace na hukumar wanda ya fara da yin bayani dangane da taron

  10. Mutum miliyan 14 suka ziyarci Masallacin Annabi a Madina a azumin bana

    Hukumomin Saudiyya sun ce aƙalla masu ibada miliyan 14 suka ziyarci Masallacin Annabi SAW a Madina tun farkon soma azumin watan Ramadan, kamar yadda kamfanin dillacin labaran ƙasar ya ruwaito.

    Hukumomin sun ce dun ɗauki matakai na lafiya sakamakon yawan masu ibadah a bana. Kuma sun ce zuwa yanzu babu ɓarkewa wata annoba ko cuta ko wani abin da ke barazana ga lafiya.

    Hukumomin sun ce ma’aikata 18,000 ke aikin kula da masu ibadah a Masallacin.

  11. Ana shirin jana'izar Alaafin na Oyo, Oba Lamidi Adeyemi

    Rahotanni sun ce idan an jima a yau ne za a binne Alaafin na Oyo, Oba Lamidi Adeyemiɗaya daga cikin manyan sarakunan Yarbawa a kudancin Najeriya.

    Masarautar Oyo ta ce ya rasu ne a ranar Juma’a yana da shekara 83.

    Shi ne wanda ya fi daɗe wa a kan gadon Sarautar.

    Bayanai sun ce ya rasu ne a asibitin koyarwa ta Jami’ar Afe Babalola a Ado Ekiti, babbar birnin jihar Ekiti da ke kudu masu yammacin Najeriya.

  12. Iran da Saudiyya na sasantawa a Iraƙi

    Rahotanni sun ce Saudiyya da Iran sun koma teburin tattaunawa da nufin kyautata alaka tsakanin kasashen biyu da ke gaba da juna.

    Kawo yanzu babu wani tabbaci a hukumance, amma wani shafin intanet na yada labarai na gwamnatin Iran ya ce an yi tattaunawar a Bagadaza.

    Kasashen biyu na adawa da juna a wasu rikice-rikicen yankin ƙasashen Larabawa da kuma rikicin siyasa.

    Sai dai sun fara tattaunawa a bara da nufin rage barazana a yankin.

    Iran ta dakatar da tattaunawar a watan da ya gabata ba tare da bayar da wani dalili ba. Matakin ya biyo bayan hukuncin kisa da mahukuntan Saudiyya suka yi wa mutum 81 a rana daya - wanda aka ce rabinsu 'yan Shi'a ne tsiraru.

  13. Ƴan sandan Najeriya sun kai samame inda ƴan IPOB ke haɗa bom

    Ƴan sanda a Najeriya sun ce sun kai samame a wata cibiyar da ake hada bama-bamai a jihar Imo da ke kudu maso gabashin kasar, inda ake ci gaba da samun tashin hankalin ƴan aware.

    Sun ce samamen ya faru ne a ranar Laraba a garin Umuaka bayan an kwarmata ma su.

    Mai magana da yawun ƴan sandan ya ce an kwarmata ma su wata maɓoyar da masu fafutikar kafa ƙasar Biafra IPOB, ke ƙera abubuwan fashewa.

    Ya ce sun kama wani da ake zargi tare da kwato kayayyaki da suka haɗa da bututun karfe fiye da 50.

    Hukumomin Najeriya na ɗora alhakin hare-haren baya-bayan nan kan ƴan ƙungiyar IPOB mai fafutukar kafa wata ƙasa ta ƴan kabilar Igbo.

  14. Rasha ta yi ikirarin kakkabo jiragen Ukraine

    Rasha ta ce ta harbo jirgin yaƙin Ukraine tare da tarwatsa wasu guda uku masu saukar angulu a yankin Kharkiv.

    Ma'aikatar tsaron Rasha ta ce dakarunta kai hari kan sojojin Ukraine tare da ikirarin samun nasarori

    BBC ba za ta iya tantance gaskiyar ikirarin ba. Ɓangaren Ukraine bai mayar da martani ba kawo yanzu.

    Tun da farko Birtaniya ta ce Rasha ta kasa yin komi a yankin tsawon sa'a 24, duk da ƙaruwar ayyukan dakarunta. Ta ce har yanzu Rasha ba ta karɓi ikon komi ba a ƙasa ko a ruwa.

  15. Isra’ila ta ce za ta rufe mashigin da ya rage a buɗe na Zirin Gaza

    Hukumomin Isra'ila sun ce za su rufe mashigin da ya rage a buɗe na Zirin Gaza a ranar Lahadi, a matsayin martani ga hare-haren rokoki da aka harba a cikin yankin Isra'ila.

    Ba a bayyana lokacin da za a sake buɗe mashigin ba.

    Mayakan Falasdinawa a Gaza sun harba rokoki guda biyu cikin Isra'ila a ranar Juma'a bayan rikici a harabar Masallacin Al Aqsa a birnin Kudus.

    An harba makamin roka na uku sanyin safiyar Asabar wanda ya faɗo a wani buɗaɗɗen wuri.

    Rufe kan iyakar Erez zai shafi dubban Falasdinawa da ke aiki a yankin Isra'ila.

  16. Alaafin na Oyo, Oba Lamidi Adeyemi, ya rasu

    Alaafin na Oyo, Oba Lamidi Adeyemi, babban basarake a yankin Yarbawa a kudancin Najeriya ya rasu.

    Masarautar ta ce ya rasu ne a ranar Juma’a yana da shekara 83.

    Shi ne wanda ya fi daɗe wa a kan gadon Sarautar.

    Bayanai sun ce ya rasu ne a asibitin koyarwa ta Jami’ar Afe Babalola a Ado ekiti, babbar birnin jihar Ekiti da ke kudu masu yammacin Najeriya

  17. Maraba

    Muna maraba da kasancewa da ku a wannan shafin da muke kawo maku labarai da rahotanni kan abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya.