Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Buhari ya taya Macron murnar lashe zaɓen Faransa
Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da Afirka da sauran sassan duniya musamman Ukraine da Rasha.
Rahoto kai-tsaye
Sani Aliyu
An kashe mutum uku a asibitin yankin Darfur
Kungiyar likitocin kasa da kasa ta Medecins Sans Frontieres, sun ce an kashe mutane uku a wani asibiti da ke yankin Darfur na Sudan a lokacin wani yamutsi da ya faru a karshen mako.
MSF ta ce an sace magungunan da ke dakin saida magani na asibitin koyarwa na El Geneina, sun kuma dakatar da aiki a wajen.
Majalisar Dinkin Duniya ta yi kiran a gudanar da bincike kan musabbabin tashin hankalin, tsakanin wasu kabilu biyu da ba sa ga maciji, sama da mutum 160 ne suka mutu a lokacin yamustin na karshen mako.
Dubun dubatar mutane rikicin ya raba da muhallansu, bayan tashin hankalin na garin Kereneik, akwai rahotannin da ke cewa kungiyar 'yan daba Janjaweed ta larabawa ce ta kai yawancin hare-haren.
Za a binne wadanda gobarar matatar mai ta kashe a kudancin Najeriya
An fara shirye-shiryen binne sama da mutum 100, wadanda suka mutu sanadin tashin wuta a wata matatar mai ba bisa ka'ida ba a Najeriya.
Tashin wutar na ranar juma'a a kudu maso gabashin jihar Imo, ta jikkata wasu gwammai da ke halin rai-kwakwai-mutu-kwakwai a gadon asibiti.
Yawancin wadanda lamarin ya rutsa da su, da mamatan da wadanda suka kone sun je sayen mai ne. Kawo yanzu babu tabbacin abin da ya haddasa tashin wutar, wadda shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana babban bala'in da ya fadawa Najeriya.
Najeriya dai ita ce a sahun gaba na fitar da danyen mai a nahiyar Afirka, amma ta na asarar kusan ganga 200,000 a kowacce rana, sakamakon masu satar mai da ke fasa bututan, tare da tace shi a masana'antun cikin gida da suka kafa ba bisa ka'ida ba.
An fara shari'a ga makusantan Jammeh gaban kotu kan zargin cin zarafin mutane
An fara zaman shari'a a Jamus, kan wani dan Gambia da ake zargi da hannu a kashe-kashen da suka faru a lokacin mulkin tsohon shugaban kasa, Yahya Jammeh.
Ana zargin Bai Lowe da laifin take hakkin dan adam da kisan kai, ciki har da kisan da aka yi wa dan jaridar Gambia Deyda Hydara shekaru 18 da suka gabata.
A baya Mr Lowe, mai shekara 46, ya sha bayyana irin aika-aikar da suka aikata a matsayinsa na direban da ya tuka motar da akae buge mutane ba tare da an tsaya ba da aka yi wa lakabi da Junglers, da su ke aiki kai tsaye da shugaba Jammeh.
A wajen kotun da ke garin Celle da ke Jamus, masu rajin kare hakkin dan adam sun yi kiran a gurfanar da hambararren shugaban Gambia da ya yi gudun hijira da makusantan shi a gaban sharia.
Ana gudanar da shari'ar ne karkashin dokokin kasa da kasa, da suka amince a yi shari'a a gaban wata kotu a waje take da damar yanke hukunci akan laifuka take hakkin dan adam, da laifukan yaki, da kisan kare dangi, ba tare da la'akkari da inda aka aikata laifukan ba.
Wuta ta tashi a bututun iskar gas da ke kudancin Yemen
Kafar yada labaran Yemen, ta rawaito cewa wani abu ya fashe tare da lalata bututn iskar gas a kudancin kasar.
An yi amanna da cewa, wata kungiyar masu tsaurin ra'ayin addinin Islama ce ta kai hari a al-Nashima da ke yankin Shabwa.
Wannan na zuwa ne kwana guda bayan, Fira Minista Maeen AbdulMalik Saeed, mai gwqamnati a Aden ya amince da fitar da mai daga cibiyar gas da ke Shabwa,aikin hadin gwiwa tsakanin kamfanin mai na Total mallakin Faransa.
Bangarorin da ke yaki da juna na gwamnatin Yemen da 'yan tawayen Houthi, da kawancen da Saudiyya ke jagoranta, da gwamnatin da kasashen waje suka aminta da su, sun dakatar da bude wuta.
Sama da shekara 7 kenan ake yakin a kasar Yemen, abin da ya janyo matsalar aikin jin kai mafi girma a duniya kamar yadda Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana.
Za a yi gwajin korona a Beijing sakamakon karuwar masu cutar
Za a fara yi wa miliyoyin mazauna wasu yankuna na Beijing babban birnin China gwajin cutar korona, har kashi uku sakamakon karuwar masu kamuwa da cutar.
Gundumar Chaoyang, ya samu sabbin wadanda suka kamu har 26 a karshen mako, adadi mafi yawa tun bayan sake barkewar cutar a Beijing.
An ga dogayen layuka a wajen manyan kantinan sayar da kayan masarufi, duk da tabbacin da gwamnati ta bai wa 'yan kasa na samar da wadatattun kayan abinci.
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da Beijing ke fuskantar kwatan-kwacin halin da birnin Shanghai ya samu kan shi a ciki, da aka hana sama da mutane kusan miliyan 25 karkashin dokar kulle na makwanni.
An raba Kur’ani sama da 30,000 ga masu ibadah a Makkah
Sarkin Saudiyya da ke kula da masallatai guda biyu mafi daraja a duniya, wato masallacin Ka'aba da ke Makka, da na Manzon Allah SAW da ke birnin Madina, ya bada kyautar littafin Al-Qur'ani mai girma samada 30,000 a matsayin kyauta ga wadanda suka kai ziyara masallatan daga farkon watan Radaman, kawo yanzu.
Kwafin Al-Qur'ani mai tsarki da madba'ar sarki Fahad ta wallafa a birnin Madina, kyuata ce ta musaman daga jagoran kula da masallatan wato sarki Salman bin Abdul'aziz al-Sa'ud ga bakin da suka shigo kasar..
Buhari ya taya Macron murnar lashe zaɓen Faransa
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya taya shugaban Faransa Emmanuel Macron murnar lashe zaɓe wa’adi na biyu.
Shugaban ya ce akwai kyakykyawar alaƙa tsakanin Najeriya da Faransa tun bayan hawan shugaba Macron a shekarar 2017, inda ya kai ziyarar aiki Najeriya a shekarar 2018.
Ya kuma ce shugaban ya samar da hanyoyi na inganta alaƙar tattalin arziki da al'adu da tsaro tsakanin Najeriya da Faransa musamman a taron Faransa da Afirka.
Shugabannin Afrika sun taya Macron murna
African leaders are congratulating French President Emmanuel Macron on his re-election after a convincing victory over rival Marine Le Pen.
Shugabannin Afrika sun taya Emmanuel Macron murnar lashe zaɓen shugaban ƙasa wa'adi na biyu.
Macron shi ne shugaban Faransa na farko da aka sake zaɓe wa'adi na biyu tsawon shekara 20.
Shugaban Senegal Macky Sall, kuma shugaban Tarayyar Afrika yana cikin waɗanda suka taya Macron murna.
Shugaban ya ce yana wa Macron fatan samun nasara a sabon wa'adinsa.
Firaministan Habasha Abiy Ahmed ya ce yana fatan aiki tare da Macron domin inganta hulɗa tsakanin ƙasashen biyu.
Shugaban Rwanda Paul Kagame ya jinjina wa shugaban Macron da ya ce "yana neman haɗin kai ba rabuwa ba."
Askarawa sun kama mabarata a Makka da kusa da Ka'aba
Jami'an tsaron Saudiyya da ke birnin Makkah sun kama wasu mazauna birnin da wadanda suka kama suna bara an kuma kama biyu a kusa da masallacin Ka'aba.
Hukumomin sun ce sun kama wani dan kasar Indiya saboda an kama shi yaa kokarin karkatar da hanulan masu ibada domi su ba shi kudi, sannan sun damke wani dan asalin kasar Moroko da yake bara a jikin wata kofar shiga masallacin Ka'aba.
Akwai kuma wani dan kasar Yemen wanda ke amfani da sandunan guragu domin yaudarar masu ibada cewa shi mai nakasa ne.
Kana an kama wani mutum da ke tura dansa ya yi bara ta hanyar saka shi a kan keken guragu. Bincike ya tabbatar cewa dan nasa kalau yake.
Hukumar da ke kula da tsaron al'umma ta Saudiyya ta sanar cewa duk wanda aka kama yana bara, ko kuma wanda ya iza wani ya yi bara, ko ma ya amince da yin barar - zai shafe kusan shekara guda yana zaman gidan kaso ko ya biya tarar Riyal 100,000 ko ma duka.
Twitter ya amince da tayin dala biliyan 43 da Elon Musk yayi na saye kamfanin
Kamfanin sada zumunta na Twitter ya sanar da cewa ciniki ya fada tsakanin shi da hamshakin biloniyan nan Elon Musk.
Rahotanni sun ce daraktocin Twitter sun ce sun amince da tayin Elon Musk na kusan dala biliyan 43 bayan tattauna wa da suka yi da shi, da kuma matsin lamba daga masu hannun jari a kamfanin na cewa a sayar masa.
Sai dai akwai yiwuwar a sake samun jan kafa kan batun, bayan da Shugaban Twitter Parag Agrawal ya bayyana cewa akwai masu hannun jarin da basu amince Mista Musk ya mallaki abin da ya wuce kashi hamsin na kamfanin sada zumuntar ba.
Tun watan Afrilu ne Mista Musk ya sayi kashi 9.2 cikin 100 na kamfanin.
Majalisar Dinkin Duniya ta bukaci a binciki yadda aka kashe mutum 168 a Darfur
Majalisar Dinkin Duniya ta bukaci a gudanar da bincike kan yadda aka kashe mutum 168 yayin wani rikici da ya barke a yankin Darfur na kasar Sudan.
Jakada na musamman na majalisar, Volker Perthes ya yi tir da tashin hankalIn da ya barke a yankin Krink na Darfur ta Yamma, inda aka kona gidaje da asibitoci baya ga wawashe dukiyar jama'a.
Kusan mutum 100 aka raunata yayin rikicin, kamar yadda wata majiya mai suna General Coordination for Refugees and Displaced in Darfur ta wallafa.
Akwai kuma rahoton da ke cewa gwamnatin mulkin soja ta Sudan ta tura wata rundunar sojoji wadda ta yi kaurin suna zuwa yankin. A shekarun baya ana kiranta Janjaweed.
'Yan Janjaweed sun kashe dubban mutane a yankin na Darfur shekara 20 da ta gabata.
'Yan majalisar Togo sun amince kasar ta shiga kungiyar Commonwealth
Majalisar kasar Togo ta kada kuri'ar amincewa da wani kudurin doka da zai ba kasar damar neman shiga kungiyar kasashen da Ingila ta raina wato Commonwealth.
Kasar na cikin kungiyar ECOWAS ta kasashen yammacin Afirka, da kuma kungiyar International Organisation of La Francophonie ta kasashe masu magana da harshen Faransanci.
Kakakin majalisar ya ce, "Togo ba ta da niyyar ficewa daga Francophonie. Wannan matakin zai karfafa bangaren koyar da harshen Turancin Ingilishi ne da kulla wasu yarjeniyoyin."
A ranar Juma'a majalisar ta amince da wannan kudurin, kuma ta bukaci gwamnatin kasar ta mika takardun neman shiga ECOWAS din, yayin taron kolin kungiyar da za a yi a Rwanda a watan Yuni mai zuwa.
Tun shekarar 2014 kasar Togo ta fara wannan kokari na shiga kungiyar ta Commonwealth.
Dan takara na shan suka kan rokon a tara masa Naira miliyan 100 na sayen fom
Wani dan takarar mukamin shugaban Najeriya a karkashin inuwar jam'iyyar APC mai mulki Adamu Garba, na shan suka saboda yada yake rokon jama'a su taimake shi da Naira miliyan 100 na kudin sayen fom din tsayawa takara daga jam'iyyarsa.
Tun da farko Mallam Garba ya koka da tsadar fom din, kuma wannan ne yasa ya nufi shafinsa na Twitter inda ya wallafa sako yana rokonsu da su tara masa kudin domin ya cimma burinsa:
"Ya ku 'yan Najeriya, shirin da nake yi dominku ya fara aiki. Ga wadanda suka yi alkawarin taimakona da kudi ga lambar asusun ajiya ta a bankin Zenith na wallafa. Naira miliyan 100 domin saye fom na nuni ga rashin damuwa da halin da muke ciki, amma yunkurowa mu sayi fom din zai mika wani sako mai karfi cewa mu masu kishin Najeriya ne."
Sai dai yawancin wadanda suka mayar da martani kan wannan sakon nasa ba su amince da bukatarsa ba, kuma ya sha suka.
@DanielRegha ya ce "Adamu Garba, ko ka yi nasarar samun wasu wawayen 'yan Najerya da ka yaudara da karerayinka, kuma suka taimaka maka tara miliyan 100, ba za ka iya lashe zaben fitar da gwamni ba maballantana ka lashe zaben shugaban kasa."
@AsiyaRodrigo ta ce: "...matasa za su fi amfana idan suka yi amfani da kudaden da kake son a tara maka ta wasu hanyoyi kamar kasuwanci, domin na san kana da wasu hanyoyin samun kudaden. Kuma me zai hana ka tsaya takara a karkashin wata jam'iyyar da babu tsofafin kuraye masu yawa cikinta?"
NDLEA ta kama masu safarar hodar Ibilis cikin ganyen shayi a Abuja da Legas
Hukumar da ke yaki da masu tu'ammalli da miyagun kwayoyi NDLEA ta kama wasu 'yan Najeriya masu safarar hodar Ibilis ta hanyar boye su a wurare kamar cikin ganyen shayi.
Hukumar ta ce ta kama akalla masu safarar hodar ta Ibilis mutum hudu yayin da suke kokarin shigowa da fitar da its Najeriya a makon jiya.
A halin yanzu suna hannun hukumar, kuma ana gudanar da bincike, kamar yadda jami'i mai hulda jama'a na hukumar, Femi Babafemi ya shaida wa manema labarai.
Ya ce sun damke daya daga cikinsu mai suna Pascal Ekene Okolo yayin da ya iso Najeriya cikin jirgin saman Qatar daga Sao Paolo a ranar Lahadi 17 ga wannan watan.
Mista Okolo ya sanar da NDLEA cewa shi mai sana'ar maganin gargajiya ne kuma bayan da aka binciki kayansa, an gano kayan shayi da aka hada ganyayyaki, wanda a ciki aka boye kilo 4.1 na hodar Ibilis.
A wannan ranar kuma hukumar ta kama wani dan Najeriya mazaunin kasar Kanada mai suna Anigo Christian Godspower a fili jirgin saman Legas wanda shi ma ya iso Najeriya daga Sao Paolo na Brazil kuma ya yada zango a biri Doha na kasar Qatar.
NDLEA ta gano yana dauke da hodar Ibilis da nauyinta ya kai kilo 2.1.
An ajiye gawar tsohon shugaban Kenya domin 'yan kasar su girmama shi
'Yan kasar Kenya sun fara taruwa a gaban ginin majalisar kasar domin ganin gawar tsohon shugaban kasar na uku, marigayi Shugaba Mwai Kibaki wanda ya mutu a makon jiya yana da shekara 90.
An saka gawar cikin wani akwati wanda aka lullube da tutar kasar Kenya, kuma sojojin kasar ne suka raka ta zuwa ginin majalisar inda za a bar ta daga Litinin har zuwa ranar Laraba.
Ana sa ran Shugaba mai-ci Uhuru Kenyatta ne zai jagoranci girmama wa tsohon shugaban kafin a bar jama'ar kasar su bi sahunsa daga baya.
Majalisar ta sanar cewa duk da tana hutu, amma za ta yi zama na musamman a ranar Laraba domin girmama tsohon sugaban kasar.
Za a binne Mista Kibaki ne da karramawa irin wadda ake ba gwarazan shugabannin kasar da suka taka rawar gani kuma aka yaba da jagorancinsu.
Wata tashar talabijin mai suna Citizen TV ta kasar Kenya ta wallafa hoton akwatin gawar yayin da ya isa ginin majalisar kasar.
Kungiyar Dattawan Arewa ta yi magana kan 'yan takarar shugaban kasa na PDP
Shugabannin Kungiyar Dattawan Arewa a Najeriya sun nisanta kansu da matsayar da wasu daga cikinsu suka dauka na mara wa Sanata Bukola Saraki da Gwamnan jihar Bauchi State Bala Mohammed baya a matsayin 'yan takarar da arewacin kasar ta amince su tsaya takarar shugaban kasa a jam'iyyar PDP.
Cikin wata sanarwa da babban jami'in da ke kula da yada labarai na kungiyar Dr Hakee Baba-Ahmed ya sanya wa hannu, kungiyar ta ce ba a shigar da kungiyar a cikin hanyoyin da aka bi na yanke wannan shawarar ba.
"Ya zama dole mu mayar da martani kan labarin da ke yawo da ke nuna cewa Kungiyar Dattawan Arewa ta taka rawa wajen fitar da wasu 'yan takara cikin manyan 'yan takarar jam'iyyar PDP ta hanyar sasantawa tsakaninsu," in ji shi.
Sanarwar ta ce "'Yan takarar ne da kansu suka yi wannan yunkuri. Gwamna Aminu Waziri Tambuwal Gwamna Bala Mohammed da Bukola Saraki da kuma Malam Mohammed Hayatudeen sun sanar tsohon shugaban kasa Janar Ibrahim Babangida aniyarsu, kuma sun bukaci ya shiga cikin maganar a matsayinsa na dattijo."
Sanarwar ta kuma ce, "Janar Babangida ya bukaci shugaban kungiyar Farfesa Ango Abdullahi ya tsara wata hanya da za a bi wajen yin maslaha tsakanin 'yan takarar hudu."
Sai dai ba a matsayinsa na daya daga cikin jagororin Kungiyar Dattawan Arewa ya yi wannan aikin ba - ya yi shi ne a matsayinsa na Farfesa Ango Abdullahi, in ji sanarwar.
Sanarwar ta kara da cewa bayan Farfesa Ango ya kammala aikin, ya fitar da wani cikakken bayani da shawarwari, kuma ya sanya wa rahoton hannu a matsayinsa na Ango Abdullahi ne.
Saboda haka ne Kungiyar Dattawan Arewan ta ce ba da ita aka yi wancan aikin ba:
"Kungiyar Dattawan Arewa ba ta da alaka kai tsaye da wata jam'iyyar siyasa ko wani dan takara, kuma ta mayar da hankali ne wajen samar da shugabanni na gari a zabukan shekarar 2023. Kuma ta yi imani cewa akwai nagartattun 'yan takara da ya dace a bar wa jam'iyun siyasar kasar su zabo da kansu."
Barkanmu da safiyar Litinin
Ga dukkan masu bibiyar shafukanmu na BBC Hausa a intanet da shafuka sada zumunta, muna muku batan alheri cikin wannan yini da ma sauran ranaku masu zua.
Suna na Sani Aliyu, kuma nine zan fara gabatar da labarai da rahotanni daga sassa Najeriya da ma wasu kasashen a wannan yini.
Ku ci gaba da kasancewa da BBC Hausa.