Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Farashin gas ɗin girki ya hauhawa a Najeriya a watan Maris

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da Afirka da sauran sassan duniya musamman Ukraine da Rasha.

Rahoto kai-tsaye

Sani Aliyu and Badariyya Tijjani Kalarawi

  1. Sai da safenku

    Nan muka kawo ƙarshen rahotanni a wannan shafi.

    Mu haɗu da ku gobe idan Allah ya kai mu.

  2. Mai ba wa Shugaba Buhari shawara kan tsaro Monguno ya ja kunnen El-Rufai

    Mai bai wa Shugaban Najeriya shawara kan harkokin tsaro, manjo Janar Babagana Moguno ja kunnen Gwamnan Kaduna Nasir El-Rufai game da kalaman da ya ce gwamnan na yi kan harkokin tsaro.

    Monguno ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis yayin da yake zantawa da manema labarai a fadar shugaban kasa a karshen wata ganawa da shugaban kasa da hafsoshin tsaro a Abuja. “Gwamna Nasir El-Rufai ya yi magana kan hukumomin tsaron kasar nan yana cewa wai mun san ko su wane ne 'yan ta'addan nan, da inda suke,” a cewarsa.

    Monguno ya kara da cewa "wannan shi ne babban haɗarin, musamman idan ka fara maganar da ba ta dace ba, sai kai ta fadin abin da ba shi kenan ba".

    Bayan harin da aka kai kan jirgin kasa a watan Maris, Gwamna El-Rufai ya bukaci jami’an tsaro su kai hare-hare a maboyar ‘yan bindigar da ke dajin maimakon a jira su kai farmaki.

    El-rufa'i ya kuma tabbatar da cewa jami'an tsaron sun san sansanonin ‘yan bindigar da lambobin wayarsu, inda ya jaddada bukatar kai hari kan ‘yan ta’addan.

    Shugaba Buhari ya gana da shugabannin hukumomin tsaro daban-daban a ranar Alhamis.

  3. Daruruwa sun fice daga asibitin Tigray saboda rashin abinci - Reuters

    Kamfanin dillancin labarai na Reaters, ya rawaito cewa babban asibitin yankin Tigray da ke kasar Habasha na tsaka mai wuya, a makon da ya wuce ne asibitin ya umarci marasa lafiya sama da 240 su koma gida tun da babu abincin da za a ba su, saboda fargabar yawanci ka iya rasa rayukansu.

    Jami'an jinya a asibitin Ayder Reffal sun shaida kamfanin dillancin labaran cewa, jarirai da ke fama da rashin abinci mai gina jiki, da masu fama da tarin fuka na daga cikin wadanda aka ce su koma gida, har da wani yaro dan shekara 14 da ke fama da cuta mai karya garkuwar jiki.

    "Iyalai da ke barin asibitin su na cewa mu taya su da addu'a, maimakon mu mutu anan gara mun koma gida mu mutu a can,'' in ji wani likitan yara mai suna Tedros Fissehaye a hirarsa da Reuters.

    Ya kara da cewa shi da sauran ma'aikatan lafiya sun gagara kuka saboda hawayen su ya kafe, a lokacin da suka lura sauran kashi 10 ne kadai ya rage na magunguna a daukacin asibitin, ''hawayaenmu ya kafe wata da watanni.''

    Kawo yanzu gwamnatin kasar Habasha ba ta ce uffan ba kan wannna batun, bayan Reuters ta tuntube su kan wannan labari mai sosa rai.

    Rabon da a biya ma'aikatan asibitin Ayder Referral albashi tun watan Yulin bara, kamar yadda ma'aikatan asibitin suka shaidawa kamfanin illancin labaran. Kuma ma'aikata su ma sun dogara ne da abincin da ake ba su a asibitin.

  4. Farashin gas ɗin girki ya hauhawa a Najeriya a watan Maris

    Hukumar Ƙididdiga a Najeriya ta National Bureau of Statistics (NBS) ta bayyana cikin rahotonta na ranar Juma'a cewa farashin tsakatsaki na gas ɗin girki ya tashi da kashi 83.62 cikin 100 a watan Maris zuwa naira 2,057.71.

    Rahoton na watan Maris ɗin 2022 ya kuma ruwaito cewa farashi na tsakatsaki da ake cika tukunyar gas mai nauyin 5kg ya kai N3778.30 a watan Maris na 2022 daga N3708.58 da yake a Fabarairun 2022, abin da ya kai ƙarin kashi 1.88 cikin 100 a ma'aunin wata bayan wata.

    Game da jihohin da suka fi tsadar gas na girki, Jihar Ekiti ce ta fi ko'ina tsadar gas ɗin da ake wa laƙabi da Liquefied Petroleum Gas (LPG) inda ake cika 5kg kan N4200.00. Sai Neja da ke biye mata da N4163.33, da kuma Imo mai N4150.00.

    A gefe guda kuma, Adsamawa ce mai farashi mafi ƙaranci da N2604.01, sai Yobe da Kano da ake cika tukunyar ta 5kg kan N2740.00 da kuma N300.00.

    'Yan Najeriya na fama da hauhawar farashi a 'yan shekarun nan yayin da darajar kuɗin ƙasar naira ke ci gaba da faɗuwa.

  5. Akwai yiwuwar Pogba ba zai sake buga wa United wasa ba a bana

    Babu tabbas ko Paul Pogba zai sake buga wa Manchester United wasa a kakar bana, a cewar kocin riƙon ƙwarya na ƙungiyar Ralf Rangnick sakamakon raunin da ya ji.

    Kwantaragin ɗan wasan na tsakiyar Faransa mai shekara 29 zai ƙare a ƙarshen kakar bana, kuma ya fita daga wasan da Man United ta sha kashi a hannun Liverpool da ci 4-0 ne minti 10 kacal da take wasan.

    Ana sa ran ɗan wasan zai yi jinyar mako huɗu "aƙalla", yayin da United za ta buga wasanta na ƙarshe ranar 22 ga watan Mayu da Crystal Palace.

    "Abu ne mai wuya ya sake buga wasa har sai ƙarshen kaka," in ji Rangnick.

    Da aka tambaye shi ko Pogba ya buga wa United wasan ƙarshe, sai kocin ya amsa da cerwa: "Likita ya faɗa min cewa zai shafe mako huɗu aƙalla kafin ya warke kuma wasan da United za ta buga na ƙarshe a ƙarshen watan Mayu ne.

    "Ba na jin zai sake buga wasa."

  6. 'Yan sandan Najeriya na neman mutum 12 kan kashe-kashe a Jihar Anambra

    Shalkwatar rundunar 'yan sandan Najeriya ta sanar cewa tana neman wasu mutum 12 da take tuhuma da hannu a hada baki da kisan kai da fashi da makami da ayyukan ta'addanci da kuma mallakar makamai ba bisa ka'ida ba.

    Tana kuma tuhumar su da fasa kofofin gida da shiga ba bisa izini ba da barnata dukiyar jama'a da kuma tayar da hankulan al'ummar Isu-Aniocha na karamar hukumar Awka North ta jihar Anambra.

    Rundunar ta bayyana sunayensu kamar haka: Edward Okoye (aka Stone), Donatus Okeke, Onyemazi Ngini, Onyebuchi Nwekeizu Okoye, da Nonso Eboh.

    Sauran su ne: Chukwuka Onyibor, Chukwujekwu Anaekeokwu, Chuka Ilodigwe, Chinedu Nwoye Okoye, Nonso Awusionwu Obinna, Cosmos Okonkwo da Chukwujekwu Okoye.

    Sanarwar ta kuma ce: "Rundunar 'yan sanda ta samu izinin kotu domin ayyana cewa tana neman mutanen, wadanda dukkansu maza ne 'yan kabilar Igbo wadanda shekarunsu na haihuwa ke tsakanin 25 zuwa 55, kuma mazauna Isu-Aniocha na Ƙaramar Hukumar Awka North ta jihar Anambra ne."

  7. Shugaban Tunisiya ya yi katsalandan a hukumar zaben kasar

    Shugaban Tunisia kais Saied ya fitar da wata dokar shugaban kasa da ta maye gurbin mambobin hukumar zabe ta kasar ma zaman kan ta da wadanda ya nada da kansa.

    Aa kallon hukumar a matsayin wadda ta rage cikin ginshikan da dimokradiyya ta dogara a kai da suka rage a Tunisiya tun bayan da Mista Saied ya kwace iko kuma ya rushe majalisar kasar a bara.

    Da alama wannan matakin zai kara yawan masu adawa da shi a cikin kasar - wadanda ke da imani cewa ya tara wa kansa ikon da ya faye yawa.

    Matakin zai kuma tayar da hankula a siyasance musamman ganin cewa za a gudanar da zabukan shiga majalisr kasar a karshen wannan shekarar.

  8. Gwamnatin mulkin soji ta Mali za ta mika mulki 'nan da shekara biyu'

    Gwamnatin Mali ta kaddamar da shirin mika mulki na tsawon wata 24, wanda zai kai ga gudanar da zabe.A watan Agustan shekarar 2020 ne dai sojoji suka kwace mulki a kasar kuma suna fuskantar matsin lamba kan mayar da kasar bisa tafarkin dimokuradiyya.

    A watan da ya gabata ne kungiyar Ecowas ta kasashen yammacin Afirka ta bukaci gwamnatin da ta takaita lokacin mika mulki zuwa tsakanin watanni 12 zuwa 16 - lokacin da ta ce ya kamata a gudanar da zabe.

    Firaminista Choguel Maïga ya nuna cewa yanayin halin da tattalin arzikin duniya ke ciki, da barkewar cutar korona da kuma takunkumin tattalin arzikin da aka kakaba wa kasar a matsayin dalilan da suka sa aka dauki tsawon lokaci na mika mulki.

    A ranar Alhamis din da ta gabata ne, firaministan ya shaida wa majalisar rikon kwarya ta kasar da majalisar dokoki cewa a cikin watanni masu zuwa za a kafa hukumar zabe da samar da ingantattun kayan zabe, da bayar da horo ga wakilan zabe da kuma sake bitar kundin zaben.

  9. Kamfanin mota na Kia ya nada Shatu Garko jakadarsa ta Najeriya

    Kamfanin mota na Kia ya nada Shatu Gorko, Sarauniyar Kyau ta Najeriya a matsayin jakadar kamfanin a Najeriya.

    Wannan nadin ya biyo bayan kyautar mota samfurin Kia Rio ga sarauniyar wadda matashiya mai shekara 18 da hahuwa ce bayan da ta lashe gasar kyau ta Miss Nigeria ta 44 da aka yi a watan Disamba.

    Manajan kamfanin Kia a Najeriya ya ce kamfanin na da zummar ganin mata sun sami daukaka da ci gaba ta hanyar tallafa musu.

    Sabuwar jakadiyar kamfanin na Kia, Shatu Garko ta ce "Abin alfahari ne da na zama cikin iyalan kamfanin Kia."

  10. Rasha ta ci tarar Google rouble miliyan 11 kan laifin yada 'bidiyon bogi'

    Wata kotu a birnin Moscow ta ci tarar kamfanin Alphabet mamallakin Google saboda ya ki cire wasu bidiyo da suke takaddama a kai tsakaninsu.

    An ci tarar katafaren kamfanin fasahar zamanin sau biyu - wadanda jumilla sun kai rouble miliyan 11 ($135,000) "saboda ya taka" dokar Rasha.

    Wata kotu a gundumar Tagansky a Moscow ta cekamfanin ya yada bayanan da ba na gaskiya ba ne kan yawan dakarun Rasha da suka mutu a Ukraine.

    Daya daga ckin bidiyon ya nuna wata hira ta wayar tarho tsakanin wasu sojojin Rasha da 'yan uwansu a gida. Bidiyon ya nuna wai suna kokawa kan yawan wadanda suka mutu ne a cikinsu.

    Baya ga Google, Rasha ta dode wasu fitattun kafofin sadarwa kamar Facebook da Instagram, amma YouTube na nan yana aiki.

    Google ya taba fuskantar hukunci a Rasha a shekarun baya. An taba cin sa tarar rouble biliyan 7.2 a watan Disambar 2012 saboda ya ki sauke wasu bayanai da suka taka dokokin kasar Rasha.

  11. PDP: A binciki 'yan takarar APC da suka sayi fom kan Naira miliyan 100

    Babbar jam'iyyar adawa ta PDP a Najeriya ta bukaci hukumomin tsaron kasar, musamman masu yaki da cin hanci da rashawa da su kaddamar da bincike kan dukkan 'yan takarar da suka biya Naira miliyan 100 ko Naira miliyan 50 domin sayen fom din tsayawa takara.

    Jam'iyyar ta ce ya dace a binciki inda suka samo kudaden.

    Cikin wata sanarwa, PDP ta ce, "Wannan abu ne mai daure kai kuma na rashin nuna tausayi matuka. Lallai ya dace a binciki wadanda ke sayen fom din tsayawa takara kan Naira miliyan 100 da Naira miliyan 50, kan tuhumar sun aikata zamba."

    Shugaban jam'iyyar PDP na kasa Iyorchia Ayu ne yayi wannan kiran, cikin sanarwar da sakataren sadarwa na jam'iyyar, Simon Imobo-Tswam ya sanya wa hannu a ranar Alhamis.

    Kalaman nasa sun biyo bayan shelar da APC ta yi ne kan farashin fom din tsayawa takara.

    Jaridar Premium Times ta ruwaito cewa APC ta ayyana farashin fom din takarar mukamin shugaban kasa kan Naira miliyan 100.

    Jam'iyyar ta ce farashin fom din na-gani-ina-so Naira milyan 30 ne kuma na neman tsayawa takara kan Nairan miliyan 70, wanda shi ne ya zama jumilla Naira miliyan 100.

    Sai dai PDP ta ce sanya wadannan kudaden na nuna cewa jam'iyyar APC ta 'yan damfara da munafukai ce.

    Ita kuwa jam'iyyar ta PDP ta sanya farashin fom dinta na takarar mukamin shugaban kasa kan naira miliyan 40 ne, kuma kawo yanzu, 'yan takara kimanin 17 suka bayyana aniyarsu ta ysayawa takara.

  12. Tsohon Shugaba Kibaki na Kenya ya mutu yana da shekara 90

    Tsohon Shugaba Mwai Kibaki na Kenya ya mutu, kamar yadda Shugaba Uhuru Kenyatta na kasar ya sanar cikin wata sanarwa.

    Mista Kibaki ne shugaban kasar na uku tun bayan da kasar ta sami 'yancin kai daga Birtaniya a 1963.

    Shugaba Uhuru Kenyatta ya ayyana kwanakin zaman makoki a fadin kasar har zuwa ranar da za a binne tsohon shugaban kasar.

    Ya kuma ce za a ba tsohon shugaba Kibaki dukkan karramawar da tsohon shugaban kasa ya kamata ya samu bayan mutuwarsa.

    Akan haka ne za a sauko da tutocin kasar kasa-kasa a gida da kuma a dukkan ofisoshin jakadancinta da ke kasashen waje.

    Mista Kibaki ya rike mukamin shugaban kasar Kenya daga 2002 zuwa 2012.

  13. Wani jirgin sama na Ukraine ya yi hadari a kudancin kasar

    Rahotanni na cewa wani jirgin sama na kasar Ukraine ya fado a kudancin kasar kuma hukumomi sun ce akai wadanda suka rasa rayukansu.

    Jirgin samfurin AN-26 ne mai jigilar kayan soji da rundunar sojojin kasar Ukraine ke amfani da shi.

    Ya fado da safiyar yau Juma'a gundumar Vilnia na lardin Zaporizhzhia.

    Hukumomin sojojin kasar sun ce ana binciken hadarin.

  14. Masu zanga-zanga sun yi dafifi a ofishin Goodluck Jonathan, sun bukaci ya fito takara

    Yayin da Najeriya ke shirin gudanar da zaben shugaban kasa, wasu masu zanga-zanga sun yi dafifi a gaban ofishin tsohon shugaban kasar Goodluck Jonathan a Abuja suna neman ya sake tsayawa takarar mukamin shugaban kasar a zaben shekarar 2023.

    Mutanen wadanda suka ce 'ya'yan wata kungiya ce ta matasa, sun isa ofishin ne dauke da sakonni bisa takardu da ke kira ga tsohon shugaban ya fito ya tsaya takara.

    Wasu takardun na dauke da hotunan Mista Jonathan inda suke cewa: "Sai ka tsaya takara Goodluck Jonathan", "Muna bukatar ka ceto Najeriya".

    Kakakin kungiyar, Mayor Samuel, wanda shi ne mai kungiyar Youth Compatriots of Nigeria ya ce "Wadanda suka ce a mika musu mulki a 2015 cewa za su gyara kasarmu sun yaudare mu".

  15. An kama masu sayar da al'aurar dan Adam a Mozambique

    Hukumomi a Mozambique na tsare da wasu mutane biyu da aka kama suna kokarin sayar da sassan al'aurar dan Adam kan kudi Kwaca miliyan 35 (dala 42,000).

    Rahotanni na cewa sassan jikin na wani mutum ne da aka kashe a yankin Milange na lardin Zambezia mai makwabtaka da kasar Malawi.

    Mutanen da aka kama suna safarar sassan jikin su biyu ne, na farkonsu mai shekara 29 da haihuwa ne inda dayan kuma mai shekara 32 ne.

    Sun tuntubi wani dan kasuwa a garin kuma sun yi masa tayin "hajar" da suke dauke da ita.

    Sai dai dan kasuwan ya sanar da jami'an tsaro wadanda suka yi wa mutanen kwanton bauna.

    A halin yanzu suna hannun 'yan sanda kafin a kai su kotu.

    Kwamandar gundumar Milange Alice Evaristo ta ce 'yan sanda na ci gaba da gudanar da bincike.

  16. Babban aboki ya kashe abokinsa kuma ya tsere da motarsa da naira miliyan biyu

    Wani matashi mai shekara 25 mai suna Bashir Ibrahim ya daba wa wani abokinsa wuka a Minna babban birnin jihar Neja, kuma ya tsere da motarsa da kudi naira miliyan biyu.

    Bashir ne babban abokin mamacin yayin da yayi aure 'yan watannin da suka gabata.

    Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa Bashir ya gayyaci mamacin ne mai shekara 28 da haihuwa zuwa unguwar Tudun Fulani ta birnin Minna kimanin mako biyu da ya gabata domin su tattauna kan wata damar kasuwanci da ta bayyana a cewarsa.

    Sai dai Bashir ya daba wa amamacin wuka bayan da ya isa wurin, kuma ya tsere da motarsa kirar Peugeot 206 da kuma naira miliyan biyu da ke cikin motar.

    Rundunar 'yan sandan Najeriya da ke jihar ta Neja ta tabbatar da aukuwar lamarin ta hannun kakakinta DSP Wasiu Abiodu, wanda yace bincike ya sa sun kama Bashir da wani wanda ya taimaka masa mai suna Aliyu Ibrahim wanda ke da shekara 22 da haihuwa.

    Akwai kuma wani Suleiman Mahmud da shi ma ake tuhuma da hannu wajen aikata wannan aika-aikar, wanda tuni ya tsere, sai dai 'yan sanda na ci gaba da nemansa.

    Jaridar ta kuma ce Bashir ya tsere da motar ne zuwa Kano domin ya sayo wasu sinadarai da ake wanke zinare da su da kudin mamacin.

    Sai dai bayan ya koma Minna ne 'yan sanda suka damke shi a wani otel da ke kan babbar hanyar Wetern Bypass a Minna.

  17. Jami'an kiyaye hadurra sun fara makala kyamarori a jikinsu yayin da suke aiki

    Jami'an hukumar da ke kiyaye hadurra, wato FRSC a Najeriya sun fara makala kyamarori a jikin kayansu na aiki domin nadar bidiyon abubuwan da ke faruwa yayin da suka fita aiki.

    Wannan matakin ya biyo baya koke-koken da direbobi da masu motoci ke yi ne cewa jami'an hukumar da ma na VIO kan muzguna musu.

    Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa shugaban hukumar ya kaddamar da wannan sabon tsarin ne tun a watan Oktoban 2021, inda ya yi alkawarin matakin zai inganta yadda jami'an ke gudanar da ayukansu ba tare da sun tsangwami kowa ba.

    Wani wakilin jaridar ya ce ya lura cewa ma'aikatan hukumar da aka fi sani da Road Safety na sanye da na'urar a jikinsu a dukkan wuraren da aka saba ganinsu cikin birnin Abuja.

    Wasu mazauna birnin sun yaba da matakin, kuma sun bukaci jami'an 'yan sandan Najeriya ma su fara sanya kayamarori yayin da suke aikinsu.

  18. Sojojin Najeriya sun kwace bindigogi fiye da 500 a hannun fararen-hula

    Rundunar sojojin Najeriya ta sanar cewa ta kwace bindigogi marasa lasisi fiye da 500 daga hannun fararen-hula a jihar Filato da ke tsakiyar kasar.

    Bindigogin wadanda yawansu ya kai 517, ciki har da wasu samfuri AK-47 da kanana da kuma wadanda aka kera a gida sun shiga hannun rundunar ne yayin wani biki da aka gudanar a birnin Jos a jiya Alhamis.

    An dai kwato su ne daga hannu masu aikata laifuka, cikinsu ma akwai 'yan fashi da makami da mambobin kungiyoyi masu satar mutane suna garkuwa da su domin kudin fansa, kamar yadda wani kakakin rundunar ya shaida wa BBC.

    An kuma kwace wasu bindigogin ne a jihohin Kaduna da Bauchi masu makwabtaka da jihar ta Filato, sannan an kama wasu mutanen da aka samu dauke da makaman.

    A shekarar da ta gabata, wani kiyasi na cewa akwai akalla bindigogi miliyan shida da rabi a hannun jama'ar Najeriya - kuma kashi 90 cikin 100 na hannun wadanda ba hukumomi ne ba.

  19. Budewa

    Barkanmu da wayar gari yau Juma'atu babbar rana daga Sashen Hausa na BBC.

    Suna na Sani Aliyu, kuma ni ne zan fara gabatar muku da rahotannin abubuwan da ke faruwa a sassan duniya.

    Sai ku biyo BBC Hausa tsawon wannan yini ke nan.