Mu kwana lafiya
Masu bibiyarmu mun zo ƙarshen rahotannin a wannan shafi.
Mu haɗu gobe idan Allah ya kai mu.
Kafin haka, Umar Mikail ne ke muku fatan alheri.
Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da Afirka da sauran sassan duniya musamman Ukraine da Rasha.
Awwal Ahmad Janyau and Umar Mikail
Masu bibiyarmu mun zo ƙarshen rahotannin a wannan shafi.
Mu haɗu gobe idan Allah ya kai mu.
Kafin haka, Umar Mikail ne ke muku fatan alheri.
Rundunar Sojan Ruwa ta Najeriya ta ce ta kama mutane da dama tare da ƙwace man fetur da aka tace ba bisa ƙa'ida ba da ya kai darajar dala 700,000 a yankunan da ke da arzikin mai na ƙasar.
Wata sanarwa daga rundunar ta ce dakarunta na shirin Dakatar da Ɓarawo ne suka aiwatar da kamen.
An ƙaddamar da shirin ne ranar 1 ga watan Afrilu da zimmar daƙile abin da aka bayyana da sace-sacen mai mai girma a Najeriya.
A watan Maris, Hukumar Kula da Man Fetur na Kan Tudu ta ce ƙasar ta yi asarar mai da ya kai darajar dala biliyan 3.27 cikin wata 14 sakamakon ayyukan ɓarayi masu fasa bututan mai.
Mai magana da yawun rundunar sojan, Adedotun Ayo-Vaughan, ya ce rundunar ta duƙufa wajen kawo ƙarshen ɗabi'ar fasa bututun da kuma satar mai.
Ƙaungiyar Gwamnonin Najeriya ta NGF ta bai wa waɗanda harin jirgin ƙasa a Kaduna ya ritsa da su kyautar naira miliyan 50.
Wata sanarwa da shugaban sashen hulɗa da jama'a na ƙungiyar Abdulrazaque Bello-Barkindo ya fitar ranar Juma'a ta ce shugaban NGF, Gwamnan Ekiti Kayode Fayemi ne ya miƙa kyautar kuɗin ga gwamnatin Jihar Kaduna.
Gwamnan ya ba da kuɗin ne a ziyarar da ya kai wa Gwamnan Kaduna Nasir El-Rufai ranar Juma'a.
Fayemi ya ce sun kai ziyarar ce don su jajanta wa gwamnati da kuma mutanen da harin ya shafa, wanda ya kashe mutum aƙalla takwas da sace wasu kusan 100.
Ya siffanta harin da "mai kaɗa zuciya" saboda yawan waɗanda lamarin ya ritsa da su.
Ɗan wasan gabaan Manchester United Cristiano Ronaldo ya ci wa ƙungiyarsa ƙwallo uku rigis a wasan da ta doke Norwich na Premier League.
Ɗan wasan na ƙasar Portugal mai shekara 36 ya fara zira ƙwallo tun a minti na 7 da take wasa, kafin ya ƙara ta biyu a minti na 32.
Norwich ta farke ƙwallon biyu ta ƙafar Dowell da Pukki cikin minti uku a tsakani.
Tsohon ɗan wasan na Real Madrid da Juventus ya sake ɗaɗa ƙwallo a raga daga bugun tazara a minti na 76.
Da wannan sakamako, United ta koma matsayi na 5 da maki 54, iri ɗaya da na Arsenal amma tana da kwantan wasa ɗaya.
Shugaban Ukraine Zelensky ya bayyana cewa idan har Rasha ta kashe sojojin Ukraine da suka rage a birnin Mariupol za su janye daga teburin tattaunawar zaman lafiya.
Rasha ta ƙwace iko da birnin bayan shafe fiye da wata ɗaya ana fafatawa.
An kashe mutum ɗaya tare da jikkata wasu da dama a wani harin makamai masu linzami a birnin Kyiv a yau Asabar, a cewar Magajin Garin Kyiv Vitali Klitschko.
Klitschko ya ƙara da cewa ma'aikatan lafiya na kula da waɗanda aka raunata.
Ya kuma bayyana cewa janar-janar na Rasha sun yi barazanar ƙarin wasu hare-haren a kan babban birnin.
A cewarsa, makaman ba da kariya daga sama na yunƙurin kare rayuwar mutane, "amma maƙiyan ba su da imani".
Ma'aikatar Harkokin Addini ta Saudiyya ta jaddada wa limamai a masallatan ƙasar da ke jan sallar dare ta tahajjud da su daina tsawaita addu'o'in Al-ƙunutu don sauƙaƙa wa masallata, a cewar rahoton Saudi Gazette.
Rahoton ya ce an nemi limaman su kammala sallar da wuri kafin kiran sallar asuba don mutane su samu isasshen lokaci tsakanin sallolin biyu.
Musulmai na yin sallar tahajjud ne da tsakar dare a kwana 10 na ƙarshen watan Ramadana. A yau Asabar ake cika kwana na 15 da fara azumin na Ramadana, wanda Musulamai za su shafe kwana 29 ko 30 suna yi.
Kazalika, ma'aikatar ta umarci dukkan masallatai su yi aiki da koyarwar Annabi Muhammadu S.A.W. game da addu'ar da aka ruwaito yana yi yayin addu'ar Ƙunutu.
"Ma'aikatar ta nemi limamai su guji tsawaita addu'o'i har ma su mayar da su matsayin huɗuba. Kuma ya kamata su guji zuzuta murya da kuma yin ƙafiya, ana so su yi addu'a cikin ƙanƙan-da-kai da kuma tawalu'u," in ji rahoton.
Shugaban Rasha Vladimir Putin ya tattauna ta wayar tarho da Yarima mai jiran gado na Saudiyya Mohammed bin Salman, kamar yadda fadar Kremlin ta fada a shafinta na intanet a ranar Asabar.
Shugabannin biyu sun tattauna kan batutuwan da suka shafi haɗin gwiwa tsakanin ƙasashen biyu, da suka hada da harkokin kasuwanci da tattalin arziki, kamar yadda fadar Kremlin ta bayyana.
Ta ƙara da cewa sun tattauna yadda za su inganta hulɗa tsakanin Rasha da Saudiyya.
Sun kuma tattauna tsarin Opec da nufin daidaita farashin mai a kasuwar duniya. Sun tattauna kan halin da ake ciki a Ukrraine da kuma Yemen.
Shugaba Putin ya taya shugabannin Saudiyya murnar azumin watan Ramadan, kamar yadda sanarwar Kremlin ta bayyana.
Shugaba Emmanuel Macron ya yi saɓani da abokiyar hamayyarsa Marine Le Pen kan shirinta na hana mata yin lulluɓi a bainar jama'a, yayin da yake neman ƙuri'un Musulmi a zagaye na biyu na zaben shugaban Faransa.
A ranar 24 ga watan Afrilu za a yi zagaye na biyu na zaɓen shugaban ƙasa inda Marine Le Pen ke neman haifar da wani yanayi mafi girma a tarihin siyasar Faransa idan har ta doke Emmanuel Macron.
Har yanzu Le Pen ba ta janye manufarta ba ta haramta hijabi, inda ta ce za ta ci tarar duk matar da ta saka hijabi a bainar jama’a a Faransa idan har ta ci zaɓe.
Sai dai Macron ya ce babu wata ƙasa a duniya da ta haramta sanya hijabi, yana mai jefa tambaya ga Le Pen cewa: Kina son ki zama ta farko ne?
Ya tattauna da wasu mata musulmi da suka shaida masa cewa sanya mayafi zaɓi ne nasu ba tursasa masu aka yi ba.
Macron ya san muhimmancin ƙuri’un Musulmin Faransa miliyan biyar, waɗanda aka ƙiyasta sun kai kusan kashi tara na yawan al’ummar ƙasar.
Sakamakon wata ƙuri’ar jin ra’ayin jama’a ta Ifop pollster ta nuna cewa kashi 69 na Musulmi sun zaɓi Jean-Luc Melenchon ne wanda ya zo na uku a zagaye na farko. Yanzu kuma Macron na neman yadda zai mamayi ƙuri’un a zagaye na biyu.
Macron a baya ya fuskanci bore daga Musulmi a ƙasashen duniya kan matakan gwamnatinsa na kallon Musulmi masu tsattsauran ra’ayi.
Kamfanin Twitter ya kafa wasu tsare-tsaren da za su datse attajirin duniyar nan Elon Musk da ga mallakar shafin baki daya.
Twitter na amfani da wani tsari da ke takaita 'yancin masu hannayen jari a kamfanin, wanda hakan ya takaita adadin hannun jari da Musk zai iya mallaka zuwa kashi 15 cikin 100.
A ranar Alhamis ya gabatar da tayin dala biliyan 43 ga kamfanin na sada zumunta, yana mai cewa yana son ya mayar da shafin wata kafar 'yancin fadin albarkacin-baki a duniya.
Nan take wasu daga cikin manyan masu hannun jari a kamfanin suka yi watsi da tayin, sai dai kamfanoni na cewa Mista Musk na sake nazarin damammakinsa domin cimma burinsa.
Rasha ta haramta wa Firaministan Birtaniya Boris Johnson shiga ƙasar saboda matsayin da Birtaniya ta ɗauka a yaƙin Ukraine.
Ma'aikatar harakokin wajen Rasha ta ce matakin ya shafi Sakataren harakokin waje Liz Truss da na tsaro Ben Wallace da wasu mambobin gwamnatin Birtaniya 10 da ƴan siyasa.
An dauki matakin ne "saboda matakin nuna ƙiyayya da gwamnatin Birtaniyya ta ɗauka, musamman na sanya takunkumi kan manyan jami'an Rasha", a cewar sanarwa da ma'aikatar ta fitar, ta kuma ƙara da cewa nan ba da jimawa ba za ta ƙara yawan sunayen.
Tuni Rasha ta haramta wa shugaban Amurka Joe Biden da wasu manyan jami'an Amurka shiga ƙasarta
Ƙungiyar haɗin kan ƙasashen Musulmi, OIC ta yi Allah wadai da farmakin da sojojin Isra’ila suka kai da ya raunata Falasdinawa 150 a Masallacin Al Aqsa a birnin Kudus.
Hedikwatar ƙungiyar da ke Saudiyya ta yi Allah wadai da abin da ta kira “barazana mai hatsari” daga sojojin Isra’ila a wuri mai tsarki.
Ƙungiyar ta ce wannan tashin hankalin wani hari ne da ya shafi tunanin al'ummar musulmi baki ɗaya da kuma keta dokokin kasa da kasa.
Gwamnatin Saudiyya ma ta yi Allah wadai da farmakin na Isra'ila tana mai cewa hari kan masu ibadah a masallacin Kudus da kuma musulmi gaba ɗaya.
Rikicin na zuwa a yayin kisan Falasɗinawa ke ƙaruwa a fito na fiton da suke yi da sojojin Isra’ila a Gaɓar Yamma da Kogin Jordan, da kuma hare-haren da ƴan bindiga daga ɓangaren Falasdinawa ke kai wa a Isra’ila.
Mummunan rikici ya barke a kasar Sweden a makon nan a birnin Linköping da ke gaɓar tekun gabashin ƙasar, inda aka yi arangama tsakanin ƴan sanda da masu zanga-zanga da suka fito domin nuna fushinsu kan ƙona Al Kur'ani mai tsarki da wani dan siyasa mai tsaurin ra'ayi ya yi a wani gangaminsa.
Rahotanni sun ce ƴan sanda uku suka jikkata.
Mutane sun sake fitowa zanga-zangar, a cewar hukumomin birnin Orebro da ke tsakiyar kasar, bayan wani gangami na nuna ƙyamar baƙi da kuma addinin Islama ƙarƙashin jagorancin mai tsattsauran ra'ayi Rasmus Paludan ɗan siyasa mai asali biyu Denmark da Sweden. A yayin zanga-zangar ‘yan sanda tara suka jikkata.
An kama mutum biyu a lokacin zanga-zangar. Ƴan sanda sun nuna cewa aikinsu shi ne su tabbatar da ƴancin mutane na bayyana ra'ayinsu, don haka ba haƙƙinsu ba ne su zaɓi wanda yake da gaskiya.
Baludan ya daɗe yana haifar da ruɗani da ce-ce-ku-ce. A watan Nuwamban 2020, hukumomin Faransa sun kama shi tare da korarsa daga ƙasar.
Shugaba Zelensky a karon farko ya ce an kashe sojojin Ukraine kusan 3,000 a yaƙin ƙasar da Rasha. Ya kuma ce akwai dubbai da suka jikkata.
Shugaban ya kuma ce Rasha akwai yiwuwar Rasha na iya kai wa Ukraine hari da makamin nukiliya ko da makami mai guba.
A lokacin da yake tattaunawa da kafar CNN, Mista Zelensky ya ce Rasha na iya aikata haka, saboda a cewarsa ba ta damu da rayuwar mutane ba.
Shi ma babban jami'i a hukumar leken asirin Amurka, CIA, Willima Burns, ya fitar da irin wannan gargaɗi a ranar Alhamis, yana mai cewa Rasha na iya aikata haka saboda yadda gaggawar mamaye Ukraine.
A watan da ya gabata kakakin fadar gwamnatin Rasha, Kremlin ya ce kasar na iya kai wa ga amfani da makamin nukiliya idan aka matsa mata da barazana.
Rasha ta yi gargadi Amurka da kawayenta a hukumance kan taimakawa Ukraine da ƙarin makamai.
Sakon na diflomasiya da kafar yaɗa labaran Amurka ta gani - an aike shi ne tun ranar Talata, kafin shugaba Biden ya sanya hannu kan umarnin sake taimakawa Ukraine da makaman da kuɗinsu ya kai dala miliyan 800.
Rasha ta ce makaman da Amurka ke turawa Ukraine na sake rura wutar rikicin, kuma suna iya haifar da mumunan yanayin da kowa zai ɗanɗana koɗarsa.
Wani dan majalisar dokoki a Birtaniya Bob Seely, ya ce yana ganin yanayi zai yi muni matuƙa, sai dai kuma abin diga ayar tambaya shi ne ya ake son Ukraine ta yi?
Kayan yaƙin da Amurka ta tallafawa Ukraine a wannan karon sun hada da makaman artilare da jirage marasa matuka, da na’urorin kakkabe makamai da helikwafta.
Muna maku maraba da kasansewa da mu a wannan shafin da muke kawo labarai da rahotanni kan abubuwan da ke faruwa a sassan duniya