Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Gwamnatin Najeriya ta ce ƴan bindiga masu satar mutane na ƙawance da Boko Haram

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da Afirka da sauran sassan duniya musamman Ukraine da Rasha.

Rahoto kai-tsaye

Umar Mikail

  1. Malaman addinin Islama shida sun rasa rayukansu a mummunan hadarin mota a Kano

    Wani mummunan hadarin mota yayi sanadin mutuwar wasu malaman addinin Islama shida a jihar Kano a yau Laraba.

    Malaman sun rasu ne a kan hanyarsu ta komawa Kano daga karamar hukumar Sumaila bayan sun kammala aikin da'awah a karkashin gidaunyar Imam Malik.

    Wata ma'aikaciyar gidauniyar ta shaida ma jaridar Daily Nigerian cewa da misalin karfe 3 na yammaci suka sami labarin hadarin.

    Ta ce hadarin ya rutsa da dukkan malamai shida, wadanda jagororin aikin da'awa ne na gidauniyar.

    Sai dai hukumar kiyaye hadurra, FRSC ta ce ba a sanar da ita aukuwar hadarin ba, amma kakakin hukumar ya shaida wa jaridar ta Daily Nigerian cewa za su gudanar da bincike.

  2. 'Yan sandan Indiya sun damke wani limamin addinin Hindu mai barazanar yi ma mata Musulmi fyade

    Yan sanda a arewacin Indiya sun kama wani limamin addinin Hindu mai tsaurin ra'ayi da ake zargi da yin barazanar yi wa mata Musulmi fyade a lokacin da suke gudanar da zanga-zangar addini a jihar Uttar Pradesh.

    An tsare Bajrang Muni Das ne sama da kwanaki goma bayan ya yi wadannan kalamai masu tayar da hankali a gaban jami’an ‘yan sanda.

    Bidiyonsa yana yayin da yake barazana ga musulman ya karade shafukan sada zumunta, abin da ya janyo masa tofin Allah-tsine.

    Ya ba da hakuri kan kalaman nasa bayan ‘yan sanda sun kaddamar da bincike a makon jiya.

    Jam'iyyar Hindu-BJP ce ke mulkin jihar.

    Kamen dai ya zo ne kwanaki bayan da aka yi arangama tsakanin mabiya addinin Hindu da Musulmi a yayin gudanar da wani jerin gwano da ke da alaka da addini.

    Masu fafutuka sun ce an lalata dukiyoyin Musulmi da dama a tashin hankalin.

  3. Ba Ukraine ce kadai ke bukatar taimako ba - WHO

    Shugaban Hukumar Lafiya ta Duniya ya ce kasashen duniya ba sa ba da muhimmanci ga bukatun gaggawa da suka shafi bakaken fata a sauran nahiyoyi kamar yadda suke ba wa Ukraine.

    Shugaban hukumar ta WHO Tedros Adhanom Ghebreyesus, kaso kalilan daga cikin taimakon da ake ba wa Ukraine ne aka kai sauran wurare.

    Ya ce ko da yake taimakon Ukraine na da matukar muhimmanci, amma amma bai kamata a manta da sauran kasashen da ke fama da yaki, kamar yankin Tigray na Habasha, da Yemen, da Afganistan da kuma Syria ba.

  4. Rundunar sojojin Najeriya ta kama sojojin gona

    Rundunar sojin Najeriya ta sanar cewa ta kama wasu mutum biyar da ake tuhuma da zama sojin gona a yammacin kasar.

    Cikin wata sanarwa da rundunar ta fitar ta hannun Manjo Janar Umar Thama Musa, ta ce a kama mutanen ne yayin da suke sanye da cikakkun kayan soja na yaki a jihohin Legas da Ogun.

    Hukumomin sojan sun ce mutanen kan kafa shingaye na bogi kan manyan hanyoyin Najeriya domin su karbi kudade a hannun matafiya.

    Sai dai babu cikakken bayani kan ko an sami mutanen da makamai.

    Rundunar sojin ta Najeriya ta kuma ce daga watan Janairun bara zuwa yanzu, ta kama mutum150 da suka yi sojan gona.

  5. Gwamnatin Najeriya ta ce ƴan bindiga masu satar mutane na ƙawance da Boko Haram

    Gwamnatin Najeriya ta ce akwai ƙawance tsakanin ƴan bindiga masu satar mutane a yankin arewa maso yammaci da kuma mayaƙan Boko Haram.

    Ministan watsa labarai Lai Mohammed ne ya bayyana haka bayan taron majalisar zartarwa da shugaba Buhari ya jagoranta a fadarsa a Abuja.

    Ya ce abin da ke faruwa a yanzu akwai ƙawance tsakanin ƴan bindiga da Boko Haram, bayan an tambaye shi ya faɗi waɗanda suka kai hari a jihar Filato.

    Ya ƙara da cewa binciken farko kan harin jirgin ƙasa da aka kai a Kaduna yna nuna “akwai alaƙa tsakanin ƴan bindiga da mayaƙan Boko Haram da ke yankin arewa maso gabashi.

  6. Mutum 28 sun mutu a hatsarin jirgin ruwa a Sakkwato

    Hukumomi a jihar Sakkwato da ke Najeriya sun tabbatar da mutuwar mutane 28 a cikin wani hadarin jirgin ruwa da ya faru a yankin karamar hukumar Shagari.

    Lamarin dai ya faru ne da yammacin jiya Talata yayin da matafiyan ke kokarin tsallaka Kogi daura da garin Gidan-Maa-gana.

    Shugaban Karamar Hukumar Shagari Alhaji Aliyu Dantani Shagari ya galibin wadanda suka rasun mata ne da kananan yara

    Sai dai kawo yanzu ba a iya tantance ko mutane nawa ke cikin jirgin ba lokacin da ya kife don haka masu ninkaya ke can suna lalabe don tsamo karin gawwaki ko kuma samun wanda ya tsira daga hadarin.

    Hadarin jirgin ruwa dai ba bakon abu ba ne a wannan yankin kuma galibi akan ta’allaka faruwarsa ga daukar mutane da kaya fiye da kima da rashin amfani da riguna kariya daga nutsewa da rashin kyawon yanayi da sauransu

    Ko a watan Yunin bara ma mutane a kalla 13 ne suka rasa rayukansu a yankin na Shagari sakamakon kifewar da jirgin da suke tafiya a ciki ya yi lokacin da suke kan hanyarsu ta dawowa daga wani bukin aure.

  7. An kammala musabaƙar Ƙur'ani da Gaskiya TV ta shirya a Ghana

    An gudanar da gasar haddar Ƙur`ani a karo na biyu a Ghana, wanda tashar talabijin ta Gaskiya TV mai shirye-shirye da harshen Hausa a Ghana ta ɗauki nauyi.

    Abdulmuhaymin Ramadan Sharfadddin ne ya zo na matsayi na ɗaya a musabaƙar, sai kuma Rahmatu Alhassan da ta zo ta ɗaya a ɓangaren mata.

    Za a bai wa waɗanda suka zo na ɗayan kyautar dala 5,000.

    Wannan ne karo na biyu da aka gudanar da musabaƙar a Ghana.

    Masu shirya gasar sun ce yanzu za a gudanar da ita tsakanin ƙasashen Afirka ta Yamma.

  8. Kotun Hukunta Manyan Laifuka ta ce an aikata laifuka a Ukraine

    Shugaban Kotun Hukunta Manyan Laifuka ta Ƙasa da Ƙasa (ICC) Karim Khan, wanda yake ziyarar aiki a garin Bucha na Ukraine, ya ce "an aikata laifuka" a Ukraine.

    "Mun zo ne saboda muna da dalilin da ya sa muka yarda cewa an aikata laifukan da suka saɓa wa dokokin wannan kotun," kamar yadda ya faɗa wa manema labarai.

    "Dole ne mu kutsa cikin lamuran yaƙin don gano gaskiya. Hakan yana buƙatar bincike mai zaman kansa kuma maras ɓangaranci," a cewarsa.

    Ya ƙara da cewa wata tawagar kotun ICC za ta fara aiki a garin.

    Ana zargin dakarun Rasha da aikata kashe-kashen farar hula a Bucha da ke kusa da birnin Kyiv lokacin da ta ƙwace shi daga hannun sojan Ukraine, kafin daga bisani ta janye daga garin.

  9. Hauhawar farashin kayayyaki ta ƙaru a Ghana

    Hauhawar farashin kayayyakin masarufi a Ghana ta yi ƙaruwar da ba ta taba yi ba cikin kusan shekara 10, inda farashin kayan abinci ya karu da kusan kashi 5 cikin 100.

    Gwamnati ta ce hauhawar farashin kayayyaki ya tashi daga fiye da kashi 15 cikin 100 a watan Fabrairu zuwa kashi 19.4, abin da ya zarce hasashen da babban bankin kasar ya yi na tsakanin kashi 6 zuwa 10.

    Bankin ya ƙara kuɗin ruwa a watan da ya gabata a kokarinsa na dakile hauhawar farashin kayayyaki, abin da masu sharhi ke cewa na barazanar jefa ɗaya daga cikin manyan kasashen na yammacin Afirka cikin mawuyacin hali.

    Mahukunta sun sanar da wani shiri na tsuke bakin aljihu da kuma ƙara darajar kuɗin ƙasar.

  10. 'Yan bindiga sun sace ɗaliban kwaleji mata a Jihar Zamfara

    'Yan bindiga sun sace ɗaliban Kwalejin Kimiyyar Kiwon Lafiya mata huɗu ranar Talata da dare a Jihar Zamfara da ke arewacin Najeriya.

    Wani mazaunin yankin ya faɗa wa BBC cewa maharan sun afka wa gidan da ɗaliban ke zaune wanda ke wajen makarantar a garin Tsafe bayan sun tarar da jami'an tsaro na gadin kwalejin.

    Shugagan kwalejin, Yusuf Idris Maradun, ya ce ɗalibai biyar 'yan bindigar suka kama amma daga baya suka saki ɗaya daga cikinsu saboda ta kasa tafiya sakamakon lalurar ƙafa.

    Rundunar ‘yan sanda a jihar ta ce jami’an tsaro sun duƙufa domin ganin an ceto ɗaliban da aka sace a gidan da suka kama haya suna kwana a cikin garin na Tsafe.

    Latsa hoton ƙasa ku saurari hira da shugaban kwalejin:

  11. Labarai da dumi-dumi, Kotu ta ɗaure ɗan ƙungiyar ISIS rai-da-rai saboda kisan ɗan majalisar Birtaniya

    Kotu ta yanke wa wani mai alaƙa da ƙungiyar ISIS hukuncin ɗaurin rai-da-rai saboda kama shi da laifin kashe wani ɗan majalisa a Birtaniya.

    A watan Oktoba ne Ali Harbi Ali ya caccaka wa Sir David Amess wuƙa fiye da sau 20 yayin da yake ganawa da 'yan mazaɓarsa ta Southend West.

  12. Rasha ta yi iƙirarin cewa sojojin Ukraine 1,026 sun miƙa wuya

    Rasha ta yi iƙirarin cewa sojojin Ukraine 1,026 sun ajiye makamansu tare da miƙa wuya a birnin Mariupol da Rashar ta yi wa zobe.

    An yi ta yi wa garin mai tashar jirgoin ruwa ruwan wuta tsawon makonni kuma ana kyautata zaton ya kusa faɗawa hannun Rasha.

    Rukunin dakarun na 36 Birged, an ce sun miƙa wuya ne a kusa da wata masana'antar ƙarafa da ke Ilyich Iron.

    Mai magana da yawun ma'aikatar tsaron Ukraine ya ce ba shi da masaniya game da rahoton ya zuwa yanzu.

    A farkon makon nan ne mataimakin magajin garin Mariupol ya ƙaryata wani rahoton da ya fito daga birged ɗin cewa suna fama da ƙarancin harsasai da kuma taimako.

  13. Rasha na ci gaba da yi mana luguden wuta, in ji sojojin Ukraine

    Sojojin Ukraine sun ce Rasha na ci gaba da yi musu luguden wuta a birnin Mariupol da ke kudu maso gabashin Ukraine, inda ake ci gaba da gumurzu da sojojin Ukraine sama da mako shida.

    Sojojin sun ce ana kai musu hare-hare ta sama musamman a tashar da ke gabar ruwa da inda ake ayyukan karafa.

    Magajin garin Mariupol ya kiyasta cewa an kashe sama da farar hula 21,000 tun baya soma mamayar Rasha a Ukraine.

  14. Buhari ya amince da kafa sabuwar kwalejin fasaha a Kano

    A Najeriya, Shugaba Muhammadu Buhari ya sanya hannu kan dokar kafa sabuwar kwalejin fasaha ta Tarayya a garin Kabo da ke Jihar Kano.

    Cikin wata sanarwa da Ma'aikatar Ilimi ta Najeriya ta fitar ranar Talata, za a kafa wasu kwalejojin a JIhar Delta da Abiya da ke kudancin ƙasar.

    Kano na da jami'o'i da manyan makarantu na gwamnatin Tarayya da gwamnatin jiha, abin da ya sa wasu ke cewa ba a bukatar karin wasu.

    Yanzu haka malaman jami'a a ƙasar na yajin aiki sakamakon rashin mutunta yarjejeniyar da gwamnatin Najeriya ta ƙulla da malaman gamed da kuɗaɗen tafiyar da jami'o'in da kuma albashinsu.

    Sai dai Sanata Barau Jibrin, wanda ya gabatar da ƙudirin kafa kwalejin fasahar ya shaida wa BBC cewa akwai bukatar kwalejin.

    Ya ƙara da cewa nan da watan Oktoba mai zuwa za a fara karatu a cikinta.

    Latsa hoton ƙasa ku saurari hira da Sanata Barau Jibrin:

  15. Ya kamata Buhari ya sauka daga mulki saboda ba zai iya magance matsalar tsaro ba - Ƙungiyar Dattawan Arewa

    Ƙungiyar Dattawan Arewa ta Northern Elders Forum (NEF) ta nemi Shugban Ƙasa Muhammadu Buhari ya sauka daga mulki nan take sakamakon kashe-kashen da ake fama da su a faɗin ƙasar, musamman a arewaci.

    Da yake magana cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Talata, kakakin ƙungiyar Hakeem Baba-Ahmed ya ce Buhari "ba zai iya kawo ƙarshen matsalar tsaro da ta addabe mu ba".

    "Da alama gwamnatin Buhari ba ta da abin cewa game da ƙalubalen tsaro da muke ciki. Ba zai yiwu mu ci gaba da zama ƙarƙashin ikon masu kisa ba, da masu garkuwa da mutane, da masu fyaɗe, da miyagun da suka hana mu 'yancinmu na zama lafiya," a cewar ƙungiyar.

    Kiran nasu na zuwa ne 'yan kwanaki bayan 'yan bindiga sun kashe kusan mutum 200 a Jihar Filato da ke tsakiyar Najeriya, da kuma sace wasu ɗaliban kwaleji mata da aka yi a Jihar Zamfara ranar Talata da dare.

    Kazalika, har yanzu 'yan bindigar da suka kai hari kan jirgin ƙasa na Kaduna-Abuja na riƙe da gwamman matafiyan da suka yi garkuwa da su, inda suke neman gwamnatin Buhari ta biya musu "buƙatunsu".

    "Kundin tsarin mulkinmu ya tanadi yadda shugabanninmu za su sauka daga mulki idan suka gaza ko kuma saboda wani dalili na ƙashin-kai," in ji NEF. "Loƙaci ya yi da ya kamata Buhari ya fara tunanin wannan zaɓin."

  16. Biden na zargin Shugaban Rasha Putin da aikata kisan ƙare-dangi a Ukraine

    Shugaba Biden na Amurka ya zargi shugaban Rasha, Vladimir Putin, da aikata "kisan ƙare-dangi a Ukraine.

    Mista Biden ya bayyana hakan ne a karon farko a lokacin da yake jawabi kan farashin man fetur a Iowa.

    "Na bayyana shi da kisan ƙare-dangi saboda a bayyana take ƙarara cewa Putin na kokarin kawar da duk wani ɗan Ukraine daga doron-kasa," in ji shi.

    Biden ya ce hujjojjin da ke tabbatar da hakan su ne karuwar aika-aika da Rasha ke yi, wanda ba su da maraba da kisan kare-dangi.

    Rasha ta musanta wadannan zarge-zarge.

  17. Amurka za ta ƙara yawan makaman da take bai wa Ukraine

    Jami'an Amurka sun ce gwamnatin Shugaba Joe Biden na kokarin ƙara yawan makaman da take bai wa Ukraine.

    Amurka ta bai wa Ukraine taimakon makamai da agajin da ya kai na dala biliyan ɗaya da miliyan bakwai tun bayan soma yakinta da Rasha.

    Daga cikiin makaman da Amurka ta bai wa IUkraine akwai nakiyoyin da ke lalata tankokin yaki da masu kakabe makamai masu Linzami, wadanda ke taimakawa wajen kare birnin Kyiv.

    Shugaba Zelensky na Ukraine ya sake kara rokon karin manyan makamai da jiragen yaki da makaman atilare domin fuskantar Rasha da ke kokarin mamaye gabashin kasar baki daya.

    Ma'aikatar tsaron Amurka, Pentagon, za ta tattauna da manyan kamfanonin kera makamai a yau Laraba domin nazari kan karin taimakon da za a bai wa Ukraine ɗin.

  18. Assalamu Alaikum

    Barkanmu da hantsin Laraba, barka da shigowa shafin labarai kai-tsaye tare da Umar Mikail.

    Za mu kawo rahotannin abubuwan da ke farua a sassan duniya, musmaman a Najeriya da kuma halin da ake ciki a yaƙin Ukraine.