Sai da safenku
Mun zo ƙarshen rahotanni a wannan shafi. Sai kuma gobe idan Allah ya kai mu za mu kawo sabbin rahotannin.
Kafin nan, Umar Mikail ke muku fatan a yi sahur lafiya.
Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da Afirka da sauran sassan duniya musamman Ukraine da Rasha.
Awwal Ahmad Janyau and Umar Mikail
Mun zo ƙarshen rahotanni a wannan shafi. Sai kuma gobe idan Allah ya kai mu za mu kawo sabbin rahotannin.
Kafin nan, Umar Mikail ke muku fatan a yi sahur lafiya.
Yayin da Faransa ke shirin gudanar da zaben shugaban kasa a gobe Lahadi, kuri'un jin ra'ayin jama'a na nuna Shugaba Emmanuel Macron da ke kan gaba na fusknatar koma-baya kan abokiyar karawarsa Marin Le Pen.
An dakatar da gangamin zabe na kuri'un zagayen farko, wanda alamu ke nuna manyan 'yan takarar biyu za su kara a zagaye na biyu a karshen wannan watan.
Wakiliyar BBC ta ce a bayaninsa na nasarar da ya samu shekara biyar baya, Emmanuel Macron ya ce zai yi iya kokarinsa ya ga bai bar wata kofa ba da mutane za su kafa hujja da ita wajen zaben Marin Le Pen.
Macron wanda ya mayar da hanakali kan rikicin Ukraine a yanzu, ya zargi Marin Le Pen da yi wa mutane karya da kuma nuna wariyar launin fata.
Ita kuwa ta rike matsalar tsadar rayuwa da kasar ke ciki a matsayin babban abin da take kamfe da shi.
Har yanzu an kasa gudanar da kuri'ar yanke ƙauna kan Firaministan Pakistan Imran Khan, duk da cewa kotun kolin kasar ta yanke hukuncin dole a kaɗa kuri'ar a yau Asabar.
Wakilin BBC a Islamabad ya ce Mista Khan ya ki yarda a yi ƙuri'ar ne domin ya san ba zai kai labari ba.
Masu adawa da shi sun shirya tsaf domin hamɓarar da shi da kuma tsayar da nasu dan takarar.
Imran Khan ya dage kan cewa akwai haɗin bakin Amurka a yunkurin tsige shi, sai dai Amurkan ta musanta hakan.
Ukraine da Rasha sun yi musayar fursunoni tsakaninsu a karo na huɗu tun bayan fara yaƙi tsakaninsu.
Mataimakiyar Firmanista Iryna Vereshchuk ce ta bayyana hakan cikin wani saƙo da ta wallafa a intanet.
A cewarta, hakan na nufin sojojin Ukraine 12 da aka kama za su koma gida.
Ta ƙara da cewa fararen hula 14 na cikin yarjejeniyar, waɗanda su ma za su koma gida.
Sai dai ba a ba da wani ƙarin bayani ba game da adadin 'yan Rashan da aka saka.
BBC ta tattauna da shugaban Nijar Mohamed Bazoum kan cikarsa shekara ɗaya kan mulki.
Birtaniya za ta aika wa Ukraine motoci masu silke 120 da kuma sabbin makaman tarwatsa jirgin ruwa, a cewar Fadar Downing Street bayan ganawar Firaminista Boris Johnson da Shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky a birnin Kyiv.
"Sakamakon jajirtaccen shugabancin Zelensky da kuma gwarzatanktarsa da mutanen Ukraine waɗanda Putin ke nufa da sharri," a cewar Boris Johnson bayan ganawar.
Tun farko wani kakakin fadar Downing Street ya ce firaministan ya je Kyiv ne don shata "sabon ƙunshin tallafin kuɗi da na kayan yaƙi".
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya saka hannu kan dokar da ta ƙara wa'adin ritayar aiki ga malaman makaranta mai suna Harmonised Retirement Age for Teachers in Nigeria Act, 2022.
Mai magana da yawun Fadar Shugaban Ƙasa Garba Shehu ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa a ranar Juma'a.
An ƙirƙiri ƙudirin dokar don a samar da tsari a hukumance da zai mayar da shekarun ritaya zuwa 65 maimakon 60 ga malaman makaranta sannan ya tsawaita shekarun aiki daga 35 zuwa 40, a cewar Ministan Ilimi Adamu Adamu.
A ranar 20 ga watan Janairu na 2020 ne Majalisar Zartarwa ta amince da ƙudirin dokar da zai tsawaita wa'adin ritaya da kuma na aiki ga malaman.
Everton ta yi nasara a kan Manchester United da ci 1-0 a wasan mako na 32 a gasar Premier League da suka kara ranar Asabar.
Anthony Gordon ne ya ci wa Everton kwallon a minti na 27 da fara karawar da suka yi a Goodison Park.
A wasan farko da suka buga a bana ranar 2 ga watan Oktoban 2021 a Old Trafford, kungiyoyin sun tashi 1-1.
Kawo yanzu, United ta yi nasara a wasa uku cikin 12 da ta buga a dukkan fafatawa, inda ta yi canjaras shida da rashin nasara uku.
Wannan ne karo na biyu da Everton ta yi nasara a kan United a fafatawa 16 a dukkan karawa, inda ta yi rashin nasara a takwas da canjaras biyar.
Da wannan sakamakon, United tana mataki na 7 da maki 51, iri ɗaya da wanda West Ham take da shi a matsayi na shida a teburin na Premier League.
Sojojin Najeriya sun ce sun kashe ɗaya cikin manyan kwamandojin Iswap da wasu mayaƙa a wani farmaki a arewa maso gabashi.
Sojojin sun ce sun kashe kwamandan mai suna Abubakar Danbuduma da mayaƙa 19.
Rundunar sojin ta ce dakarunta sun kai harin ne a yankin Tafkin Chadi ta hanyar amfani da jiragen yaƙi.
Abu ne mai wahala a iya tantance gaskiyar labarin. Amma wannan na zuwa a yayin da mayaƙan Iswap ke karɓe ikon wasu ƙauyuka tana tilasta wa mutane biyan haraji
Firaministan Birtaniya Boris Johnson ya gana da shugaba Zelensky na Ukraine a Kyiv a ranar Asabars.
Ofishin jekadancin Ukraine a London ya wallafa hoton shugabannin biyu suna tattaunawa.
Gwamnatin Najeriya ta ce an samu matsala ne a babban layin samar da lantarki na ƙasa.
Wata sanarwar daga ofishin ministan lantarki na Najeriya Injiniya Abubakar Aliyu ta ce ana gudanar da bincike domin gaggauta magance matslar.
An fuskanci katsewar lantarki a sassan Najeriya a ranar Juma'a.
Sanarwar ta ce: "muna sanar da al'umma cewa matsalar ta faru ne karfe 18:30 a ranar 8 ga Afrilu, wanda ya haifar da matsalar lantarki a sassa da dama na ƙasa."
Ministan ayyuka da gidaje tsohon gwamnan Legas Babatunde Raji Fashola ya gabatar da takardun gidaje ga tsoffin ƴan wasan ƙwallon kafa na Super Eagles da gwamnatin tarayya ta yi masu alƙawali.
Hotunan da ma’aikatar ayyuka da gidaje ta wallafa a Twitter sun nuna lokacin da ƴan wasan ke karbar takardun gidajen hannun Fashola a ranar Juma’a.
An ba tawagar Super Eagles da suka buga wa ƙasar wasa a 1994 gidajen ne gidajen, bayan shekara 28 da gwamnatin marigayi Janar Sani Abacha ta yi masu alƙawali lokacin da ƴan wasan suka lashe kofin Afirka a Tunisia.
Ministan sufuri Rotimi Amaechi ya sanar da aniyarsa ta takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2023.
Amaechi ya ayyana takararsa ne a wani taron siyasa a Fatakwal a ranar Asabar.
“Na tsaya a gabanku yau don bayyana aniyata tare da gabatar da bukatar zama shugabanku na gaba," in ji shi.
Yanzu Amaechi da tsohon gwamnan Legas Bola Tinubu da gwamnan Kogi Yahaya Bello ne suka fito suka ayyana takararsu ta shugaban ƙasa.
Jami’an Rasha sun zargi kafar YouTube da toshe shafin majalisar wakilan ƙasar.
Rasha ta ce Amurka ta keta haƙƙin da ƴan Rasha suke da shi, kamar yadda Vyacheslav Volodin, shugaban majalisar ta Duma ya bayyana.
“Amurka na son mallake dukkanin bayanai, in ji Volodin a Telegram yana mai cewa “ba za mu amince ba.”
Ƙungiyar kare haƙƙinɗan adam ta Human Rights Watch ta buƙaci hukumomi a Kamaru da su kare fursunoni daga cutar kwalara da ta ɓarke bayan mutuwar akalla fursunoni shida a wani gidan yari.
Ta ce wanda ya mutu a baya bayan nan- fursunan siyasa - ya mutu ranar Alhamis a gidan yarin New Bell na Douala.
Ƙungiyar ta ce adadin wadanda abin ya shafa na iya karuwa sosai saboda cunkoson fursunonin da inda ake tsare da su.
Mata masu juna biyu za su iya fuskantar zuban jini a yayin da cikinsu yake karami da kuma lokacin da ya fara tsufa.
Ga shirin Lafiya Zinariya
Firaministan Pakistan Imran Khan ya bayyana cewa idan har aka hambarar da shi daga kan mulki, ko shakka babu ba zai amince da wata gwamnati da za a shigo musu da ita daga waje ba.
Firaministan na magana ne gabanin kada kuri'ar yankan kaunar da za a yi a majalisar dokokin kasar nan da wasu sa'oiwadda ake kuma sa ran zai sha kasa.
A cikin wani sako da ya gabatar a daren Jumma'a, Mr Khan ya ce ya amince da hukuncin kotun kolin kasar akan cewa dole a kada kuri'ar, amma ya haƙiƙance cewa ba wani abu ake masa ba, face makarkashiya ta duniya wadda Amurka ta tsara.
Amurka ta musanta zargin
Ƙasashen yammaci sun ce an nada wani babban Janar mai kwarewa sosai a yakin Syria don ya jagoranci mamayen da Rasha ke yi a Ukraine.
An ba Janar Alexander Dvornikov damar inganta irin yadda sojojin Rasha ke kai hare hare a Ukraine.
Ƙasashen yammaci sun ce ba su da masaniya akan ko Rasha ta koyi wasu darussa a game da dabarun yaƙi da kuma yadda za su kare kansu don kaucewa kwantan ɓauna daga sojojin Ukraine.
Rasha ta ƙagu ta ga ta samu nasara kafin nan da 9 ga watan Mayu a lokacin da za ta yi bikin tunawa da nasarar da ta yi a lokacin yakin duniya na biyu
Gwamnan Luhansk – a gabashin Ukraine ya ce Rasha ta ƙara yawan luguden wuta tare da kira ga mazauna yankin su fice.
Jami’an tsaro na musamman da ke kula da aikin Hajji da Umrah a Saudiyya sun ƙaddamar da bincike kan faɗa da ya ɓarke tsakanin wasu mutane biyu a wurin da ake Safa da Marwa da ke cikin Masallacin Harami na Makkah a ranar Alhamis.
Ba a samu rahoton wani rauni ba sakamakon faɗan da suka yi amma an ɗauki matakai game da mutanen biyu, kamar yadda jaridar Saudi Gazette ta ruwaito.
Jami’an tsaron da ke aikin kula da Hajji da Umrah sun yi kira ga masu ibadah da su mutunta alfarmar Ka’aba da kuma kiyayewa tare da kasancewa cikin natsuwa yayin gudanar da aikin ibadar Umrah da sauran ibadu a Masallatai biyu masu alfarma a Saudiyya.
Saudiyya ta ƙara adadin maniyyatan bana zuwa miliyan ɗaya daga ciki da wajen kasar, kamar yadda kamfanin dillancin labaran kasar SPA ya ruwaito.
Ma'aikatar kula ayyukan Hajji da Umrah ta kasar Saudiyya ce ta sanar da matakin ƙara yawan masu aikin Hajjin hajjin zuwa miliyan daya daga ciki da wajen Saudiyya.
Adadin ya ƙaru idan aka kwatanta da shekaru biyu da suka gabata, saboda annobar korona wanda ya tilasta wa Saudiyya rage yawan waɗanda za su aikin Hajji.
Sanarwar da hukumomin Saudiyya suka fitar sun ce an hana wa waɗanda suka haura shekara 65 zuwa aikin Hajjin bana.
Ƴan ƙasa da shekara 65 da za a bari su yi aikin Hajjin sai sun yi allurar rigakafin korona da ma’aikatar lafiya ta Saudiyya ta amince da ita.