Mayaƙan I-S sun kashe sojojin Burkina Faso 12 yayin wani hari
Rundunar sojin Burkina Faso ta ce wasu mahara da ake alakantawa da kungiyoyin jihadin sun halaka akalla sojojinta 12 tare da wasu 'yan sa-kai hudu a wani hari da aka kai kan wani sansanin sojoji.
Rundunar ta kuma ce an raunata wasu sojojin 21 yayin harin wanda aka kai kan sansanin Namissiguima a arewacin kasar.
A watan jiya ma akalla sojoji 10 aka kashe a yankin gabashin Burkina Faso.
Mayakan kungiyoyin da ke ikirarin jihadi sun fara kai hare-hare a Burkina Faso ne a 2015 daga sansanoninsu da ke kasar Mali mai makwabtaka.