Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

An saki Alwan Hassan shugaban Bankin Noma da aka sace a harin jirgin ƙasa

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da Afirka da sauran sassan duniya musamman Ukraine da Rasha.

Rahoto kai-tsaye

Umar Mikail

  1. Nan za mu rufe wannan shafin sai kuma gobe

  2. Ana wahalar man girki a Nijar

    Matsalar karancin gas din girki na ci gaba da yin kamari a wasu yankuna na jumhuriyar Nijar.

    A birnin Katsinar Maradi, mazauna birnin sun shafe sama da mako biyu babu wadataccan gaz na girki a wuraren sayar da shi.

    Wannan dai ya sa wasu mata suka koma girki da itace, wasu kuma da gawayi.

    Ga rahoton da Abdou Halilou ya aiko mana daga Abuja.

  3. Buhari ya naɗa sabon ministan muhalli

    Shugaba Muhammadu Buhari ya amince da Mohammed Hassan Abdullahi a matsayin sabon ministan muhalli.

    Sakataren gwamnatin tarayya Boss Mustapha ne ya sanar da naɗin nasa a cikin wata sanarwa a ranar Laraba.

    Sanarwar ta ce: “Shugaban Muhammadu Buhari ya amince da naɗa Mohammed H. Abdullahi a matsayin sabon Ministan Muhalli daga ranar 6 ga Afrilu, 2022.”

    Mohammed Hassan Abdullahi wanda lauya ne kuma ɗan asalin jihar Nasarawa, shi ne ƙaramin minista ma’aikatar kimiya da fasaha kafin nada shi babban minista.

  4. Matar Sankara ta yi na'am da hukuncin da aka yanke wa Blaise Compaoré

    Matar tsohon shugaban Burkina Faso Thomas Sankara ta yi na'am da hukuncin ɗaurin rai da rai da aka yanke wa tsohon shugaban ƙasar Blaise Compaoré ba a gaban idon sa ba kan kisan mijinta a 1987.

    "Ina ganin mutanen Burkina Faso da al'umma sun san wane ne Thomas Sankara, wanda shi ne mutum, kuma ɗan siyasa, da abin da yake so da abin da mutanen da suka kashe shi suke so. Daga wannan na samu sauƙi domin mun san ko wane ne shi," in ji Miriam Sankara.

    Wani dan uwansa Mousbila Sankara ya ce yana fatan hukuncin zai kawo ƙarshe.

    "Muna fatan wannan zai zama darasi, ga kowa, da kuma iyalan waɗanda abin ya shafa zuwa ga al'umma gaba ɗaya. Saboda wannan ba al'amari ba ne da ya shafi mutanen ƙasa kawai ba, amma har magoya baya daga wajen ƙasa," in ji shi.

    Sankara mai shekara 37, an harbe shi ne tare da wasu mutum 12 a juyin mulkin 1987, wanda ya ba Compaoré damar ɗarewa kan mulki.

    Compaoré wanda ya gudu, bai ba kotun da ta yanke masa hukunci ba haɗin kai.

  5. An saki Alwan Hassan shugaban Bankin Noma da ƴan bindiga suka sace a harin jirgin ƙasa

    Ƴan bindiga da suka kai harin bom a jirgin ƙasa a hanyar Abuja zuwa Kaduna sun saki shugaban bankin noma Alwan Ali Hassan ɗaya daga cikin fasinjojin da suka yi awon gaba da su a cikin jirgin.

    An sake shi ne a ranar Laraba, kamar yadda wata majiya daga iyalinsa ta tabbatar wa BBC.

    A ranar Litinin 28 ga watan Maris ƴan bindiga suka kai harin bom a jirgin ƙasa da ke kanyar zuwa Kaduna daga Abuja.

    Hukumar kula da sufurin jiragen ƙasa ta ce jirgin na ɗauke da fasinja 362, kuma har yanzu ba a san makomar sama da 160 bayan tabbatar da mutum 182 da suka tsira.

  6. Ƴan Nijar na ce-ce-ku-ce kan yawan mashawartan kakakin majalisa fiye da 1,000

    Al’ummar Jamhuriyar Nijar na ce-ce-ku-ce game da yawan mashawartan kakakin majalisar dokoki kasar inda yanzu haka suka hauradubu daya.

    Daga cikin mashawartan, jam’iyar shugaban majalisar dokokin, Seyni Oumarou, MNSD Nasara ta kwashi mutum 600 ita kadai sai jam’iyar PNDS mai mulki da ta ke da mutum 250.

    Majalisar na biyan ko wane mashawarci CFA jika 302.000 duk wata, kamar yadda zaku ji a cikin wannan rahoton da Tchima Illa Issoufou ta aiko daga Yamai.

  7. Labarai da dumi-dumi, Amurka ta sanya wa ƴaƴan Putin mata takunkumai

    Fadar White House ta Amurka ta sanar da sabbin takunkuman da ta sanya a kan wasu manyan masu faɗa a jin Rasha da iyalansu, da suka haɗa da manyan ƴaƴan Putin mata da wasu dangin Ministan Harkokin Wajen ƙasar Sergei Lavrov.

  8. Labarai da dumi-dumi, APC za ta fitar da ɗan takarar shugaban ƙasa a watan Mayu

    Jam'iyyar APC ma mulkin Najeriya ta ce za ta gudanar da zaɓukan fitar da 'yan takara a muƙamai daban-daban a watan Mayun 2022.

    Jam'iyyar za ta fitar da ɗan takarar shugaban ƙasa ranar 30 ga watan Mayu.

    Za a fara zaɓuakan ne da na 'yan majalisar jiha a ranar 17 ga Mayu, yayin da da na 'yan majalisar wakilai zai biyo baya ranar 19, sai kuma na 'yan majalisar dattawa ya gudana a ranar 21.

    Zaɓen fitar da 'yan takara a muƙamin gwamna zai gudana ne ranar 24 ga watan na Mayu.

  9. An cire dokar hana taruwar jama'a da fitar dare a Najeriya

    Gwamnatin Najeriya ta cire dokar hana fita ta tsakar dare da kuma taruwar jama'a a tarukan bikin aure da na waƙe-waƙe waɗanda aka saka da zimmar yaƙi da annobar korona.

    Kwamatin yaƙi da cutar na shugaban ƙasa ya ce an ɗauki matakin ne sakamakon raguwar mutanen da ke kamwua da cutar a ƙasar.

    Najeriya ta saka dokokin ne tun bayan ɓullar annobar cikin ƙasar a watan Fabarairun 2020.

    Wata sanarwa daga kwamatin ta ce an kuma samu raguwar haɗarin yaɗa sabon nau'in cutar.

    Sai dai kuma, ya jaddada cewa wajibi ne mutane su ci gaba da saka takunkumi idan suna cikin wani rufaffen wuri amma bai zama lallai su saka ba idan suna buɗaɗɗen wuri ko kuma fili.

    An janye ƙayyadewar adadin mutanen da za su halarci wani taron addini amma kwamatin ya ce lallai ne a saka takunkumi a wurin.

  10. Rasha ta zafafa hare-hare a gabashin Ukraine

    Dakarun Rasha na ci gaba da ruwan wuta a biranen da ke gabashi da kudancin Ukraine, yayin da sojojin na amfani har da makamai masu linzami wajen kai hare-haren.

    A birni na biyu mafi girma a Ukraine wato Kharkiv, an shafe tsawon dare ana ɓarin wuta.

    Sannan an kai hari da makaman atilare a wasu yankunan Luhansk da Donetsk—inda ake hasashe lamura za su sake muni nan da makwanni - yayin da Rasha ke ƙara girke sojoji a waɗannan yankuna.

    Kazalika, an zafafa hare-hare a Mariupol, wanda suka yi wa ƙawanya da luguden wuta fiye da wata ɗaya.

    An ƙiyasta kusan mutum 130,000 ne suka maƙale a yankunan.

    "Ana yi mana ruwan wuta ta ko’ina, a waje muke girki, ruwan sha ya yi wuya, muna matukar bukatar agaji," a cewar wata mazauniyar Mariupol.

    A wani yankin kuma, Rasha ta lalata wani wurin adana man fetur da ke kusa da birnin Dnipro, sannan sun far wa yankin Vinnytsia da ke tsakiyar Ukraine da kuma Redekhiv da ke yammaci.

  11. Labarai da dumi-dumi, Majalisa ta ƙara wa'adin kasafin kuɗin Najeriya

    Majalisar Wakilan Najeriya ta amince da ƙudirin ƙara wa'adin kasafin kuɗin ƙasar da wata biyu.

    A zamanta na yau, majalisar ta yi wa Dokar Kasafin Kuɗi ta 2021 kwaskwarima, inda aka sauya wa'adin ƙarewar dokar daga 31 ga watan Maris 2022 zuwa 31 ga Mayun 2022.

    Majalisar ta ce ta ɗauki matakin ne bayan kwamatinta ya je zagayen ganin ayyuka kuma shi ne ya ba da shawarar ƙara wa'adin don samun gudanar da ayyukan a cikin dokar ta 2021.

  12. NDLEA ta ce ta kama 'sarauniyar ƙwaya' a Jihar Taraba

    Hukumar yaƙi da miyagun ƙwayoyi a Najeriya NDLEA ta ce ta kama wata mace da ta kira "Sarauniyar Ƙwaya" a Jihar Taraba da ke tsakiyar ƙasar sakamakon zarginta da ta'ammali da tabar wiwi.

    Sanarwar da NDLEA ta fitar a yau Laraba ta ce jami'anta sun kama Lami Mai Rigima a Ƙaramar Hukumar Ardo Kola ranar Litinin da ta gabata.

    Hukumar ta ce ta fara neman Lami tun daga Oktoban 2021, lokacin da aka kama da gurfanarwa da ɗaure wani mai suna Abdullahi Madaki mai shekara 50.

    An kama sarauniyar da tabar wiwi da ta kai nauyin 150 giram, a cewar NDLEA.

    Kazalika, hukumar ta kama wani mai suna Emeka Okiru mai shekara 40 da zargin mallakar ƙwayar tramadol 32,700 a Adamawan.

  13. Labarai da dumi-dumi, Kotu ta yanke wa tsohon shugaban Burkina Faso Compaore hukuncin ɗaurin rai-da-rai

    Wata kotun soja a Burkina Faso ta yanke wa tsohon Shugaban Ƙasa Blaise Compaore hukuncin ɗaurin rai-da-rai sakamakon kama shi da hannu a kisan wanda ya gada Thomas Sankara.

    An yi wa Compaore shari'a a bayan idonsa yayin da yake gudun hijira yanzu haka.

    An yanke wa tsohon shugaban sashen tsaro na gwamnatinsa, Hyacinthe Kafando, hukuncin ɗaurin rai-da-rai shi ma.

    Mista Sankara wanda ɗan neman sauyi ne mai aƙidar Markisanci, wasu 'yan bindiga ne suka harbe shi a babban birnin ƙasar Ouagadougou a 1987.

    Daga nan ne kuma Compaore ya mulki ƙasar tsawon shekara 27 har zuwa lokacin da aka tumɓuke shi a 2014.

  14. Labarai da dumi-dumi, Buhari ya kafa dokar kula da ofisoshin gwamnati a Najeriya

    Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya sanya wa wani Umarnin Shugaban Ƙasa 11 hannu da zai tabbatar da kula da ofisohsin gwamnati a faɗin ƙasar.

    Buhari ya saka hannu kan dokar da ake yi wa laƙabi da Executive Order 11 jim kaɗan kafin fara zaman Majalisar Zartarwa a yau Laraba a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja.

    Jim kaɗan kafin saka hannun, Buhari ya nemi dukkan ma'aikatun gwamnati, da sashe-sashe, da hukumomi da su kafa sashen kula da tafiyarwa ƙarƙashin sabuwar dokar.

    Bayan kammala sa hannun ne Buhari ya jagoranci zaman majalisar, wanda ministoci da sauran ƙusoshin gwamnati ke halarta.

  15. An kashe 'yan jarida takwas a Mexico cikin 2022

    Wani sabon rahoto da ƙungiyar kare haƙƙin dan Adam ta fitar ya nuna an kai ƙololuwa a munanan hare-haren da ake kai wa 'yan jarida a Mexico, lamarin da ke nuna mummunan matakin da gwamnati ke ɗauka kan 'yan jaridar.

    Rahoton kungiyar da ƙungiyar Article Nineteen ta fitar ya ce a wa'adin farko na gwamnatin Shugaba Andres Manuel Lopez Obrador, an samu karuwar kai wa 'yan jarida hari da kashi 85 cikin 100 idan aka kwatanta da zamanin mulkin wanda ya gada.

    Wakiliyar BBC ta ce ya nuna wata ukun farko na shekarar nan su ne mafiya muni ga 'yan jaridar Mexico, inda aka kashe 'yan jarida takwas.

    An kai wa 'yan jarida hari sau 2,000, ciki har da kisan akalla 33 cikin shekara uku.

    Mista Lopez Obrador da gwamnatinsa sun sha cin zarafin 'yan jarida a lokacin taron manema labarai.

  16. Ɗan majalisar Najeriya na son a fara ɗaure 'yan daudu ko tarar N500,000

    Wani ƙudiri da aka gabatar a gaban Majalisar Wakilan Najeriya da ke son a yi wa Dokar Haramta Auren Jinsi a kwakwarima ya nemi a haramta daudu a ƙasar.

    Da yake karanto sashe na 4 na dokar ranar Talata, ɗan majalisa mai wakiltar Toro daga Jihar Bauchi, Umar Muda Lawal, ya nemi a haramta daudu a fili ko kuma a ɓoye.

    Ya nemi a saka ɗaurin wata shida a cikin dokar ko kuma tarar naira 500,000 ga duk wanda aka kama a matsayin ɗan daudu.

    Ɗan majalisar na so a ƙara wani ƙaramin sashe na 4 cikin baka a cikin Dokar Haramta Auren Jinsi ta 2013 da zai ayyana cewa: "Duk wanda aka kama yana aikata daudu ya yi laifin da zai iya fuskantar hukuncin zaman gidan yari na wata shida ko kuma tarar N500,000."

    A jiya Talata ne 'yan majalisar suka yi wa ƙudirin karatun farko. Sai sun yi karatu na biyu da na uku sannan ya zama doka.

  17. An gano ma'aikatan tarayya na boge 1,500 a Najeriya, an dakatar da albashin 3,000

    Gwamnatin Najeriya ta ce ta gano ma'aikata 1,500 da suka gabatar da takardun shaidar ɗaukar aiki na boge ga kwamatin da ta kafa na tantance ma'aikata.

    Shugabar Ma'aikatan Gwmanatin Tarayya, Folashade Yemi-Esan, ita ce ta bayyana hakan yayin wani taron tattaunawa da hukumar yaƙi da rashawa ta ICPC ta shirya a Abuja ranar Talata.

    Ta ce gwamnatin tarayya ta dakatar da biyan albashin ma'aikata 3,000 da suka gaza bayyana a gaban kwamatin don tantancewa.

    An ƙaddamar da shirin ne don bankaɗowa da kuma korar ma'aikatan da suka shiga aikin ba ta hanyar doka ba, a cewarta.

    "Wani lokaci a watan Maris na 2021, wannan ofis ɗin ya faɗa wa ICPC cewa akwai wasiƙun ɗaukar aiki masu yawa da ke zagaye a ma'aikatu," in ji ta kamar yadda Channels TV ta ruwaito ta tana faɗa.

    "A lokacin, mun gano cewa a ma'aikata ɗaya kacal, akwai masu ɗauke da wasiƙun boge 1,000, kuma tuni aka saka su cikin masu karɓar albashi."

  18. Ukraine: Dubban mazauna yankin Donbas na tsere wa harin Rasha

    Dubban mazauna yankin Donbas a gabashin Ukraine na tserewa zuwa yammacin ƙasar.

    Wakililin BBC Jonathan Beale ya ce sun tarar da wani zungureren cunkoson ababen hawa yayin da tawagarsu ke nausawa cikin yankin - inda ake fafata yaƙin.

    A nan ne kuma Rasha ke ƙara ɗaura ɗamarar yaƙi bayan ta janye dakarunta daga arewaci.

    Sojojin Ukraine na ba da tsaro a wuraren duba ababen hawa kan dukkan titunan da ke shiga da fita daga yankin.

    Kazalika, suna kuma sake tsara hanyoyin kariya tare da wasu ƙwararrun sojan Ukraine a yankin.

    Da ma dai sojan Ukraine sun shafe shekara takwas da suka wuce suna yaƙar 'yan tawaye masu samun goyon bayan Rasha a yankin na Donbas.

    Yanzu kuma dakarun Rasha ne ke riƙe da mafi yawan Luhansk da kuma fiye da rabin Donetsk, yayin da suke ƙoƙarin yi wa sojojin Ukraine zobe.

  19. Turai da Amurka na shirin ƙara ƙaƙaba wa Rasha takunkumai

    Nan gaba a yau Amurka da Tarayyar Turai za su kara saka wa Rasha sabbin takunkumai a matsayin martani kan zargin aikata laifukan yaki da Ukraine ke yi wa sojin Rasha kan kisan fararen hula a garin Bucha.

    Sakatariyar yaɗa labaran fadar White House, Jen Psaki, ce ta sanar da hakan a wajen taron manema labarai.

    "Ku sa ran za a sanya takunkumin kan jami'an gwamnatin Rasha da iyalansu, da kamfanoni, da haramta zuba jari da ɗora alhakin duk abin da ya faru a kan jami'an Rasha," in ji ta.

    Mujallar Wall Street Journal ta rawaito cewa Amurka na duba yiwuwar sanya wa babban bankin Rasha Sberbank takunkumi.

  20. Assalamu Alaikum

    Kun shigo shafin labarai kai-tsaye na BBC Hausa a wannan hantsi na Laraba tare da Umar Mikail.

    Ku biyo don sanin halin da duniya ke ciki, musamman a Ukraine da kuma abubuwan da ke faruwa a Najeriya.