Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Trump ya ce Amurka na buƙatar komawa Afghanistan

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da Afirka da sauran sassan duniya musamman Ukraine da Rasha.

Rahoto kai-tsaye

Umar Mikail

  1. Nan za mu rufe wannan shafin sai kuma gobe

  2. Zelensky ya zargi sojojin Rasha da aikata kisan kiyashi

    Shugaba Zelensky na Ukraine ya zargi sojojin Rasha da suka janye daga kasar da aikata kisan kare dangi a Bucha da wasu garuruwa da ke wajen birnin Kyiv.

    Ya yi wannan bayani, bayan da babbar mai shigar da kara ta Ukraine ta ce ya zuwa yanzu sun gano gawarwaki 410 a yankin, ta ce ofishinta na bincike a kan yiwuwar aikata laifukan yaki.

    Cikin wata tattaunawa da ya yi da gidan talabijin na CBS, Zelensky ya ce abin da Rasha ta yi, shi ake kira kisan kare dangi.

    Zelensky ya ce wannan, wanikokari ne na share kasa baki daya.

  3. Trump ya ce Amurka na buƙatar komawa Afghanistan

    Donald Trump ya ce yana ganin Amurka na bukatar komawa kasar Afganistan domin kwato Amurkawa da biliyoyin daloli na kayan soji.

    "Yan Taliban sun tsare Amurkawa da dama. Bai kamata gwamnati ta samu wani abu ba na miƙawa Taliban dala biliyan 85. Watakila ya kamata mu koma Afganistan," in ji tsohon shugaban a wani gangamin yakin neman zabe a Michigan.

    Ya ce "wauta ne" cewa "kayan aikin soji mafi fa’ida a duniya, da suka ƙunshi manyan bindigogi 700,000" su kasance a hannun Taliban.

    Mista Trump ya sha caccakar Biden na ficewa Afghanistan, yana mai kiran matakin wanda “bai dace ba.”

    Biden ya ce gwamnatin Trump ce ta fara ɗaukar matakin wanda aka samu tsaiku na tsawon wata uku.

    Tsohon shugaban ya ce gwamnatin Biden ta “ƙunyata” Amurka na ficewa Afghanistan tare da ganin lafinsa kan abin da ke faruwa a Ukraine.

    Trump ya ce ya yi imanin inda shi ne shugaban ƙasa, Rasha ba za ta abka wa Ukraine ba.

  4. An yi wa ɗaruruwan fursunoni afuwa albarkacin Ramadan

    Shugaban Algeria Abdelmadjid Tebboune, ya yi wa fursunoni fiye da dubu ɗaya afuwa a daidai albarkacin azumin watan Ramadan a ake ciki.

    A cikin wata sanarwa da ofishinsa ya fitar ya ce za a yi wa karin masu zanga-zanga 70 magoya bayan ƴan Hirak masu rajin kare demokradiyya - wadanda ke jiran shari'a kan laifukan da suka shafi haifar da tarzoma - za a yi musu sassauci.

    Daga cikin waɗanda aka saki har da wani mai fafutukar kare hakkin ɗan Adam, Zaki Hannache, wanda aka kama shi a watan Fabrairu bisa zargin goyon bayan ayyukan ta’addanci da yada labaran ƙarya.

  5. Sheikh Nuru Khalid: Ba zan janye kalamaina ba sai idan ya ci karo da tsaron ƙasa

    Sheikh Nuru Khalid a Najeriya ya ce ba zai janye kalamansa ba da ya yi a huɗubar Juma'a da ta gabata, wadda ta sa aka dakatar da shi daga limanci a Masallacin Apo da ke Abuja saboda sukar gwamnatin Shugaba Buhari.

    Limamin da ake yi wa laƙabi da Digital Imam, ya soki gwamnatin Buhari cewa "shugban ƙasa ya gaza" wajen kare rayukan 'yan Najeriya biyo bayan hare-haren 'yan bindiga kan jirgin ƙasa na Abuja zuwa Kaduna ranar Litinin da ta wuce.

    Cikin wani sauti da ya wallafa a shafinsa na Facebook na hira da manema labarai, Sheik Nuru ya ce ba zai janye kalaman da ya yi ba har sai idan akwai na tashin hankali a cikinsu.

    "A gaskiya ba zan janye ba saboda ba kalma ɗaya na yi ba, sai dai idan akwai wani abu da ke tayar da hankalin al'umma ko ƙasa, ko yake barazana ga tsaron ƙasa; idan an nuna min cikin nutsuwa da bayanan hankali zan iya janyewa," in ji malamin.

    Ya ƙara da cewa zuwa yanzu "ba a faɗa min cewa kalma kaza ta saɓa wa tsaron ƙasa ba".

    Game da karatun tafriin Ƙur'ani kuma da ya saba yi a Masallacin na Apo, Nuru Khalid ya ce zai ci gaba da karatuttukan, amma a fahimtarsa dakatarwar da aka yi masa har da karatun.

    Kazalika, wata sanarwa da ya fitar a shafin nasa ta ce za a gudanar da karaun tafsirin a ɗakin karatunsa.

  6. IS ta ce ta kashe mayaƙan Abzinawa 30 a Mali

    Ƙungiyar IS mai da’awar jihadi reshen yankin Sahel ta ce ta kashe sama da mutum 30 mayaƙan Abzinawa da ke hamayya da ita a arewa maso gabashin Mali.

    Kungiyar I-S ta ce ta kai farmaki kan wasu wuraren da kungiyar mai fafutukar ƙasar Azawad ke rike da su a yankin Manaka.

    Masu sharhi sun ce a baya-bayan nan kungiyar I-S ta kara ƙaimi a yakin da take yi a kasar Mali, inda take kai hari kan mayakan Abzinawa da sojojin gwamnati.

    Majiyoyin yankin sun ce daruruwan fararen hula na daga cikin wadanda suka jikkata.

  7. An kama ƴan Najeriya 12 masu damfara ta intanet a ƙasar Gambia

    Rahotanni daga Gambia sun ce hukumomin ƙasar sun kama wasu mutum 13 da ke damfarar mutane ta intanet.

    Mutum 12 daga cikinsu ƴan Najeriya ne, ɗaya kuma mutumin Saliyo, kamar yadda kafar yaɗa labarai a Fatu Radio ta ruwaito.

    Hukumar hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ne ta kama mutanen a Old Yundum da ke yankin yammacin Gambia, kamar yadda rahotanni suka bayyana.

  8. An rushe majalisar Pakistan bayan Imran Khan ya sha da kyar

    Shugaban Pakistan ya rushe majalisar ƙasar a wani yunƙuri na gudanar da zaɓe da wuri, bayan yunƙurin tsige Firaminista Imran Khan.

    An ɗauki matakin ne bayan kakakin majalisar ya yi watsi da buƙatar jefa ƙuri'ar yanke ƙauna kan Imran Khan, wadda aka kyautata zaton ba zai tsallake ba.

    Mista Khan ya yi iƙirarin cewa Amurka ce ke jagorantar manaƙisar cire shi saboda sukar manufofinta na ƙasashen waje da yake yi da matakan da yake ɗauka.

    Amurka ta musanta zargin sannan 'yan adawa sun hofintar da batun.

    Imran Khan ya kai ziyara Rasha don ganawa da Shugaba Putin yayin da Rashar ke tsaka da kai hare-hare a Ukraine. Ya kuma sha sukar Amurka kan shirinta na "yaƙi da ta'addanci".

  9. 'Yan bindiga sun harbe mutum shida a Amurka

    Mutum aƙalla shida ne aka kashe tare da raunata wasu 10 sakamakon harbe-harbe a Sacramento da ke Amurka, a cewar 'yan sandan California.

    Mutane sun fara neman gidan ɓuya daga kan titi bayan sun ji ƙarar harbi daga yankin da ke cike da gidajen cin abinci da na shan giya a yau Lahadi.

    'Yan sandan suna shawartar mazauna yankin da su ba ta duk wasu bayanai da suka sani da zai taimaka wajen gano maharan.

    Shugaban 'yan sandan Sacramento Katherine Lester ta faɗa wa manema labarai cewa 'yan sanda da ke kusa da yankin da lamarin ya faru sun ji ƙarar harbe-harbe da misalin ƙarfe 2:00 agogon ƙasar - 10:00 agogon Najeriya da Nijar.

    "Wannan bala'i ne mai girma," a cewarta.

  10. NDLEA ta kama hodar ibilis a zanin gado, ta kama mutum bakwai a Kano

    Hukumar yaƙi da shan miyagun ƙwayoyi a Najeriya NDLEA ta ce ta kama ƙunshin hodar ibilis ko kuma koken a filin jirgin sama na Fatakwal da ke Jihar Rivers a kudancin Najeriya.

    NDLEA ta wallafa wani bidiyo a yau Lahadi da ta ce yana nuna yadda masu safara suka ɓoye ƙunshi 73 na koken ɗin a cikin zanin gado.

    Kazalika, hukumar ta ce ta ƙwace ƙwayar tramadol miliyan tara da rabi a Legas da ta kai darajar naira biyan biyar.

    Hakan nan, hukumar ta ce ta kama mutum bakwai a Kano saboda zargin su da mu'amala da miyagun ƙwayoyin.

  11. Girke-girken Ramadan: Yadda ake yin Faten Dankalin Hausa

    A ci gaba da kawo muku girke-girken Ramadan, a yau mun wallafa bidiyon yadda ake yin faten dankalin Hausa.

    Maryam Sa'idu ce ta shirya, ta gabatar kuma ta aiko wa BBC.

  12. Sauƙaƙan dokokin korona kan matafiya a Najeriya za su fara aiki daga Litinin

    Gwamnatin Najeriya ta ce sabbin dokokin yaƙi da annobar korona da ta sauƙaƙa wa matafiya za su fara aiki ne daga gobe Litinin, a cewar shugaban kwamatin yaƙi da korona na shugaban ƙasa Boss Mustapha.

    Sabbin dokokin da kwamatin ya fitar sun ƙunshi cewa duk wanda ke son shiga Najeriya ba sai ya yi gwajin cutar na shigowa ba da kuma bayan sauka matuƙar dai an yi masa rigakafin cutar.

    Su ma yara 'yan ƙasa da shekara 18 za su samu wannan alfarmar ko da ba a yi musu rigakafin cutar ba.

    Sai dai kuma, masu son shiga ƙasar da ba a yi wa rigakafin ba, ko kuma ba su samu cikakkiya ba, har yanzu dole ne sai sun yi gwaji kwana biyu kafin su shiga sannan kuma su yi na bayan sauka, da kuɗinsu.

    A gefe guda kuma, dukkan fasinjojin da ke son zuwa Najeriya sai sun yi rajista a shafin matafiya na gwamnati a adireshin NITP– https://nitp.ncdc.gov.ng.

    'Yan Najeriyar da ke son zuwa ƙasashen waje kuwa, an shawarce su da su yi rigakafin sannan kuma su san dokokin ƙasashen da za su je na yaƙi da korona kafin su tafi.

  13. Harin Rasha ya ragargaza matatar man fetur a Ukraine, in ji gwamnan yankin

    Harin da Rasha ta kai kan unguwar Kremenchuk da ke tsakiyar Ukraine ya lalata wata matatar man fetur baki ɗaya, a cewar gwamnan yankin Poltava.

    Kamfanin labarai na Reuters ya ruwaito Gwamna Lunin Dmytro Lunin na cewa an kashe wutar da ta tashi a matatar "amma an lalata matatar baki ɗayanta ta yadda ba za ta yi aiki ba".

    Jaridar Kyiv Independent ta wallafa cewa harin makami mai linzami a ranar Juma'a ya lalata matatar man mafi grima a Ukraine.

    Yankin Kremenchuk na da muhimmanci sosai ta ɓangaren kasuwanci a tsakiyar ƙasar.

  14. Girke-girken Azumi: Yadda ake yin faten dankalin Hausa

    A ci gaba da kawo muku girke-girken azumi, a yau mun wallafa bidiyon yadda ake yin faten dankalin Hausa.

    Maryam Sa'idu ce ta shirya, ta gabatar kuma ta aiko wa BBC.

  15. 'Yan Najeriya na Allah-wadai da dakatar da Sheikh Nuru Khalid daga limanci kan sukar Buhari

    Tun bayan da BBC Hausa da sauran kafofin yaɗa labarai a Najeriya suka ruwaito matakin dakatar da Sheikh Nuru Khalid daga limanci, kafofin sada zumunta na ƙasar suka cika da muhawara zazzafa da kuma Allah-wadai.

    An dakatar da limamin daga Masallacin Apo da ke Abuja babban birnin ƙasar ne sakamakon huɗubarsa ta ranar Juma'a, inda a ciki ya soki Shugaba Buhari game da ƙin zuwa yi wa mutanen Kaduna jajen harin jirgin ƙasa da ya kashe mutum aƙalla takwas da kuma sace wasu da dama.

    "Lokacin da yake neman ƙuri'a bai je Kaduna ba? To me ya sa ba zai je yi musu jaje ba?," a cewar limamin.. "'Yan siyasa sun gaza...musamman shugaban ƙasa...a ƙarƙashin mulkinka 'yan fashi na saka wa 'yan Najeriya haraji."

    Kwamatin masallacin ya ce sun dakatar da shi ne "saboda yana tunzura mutane" da kar su yi zaɓe bayan ya nemi 'yan Najeriya da kar su fito zaɓe mai zuwa idan ba a kawo ƙarshen kashe-kashen da 'yan bindiga ke aikatawa ba.

    Ya zuwa lokacin haɗa wannan rahoton, sunan Sheikh Nuru Khalid ne ya fi komai tashe a dandalin Twitter na Najeriya, inda aka ambace shi sau fiye da 11,000. A Facebook ma, mutum kusan 10,000 ne ke tattaunawa a kan limamin.

    Akasarin saƙonnin na ɗauke ne da bidiyon huɗubar da malamin ya yi cikin harsunan Hausa da Ingilishi.

    • Kwamitin Masallacin Apo ya dakatar da Sheikh Nuru Khalid daga limanci

    "Ko a gaban Allah Sheikh Nuru Khalid ya yi nasa aikin. Sai dai kawai su dakatar da shi a nan duniya amma ba za su iya ƙwace ilimin da Allah ya ba shi ba," in ji wani mai suna Shehu Zubair a Twitter.

  16. Zuwa yanzu babu wanda ya mutu a harin da Rasha ta kai a Odesa

    Ƙarin bayanin da aka samu game da hare-haren da Rasha ta kai kan birnin Odesa a Ukraine na cewa zuwa yanzu babu wanda ya rasa ransa.

    Cikin wani saƙo da ya wallafa a tasharsa ta dandalin Telegram, wani jami'in sojan Ukraine Vladislav Nazarov ya ce ya zuwa yanzu ba a iya gano ko akwai wanda harin ya ritsa da shi ba.

    Nazarov ya ƙara da cewa an lalata kayan aiki masu amfani amma bai ba da wani ƙarin bayani ba game da inda aka kai harin.

  17. Ukraine na shirin fafatawa da Rasha a gabashin ƙasar

    Gwamnatin Ukraine ta ce tana kara karfin sojinta a gabashin kasar saboda tsammanin da take yi na karin hare-hare daga Rasha.

    A cikin jawabinsa ta bidiyo, Shugaba Volodymyr Zelensky ya ce Rasha na son kwace ikon da baki dayan yankin Donbas, da ma kudancin Ukraine.

    "Mene ne manufar sojojin Rasha ne? Suna son ƙwace Donbas da kuma kudancin kasarmu. Burinmu ne mu kare 'yancinmu da kasarmu har ma da mutanenmu," a cewarsa.

    Mista Zelensky na jawabin ne bayan da ma'aikatar tsaron kasarsa ta ce baki dayan yankin Kyiv babban birnin ƙasar na karkashin ikonta.

    A yayin da dakarun Rasha ke janyewa daga garuruwan da ke kusa da babban birnin, an gano gawarwakin mutane yashe a kan tituna.

    Manema labarai da suka ziyarci Bucha sun ce yawancin gawarwakin na fararen hula ne kuma an gansu da hannu a daure sannan kuma ga harbi a kansu.

  18. Assalamu Alaikum

    Barka da shigowa shafinmu na rahotanni kai-tsaye.

    Umar Mikail ne zai kawo muku abubuwan da ke faruwa a sassan duniya tun daga wannan hantsi na Lahadi har darensa.