Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
"Ya kamata a kama Putin"
Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da Afirka da sauran sassan duniya musamman Ukraine da Rasha.
Rahoto kai-tsaye
Umar Mikail
Yahaya Bello ya ayyana takarar shugaban kasa a zaɓen 2023
Gwamnan Kogi Yahaya Bello ya ayyana aniyarsa ta tsayawa takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2023, ƙarƙashin tutar jam’iyyar APC.
Gwamnan ya sanar da matakin ne a wani taron siyasa a Abuja a ranar Asabar.
Da yake jawabi ya yi alƙawalin cewa zai mayar da ƴan Najeriya miliyan biyu masu arziki da za su mallaki miliyoyi nan da 2030.
Ya ce ya fahimci cewa ci gaban Najeriya ya dogara ne da fitar da ƴan ƙasar daga talaucin da ya yi katutu.
Sirrin mallakar mijinki da na mallakar matarka
Idan ke mace ce na san babban burinki bai wuce ki mallaki mijinki a tafin hannunki ba, haka kai ma namijin ba ka da burin da ya wuce a ce kai ne sitiyarin juya matarka yadda kake so.
Shirin zamantakewa na wannan makon zai ba ku sirrin mallakar miji da na mata ba boka ba mallam kuma ba tare da amfani da karfi ko cin zali ba.
Yaƙin Yemen: Iran da Saudiyya sun yi na'am da tsagaita wuta
Saudiyya da Iran sun yi na'am da tsagaita buɗa wuta a Yemen da ta soma aiki a yau kuma ake fatan ta ci gaba tsawon wata biyu wacce majalisar Dinkin Duniya ta jagoranta.
Yarjejeniyar ta soma aiki daga yau Asabar, yarjejeniyar tsagaita wuta ta ƙasa baki ɗaya ta farko a yƙin Yemen na shekara bakwai tun 2016
The truce took effect on Saturday, the first nationwide ceasefire in Yemen's seven-year war since 2016.
Ministan harakokin wajen Saudiyya wacce ke goyon bayan gwamnatin Yemen, ya jaddada cewa yarjejeniyar na daga cikin manufar tabbatar da zaman lafiya da Saudiyya ta gabatar a bara.
Iran wacce ke goyon bayan mayaƙan Houthi, ta bayyana fatan cewa wannan zai kai ga haifar da tsagaita wuta ta dindin domin samar da mafitar siyasa a rikicin Yemen.
Ukraine ta yi ikirarin sake kwato wasu garuruwa a kusa da Kyiv
Dakarun Ukraine sun sake kwato garuruwa fiye da 30 daga hannun dakarun Rasha a lardin Kyiv, kamar yadda mai bai wa shugaban kasa shawara Oleksiy Arestovych ya bayyana ranar Asabar.
Sai dai a yayin da dakarun Ukraine suke sake kwato wadannan garuruwa, a gefe guda dole sai an yi ba-ta-kashi a wasu yankunan, a cewar jami’in gwamnatin a hirar da ya yi da wani gidan talbijin na kasar.
"Ba za mu yaudari kanmu ba - akwai gwagwarmaya a nan gaba a kudanci domin kwato Mariupol, da kuma gabashin Ukraine," a cewar Arestovych.
Mako daya ke nan tun da jami’an rundunar sojin Rasha suka sanar da shirinsu na mayar da hankali wajen “ceto” yankin Donbas da ke gabashinUkraine.
Amurka ta yaba da yarjejeniyar tsagaita wuta a Yemen
Shugaba Biden ya yaba da yarjejeniyar zaman lafiya da Majalisar Dinkin Duniya ta jagoranta kan rikicin Yemen da cewa abu ne da al'ummar Yemen suka dade suna jira.
Amma ya ce hakan bai wadatar ba sannan kuma dole a kawo karshen yaki.
Yarjejeniyar ta wata biyu tsakanin sojin hadakar da Saudiya ke jagoranta da kuma 'yan tawayen Houthi da ke samun goyon bayan Iran zata fara aiki daga yau asabar.
Sakatare janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres, ya bukaci dukkan bangarorin biyu da su tabbata an aiwatar da yarjejeniyar.
Ya ce ina mai yabawa gwamnatin Yemen da hadakar sojin da Saudiya ke jagoranta da kuma 'yan Houthi dangane da amincewa da cimma yarjejeniya watanni biyu ta tsagaita wuta ciki kuwa har da daina kai hare hare kan iyakoki.
Wakili na musamman a Majalisar Dinkin Duniya, Hans Grundberg, ya ce za a iya sabunta yarjejeniyar idan dukkan bangarorin sun amince da hakan.
Yarjejeniyar zata bayar da damar kai kayan agajin da ake matukar bukata ga fararen hula.
Tsohuwar babbar mai shigar da ƙara a kotun duniya ta yi kiran a kama Putin
Tsohuwar babbar mai shigar ta kotun hukunta laifukan yaƙi ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta yi kiran a kama shugaba Vladimir Putin kan mamayar Ukraine.
Yar ƙasar Switzerland Carla Del Ponte ta ce kamata ya yi a bayar da sammacin kama Putin da wasu manyan jami’an Rasha.
“Putin mai laifin yaƙi ne,” kamar yadda ta shaidawa jaridar Le Temps ta Switzerland.
Del Ponte ta taba aiki a matsayin babban mai shigar da ƙara ta Majalisar Ɗinkin Duniya a shari’ar rikicin Yugoslavia da kuma Rwanda.
An ƙaddamar da bincike kan laifukan yaƙi a Ukraine a watan da ya gabata bayan zargin Rasha da kai harin bom kan fararen hula.
Babban mai shigar da ƙara a kotun hukunta laifukan yaƙi ta ICC Karim Khan ya ce akwai hujjoji da aka tattara kan zargin aikata laifukan yaƙi da kisan kiyashi.
Za a tura ƙarin jami'an tsaro kan hanyar Abuja-Kaduna
Rundunar 'Yan Sandan Najeriya ta ce za ta tura ƙarin dakaru don kyautata tsaro a kan babbar hanyar Abuja zuwa Kaduna.
Matakin ya biyo bayan hare-haren da 'yan bindiga suka kai kan jirgin ƙasa, inda suka kashe mutum aƙalla takwas da raunata wasu 41 sannan suka sace wasu da dama a yammacin Litinin da ta gabata.
Wani saƙo ɗauke da hotuna da mai magana da yawun rundunar, Olumuyiwa Adejobi, ya wallafa a shafinsa na Twitter ya nuna dakarun jere a kan layi.
"Dakaru sun shirya tsaf don tura su aiki na musamman a kan hanyar Abuja-Kaduna. Ana yi musu jawabi a hedikwatar 'yan sanda ta ƙasa kafin su fita a yau (Asabar)," in ji Mista Adejobi.
Babban Sufeton 'Yan Sandan Najeriya Usman Alkali Baba ya kai ziyara wurin aikin da ake yi na gyara layin dogon da 'yan bindigar suka ragargaza da bam a harin na ranar Litinin.
Gwamnan Kaduna Nasir El-Rufai ya ce 'yan Boko Haram ne da haɗin gwiwar 'yan fashin daji suka kai harin.
Shekaru a wajena baiwa ce: Hira da Abdullahi Adamu sabon shugaban APC
Shirin Gane Mani Hanya na wannan makon ya yi tattaunawa ta musamman da Sanata Abdullahi Adamu, wanda aka zaɓa a matsayin sabon shugaban jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya.
Twitter na shirin samar da maɓallin gyara saƙo
A ƙarshe dai, dandalin sada zumunta na Twitter ya fara shirin ɓullo da maɓallin gyara saƙonni bayan wallafa su da masu amfani da shi suka daɗe suna nema.
Wannan ne karon farko da kamfanin na Twitter Inc. zai samar da damar gyara saƙo bayan wallafa shi tun bayan kafa dandalin shekara 15 da suka gabata.
"Muna aiki kan maɓallin gyara saƙo," a cewar Twitter cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na dandalin.
Mutum kusan miliyan 217 ne ke amfani da Twitter a kowace rana a faɗin duniya, amma duk wanda ya wallafa saƙo to ba zai iya yi masa kwaskwarima ba - sai dai ya goge shi ko kuma ya wallafa sabo.
Sauran manyan dandalin zumunta kamar Facebook da Instagram na da maɓallin gyara saƙo.
Ra'ayi Riga: Muhawara kan harin 'yan fashi a jirgin ƙasa na Kaduna-Abuja
Shirin Ra'ayi Riga na wannan makon ya tafka muhawara ne kan harin 'yan fashi da suka kai kan jirgin ƙasa na Kaduna zuwa Abuja.
Latsa hoton ƙasa ku saurari shirin:
Waɗanda harin roka ya kashe a Ukraine sun kai 33
Hukumomi a Ukraine sun ce ya zuwa yanzu mutum 33 ne aka tabbatar sun mutu a harin roka da aka kai kan wani ginin gwamnati a garin Mykolaiv da ke tekun Black Sea.
Harin ya kuma raunata wasu 34.
Har yanzu ma'aikatan agaji na ci gaba da duba ɓaraguzan ginin tare da kwashe gawarwaki daga wurin, a cewar hukumar agaji ta Ukraine kwana huɗu da kai harin.
Harin da Rasha ta kai ya haƙa wani rami a tsakiyar ginin na gwamnatin yankin Mykolaiv da safiyar Talatar da ta gabata.
Gwamnan Mykolaiv da ke da ofis a wurin, Vitaliy Kim ya ce ba ya wurin lokacin da makamin ya faɗa kan ginin saboda ya makara zuwa wajen aiki.
‘Ramin hakori na jawo ciwon zuciya’
Kwayoyin cutar da ke maƙalewa a cikin ramin hakori na iya janyo ciwon zuciya, idan ba a dauki matakan da suka dace ba, a cewar likitoci.
Hakan a cewarsu, yana daya daga cikin matsalolin da rashin tsaftace baki ke janyo wa.
Kwayoyin cutar dai suna bi ta cikin jini ne, su je har cikin zuciya, su yi wa mutum lahani.
Rashin tsaftar baki kuma na janyo karfin hakori ya yi ta raguwa, har ta kai ana cire su.
Wata matsalar kuma da rashin tsaftace baki ke janyowa ita ce ta warin baki, wanda shi ma ramin hakori na taimakawa wajen kawo shi.
Latsa hoton ƙasa ku saurari shirin Lafiya Zinariya:
Jirgin ƙasa ya yi hatsari a Kaduna bayan 'yan bindiga sun sake lalata titinsa
Wani jrigin dakon kaya daga Jihar Legas a kudancin Najeriya da ke kan hanyarsa ta zuwa Kano a arewaci ya sake yin hatsari a Jihar Kaduna.
Shugaban ma'aikatan hukumar sufurin jiragen ƙasa ta Najeriya (NRC) ya faɗa wa BBC Hausa cewa 'yan bindiga ne suka lalata wani ɓangare na layin dogon, abin da ya sa jirgin ya kauce daga titinsa.
Hatsarin ya jawo mutuwar direban jirgin wanda rahotanni suka bayyana sunansa da Bala Kawu.
Lamarin ya faru ne a ranar Alhamis a Ƙaramar Hukumar Igabi, kusa da sansanin sojoji na Jaji. Wasu hotuna da aka yaɗa a shafukan zumunta sun nuna yadda jirgin ya kife a gefen titinsa.
Kazalika, hatsarin ya afku kwana uku bayan harin da 'yan bindigar suka kai kan jirgin ƙasa na Kaduna zuwa Abuja, wanda ya yi sanadiyyar kisan mutum takwas da jikkata kusan 40.
Red Cross za ta sake gwada aikin agaji a Mariupol yau Asabar
Kungiyar agaji ta Red Cross ta ce za ta sake gwadawa a yau Asabar domin ganin ta taimaka wa mutanen da suka makale a birnin Mariupol.
Duk yunkurin da ta yi a baya na aikewa da kayan agaji da kuma kwashe mutanen ya ci tura.
Mazauna birnin na cikin mawuyacin yanayi tun bayan da Rasha ta fara luguden wuta makonni da suka gabata.
Gwamnan yankin ya zargi Rasha da karya alƙawarin da ta yi na barin kafar da mutane za su fice a birnin.
Kazalika, wani ayarin motoci ɗauke da wasu daga cikin mazauna Mariupol ya isa birnin Zaporyzhzhia a jiya Jumma'a.
Za mu ɗauki sojojin haya don kare al'ummarmu idan gwamnatin tarayya ta gaza - El-Rufai
Gwamnan Jihar Kaduna a arewacin Najeriya Nasir El-Rufai ya yi barazanar cewa shi da sauran gwamnonin yankin za su ɗauki sojojin haya don kare rayukan mutanensu idan gwamnatin tarayya ƙarƙashin Shugaba Buhari ta kasa kawo ƙarshen hare-haren 'yan fashi a yankin.
Da yake magana da manema labarai jim kaɗan bayan ya gana da Buharin a ranar Juma'a, El-Rufai ya ce ba 'yan fashin daji ne suka kai hari kan jirgin ƙasa na Kaduna zuwa Abuja ba - "yan Boko Haram ne".
"Na faɗa wa shugaban ƙasa cewa wallahi idan ba a ɗauki mataki ba wannan abin ba zai tafi ba...dole sai dai mu gwamnoni mu ɗauki mataki don kare rayukan al'ummarmu," in ji shi.
"Ko da hakan na nufin ɗaukar sojojin haya don su zo su yi aikin, za mu yi hakan don kawo ƙarshen lamarin."
Sai dai gwamnan ya ce shugaban ƙasa ya faɗa masa cewa gwamnati za ta ɗauki matakin daƙile hare-haren a watanni masu zuwa.
Wasu rahotanni sun sha zargin cewa gwamnatin Najeriya ƙarƙashin tsohon Shugaba Goodluck Jonathan ta ɗauki sojojin haya don yaƙar Boko Haram a arewa maso gabas, amma babu tabbas game da rahoton saboda gwamnatin ba ta taɓa bayyana haka ba.
Harin da 'yan bindigar suka kai kan jirgin ƙasa a yammacin Litinin da ta gabata ya yi sanadiyyar mutuwar mutum aƙalla takwas tare da raunata kusan 40. Har yanzu ba a tantance yawan waɗanda suka yi garkuwa da su ba.
Rundunar sojan Mali ta ce ta kashe 'yan bindiga 203
Rundunar Sojin Mali ta ce ta kashe masu tayar da kayar baya 203 a wani samame da sojojinta suka kai a ƙasar da yankin Sahel.
A cewar rundunar, sojojin nata sun kuma kama mutum 51 sannan sun kwace makamai da dama a yankin Moura.
Tun a shekarar 2012 Mali ke fuskantar hare-haren masu iƙirarin jihadi, inda aka kashe dubban sojoji da kuma fararen hula.
'Yan gudun hijirar Ukraine na komawa ƙasarsu
Jumillar 'yan Ukraine 2,437,000 ne suka tsallaka cikin maƙociyarsu Poland tun bayan da Rasha ta ƙaddamar da yaƙi a ƙasar, a cewar jami'an tsaro na iyakar Poland a yau Asabar.
Sai dai adadin masu tsallakawar ya ragu matuƙa yayin da aka samu adadi mafi ƙaranci a jiya Juma'a tun bayan fara yaƙin a 24 ga watan Fabarairu.
A gefe guda kuma, adadi mai yawa na mutanen na komawa cikin Ukraine - mutum 421,000 ne suka koma ta kan iyakar Poland, in ji hukumar.
A ranar Juma'a kaɗai, 15,000 ne suka tsallaka zuwa Ukraine daga Poland.
Jumillar mutum fiye da miliyan 10 ne suka tsere wa yaƙin a Ukraine, a cewar kwamashinan 'yan gudun hijira na Majalisar Ɗinkin Duniya (MDD).
An yi hasashen cewa ba ya ga miliyan huɗu da suka shiga sauran maƙotan ƙasashe, akwai miliyan shida da rabi da ke gudun hijira a cikin Ukraine ɗin.
Barkanmu da Ramadana
Maraba da sake haɗewa a shafin labarai kai-tsaye, wanda zai kawo rahotanni na abubuwan da ke faruwa daga sassan duniya, musamman a Ukraine da kuma Najeriya.
Umar Mikail ne zai kasance da ku a wannan hantsi na Asabar, 1 ga watan Ramadana.