Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Sarkin Musulmi ya umarci a soma duba sabon watan Ramadan

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da Afirka da sauran sassan duniya musamman Ukraine da Rasha.

Rahoto kai-tsaye

Umar Mikail and Umaymah Sani Abdulmumin

  1. Rufewa

    Da haka muke bankwana da ku sai kuma gobe Juma'a da yardar Allah...Umaymah Sani Abdulmumin ke muku fatan alheri. A kwana lafiya

  2. 'Yada naji da mutuwar ƴata Farida a jirgin kasan Abuja-Kaduna'

    Adaidai lokacin da wasu 'yan uwa da abokan arzikin suke ci gaba da kukan rashin sannin makomar 'yan uwansu da wannan harin da jirgin kasa ya rutsa da su a ranar Lahadi, saboda watakila an sace su ko koma rai ya yi halinsa amma kuma ba a ga gawarsu ba, shi kuma wani uba har yanzu yana cikin yanayi mare dadi saboda kashe 'yarsa da 'yan bindigar suka yi a cikin jirgin kasan.

    Farida Muhammad na daga cikin mutum takwas da hukumomi suka tabbatar da rasuwarsu a harin jirgin kasan. Kuma ya shaidawa BBC halin da yake ciki;

  3. Putin ya yi barazanar daina sayarwa Turai gas daga gobe Juma'a

    Shugaban Rasha Vladimir Putin ya yi gargadi cewa kasarsa za ta daina sayar da iskar gas ga ƙasashen Turai daga gobe Juma'a, sai idan ƙasashen sun amince su fara biyan kuɗin gas din da takardar kuɗi na Rasha wato Rouble.

    Yayin wani jawabi da yayi ta bidiyo, Mista Putin ya ce tuni ya sanya hannu kan wata doka da za ta fayyace tsarin kasuwanci da ƙasashen da ba amintatu ne ba, kamar yadda ya ce.

    Ya ce ya ɗauki matakin ne saboda ƙasashen yamma na amfani da tsarin kasuwancin a matsayin makami, saboda haka babu dalilin da zai sa Rasha ta ci gaba da amfani da takardun kuɗaɗen ƙasashen waje.

    Sai dai ƙasashen Jamus da Faransa da Austria sun yi watsi da bukatun na Rasha.

  4. Sarkin Musulmi ya umarci a soma duba sabon watan Ramadan

    Sarkin Musulmi, Sultan Muhammad Sa'ad Abubakar wanda shi ne shugaban majalisar koli kan harkokin addinin Musulunci ta Najeriya, ya buƙaci al'ummah Musulmi su soma duba sabon watan Azumin Ramadana.

    Wannan na kunshi cikin wata sanarwa da ya fitar dauke da sa hannun babban jami'i a majalisar, Arc. Zubairu Haruna Usman-Ugwu.

    Sanawar ta umarci Musulmi su soma duba sabon watan daga yammacin Juma'a 1 ga watan Afrilun, 2022, wanda ya yi daidai da 29 ga watan Sha'aban shekara ta 1443 bayan hijira.

    Idan aka yi nasarar ganin watan a gobe Juma'a to za a tashi da Azumi ranar Asabar a matsayin 1 ga watan Ramadana kenan. Idan kuma ba a ga wata ba to 1 ga watan Ramadan zai kasance Lahadi 3 ga watan Afrilu, a cewar sanarwar.

  5. Mun san cewa za a kai hari jirgin kasa - El-Rufa'i

    Gwamnan Kaduna a Najeriya Nasir El-Rufa'i ya ce watanni biyu kenan da suka samu bayanan sirri daga jami'an tsaro cewa ana kitsa kai hari kan jirgin kasa.

    Saboda duk zirga-zirga da abubuwan da 'yan bindiga ke aikatawa ana sani, har daga inda suke komai an sani, a cewarsa.

    Hatta maganganunsu ta waya, kuma an rubuta wasiƙa zuwa ga hukumar kula da sufurin jiragen kasa kan cewa a daina zirga-zirga daren amma aka ƙi.

    Ya ce wasikarsu na cewa a rinƙa komai da rana saboda zai fi tsaro da sauƙi wajen kai agaji idan wani abu ya faru. Zirga-zirgar jiragen kar su ke wuce 4 na yamma.

    Ya ce yana sanar da hakan ne domin mutane sun san abin da ke faruwa saboda akwai waɗanda ya kamata suyi wasu ayyukan amma sun ƙi.

    Sai dai gwamnan ya ce ba za su daina matsawa shugaban ƙasa da sojoji ba.

  6. Shugaba Bazoum na Nijar ya ce a shirye yake ya taimakawa Najeriya don yaƙar 'yan ta'adda

    Shugaban Jamhuriyar Nijar Mohammed Bazoum yace kasarsa a shirye take ta ba da hadin kai idan Najeriya ta yanke shawarar hada rudunar hadin gwiwa daga kasashe makwabta don yakar ‘yan fashin daji a arewa maso yammacin kasar.

    Shugaba Bazoum ya fadi hakan ne dazu yayin wata ziyarar aiki da ya kai Abuja babban birnin kasar.

    A shekara ta 2015 kasashen biyu tare da kasashen Kamaru da Chadi da Benin suka hada rundunar hadin gwiwa ta kasashen tafkin Chadi wadda ta taimaka wajen fatattakar mayakan Boko Haram daga shiyyar arewa masu gabashin Najeriyar.

  7. Nasir El-Rufai: Mun gaza a matsayinmu na shugabanni a Najeriya

    Gwamnan Jihar Kaduna a arewa maso yammacin Najeriya Nasir El-Rufai ya nemi gafara al'umma bisa hare-haren da 'yan bindiga da ke ci gaba da salwantar da rayukan a yankunan Jihar Kaduna, musamman harin da aka kai wa jirgin kasa a ranar Alhamis.

    Gwamnan, wanda cikin yanayi mai cike da damuwa ya ce haƙiƙanin gaskiya yana cikin matuƙar bakin ciki saboda rabonsa da ya yi bacci tun ranar Alhamis, kuma ba ya iya bacci ko da ya sha maganin bacci saboda tsananin tashin hankali.

    El-Rufa'i ya yi waɗannan kalamai ne lokacin da ya je karamar hukumar Giwa domin bai wa al'umma hakuri da ta'azziya da jaje bisa abubuwan da ke faruwa.

    Ya kai ziyarar ne ranar Alhamis ƙarƙashin rakiyar mataimakiyarsa Hajiya Hadiza Sabuwa Balarabe da kuma wasu mukaraɓan gwamnatinsa.

    A wani saƙon murya da masu taimaka wa gwamnan kan yaɗa labarai suka bai wa BBC, gwamnan ya ce hakkin shugabanci abu ne da wata rana zai tashi ya tsaya gaban Ubangiji domin ya yi bayyani kan abubuwan da ke faruwa da abubuwan da ya aiwatar.

  8. Kotu taƙi amincewa da sauye-sauyen da shugaba Kenyatta ya bijiro da su

    Kotun Kolin Kenya ta ki amincewa da wasu sauye-sauye da Shugaba Uhuru Kenyatta ya gabatar, gabanin zaɓen shugaban ƙasar da za a yi a ƙarshen wannan shekarar.

    Kotun ta kuma amince da wani hukuncin da ke cewa shugaban ƙasar ba shi da ikon gabatar da sauye-sauye ga tsarin mulkin ƙasar.

    Cikin sauye-sauyen akwai na kafa ofishin Firaminista -- matakin da bai sami karɓuwa ba a wajen 'yan kasar.

    Masu sukar matakin - ciki har da mataimakin shugaban kasar William Ruto na cewa wannan wani yunkurin kwace iko ne ta bayan fage kawai.

  9. NATO ta ce Rasha ba ta cika alƙawarin da ta ɗauka ba kan dakatar da hari a Ukraine

    Shugaban ƙawancen tsaro na NATO ya ce hukumomin leƙen asiri na kasashen Yammacin duniya sun tabbatar da cewa Rasha ba ta cika alƙawuran da ta dauka na rage yawan hare-haren da dakarunta ke kaiwa a yankin birnin Kyiv da arewacin Ukraine ba.

    Jens Stoltenberg ya ce sojojin Rasha ba su janye ba, sai dai ana sauya musu wuri ne domin su kara shirin kai wasu hare-haren a yankin Donbas da ke gabashin kasar.

    Mista Stoltenberg ya kuma ce Rasha na ci gaba da harin da ta ke kai wa biranen Kyiv da sauran birane, kuma ya ce Rasha ta ci gaba da yin karyar cewa za ta janye daga yankunan.

    Wata mazauniyar birnin Chernihiv ta ce: "Ta yaya za su ce sun rage yawan sojojinsu? Muna ci gaba da jin karar bama-bamai. Ba ma iya barci, mun fuskanci tashin hankali cikin kwanaki biyun da suka gabata."

  10. Masu garkuwa da mutane a Kaduna sun sace jami'in Kwastam a gidansa

    Wasu 'yan bindiga sun kai hari kan rukunin gidaje na low-cost da ke Ƙaramar Hukumar Zaria ta Jihar Kaduna tare da yin garkuwa da wani jami'in hukumar Kwastam.

    Rahotanni sun ce maharan sun kutsa unguwar da misalin ƙarfe 8:00 na yammacin Laraba, inda suka buɗe wuta kan mai tsautsayi.

    Daga baya sun wuce kai-tsaye zuwa gidan ofisan tare da tafiya da shi da kuma ɗansa.

    Kafar yaɗa labarai ta Channels TV ta ruwaito cewa 'yan bindigar sun sace ƙarin wasu mutum shida.

    Lamarin ya faru kwana biyu bayan wasu 'yan bindiga sun kashe mutum aƙalla takwas da jikkata kusan 30 a harin da suka kai kan jirgin ƙasa na Kaduna zuwa Abuja. Kazalika, sun sace mutanen da har yanzu ba a tantance yawansu ba.

  11. Kotun Ƙolin Kenya ta yi watsi da buƙatun shugaban ƙasa kan sauya tsarin mulki

    Kotun Koli a Kenya ta ƙi amincewa da wasu sauye-sauye da Shugaba Uhuru Kenyatta ya gabatar gabanin zaɓen shugaban kasar da za a yi a karshen wannan shekarar.

    Kotun ta kuma amince da wani hukuncin da ke cewa shugaban kasar ba shi da ikon gabatar da sauye-sauye ga tsarin mulkin kasar.

    Cikin sauye-sauyen akwai na kafa ofishin firaminista -- matakin da bai sami karbuwa a wajen 'yan kasar ba.

    Masu sukar matakin, ciki har da mataimakin shugaban kasar William Ruto, na cewa wannan wani yunkurin kwace iko ne ta bayan fage.

  12. Shugaban Nijar Bazoum na ganawa da Buhari a Abuja

    Shugaban Nijar Mohamed Bazoum ya isa Fadar Shugaban Ƙasar Najeriya don ganawa da Shugaba Muhammadu Buhari.

    Tun farko fadar ta Buhari ta ce shugabannin biyu za su tattauna kan alaƙa tsakanin ƙasashensu, musamman matsalar tsaro da maƙotan biyu ke fuskanta.

  13. Jami'an tsaron Isra'ila sun kashe Falaɗinawa biyu

    An kashe wasu Falasɗinawa biyu tare da raunata wasu 15 yayin wani samame da jami'an tsaron Isra'ila suka kai kan sansanin 'yan gudun hijira a yankin Gaɓar Yamma da Kogin Jordan, a cewar hukumomin Falasɗinu.

    Rundunar sojan Isra'ila ta ce ta amsa wani kira ne cewa wasu 'yan bindigan Falasɗinawa sun buɗe wuta lokacin da suke kama "wasu 'yan ta'adda". An jikkata soja ɗaya yayin samamen.

    An kai samamen ne bayan wani mutum ya kashe mutum biyar a Isra'ila.

    A wani ɓangaren na yankin a ranar Alhamis, wani Bafalasɗine ya raunata wani ɗan Isra'ila da wuƙa, wanda daga baya aka harbe shi.

    Cikin mako biyu da suka wuce, an kashe mutum 11 jumilla a Isra'ila.

  14. MDD na neman dala miliyan huɗu don tallafa wa Afghanistan

    Majalisar Dinkin Duniya (MDD) ta ce tana neman kusan dala biliyan huɗu da rabi domin gudanar da ayyukan jin kai a Afghanistan.

    Kiran da aka yi a wani taro a Geneva ranar Alhamis, shi ne mafi girma da MDD ta taba yi don tallafa wa kasa ɗaya.

    A halin da ake ciki, Afghanistan na cikin wani mawuyacin hali na jin kai.

    Fari da takunkuman ƙasa da ƙasa da aka ƙaƙaba mata bayan ƙwace iko da kungiyar Taliban ta yi, ya kara ta'azzara halin da ake ciki.

    Duk mutum biyu cikin uku a kasar na fama da yunwa, abin da ya sa jama'a ke sayar da kayayyakinsu don samun abin kai wa ga bakin salati.

  15. Nijar za ta ɗauki ƙarin soja 5,000 maimakon 2,000

    Hukumomi a Jamhuriyar Nijar sun sanar da shirin ɗaukar sabbin dakarun soja 5,000 a rundunar sojan ƙasar a yaunƙurin gwamnati na yaƙar 'yan bindigar da ke addabar yankuna daban-daban na ƙasar.

    Akasari gwamnatin Nijar na ɗaukar mutum 2,000 ne duk shekara a aikin soja.

    Hukumomi sun nemi matasa 'yan shekara 18 zuwa 25 da su gabato da kansu don shiga aikin tsaron na soja da zummar kare ƙasarsu.

    Matakin na zuwa ne yayin da Boko Haram ke ƙara tsaurara hare-hare a garuruwan da ke kudancin ƙasar masu iyaka da Najeriya da kuma ƙungiyoyin masu iƙirarin jihadi ƙawayen IS da al-Ƙa'ida a yammaci da ke da iyaka da Mali da Burkina Faso.

    A cewar wata sanarwar gwamnati, za a fara ɗaukar sabbin dakarun daga watan Mayu mai zuwa.

    Ficewar sojojin Faransa da ke yaƙi da masu iƙirarin jihadi a Mali ta jawo giɓi na tsaro bayan shafe shekara kusan 10.

  16. Sojojin sama ne za su dinga raka jirgin ƙasa na Kaduna-Abuja - Amaechi

    Gwamnatin Najeriya ta ce daga yanzu jiragen sama ne za su dinga yi wa jirgin ƙasa na Abuja zuwa Kaduna rakiya da zarar ya ci gaba da aiki.

    Ministan Sufuri Rotimi Amaechi ne ya bayyana hakan ranar Laraba lokacin da ya kai ziyara jihar don gane wa idonsa abin da ya faru bayan harin da 'yan fashi suka kai kan jirgin a ranar Litinin, wanda ya yi sanadiyyar kashe mutum takwas.

    Bayan ya duba waɗanda suka jikkata a Asibitin 44 na Sojoji a Kaduna, Mista Amaechi ya kuma gana da Hafsan Sojojin Sama Air Marshal IO Amao da kuma Gwamna Nasir El-Rufai na Kaduna.

    "Na faɗa wa hafsan sojan sama cewa idan muka gama gyaran layin dogo, jirgin zai ci gaba da aiki bisa rakiyar tsaro ta sama daga sojan sama har sai an saka kayayyakin tsaro daga nesa kamar yadda shugaban ƙasa ya ba da umarni," in ji Amaechi cikin wani saƙon Twitter.

    Ministan ya zargi "abokan aikinsa" cewa su ne ke hana ruwa gudu tun lokacin da ma'aikatarsa ta nemi kuɗin sayen kyamarorin tsaron a baya.

  17. Rundunar Sojan Sama ta Najeriya ta kashe 'yan fashi 34' a Kaduna

    Rundunar sojan sama ta Najeriya ta ce ta kashe 'yan bindiga fiye da 30 a kan Titin Sarkin Pawa da ke tsakanin jihohin Neja da Kaduna a arewacin ƙasar ranar Laraba.

    Wata sanarwa da rundunar ta fitar ta ce sun yi nasarar kashe 'yan bindigar da take kira 'yan ta'adda ne sakamakon bayanan sirri da ta samu cewa wasu mahaya babura kusan 40 na tafiya a kusa da garin Akilibu zuwa Sarkin Pawa.

    Nan take jiragen sama suka far musu tare da karkashe su ta hanyar harba musu makaman roka, a cewar sanarwar.

    Mazauna garin Mangoro da suka kai wa sojoji rahoto sun ce sun ga babura 17 da kuma gawar mutum 34 yashe a ƙasa.

    Kazalika, mutanen sun ce sun ga bindigogi ƙirar gida 14 na 'yan bindigar.

  18. Majalisar Wakilan Najeriya ta tilasta wa hafsoshin tsaro bayyana a gabanta kan harin jirgin ƙasa

    A yau Alhamis ake sa ran shugabannin tsaro na Najeriya za su bayyana a gaban Majalisar Wakilan Ƙasar bayan majalisar ta umarce su da yin hakan a zamanta na jiya Laraba.

    Sai dai tun a Larabar shugabannin tsaron suka nemi su gana da shugabancin majalisar ƙarƙashin Mataimakin Kakakin Majalisa Ahmed Idris Wase, amma sai majalisar ta ƙi yarda da hakan, tana mai tilasta musu bayyana a gabanta a yau Alhamis.

    Majalisar dai na son hafsohin tsaron su yi mata ƙarin bayani ne g ame da yadda 'yan fashi suka kai hari kan jirgin ƙasa na Kaduna zuwa Abuja ranar Litinin, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar aƙalla mutum takwas.

    Kazalika, tana so ta ji yadda 'yan bindigar suka kai wani harin kan filin jirgin sama na Kaduna kwana biyu kafin na jirgin ƙasan.

    Waɗanda majalisar ke son su bayyana a gabanta sun haɗa da hafsoshin tsaron ƙasa, da sufeton 'yan sanda na ƙasa, da ministocin da lamarin ya shafi ma'aikatunsu bisa umarnin shugabannin kwamatocin soja da na sufurin jirgin sama da na 'yan sanda da na sufuri.

    Da ƙarfe 3:00 agogon ƙasar ake sa ran za su bayyana a zauren majalisar.

  19. Mashawartan Shugaba Putin na tsoron faɗa masa gaskiya - Amurka

    Jami’an leƙen asirin Birtaniya da Amurka sun ce mamayar da Rashar ke yi a Ukraine ta gamu da cikas, saboda yadda mashawartan Shugaba Putin suka dinga ba shi bayanan da ba sahihai ba.

    Fadar mulki ta White House ta ce hakan ya haifar da rashin jituwa tsakanin shugaban da manyan janar-janar ɗinsa.

    Mai magana da yawun ma'aikatar tsaron Amurka ta Pentagon, John Kirbi, ya ce hakan na iya sa shugaban ya ki bayar da haɗin kai a tattaunawar zaman lafiya.

    Ya ce "sojojinsa ne, yaƙinsa ne wannnan, shi ya zabi ya sa kansa, ganin sojojinsa na rashin nasara abu ne da ka iya sake tunzura shi".

    Ita dai fadar mulki ta shugaban Rashar wato Kremlin ta yi gum da bakinta a kan wannan ikirari, wanda ta sha bayyanawa a matsayin farfagandar ƙasashen Yamma.

  20. Ina kwananku

    Barkanmu da sake saduwa a shafin labarai kai-tsaye tare da ni Umar Mikail.

    Ku biyo mu don samun rahotanni kai-tsaye na abubuwan da ke faruwa a sassan duniya, musamman a yaƙin Ukraine da kuma Najeriya.