Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Mutum biyu sun yi kashin hodar ibilis a filin jirgi na Abuja

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da Afirka da sauran sassan duniya musamman Ukraine da Rasha.

Rahoto kai-tsaye

Awwal Ahmad Janyau and Umar Mikail

  1. Sai da safenku

    Ƙarshen rahotannin kenan a wannan shafi, sai kuma gobe Litinin.

    Kafin nan, Umar Mikail ke muku fatan alheri.

  2. Gwamnan Rivers Wike ya ce zai nemi shugabancin Najeriya a 2023

    Gwamna Nyesom Wike na Jihar Rivers a kudancin Najeriya ya ayyana neman shugabancin Najeriya, yana mai cewa yana da ƙwarewar da zai lashe zaɓen na 2023 a ƙarƙashin jam'iyyar adawa ta PDP.

    Gwamnan ya bayyana haka ne yayin ganawar da ya yi da shugabannin PDP na Jihar Benue a gidan gwamnatin jihar da ke Mukudi ranar Lahadi.

    Ya nemi wakilan jam'iyyar su jefa masa ƙuri'a a zaɓen fitar da gwani yana mai jaddada batun karɓa-karɓa.

    "Idan ana son korar APC daga kan mulki, ni ne zan faɗa musu ya isa haka," in ji shi kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

    Ya ƙara da cewa; "Dole ne mu ƙwace mulki kuma na shirya yin hakan a PDP. Allah na tare da mu, shi ya sa APC ke taɓarɓarewa koyaushe.

    "Ina shelar (takarar) a Benue tukunna, zan yi takara."

  3. Rasha ta hana yaɗa hirar da kafafen yaɗa labarai suka yi da Shugaban Ukraine Zelensky

    Hukumar da ke kula da harkokin yaɗa labarai ta Rasha ta yi gargaɗi ga kafofin yada labarai na ƙasar kan cewa kar su wallafa tattaunawar da suka yi da shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky.

    Hukumar ta ce tana gudanar da binciken kwakwaf kan wanda ya yi tattaunawar da kuma dalilin yinta.

    Ta ce akwai kafafen yada labaran da aka bude a Rasha domin su yi wa kasashen waje aiki.

    Rasha ta ƙaddamar da wata sabuwar doka da za ta iyakance rahotannin da za a iya yi kan yakin Ukraine, kuma duk wanda ya karya dokar zai yi zaman gidan yari na shekara 15.

  4. Ukraine ta zargi Rasha da tilasta wa fararen hula shiga cikin ƙasarta

    Ukraine ta zargi Rasha da tilasta wa 'yan ƙasarta fararen hula barin garin Mariupol mai tashar jirgin ruwa da yaƙi ya ɗaiɗaita.

    Rasha ta karɓi mutanend a aka ƙiyasta yawansu kan 5,000 a wani sansani na wucin gadi da ke Bezimenne da aka gani ta hotunan tauraron ɗan Adam.

    Mataimakin Firaministan Ukraine Iryna Vereshchuk ya ce an kwashe mutum 40,000 zuwa wuraren da Rasha ke iko da su ba tare da amincewar gwamnatin Ukraine ba.

    Wata 'yar gudun hijirar Mariupol da yanzu take a Rasha ta ce: "Dukkanmu tilasta mana aka yi".

    Wasu jami'an Ukraine sun siffanta yunƙurin na Rasha a matsayin "tasa ƙeya" zuwa "sansanin tantancewa", wani abu da ya yi kama da yaƙin Rasha a Chechnya, lokacin da aka yi binciken rashin imani a kan dubban mazauna yankin a sansanoni kuma aka ɓatar da wasu da yawa.

  5. Taliban ta hana yaɗa shirye-shiryen BBC a kafafen yaɗa labarai na Afghanistan

    An dakatar da yada shirye-shriyen BBC na talabajin a harsunan Pashto da Fasha da kuma Uzbek a Afghanistan, bayan umarnin da Taliban ta bayar na daina yaɗa duk wani shirin kafafen yada labarai na kasahsen waje a kasar.

    Shugaban sashen harsuna na BBC, Tarif Kafala, ya ce 'yan Afghanistan miliyan 6 ne ke kallon shirye-shiryen BBC a kowane mako cikin harsunansu, inda ya ce yana da muhimmanci 'yan kasar su dinga samun damar kallon labaran da babu nuna ɓangaranci a cikinsu.

    Wakilin BBC ya ce wannan wani mataki ne da Taliban ta dauka domin fadada ikonta a kasar.

    Tuni Mista Kafala ya yi kira ga Taliban da ta janye umarnin kuma ta tabbatar an ci gaba da yaɗa shirye-shiryen BBC a Afghanistan.

  6. Rasha da Ukraine za su ci gaba da tattaunawa a Turkiyya

    Zama na gaba da za a yi gaba-da-gaba tsakanin Rasha da Ukraine za ta gudana ne a Turkiyya, wadda za a fara gobe Litinin, a cewar wakilan Ukraine.

    David Arakhamia ya faɗa a Facebook cewa tattaunawar za ta gudana daga Litinin zuwa Laraba.

    Ukraine ta siffanta tattaunawa da Rasha tun bayan fara gwabza yaƙi a matsayin "mai wahalar gaske".

    An fara zagayen farko na tattaunawar a Belarus, wadda ƙawar Rasha ce, amma Turkiyya ta taka rawa a tattaunawar don kawo ƙarshen yaƙin.

  7. Mutum biyu sun yi kashin hodar ibilis a filin jirgi na Abuja

    Jami'an hukumar yaƙi da shan miyagun ƙwayoyi a Najeriya ta NDLEA sun kama mutum biyu da ake zargi da safarar hodar ibilis ko kuma koken ƙwaya 165.

    Sanarwar da hukumar ta fitar a yau Lahadi ta ce Elvis Uche Iro mai shekara 53 da Uwaezuoke Ikenna Christian mai shekara 42 sun yi kashin hodar ce a filin jirgin sama na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja.

    An kama Elvis jim kaɗan bayan ya sauka daga jirgi a ranar Asabar 19 ga watan Maris daga Addis-Ababa na Habasha saboda ya haɗiye ledar koken 65, wadda ta kai nauyin kilogiram 1.376.

    Wani fasinjan da ke cikin jirgin mai suna Christian, a cewar sanarwar, ya haɗiye leda 100 ta koken mai nauyin kilogiram 2.243.

    Uwaezuoke ya faɗa wa masu bincike cewa ya sayar da filinsa a ƙauyensu sannan ya karɓi bashi daga abokansa don sayen ƙwayoyin.

  8. 'Rasha na yunƙurin raba Ukraine biyu'

    Babban hafsan sojan Ukraine ya yi gargaɗin cewa Rasha na yunƙurin abin da ya kira "yanayin Koriya" a kan Ukraine, bayan ta kasa kama babban birnin ƙasar Kyiv tare da hamɓarar da gwamnati mai-ci.

    Kyrylo Budano ya ce niyyar Vladimir Putin ita ce kama gabashi da kudancin Ukraine bayan sun gaza samun ci gaba a yaƙin da suke yi.

    Idan ya samu damar haɗa kan yankunan, Putin zai yi ƙoƙarin shata layi da zai raba su da sauran ƙasar - kusan dai kamar yadda aka yi bayan yaƙin Koriya.

  9. IS ta yi iƙirarin kashe sojojin Nijar

    Ƙungiyar IS mai da’awar jihadi ta yi ikirarin kashe sojojin Nijar a kwaton ɓauna a yankin Tillaberi da ke kudu maso yammaci.

    IS ta yi ikirairn ne a wani shafinta na kafar Telegram. Ta ce sojoji bakwai na Nijar ta kashe.

    Tun da farko wasu kafofin yaɗa labaran Nijar sun bayar da rahoton kai wa ayarin sojin Nijar hari a ƙauyen Kolamne a Tallaberi amma sun ce soja shida aka kash.

  10. Ƴan tawayen Houthi sun ce za su daina kai hari Saudiyya na kwana uku

    Ƴan tawayen Houthi sun sanar da dakatar da kai hare-hare ta hanyar harba makamai masu linzmi da jiragen yaƙi na tsawon kwana uku.

    Shugaban majalisar ƙoli na ƴan tawayen Mahdi al-Mashat, ne ya sanar da tagaita wutar a ranar Asabar, kamar yadda kamfanin dillacin labarai na ƴan tawayen Saba ya ruwaito.

    Mayaƙan sun ce a shirye suke su tsagaita buɗa wuta gaba ɗaya amma sai idan Saudiyya ta amince ta kawo ƙarshne ƙawanya da kuma hare-hare ta sama a Yemen.

  11. Ko kin san hantara na hana yara tsawo?

  12. Macron ya yi kiran kauce wa furta kalaman da za su ƙara rura yakin Ukraine

    Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya yi gargaɗi game da furta kalaman da za su ƙara rura yakin Ukraine, kwana guda bayan da shugaba Biden ya bayyana Vladimir Putin a matsayin wanda bai kamata a bar shi ya ci gaba da mulki ba.

    Mista Macron ya shaidawa kafafen yada labaran Faransa cewa manufar ita ce tsagaita buɗe wuta a Ukraine sannan kuma a janye sojojin Rasha.

    Ya ce hakan ba zai yiwu ba ta hanyar furta zafafan kalamai.

    Hukumomin Amurka sun musanta cewa shugaba Biden yana nufin kiran sauyin shugabanci a Rasha a jawabinsa kan Mista Putin a ziyarar da ya kai kasar Poland.

    Sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken ya ce Mista Biden yana magana ne kawai kan cewa ba za a bar Mista Putin ya yi yaki da Ukraine ba.

    Mista Macron ya ci gaba da tattaunawa da shugaban Rasha tun soma rikicin Ukraine.

  13. Rasha na son raba Ukraine biyu, in ji sojin Ukraine

    Rasha na ƙoƙarin ta raba Ukraine biyu domin ta kafa yankin da take da iko da shi bayan ta kasa ƙwace ikon ƙasar ba ki ɗaya, kamar yadda hukumar leƙen asirin sojin Ukraine ta bayyana.

    Kamfanin dillacin labarai na Reuters ya ruwaito Kyrylo Budanov yana cewa Rasha tana diba yiyuwar “kafa arewa da Koriya ta kudu a Ukraine”, yana mai cewa ƙasar za ta ƙaddamar farmaki a yankunan da Rasha ta mamaye.

  14. Gane Mini Hanya: Yawan ƴan gudun hijira a Najeriya

    Yayin da ake ci gaba da fuskantar hare-haren ƴan bindiga da ke sanadin karuwar ƴan gudun hijira a arewa maso yammacin Najeriya, hukumar da ke kula da ƴan gudun hijira ta kasar ta ce tana fadi-tashin inganta rayuwar dubban mabuƙatan da ake samu a kullum.

    A cewar hukumar da ke kula da ƴan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya, yanzu haka waɗanda suka rasa matsugunansu saboda bala’i a Najeriya sun haura mutun miliyan uku.

    A filinmu na gane Mini hanya na wannan makon, Jabir Mustapha Sambo ya tattauna da Shugabar hukumar da ke kula da ƴan gudun hijira da Ci Rani ta Najeriya, Imaan Sulaiman Ibrahim, ta bayyana irin ƙalubalen da ke hana samun ainihin alƙaluman ƴan gudun hijira a lokaci guda.

  15. Taliban ta haramta cuɗanyar mata da maza wuraren shakatawa

    Gwamnatin Taliban a Afghanistan ta ce daga yanzu maza da mata ba za su tafi wuraren shakatawa ba lokaci guda a Kabul.

    Sanarwar da gwamnatin ta fitar ta ce a wasu kwanaki na mako, "mata masu sanye da nikabi" ne za su tafi wuraren shakatawar kuma Taliban ba ta da ƴancin zuwa wuraren a kwanakin.

    Sanarwar ta ce an ware wa maza ranakin Laraba da Alhamis da Juma'a da Asabar, mata kuma a ranakun Lahadi da Litinin da Talata.

    Taliban ya kuma buƙaci mata su sanya nikabi a wuraren shakatawar ko kuma su fuskanci fushin hukuma.

  16. Ƴan bindiga sun kashe sojojin Nijar shida

    An kashe sojojin Nijar shidaa wani hari da ƴan bindiga suka kaia kudu maso yammacin ƙasar, kusa da iyaka da Burkina Faso, kamar yadda ma’aikatar tsaron kasar ta sanar ranar Asabar.

    Harin wanda aka kai a ranar Alhamis, shi ne na biyu cikin kwanaki 10 da ke nuna dawowar hare-hare a yankin bayan shafe makwanni ba a kai hari ba.

    Sanarwar ma’aikatar tsaron ta ce "Wasu gungun ƴan ta’adda ɗauke da makamai sun yi wa ayarin sojojin Nijar kwanton ɓauna a kusa da kauyen Kolmane.”

    Sanarwar ta ce sojoji shiga aka kashe yayin da ɗaya ya samu rauni da kuma mota da aka lalata. Babu ƙarin bayani kan makomar maharan.

    Yankin Tallaberi ya sha fama da hare-hare musamman a yankunan da ke kan iyaka da Burkina Faso da Mali inda mayaƙa masu iƙirarin jihadi masu alaƙa da Al Qaeda da IS ke kai hare-hare.

  17. Zelensky ya sake roƙon ƙasashen yamma su ba shi makamai

    Shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky ya yi kira ga gwamnatocin ƙasashen yammaci su ba shi jirage da tankokin yaƙi da makaman kakkabo makami mai linzami.

    A jawabin da shugaban ya yi mai sosa rai, ya ce manyan makaman da ya kamata a kare ƴancin Turai da su na can a jibge sun yi ƙura.

    Mr Zelensky ya yi koken cewa ba a iya kakkabo jiragen Rasha da bindiga.

    “Me Nato take yi? Shin Rasha ce ke jagorantarta? Me suke jira? Kwana 31 yanzu. Abin da kawai muke nema kashi ɗaya na abin da Nato ta mallaka,” in ji shugaban.

  18. Biden ya ce ‘Putin ba zai ci gaba da zama kan mulki ba’

    "Saboda Allah, wannan mutumin ba zai ci gaba da zama kan mulki ba", a cewar shugaban Amurka Joe Biden da yake magana game da takwaransa na Rasha Vladimir Putin yayin wani jawabi a Warsaw babban birnin Poland a ranar Asabar.

    Nan take Fadar White House ta fayyace cewa Biden ba yana kiran sauyin gwamnati ba ne, a maimakon haka yana magana game da hana Putin yin amfani da ƙarfi kan makwabta.

    Da yake magana game da Rasha, Biden ya ce “ba maƙiyanmu ba ne, tare da kammala jawabin da cewa “wannan mutumin ba zai ci gaba da mulki ba.”

    Bayan jawabin Biden, gwamntin Rasha ta fitar d sanarwa tana mayar da martani, inda ta ce abin da Biden ya faɗa ba zai tantance ko Putin zai tabbata kan mulki ba. “Biden bai isa ya bayyana haka ba. Ƴan Rasha ke zaɓen ke zaɓen shugaban Rasha.”

  19. Ɗan majalisar Amurka ya rasa kujerarsa saboda ɗan Najeriya

    Wani ɗan majalisar wakilan Amurka ɗan jam'iyar Republican ya sanar da ajiye muƙaminsa bayan samunsa da laifin zabga ƙarya kan batunwani tallafin kudi na siyasa da ke da alaka da wani attajiri dan Najeriya.

    Jeff Fortenberry ya wakilci Jihar Nebraska tsawon shekara 17.

    A ranar Alhamis, masu taimaka wa alkali yanke hukunci, na tarayya suka gano cewa Jeff Fortenberry ya yi wa jami'an hukumar binciken manyan laifuka ta Amurka, FBI, karya kan karbar dala dubu talatin daga wani babban atajiri ɗan Najeriya.

    Mista Fortenberry ya ce zai sauka a ƙarshen wannan watan da muke ciki.

    Haka kuma akwai yiwuwar zai shafe shekara 15 a gidan yari kuma idan haka ta tabbata a watan Yuli mai zuwa za a tasa ƙeyarsa zuwa can.

  20. Maraba

    Muna maku mabara da kasance da mu a wannan shafin da muke kawo maku labarai da rahotanni kan abubuwan da ke faruwa a sassan duniya.