Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Rasha ta bayyana buƙatunta ƙarara don kawo ƙarshen yaƙin Ukraine

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da Afirka da sauran sassan duniya musamman Ukraine da Rasha.

Rahoto kai-tsaye

Sani Aliyu and Umar Mikail

  1. Mu kwana lafiya

    Ƙarshen rahotannin ke nan a wannan dare na Alhamis. Mu haɗu da ku a safiyar Juma'a idan Allah ya kai mu.

    Umar Mikail ke muku fatan alheri.

  2. An ƙaddamar da shirin noma ga tsofaffin 'yan N-Power

    Ministar harkokin jin ƙai da ci gaban al'umma a Najeriya, Sadiya Farouq, ta ƙaddamar da wani shirin noma don taimaka wa matasan da suka gama aikin N-Power na rukunin A da B.

    Daga cikin mutum 467,183 da suka yi aikin, 75,600 ne suka nuna sha'awar shiga tsarin, kuma za a ba su horo a zagayen farko da zai kai ga ba su bashin naira miliyan uku daga Babban Bankin Najeriya CBN.

    An ƙaddamar da shirin ne mai suna NEXIT/CBN Agri-Business Small and Medium Enterprises Investment Scheme da haɗin gwiwar CBN.

    Babban Sakatare Bashir Nura Alkali, wanda ya wakilci ministar, ya taya matasan murna waɗanda suka fito daga cikin 500,000 da suka fita daga cikin tsarin samar da aiki na N-Power a baya.

  3. Rasha ta bayyana buƙatunta ƙarara don kawo ƙarshen yaƙin Ukraine

    Turkiyya ta fitar da bayani dalla-dalla kan yarjejeniyar zaman lafiyar da Rasha ta gabatar da nufin tsagaita wuta a yakin da ake yi a Ukraine.

    Sanarwar na zuwa ne bayan Shugaban Turkiyya Recep Tayyib Erdogan ya tattauna ta waya a yau da Shugaba Putin na Rasha.

    Dole ne Ukraine ta amince cewa ko a nan gaba ba za ta shiga cikin ƙungiyar ƙawancen tsaro ta NATO ba.

    Sannan Rasha ta buƙaci cewa Ukraine ta amince yankin Crimea da Rasha ta ƙwace a 2014 da wasu ɓangarori na gabashin Ukraine ɗin za su zamo a ɓangarenta.

    Shugaba Putin ya shaida wa Mista Erdogan cewa wadannan batutuwa za a cimma su ne idan sun haɗu gaba da gaba tare da Shugaban Ukraine, Zelensky.

    Shugaban Ukraine ya ce a shirye yake ya tattauna da Putin.

  4. Turkiyya za ta kai wa Kamaru fenti mai korar sauro

    Turkiyya ta ɓullo da wani sabon mataki a fannin hulɗar tsakaninta da Kamaru ta hanyar yaƙi da zazzaɓin cizon sauro.

    Turkiyyar za ta fara shigar da wani fenti cikin Kamaru da zai dinga korar sauro idan aka shafa shi a cikin daki.

    An ɓullo da wannan fentin ne mai suna “Isonem Contertop Paint" a lokacin da adadin masu kamuwa da cutar cizon sauro ke ƙaruwa a Kamaru, kamar yadda ma’aikatar kiwon lafiya ta bayyana.

    Ana sa ran kuma fentin zai maye gurbin gidajen sauro waɗanda a yanzu haka ingancinsu ya ragu, a cewar wakilin BBC Hausa a Kamaru Mohaman Babalala.

  5. Mutum 190 kacal suka yi aure a Koriya ta Kudu a 2021

    Adadin mutanen da suka yi aure a Koriya ta Kudu a shekarar da ta wuce ya ragu sosai idan aka kwatanta da shekarun baya.

    Mutum 190 ne kacal suka yi aure a bara, adadi mafi karanci tun shekarar 1970.

    An dora alhakin hakan a kan annobar korona wadda ta hana masoya haɗuwa da juna da kuma fita shaƙatawa.

    Adadin ma'auratan ya ragu da kashi 40 cikin 100 idan aka kwatanta da shekara 10 da suka wuce.

    Kazalika, an samu raguwar haife-haife a ƙasar, abin da ya janyo yawan al'ummarta ke raguwa.

  6. 'Yan sandan Najeriya sun kama mutanen da ake zargi da yi wa mace tsirara a titi

    Rundunar 'yan sandan Najeriya ta ce ta kama mutum shida da zargin yi wa wata mata tsirara tare da yin holenta a titi.

    Lamarin ya faru ne a garin Aguleri da ke Jihar Anambra a kudancin ƙasar bayan mutanen sun zarge ta da hannu a mutuwar mijinta saboda lalata da take yi da wasu mazan, zargin da ta musanta.

    Daga cikin waɗanda aka kama akwai wani mai maganin gargajiya da ya kula da mijin nata, wanda daga baya ya faɗa wa 'yan uwansa cewa matar na da hannu wajen mutuwarsa.

    'Yan sanda sun kama mutanen bayan wani bidiyo ya karaɗe shafukan zumunta, inda ya nuna mutanen suna yawo da matar a titi tsirara. 'Yan Najeriya da dama sun nuna ɓacin ransu da ganin bidiyon.

    Mai magana da yawun 'yan sandan Anambra ya faɗa wa BBC cewa suna gudanar da bincike kan mutanen da suka kama da zargin abin da suka kira laifin cin zarafi kafin a kai su kotu.

  7. An lalata kusan baki ɗayan birnin Mariupol - Ukraine

    Hukumomi a birnin Mariupol da dakarun Rasha suka yi wa ƙawanya sun ce an lalata kusan kashi 90 cikin 100 na birnin sakamakon hare-hare.

    Lesia Vasylenko, wani ɗan majalisar Ukraine, ya wallafa a shafinsa na Twitter cewa "ana ragargaza birnin daga sama" kuma ya jaddada kiran Shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky na neman ƙasashen Yamma su saka haramcin tashin jirage a sararin samaniyar ƙasar.

    Rahoton na zuwa ne a lokacin da mahukunta ke cewa suna yunƙurin ceto mutane kusan 1,000 daga cikin wani gini da ake zargin Rasha ta kai wa hari. Mafi yawan mutanen mata ne da ƙananan yara da ke fakewa a ciki.

    Ana ci gaba da aikin ceton yayin da sojojin Rasha ke ci gaba kuma da luguden wuta a birnin.

  8. Fararen hula fiye da 1,000 sun tsere daga Mariupol

    Mahukunta a birnin Mariupol da aka yi wa zobe sun ce jami'an ceto sun samu nasarar fitar da mutum fiye da 1,000 da suka ɓuya a wajen da ke kare mutane daga harin bama-bamai da ke wani ɗakin wasa da dakarun Rasha suka kai hari jiya Laraba.

    Wani ɗan majalisa daga birnin ya shaida wa BBC cewa da alama babu wanda ya rasa ransa a wajen.

    Tuni Rasha ta musanta kai hari wajen.

    Dubban mazauna Mariupol ne suka makale kwana da kwanaki saboda guje wa hare-haren Rasha, inda wadanda suka yi kokarin barin birnin ma kan fuskanci lugudan wuta.

    Magajin garin Mariupol, Boychenko, ya ce dakarun Rasha na kokarin tarwatsa Ukraine da ma mutanenta.

    Ya ce: "Kalma daya da za mu kira abin da ke faruwa a kasarmu yanzu ita ce kisan ƙare-dangin da ake yi wa ƙasarmu da al'ummarmu. Sannan na san cewa akwai ranar da za ta zo da za mu hadu domin sake gina birninmu da ma kasar kanta."

    Ukraine na kokarin samar da wata hanyar tsira ga fararen hula a yankuna tara na kasar ciki har da Mariupol, ta yadda za su samu su guje wa fadan da ake yi a kasar.

  9. An kashe mutum 53 a garin Chernhiv ranar Laraba, in ji gwamnan garin

    Fararen hula aƙalla 53 aka kashe sakamakon hare-haren Rasha a birnin Chernihiv da ke arewacin Ukraine ranar Laraba, a cewar gwamnan yankin Vyacheslav Chaus.

    "Abokan gaba na ci gaba da luguden wuta ba ƙaƙƙautawa da makaman atilare da kuma ta sama. Suna ta rusa gine-ginen jama'a," kamar yadda ya wallafa a shafinsa na Telegram.

    "Muna ta yin rashin nasara. An kai gawar mutum 53 mutuware a kwana ɗaya kacal."

    Mista Chaus ya ce suna ta ƙoƙarin dawo da wutar lantarki da ruwan sha da iskar gas zuwa garin duk da luguden wutar da ake ci gaba da yi.

    Kazalika, ya ce ana ƙoƙarin ci gaba da tattaunawa don sake buɗe hanyoyin jin ƙai don tserar da farar hula daga garin.

  10. Majalisa na bincike kan yawan kuɗaɗen da bankuna ke cazar 'yan Najeriya

    Majalisar Wakilai a Najeriya ta ƙaddamar da bincike kan ƙorafin da 'yan ƙasar ke yi kan yawan cazar kuɗi da bankunan kasuwanci ke yi.

    Yayin zamanta na jiya Laraba, majalisar ta umarci kwamatinta mai kula da harkokin bankuna da kuɗi da ya gudanar da bincike sannan ya kawo rahotonsa cikin mako huɗu masu zuwa.

    Matakin ya biyo bayan ƙorafe-ƙorafen da mutane ke yi ne game da kuɗaɗe daban-daban da bankuna ke cire musu a matsayin ladan aikinsu da kuma na gudanarwa.

    Kuɗaɗen sun haɗa da na tura kuɗi tsakanin bankuna da cire kuɗi daga na'urar ATM da ladan tura wa mutum saƙon tes da kuɗin gudanarwar katin ATM ɗin da kuma na sayen kayayyaki ta intanet.

  11. Birtaniya za ta tura sojojinta zuwa Poland

    Mun sami karin bayani kan labarin da ke cewa Biratniya za ta tura wasu makamai masu iya harbo rokoki masu linzami zuwa kasar Poland wadda mamba ce ta NATO tare da sojojin da ke kula da su guda 100.

    Za a tura sojojin ne na wani takaitaccen lokaci wanda ba zai wuce wata uku zuwa wata shida ba.

    Wani kakakin ma'aikatar tsaro ta Birtaniya ya ce za a aika da makaman da ake kiransu "Sabre missile system" domin su kare sararin samaniyar kasar Poland, kuma an tura su ne kawai domin su zama garkuwa, ba hari za su kai ba.

    Kasashen Amurka da Jamus tuni suka aika da makaman kariya zuwa kan iyakar yankin NATO da na kasashen gabashin Turai.

  12. Iran ta ceto ma'aikatan wani jirgin ruwa mallakin Hadaddiyar Daular Larabawa da ya nutse a mashigar ruwa ta Gulf

    Iran ta ceto mutum 29 cikin mutum 30 wadanda ma'aikatan wani jirgin ruwa ne mai aiki karkashin tutar Hadaddiyar Daular Larabawa da ya nutse a mashigar ruwa ta Gulf bayan ya ci karo da guguwa da igiyar ruwan teku mai karfi, kamar yadda kafar watsa labarai mallakin gwamnatin kasar ta sanar.

    Masu aikin ceto na can suna kokarin gano mutum daya da ba a gani ba.

    Jiragen ruwa biyu da wani jirgi mai saukar ungulu aka aika da su bayan da jirgin ruwa Al Sumy ya nutse kimanin kilomita 48 daga tashar jirgin ruwa ta Assaluyeh a yau Alhamis.

    Wani jami'in kasar Iran ya ce guguwa mai karfi ce, wadda ke tafiya kan kilomita 70 cikin kowace sa'a a lokacin da al'amari ya auku.

    Ma'aikatan jirgin ruwa sun hada da 'yan kasashe da dama ciki har da 'yan Sudan da India da Pakistan da Uganda da Tanzania da kuma Habasha.

  13. Gwamnatin Mali za ta hana tashoshin RFI da France 24 aiki a cikin kasarta

    Hukumomin Mali sun ce za su hana wasu gidajen rediyo biyu na Faransa yin aiki a cikin kasar, bayan da suka tuhume su da "yada labaran kanzon kurege".

    Gidan rediyo na RFI da tashar talabijin ta France 24 da tsohuwar kasar da ta yi wa mali mulkin mallaka wato Faransa ke daukan nauyinsu za su daina aiki a cikin kasar ta Mali na wani lokacin da ba a fayyace tsawonsa ba.

    Cikin wata sanarwar da hukumomin Mali suka fitar, sun ce tashoshin biyu sun yada wani rahoto - kan kalaman da Michelle Bachelet ta Majalisar Dinkin Duniya da kungiyar kare hakkin bil Adama ta Human Rights Watch - da ke cewa sojojin Mali da na wani kamfanin sojojin haya na Rasha sun kashe fararen hula masu yawa a 'yan watannin da suka gabata.

    Kamfanin France Médias Monde, wanda shi ne ke kula da tashoshin biyu na France 24 da RFI, ya ce bai "ji dadin wannan hukuncin ba," kuma ya "sona kan bakarsa ta goyon bayan kokarin inganta 'yancin fadin albarkacin baki da kaucewa bangaranci na 'yan jaridar da ke aiki da shi."

  14. Hotunan ginin da Rasha ta rusa a birnin Mariupol na baya da kuma na yanzu

    Wadannan hotunan na nuna irin barnar da rasha ta yi bayan harin da ta kai kan gidan wasan kwaikwayo na birnin Mariupol, inda aka ce fiye da mutum 1,000 ke neman mafaka.

    Kamar yadda aka ruwaito, jami'an gwamnatin Ukraine sun ce an yi sa'a yawancin mutanen sun tsira da rayukansu.

  15. Wai mece ce bukatar Putin?

    Da alama muradun da Shugaban Rasha Vladimir Putin ya sa a gaba a farkon mamayar da kasarsa ke yi a Ukraine sun ragu ganin yadda yakin da dakarunsa ke yi ke kara jan kafa, ba yadda ya so ba.

    Sai dai a bayyane yake cewa yana kallon wannan yakin a matsayin wanda zai sauya alkiblar kasarsa a tarihin duniya.

    Da farko shugaban na Rasha ya so ya mamaye Ukraine ne kuma ya hambarar da gwamnatin kasar, wanda zai kawo karshen bukatarta na shiga kungiyar tsaro ta NATO.

    Ya shaida wa 'yan kasarsa cewa: "Ba niyyarmu ba ce mu mallaki kasar Ukraine. Ba ma son cusa wani abu kan wasu mutane da karfin yaki."

    Sai dai maimakon haka Rasha ta dauki matakan murkushe gomman garuruwan Ukraine, kuma ya hada kan 'yan kasar kan kiyayya ga mamayar da Rasha ke yi.

    Amma da alama ya fara samun nasarori kan wasu abubuan da ya ke son cimma wa. Da shugaban kasar ta Ukraine da kasashen yammacin Turai sun bayyana cewa babu batun shigar da Ukraine cikin kungiyar ta NATO, kuma akwai alama ba za a shigar da Ukraine din cikin tarayyar Turai ba.

    Da akwai sauran hazo a fagen yakin da Rasha ke yi, kuma sai nan gaba ne za a san ainihin inda Rasha ta sa kai a wannan yakin da ta ke yi a Ukraine.

  16. Zelensky na yi wa majalisar Jamus jawabi

    A halin yanzu Shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky na yi wa majalisar kasar Jamus wato Bundestag da ke Berlin jawabi.

    Yana yin jawabin ne ta kafar intanet.

    Bayan ya sami gagarumin yabo a farkon jawabin nasa, Zelensky na maimaita kalaman da yayi wa majalisar Birtaniya da majalisar Amurka na neman su dauki kwarararan matakai domin taka wa mamayar da Rasha ke yi birki.

    Ya yi kira ga Jamus ta rungumi jagoranci da ta ke da shi tsakanin kasashen Turai, kuma ya nemi shugaban gwamnatin kasar Olaf Scholz da ya "rusa katangar" da Rasha ke son ginawa a Turai.

    Zelensky ya kuma soki rashin kokarin da kasashen tarayyar Turai suka nuna gabanin wannan mamayar, inda ya ce takunkuman da aka saka wa Rasha sun makara.

  17. Ƴan bindiga sun kashe fasinjoji 21 a wata bas a Nijar

    Wasu 'yan bindiga a Nijar sun kashe akalla mutum 21 kuma sun raunata wasu mutane masu yawa yayin wani hari da suka kai kusa garin tera da kan iyakar kasar da Burkina Faso.

    Magajin Garin Tera Hama Mamoudou ya shaida wa BBC cewa maharan sun isa yankin ne bisa babura kuma sun dakatar da wata motar bas a kan wata hanya da ke kusa da kan iyakar kuma sun harbe mutum 19 sannan sun kona wasu mutum biyu da ransu cikin wata motar.

    Magajin Garin ya bayyana matsalar tsaron da ta addabi yankin a matsayin "mai matukar wahalarwa".

    Kungiyoyi masu alaka da IS da al-Qaeda na kai munanan hare-hare a wannan makeken yankin da y ahada Nijar da Burkina Faso da Mali.

  18. 'Rasha ce ta kai harin bam kan gidan da mutum 1,000 ke fakewa' - Ukraine

    Wani dan majalisa a Ukraine ya ce dakarun Rasha ne suka kai harin bam kan gidan wasannin kwaikwayo a birnin Mariupol da mazauna birnin ke fakewa cikinsa.

    Dan majalisa Dmytro Gurin ya shaida wa shirin BBC Today na talabijin cewa "fiye da mutum 1,000" ne ke fakewa cikin ginin yayin da dakarun Rasha suka kai ma sa hari, duk da wani sako da aka rubuta ɓaro-ɓaro a saman ginin da ke cewa akwai kananan yara cikinsa.

    Gurin ya ce "direban jirgin yakin ya ga wadannan kalaman, duk da haka sai ya jefa bam din a kan ginin."

    Ya kuma ce wani wanda ya tsira da ransa ya sanar da hukumomi cewa bam din mai karfin kilo 1,000 ya lalata ginin baki dayansa:

    "Babu sauran ginin a wurin sai baraguzai, kuma ba mu san yawan mutanen da suka halaka ba."

  19. Ukraine na fatan Rasha za ta kyale jami'anta su bude hanyoyin jin-kai tara domin fitar da mazauna birnin

    Jamai'an kasar Ukraine sun ce suna fatan Rasha za ta bari su bude wasu hanyoyin jin kai guda tara daga birane masu yawa na kasar, ciki har da birnin Mariupol da ke kudu maso gabashin kasar.

    Mataimakiyar firaministar Ukraine Iryna Vereshchuk ta ce gwamnatin kasar na kuma fatan far bude hanyoyin cikin yinin yau Alhamis.

    Wannan matakin ya biyo bayan kalaman da Shugaba Zelensky yayi yana cewa dakarun Rasha sun kai hari kan wani gidan wasa a birnin Mariupol, wurin da kusan mutum 1,000 ke fakewa.

  20. Ga wasu muhimman abubuwan da suka faru a yakin da ake yi tsakanin Ukraine da Rasha

    Idan yanzu ka fara bibiyarmu, kuma kana son sanin halin da ake ciki a Ukraine da wayewar gari yau Alhamis:

    • A birnin Mariupol da Rashawa ke yi wa kawanya, motocin bas dauke da 'yan gudun hijira kimanin 300 sun tsallaka kan iyaka zuwa yankin Rostov na Rasha.
    • A jiya Laraba wasu rokokin da Rasha ta harba sun lalata wani gidan wasannin kwaikwayo inda ake tsammanin akwai mutum 1,000 da ke fakewa, kamar yadda mataimakin Magajin Garin birnin ya sanar
    • Shugaba Zelensky na Ukraine ya tuhumi Rasha da kai wa gidan wasan hari da gangar. Rasha ta musanta kai harin
    • A birnin Kyiv an kashe mutum guda kuma an raunata mutum uku bayan da wani rokan da aka harbo ya afka kan ginin. Masu aikin ceto na can suna neman ko akwai wadanda baraguzan ginin suka danne, inji hukumar bayar da agajin gaggawa ta Ukraine
    • A Cherniv kuwa wasu mutum 13 da ke an layin sayen biredi sun halaka bayan da wani bam da Rasha ta harba ya fado kansu
    • A fagen diflomasiyya kuwa, dangantaka tsakanin Rasha da Amura ta kara yin tsami bayan da Shugaba Joe Biden ya kira Shugaban Rasha Vladimir Putin "mai aikata laifukan yaki". Fadar Kremlin ta kira kalaman Biden "wadanda ba za a iya yafewa ba"

    Suna na Sani Aliyu kuma zan jagoranci wallafa rahotanni daga wakilan BBC a fadin duniya har zuwa yammacin yau Alhamis.