Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

NATO ta yi shuri da roƙon Ukraine

Wannan shafi na kawo muku abubuwan da ke faruwa a sassan duniya kai-tsaye, musamman game da yaƙin Ukraine.

Rahoto kai-tsaye

Umar Mikail and Imam Saleh

  1. Bissalam

    To jama'a a nan za mu muku sallama, sai kuma gobe idan Allah ya kai mu.

    Imam Saleh ke cewa mu kwana lafiya daga nan sashen Hausa na BBC.

  2. Rasha ta toshe shafin Facebook

    Kasar Rasha ta toshe shafin Facebook, yayin da ake ci gaba da yaƙi a Ukraine

    Hukumar kula da harkokin sadarwa ta kasar ta ce ta toshe shafin Facebook na a matsayin martani ga matakin da ya ɗauka na hana wasu kafofin watsa labaran ƙasar amfani da shi.

    Dazun nan ne Rashan ta toshe shafukan wasu jaridu da dama, ciki har da BBC.

  3. Yadda ƙasashen Afrika suka kaɗa ƙuri'ar ƙin amincewa da mamayar Ukraine da Rasha ke yi

  4. NATO ta yi shuri da roƙon Ukraine

    Kungiyar tsaro ta NATO ta ki amincewa da rokon da Ukraine ta gabatar mata na sanya dokar hana shawagin jiragen sama a wasu sassan kasar domin kare jama'a daga hare-haren sama na Rasha.

    Ƙungiyar na cewa hakan ka iya sa yakin ya fantsama a Turai.

    Bayan ganawa da ministocin harkokin waje na kasashen Turai, babban Sakataren kungiyar ta NATO Jens Stoltenberg, ya ce an cimma matsaya cewa jiragen saman yaki na kungiyar da dakarunta ba za su yi aiki a yanki ko sararin samaniyar Ukraine ba.

    Mista Stoltenberg ya yi kira ga Rasha da ta dakatar da hare-haren da take kaiwa

    Ya ce ''tun watanni da dama, muka yi gargadi cewa Shugaba Putin na da niyyar mamaye Ukraine. Abin da ya sa kenan kawayen NATO suka yi ta kai gauro suna kai mari domin samar da maslahar diflomsasiyya''.

    A hakan kuma muka yi gargadin cewa Rasha za ta dandana kudarta a kan sabbin hare-haren da take kai wa Ukraine.

    Kasashen NATO da dama na ta aika wa Ukraine makamai, sannan kuma kungiyar na karfafa tsaronta a baryar gabas.

  5. An kusa cimma yarjejeniya kan shirin Nukiliyar Iran

    Babban jami'in diflomasiyya na Birtaniya a tattaunawar Vienna ta farfado da yarjejeniyar nukiliyar Iran ta 2015, ta ce ana dab da cimma yarjejeniya.

    Stephanie al-Qaq ta ce masu shiga tsakani za su koma kasashensu su yi wa ministocinsu bayani, kan matsayin da ake ciki, amma kuma za su koma nan ba da jimawa ba.

    A cikin kwanakin nan, yawancin wadanda ke cikin yarjejeniyar suna ta cewa, kusan an riga an kammala ta gaba daya, amma kuma suna gargadin cewa, kada a yi riga-mallam masallaci, har sai an tabbatar an yarda da kafitanin sharuddan yarjejeniyar.

    Manufar tattaunawar, wadda take a zagaye na takwas a yanzu, ita ce, a shawo kan Amurka ta sake komawa cikin yarjejeniyar, ita kuwa Iran ta koma ta yarda da rage inganta sinadarin Uranium da take yi, kar ta kai ga kera makaman kare-dangi.

  6. 'Yan gudun hijira daga Ukraine na ci gaba da kwarara zuwa makwabtan kasashe.

    'Yan gudun hijira daga Ukraine na ci gaba da kwarara zuwa makwabtan kasashe.

    Fiye da mutane miliyan daya ne suka fice daga Ukraine kuma fiye da rabinsu sun tsallaka Poland ne.

    Hukumomi a Polland sun ce tun bayan da Rasha ta kutsa Ukraine mutane fiye da dubu 670 ne suka tsallaka kasar daga Ukraine.

    Jami'ai da kuma masu aikin sakai na ta bayar da taimakon abinci da na lafiya. Hungary ta bude iyakokinta ga 'yan gudun hijira daga Ukraine inda take ba su damar shiga jiragen kasa kyauta domin zuwa wuraren da suke kokarin yada zango.

  7. 'Toshe BBC a Rasha ba zai ceci Putin daga jin gaskiya ba'

    Ministan tsaron Birtaniya ya ce toshe BBC a Rasha da mahukuntan ƙasar suka yi ba zai ceci Putin daga jin gaskiya ba.

    Ben Wallace ya faɗa wa manema labarai a Copenhagen cewa ''Wannan matakin na Rasha kuskure ne, ba zai hana faɗa wa Putin gaskiya ba, mataki ne da ya saɓa wa ƴancin ɗan adam''.

    A Kwanakin baya ne dai ita ma Birtaniya ta toshe wasu kafofin watsa labaran Rasha a ƙasarta, kamar yadda sauran ƙasashen Turai suka yi.

  8. An zargi sojojin Rasha da yin dabaru irin wadanda aka gani a Syria

    Mataimakin magajin garin Mariupol mai tashar jirgin ruwa, wanda dakarun Rasha suka yi wa kawanya ya zargi sojin na Rasha da yin dabaru irin wadanda aka gani a birnin Aleppo na Syria.

    Sergei Orlov ya gaya wa BBC cewa sojojin Rasha na son birnin ya mika wuya domin su jefa jama’a cikin mawuyacin hali.

    Ya ce dabarun sun hada da ruwan makamai ta sama ba kakkautawa , da bata gine-gine, wadanda suka hada da makarantu da asibitoci.

    Birnin na Mariupol ya shiga kwana na uku ke nan ba wutar lantarki ba ruwa.

    A ‘yan mintunan da suka gabata Sakatare janar na NATO, Jens Stoltenberg, ya ce ƙawancen zai karfafa kariyarsa ta kasa da sama da kuma ta ruwa.

    Ya ce wannan shi ne kutsen soji mafi muni a Turai a tsawon gomman shekaru, inda birane ke karkashin mamaya, ake ruwan wuta a kan makarantu, asibitoci da gidajen jama'a.

    Sannan ana yin abubuwan da ba su dace ba a kusa da tashar nukiliya a jiya da dare, inda aka kashe farar hula da yawa ko jikkata su.

    Fadan da ake gwabzawa kuma ya yadu zuwa wajen wani birnin na kudancin kasar ta Ukraine, Mykolaiv.

  9. Kame tashar nukiliya mafi girma ta Ukraine bai sa an saki burbushin makaman kare dangi ba

    Shugaban hukumar nukiliya ta duniya Rafael Grossi, ya ce kame tashar nukiliya mafi girma ta Ukraine da sojojin Rasha suka yi, hakan bai sa an saki burbushin makaman kare dangi ba.

    Wuta ta tashi a tashar da ke Zaporizhzhia a lokacin ruwan makamai da sojin Rashan suka yi kafin su karbe iko da ita.

  10. Labarai da dumi-dumi, Mutane da dama aka kashe a harin da Rasha ta kai kan tashar nukilya - Ukraine

    Mutane da dama aka kashe ko jikkata a gobarar da ta tashi bayan harin Rasha a kan tashar nukiliya ta Ukraine, kamar yadda ma'aikatar harkokin wajen ƙasar ta bayyana.

    Ma'aikata na ci gaba da lura da tashar ta Zaporizhzhia don tabbatar da cewa tana aiki yadda ya kamata ba tare da tiriri mai guba ya tashi ba, a cewar ma'aikatar cikin wata sanarwa a Facebook.

    Kamfanin labarai na AP ya ruwaito cewa an kashe sojojin Ukraine uku da jikkata biyu a harin da Rasha ta kai cikin dare.

    Idan har na'urorin da ke sanyaya tashar suka samu matsala za a fuskanci bala'i mai girman gaske na yaɗuwar tiriri mai guba na radiation.

    "Dubban mutane - ciki har da farar hula da suka gaza guduwa daga yankin saboda luguden wuta - za su shiga tasku," in ji sanarwar.

    Shugaban Ukraine ya ce bala'in fashewar nukilya a Zaporizhzhia zai zarta na baya da aka taɓa gani sau 10 idan ya faru. .

  11. Ɗan bindiga ya kashe mutum 30 suna sallar Juma'a a Pakistan

    Mutum aƙalla 30 ne suka mutu sannan wasu 80 suka ji raunuka sakamakon wani harin ƙunar-bakin-wake a kan masu sallar Juma'a a masallacin 'yan Shia da ke Peshawar da ke arewacin Pakistan.

    Wani da ya gane wa idonsa faruwar lamarin ya ga maharin kafin ya buɗe wa masallatan wuta, yana harbinsu ɗaya bayan ɗaya, kamar yadda kamfanin labarai na AFP ya ruwaito.

    "Daga nan kuma sai ya tarwatsa kan sa," in ji shaidar mai suna Ali Asghar.

    Muhammad Ali Saif, mai magana da yawun gwamnatin yankin, ya faɗa wa AFP cewa mutum fiye da 30 aka kashe sannan aka jikkata wasu 80, yana bayyana shi da "harin ƙunar-baƙin-wake".

    Wakilin AFP ya ga gawarwakin mutane warwatse a wurin da kuma 'yan sanda suna rarrashin 'yan uwansu.

  12. Shugabancin APC: Idan Buhari ya ce na janye zan janye - Sanata Sani Musa

    Ɗaya daga cikin masu neman takarar shugabancin jam’iyyar APC mai mulki a Nijeriya Sanata Sani Musa ya ce har yanzu yana nan yana ci gaba da takararsa "har sai Shugaba Buhari ya umarce ni na janye wa wani".

    Sanatan mai wakiltar Mazaɓar Neja ta Gabas ya shaida wa BBC cewa yana da ƙwarin gwiwar APC za ta cimma matsaya kafin babban taronsu na ƙasa da za a yi ranar 26 ga watan Maris.

    "Idan ya [Buhari] ce na janye wa Abdullahi Adamu ko wani shikenan sai na janye saboda shi ne shugabanmu," in ji sanatan.

    Latsa hoton ƙasa ku saurari hirar:

  13. BBC ta biya ni albashi kamar yadda ya kamata - Mamman Barmou

    A yayin da BBC Hausa ke cika shekara 65 da kafuwa ranar 13 ga watan Maris, sashen zai rika kawo muku hirarraki da tsofaffin ma'aikatansa.

    Mun fara fitar da jerin hirarrakin ranar Talata 1 ga watan Maris na shekarar 2022.

    Tsoffafin ma'aikatan sun yi bayanai ne a kan yadda suka samu aikin BBC da yadda ya kasance musu, da rayuwa bayan sun bar aikin da dai wasu abubuwan da suka shafe su.

    A yau za mu gabatar muku da hira ne da tsohon wakilinmu na Jamhuriyar Nijar, Mammam Barmou.

  14. Harin Rasha a Chernihiv ya kashe mutum 47, in ji Ukraine

    Mutum 47 ne suka mutu a hari ta sama da sojojin Rasha suka kai a birnin Chernihiv ranar Alhamis, kamar yadda jami'ai a yankin suka ce.

    Sai da masu aikin ceto suka dakatar da aiki ranar Alhamis sakamakon muggan hari da aka dinga kaiwa, kamar yadda hukumar agajin gaggawa ta kasar ta ce.

    Kusan jumillar fararen hula 148 ne suka rasa rayukansu tun da aka fara rikici a yankin, inji jami'an kasar.

    Garin Chernihiv mai mutum aƙalla 300,000 da ke arewacin kasar, ya yi iyaka da Rasha da kuma Belarus.

  15. Sojojin Sweden za su fice daga Mali kafin lokacin da aka tsara

    Kasar Sweden ta ce za ta janye sojojinta kafin lokacin da aka tsara saboda kudirin Majalisar Ɗinkin Duniya (MDD) kan tabbatar da zaman lafiya a Mali, kamar yadda kamfanin dillacin labarai na Reuters ta rawaito.

    Jami'an sojin Sweden sun sanar a ranar Alhamis cewa sojinta 220 za su tattara yanasu-yanasu su bar Mali a watan Janairun 2023, in ji Reuters.

    Babu wasu dalilai da aka bayyana kan janyewar sojojin, amma sojojin sun ce kawo sojojin Rasha ƙasar Mali na daga cikin dalilin ficewarsu.

    Sojoijn Sweden sun ce al'amura sun sauya a kasar a baya-bayan nan.

    Mai magana da yawun MDD ya ce sojojin Sweden sun taka muhimmiyar rawa a Mali, amma duk da haka suna da damar zaɓar wasu hanyoyi don tabbatar da zaman lafiya.

  16. Yau Juma'a ce 1 ga watan Sha'aban a Najeriya

    Fadar Sarkin Musulmi a Najeriya Alhaji Sa'ad Abubakar III ta ce yau Juma'a ce 1 ga watan Sha'aban na shekarar Hijira ta 1443 a kalandar Musulunci.

    Matakin ya biyo bayan ganin sabon wata da aka yi a yammacin jiya Alhamis bayan watan Rajab ya cika kwana 29. A kalandar Musulunci, kowane wata yana da kwana 29 amma idan ba a ga sabon wata ba za a ƙara kwana ɗaya zuwa 30.

    Hakan na nufin saura wata ɗaya cif kafin fara watan Azumin Ramadana mai tsarki. Al'ummar Musulmi kan wuni tun daga assalatu zuwa almuru ba tare da sun ci ko shan wani abu ba a Ramadana.

    Da zarar an kammala Azumin Ramadana kuma sai bikin Ƙaramar Sallah ya biyo baya, wanda ake kira Eid al-Fitr.

  17. Senegal ta ce shelar neman sojojin sa-kai da Ukraine ta yi ya saɓa dokokinta

    Ma'aikatar harkokin waje ta ƙasar Senegal ta ce kiran da ƙasar Ukraine ta yi na neman tallafin sojojin sa-kai a yaƙin da take yi da Rasha ya saɓa wa dokokin Senegal ɗin.

    Wata sanarwa daga ma'aikatar ta ce ɗaukar sojojin haya da na sa-kai da ma sauran mayaƙa ya saɓa wa dokokin ƙasar.

    Hukumomi sun kira jekadan Ukraine a Senegal, Yurii Pyvovarov, don ya yi musu ƙarin bayani game da shelar da suka yi a Facebook. Bayan an tabbatar da ingancin shelar, an nemi jekadan ya goge sanarwar.

    Sai dai ba a bayyana ba ko hukumomin Senegal za su ɗauki wani ƙarin mataki.

    Senegal na cikin ƙasashen Afirka 17 da suka ƙaurace wa kaɗa ƙuri'a don yin Allah wadai da hare-haren Rasha a Babban Zauren Majalisar Ɗinkin Duniya (MDD).

  18. 'Yan majalisar Amurka na son a hana Rasha cinikin man fetur

    Sanatocin Amurka na bangarorin da ke adawa da juna sun gabatar da kudirin doka da zai haramta wa Rasha fitar da man fetur a yunkurin kasashen Yamma na durkusar da tattalin arzikinta kan mamayar Ukraine.

    Idan majalisa ta amince da kudurin, sai Fadar White House ta yarda da shi kafin ya zama doka.

    Sai dai Shugaba Biden na kaffa-kaffa kan karin takunkuman da ka iya haifar da matsin tattalin arziki a duniya baki ɗaya.

    Ita ma Canada na kara matsawa da wasu dokoki masu tsauri, inda ta dakatar da jiragen da ke daukar 'yan asalin Rasha daga filin jirgin Yellowknife da ke arewacin ƙasar.

  19. Rasha ta toshe shafin BBC da wasu kafofin yaɗa labarai a ƙasar

    Hukumar da ke kula da kafofin yaɗa labarai a Rasha ta hana shiga shafukan wasu kafofin labarai na ƙasashen Yamma, ciki har da BBC bayan masu shigar da ƙara sun yi mata ƙorafi.

    Hukumar Roskomnadzor ta ce sauran shafukan labaran da ta toshe sun ƙunshi Deutsche Welle ta Jamus, da Meduza, da kuma na gidan rediyo mai yaɗa shiri cikin Rashanci wanda Amurka ke kula da shi mai suna Radio Liberty.

    Tun a farkon mako ƙungiyar Tarayyar Turai ta toshe wasu kafafen yaɗa labarai na Rasha daga ƙasashe mambobin ƙungiyar, ciki har da gidan talabijin na RT da Sputnik.

  20. Kashin farko na 'yan Najeriya daga Ukraine ya sauka a Abuja

    Kashin farko na 'yan Najeriya da suka tsere wa yakin da ake yi a Ukraine ya isa filin jirgin saman Abuja, babban birnin kasar ranar Juma'a da safe.

    Shugaban kwamitin harkokin waje a Majalisar Wakilan Najeriya Yusuf Buba ya shaida wa BBC dalibai 451 ne suka iso kasar.

    Yana cikin jami'an gwamnatin kasar da suka je Bucharest, babban birnin Romania domin taho da 'yan kasar ta Najeriya.

    Ita ma shugabar hukumar da ke kula da 'yan kasar mazauna kasashen waje Abike Dabiri Erewa ta tabbatar da isar 'yan Najeriya gida a cikin jirgin saman Max Air samfurin VM602.