Bis-salam
To jama'a, a nan muka zo ƙarshen kawo muku labaran duniya kai tsaye, sai ku biyo mu gobe idan Allah ya kai mu don ci gaba.
Imam Saleh ke cewa mu wayi gari lafiya.
Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Wannan shafi na kawo muku abubuwan da ke faruwa a sassan duniya kai-tsaye, musamman game da yaƙin Ukraine.
Awwal Ahmad Janyau and Imam Saleh
To jama'a, a nan muka zo ƙarshen kawo muku labaran duniya kai tsaye, sai ku biyo mu gobe idan Allah ya kai mu don ci gaba.
Imam Saleh ke cewa mu wayi gari lafiya.
Mutum 59 ne suka mutu a Najeriya a makonnin shidan farko na shekarar 2022 sakamakon zazzabin cutar Lassa, a cewar hukumar dakile cututtutuka masu yaduwa ta NCDC.
Hukumar ta ce mutum 59 ne suka mutu daga cikin 358 da suka kamu da cutar a cikin wannan lokaci.
Baya da wannan adadi kuma ma'aikatan lafiya 27 ne suka rasu bayan kamuwarsu da cutar.
Wadannan mace-mace an same su ne daga kananan hukumomi 65 daga fadin jihohin Najeriya 19.
Kashi 70 cikin 100 na masu cutar sun fito ne daga jihohin Ondo mai 115 da Edo mai 83 da Bauchi 64.
Wasu na bayyana cutar Lassa da 'yar uwar Ebola kuma ta kan zama annoba a wasu kasashen yammacin Afirkan.
Idan mutum ya kamu da cutar yana iya yada wa wasu ta hanyar gumin jikinsa ko duk wani abu mai ruwa daga jikinsa.
Ana kamuwa da cutar ne idan bera ya hau kan abinci ko ya yi fitsari akai sannan aka ci abincin.
Wasu ƴan Najeriya sun yi zanga-zangar lumana a gaban ofishin jakadancin Rasha da ke Abuja, babban birnin kasar, domin kira da a kawo karshen yaƙin da ke gudana tsakanin kasar ta Rasha da maƙwabciyarta Ukraine.
Najeriyar dai na da mutane da dama da ke zaune a kasashen biyu inda rikicin ya barke, wadanda suka hada da dalibai, da kuma masu neman halaliya.
Kasashe da dama ne ke nuna damuwa kan samamen da Rashar ke yi wa Ukraine, inda ake samun zanga-zangar neman samun zaman lafiya a birane daban-daban na duniya.
Masu zanga-zangar sun yi ta sowa tare da ambaton "Muna so a samu zaman lafiya a Ukraine," ɗauke da kwalaye a hannayensu masu rubuce-rubucen neman Shugaba Putin na Rasha ya dakatar da yaƙin.
Sannan sun nuna damuwarsu kan halin da ƴan Najeriyar ke ciki a can Ukraine ɗin.
Hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce ƴan gudun hijira sama da miliyan daya ne zuwa yanzu suka tsere zuwa maƙwabtan kasashe, sakamakon mamayar da Rasha ta yi wa Ukraine, a makon da ya gabata.
Da take tattaunawa da BBC mai magana da yawun hukumar, Shabia Mantoo, ta bayar da bayanai inda ta ce alƙaluman da muke gani na ta tayar da hankali, zan iya gaya ma abin da na samu daga abokanan aikina ne kawai, inda yanzu muna ganin rabin miliyan, waɗanda suka tsere daga Ukraine zuwa maƙwabtan ƙasashe, a cikin kwanaki biyar da suka gabata kawai.
Poland ta ce a yanzu akwai 'yan Ukraine 250,000, yawancinsu mata da yara da ake duba takardunsu a kan iyaka; kuma yawanci ana barinsu su shiga, har ma wadanda ba a tantance takardunsu ba.
Maƙwabtan Ukraine ɗin na bangaren yamma sun bar iyakokinsu a bude ga 'yan gudun hijirar.
Kwamishinar kula da harkokin cikin gida ta Tarayyar Turai Ylva Johansson, ta ce akwai bukatar Tarayyar ta shirya karbar karin wasu miliyoyin 'yan gudun hijirar.
Majalisar Dinkin Duniya ta ce, akwai mutane da dama da fadan ya raba su da gidajensu a cikin kasar ta Ukraine ma.
Moscow ta yi gargaɗi game da kai muggan makamai Ukraine
Ma'aikatar harkokin wajen Rasha ta ce waɗanda ke ba wa Ukraine munanan makamai don su yaƙi Rasha su kwana da sanin cewa suna kai su ne suna baro su.
Ta kara da cewa matakin da Tarayyar Turai ta dauka na kai wa Ukraine ɗin makamai wani abu ne da za ta ɗauki tsatstsauran matakai a kai.
Shugaban Turkiyya, Recep Tayyip Erdogan ya bayyana mamayar da Rasha ta yi wa Ukraine a matsayin abin da ba za a amince da shi ba.
Ya ce yana martaba kasar Ukraine, amma kuma ya kara da cewa ba zai juya bayansa a kan kowacce daga cikin kasashen biyu ba.
Mista Erdogan, wanda ya kulla wata sabuwar alaka ta kut da kut da Shugaba Putin a 'yan shekarun nan, ya kuma ce zai iya rage yawan zirga-zirgar jiragen ruwan Rasha da ke bi ta ruwan Turkiyya.
Can kuma a gefe daya Ministan Harkokin Wajen Isra'ila, Yair Lapid, ya ce kasarsa za ta kada kuri'ar goyon bayan kudurin Majalisar Dinkin Duniya na yin Alla-wadarai da mamayar da Rasha ta yi wa Ukraine.
Ministan ya sanar da hakan ne, 'yan kwanaki bayan da kasar tasa, Isra'ila, ta ki yarda ta goyi bayan irin wannan kuduri a kwamitin tsaro na Majalisar duk da matsin lambar babbar kawarta, Amurka.
Gwamnatin jihar Kaduna da ke arewa maso yammacin Najeriya ta yi kira ga ƴan jihar su sanya ido sosai kan abubuwan fashewa da ƴan ta'adda ke ajiyewa a wuraren taruwar jama'a.
Cikin wata sanarwar ma'aikatar tsaro ta jihar, gwamnatin ta ce hakan ya biyo bayan binciken da hukumomin tsaro ke ci gaba da yi a kan zargin cewa ƴan ta’addan na neman cutar da jama'a ta hanyar binnewa, da kuma ajiye abubuwan fashewar a makarantu, da asibitoci, da otal-otal, da gidajen cin abinci, da wuraren shakatawa, da wuraren ibada.
Sanarwar ta ƙara da cewa hukumomin tsaro suna aiki don tabbatar da cewa babu wanda aka cutar a cikin jama'a.
Ta kuma yi kira ga jama'a su bayar da rahoton duk wani mutum ko wani abu da aka gani ba a yarda da shi ba.
Attajirin nan na Rasha, Roman Abramovich ya ce ya amince da bukatar Ukraine na neman goyon bayansa wajen cimma matsaya kan yaki a Ukraine.
Mai magana da yawun mai kungiyar kwallon kafa ta Chelsea ta ce yana kokarin taimakawa tun farkon da aka tuntube shi.
Ta ce wannan shigar ta hana Mista Abramovich- na hannun damar Shugaba Vladimir Putin fiye da shekaru ashirin- kan halin da ake ciki a Ukraine.
Wani babban dan kasuwar kasar Rasha- Oleg Deripaska - ya fitar da wata sanarwa da ke kira a kawo karshen jari-hujja a Rasha.
Hakan ya biyo bayan kalaman nasa a makon jiya, inda ya yi kira da a gaggauta tattaunawa kan zaman lafiya; yayin da wani attajirin Rasha, Mikhail Fridman, ya bukaci da a kawo karshen zubda jini.
Yayin da ake tsaka da kai ruwa rana tsakanin Rasha da Ukraine, Ukraine ɗin ta cike takardun neman izinin shiga ƙungiyar tarayyar turai wato EU a hukumance.
Babban jami'in ofishin shugaban Ukraine ɗin Andrii Sybih, ya ce tuni shugaba Voladymyr Zelensky ya rattaba hannu a takardun, kuma yanzu haka an kama hanyar tafiya da su zuwa shalkwatar EU da ke Brussels.
Akwai buƙatar dukkan ƙasashen da ke cikin ƙungiyar su amince da buƙatar Ukraine kafin ta zama mamba, sannan hakan na iya ɗaukar shekaru da dama.
Kakakin fadar gwamnatin Rasha, Dmitry Peskov, ya ce umarnin da Shugaba Putin ya bayar ranar Lahadi ga dakarun ƙasar na su kasance cikin shirin amfani da makaman ƙasar ciki har da na Nukiliya martani ne ga Sakatariyar harkokin Wajen Birtaniya Liz Truss.
Mista Peskov ya ce akwai kalamai na rashin kamun kai waɗanda ba za a lamunta ba, da ke fitowa daga bakin wakilai daban-daban na ƙasashen Turai game da fito-na-fito tsakanin NATO da Rasha, ciki har da wanda ministar harkokin wajen Birtaniyar ta yi.
Ministan tsaro na Birtaniyar, Ben Wallace, ya ce Birtaniya ta kalli matsayin na Rasha a kan makaman kare-dangi, kuma ta lura cewa babu wani sauyi na a zo a gani a kai.
Ya ce Mista Putin, yana son ya nuna karfin Rasha ne, ta hanyar ambato shirin ko ta kwana na amfani da makaman nukiliyar na kasarsa.
Rahotanni daga Ukriane na cewa wani harin makamin roka da Rasha ta kai ya kashe mutane 11 a Kharkiv, in ji jami'an yankin
Shugaban hukumar kula da yankin na Kharkiv, Oleg Synegubov, ya ce akalla mutane 11 ne suka mutu, yayin da wasu da dama suka jikkata, yayin da wasu makaman roka da Rasha ta harba a gabashin kasar ta Ukraine suka sauka a wasu unguwannin jama'a..
Kharkiv, wanda shine birni na biyu mafi girma a kasar Ukraine, ya zama ɗaya daga cikin manyan fagagen daga da Moscow ta kaddamar da mamaya.
Rahotanni daga jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya sun ce mayaƙan ISWAP sun kashe aƙalla mutum 13 a ƙauyuka da dama na jihar Borno.
An kai hare-haren ne a ƙauyuka huɗu, cikin kwanaki biyu.
Wasu mazauna ƙauyukan sun shaida wa wasu jaridun Najeriya cewa mayaƙan sun kuma sace mutane da dama.
Shugaban Rasha Vladmir Putin ya caccaki ƙasashen Turai wadanda ya kira a matsayin ''Taron maƙaryata''.
Yayin wata ganawa da firaiministan Rashar Mikhail Mishustin da wasu manyan muƙarrabansa biyo bayan jerin takunkuman da ƙasashen EU suka ƙaƙaba wa ƙasarsa sakamakon mamayar Ukraine, shugaban ya ce burinsa na nakasta Rasha ba zai cika ba.
Fadar mulki ta Kremlin ta rawaito Putin na cewa ''Ni da Mishustin mun tattauna takunkuman da ''Waɗannan taron maƙaryatan suka ƙaƙabawa ƙasarmu, za mu rayu da su, kuma burinsu ba zai cika ba''.
Yariman Saudiyya mai jiran gado Muhammad Bin Salman mataimakin Firaminista kuma ministan tsaro ya zanta da shugaban Najeiriya Muhammadu Buhari ta wayar tarho.
A zantawar, sun tattauna kan dangantakar ƙasashen biyu tare da diba fanonin da za su ƙara inganta alaƙa tsakanin Najeriya da kuma gwamnatin Saudiyya, kamar yadda kamfanin dillacin labaran Saudiyya ya ruwaito.
An tillastawa jiragen Rasha yin dogon zango ta hanyar ratsawa yankin Kaliningrad da ke tekun Baltic yayin da kasashen Tarayyar Turai suka rufe sararin samaniyarsu ga jiragen ƙasar.
Kaliningrad, sarari ne mai fadin gaske mallakin Rasha, yana da tazarar kilomita 300 daga yammacin yankin, kuma yana tsakanin Baltic da ƙasashen Lithuania da Poland na Tarayyar Turai
Maimakon bin hanya kai tsaye ta Latvia da Lithuania, an tilasta ma jiragen Rasha bi hanyar yankin arewaci kusa da St Peterburg da kuma tekun Baltic.
Canada ce kasa ta farko kafin kungiyar kasashen Turai da Birtaniya da suka hana jiragen Rasha ratsawa sararin samaniyarsu.
Rasha ta sanar da haramtawa jirage daga ƙasashe 36 shiga ƙasarta da suka ƙunshi Birtaniya da Jamus da Spain da Italiya da Canada.
Wannan na zuwa bayan matakin da Tarayyar Turai ta ɗauka na haramta wa jiragenta ratsawa sararin samaniyar mambobin ƙungiyar
Birtaniya kuma ta haramta wa Aeroflot sauka cikin Birtaniya, wanda ya sa Rasha ta mayar da martani na haramta wa jiragen Birtaniya shiga ƙasarta.
Ma'aikar tsaro n Ukraine ta yi ikirarin cewa sama da sojojin Rasha 5,000 suka mutu cikin kwana hudu da ake gwabza fada a Ukraine.
A wata sanarwa da aka wallafa a shafin Facebook, jami'an Ukraine sun ce sojojinsu sun halaka kusan sojojin Rasha 5,300 tare da da iƙirarin tarwatsa tankuna 191 da jirgin yaki 29 da masu saukan angulu 29 da kuma motoci masu sulke 816.
BBC ba ta tabbatar da wadannan ikirarin ba, kodayake ma'aikatar tsaron Birtaniya ta yi amannar cewa dakarun Rasha sun fi shan wahala a farkon soma yakin.
Ma'aikatar tsaron Rasha ta tabbatar da wadannan iƙirarin ranar Lahadi tana cewa ta rasa sojojinta, amma ba tare da yin cikakken bayani game da adadinsu ba.
Kawo yanzu, masu sa ido na Majalisar Dinkin Duniya sun tabbatar da mutuwar akalla mutum 94 a kwanakin farko na yakin.
Sun ce harin ya haifar da "mummunan sakamako na ayyukan jin-kai" kuma adadin wadanda suka jikkata na iya karuwa sosai.
Kusan mutum 30 sun mutu yayin da 50 suka jikkata bayan mota kirar bas guda biyu sun yi taho mu gama a Chad, kamar yadda ma'aikatar sufuri ta ƙasar ta tabbatar wa kamfanin dillacin labaran Faransa
Lamarin ya faru ne cikin dare a ranar Lahadi lokacin da motar fasinja daga N'Djamena ta yi taho mu gama da wata motar da ta fito daga Abeche, gari na uku mafi girma a Chadi, kamar yadda ma'aikatar sufurin ta bayyana.
Fetur ya ƙara tsada sakamakon tsadar farashin mai a duniya da mamayar Rasha da Ukraine ya haddasa.
Farashin fetur ya cira zuwa fam 1.51 kan lita a ranar Lahadi, kamar yadda kamfanin RAC ya bayyana, kuma gas ya kai fam 1.55 duk lita ɗaya.
Rasha ita ce ta biyu da ta fi fitar da ɗanyen mai a duniya, amma duk da kashi shida ne kawai na man Rasha da Birtaniya ke shigowa da shi amma akwai fargabar takunkuman da aka ƙaƙabawa Rasha zai shafi kasuwar mai a duniya.
Babban bankin Rasha ya bayar da umarnin dakatar da tallata hannayen jarin ƙasashen waje da kuma waɗanda ke son sayar da hannun jarinsu na Rasha.
Wannan na zuwa a yayin da darajar kuɗin Rasha na rubble a kasuwannin nahiyar Asiya ta faɗi da kashi uku bisa huɗu
Farashin ɗanyen mai ya yi sama da kusan kashi huɗu cikin 100.
Ƙasashen yammaci sun ƙaƙaba wa Rasha sabbin takunkumai a matsayin martani ga da yaƙin da ta ƙaddamar a Ukraine