Mu kwana lafiya
Mun zo ƙarshen rahotanni a wannan shafi.
Sai kuma gobe idan Allah ya kai mu. Umar Mikail ne yake muku fatan mu kwana lafiya.
Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Wannan shafi na kawo muku abubuwan da ke faruwa a sassan duniya kai-tsaye, musamman a Najeriya da Nijar maƙotansu.
Awwal Ahmad Janyau
Mun zo ƙarshen rahotanni a wannan shafi.
Sai kuma gobe idan Allah ya kai mu. Umar Mikail ne yake muku fatan mu kwana lafiya.
Kungiyar Tarayyar Turai (EU) ta sanar da sanya jerin takunkumai kan wasu daidiaikun shugabannin Rasha da kamfanoni saboda yarda da ƙasar ta yi da 'yancin kan wasu yankunan Ukraine.
Mutanen sun hada da 'yn majalisar wakilai na Rashar wadanda suka jefa kuri'ar amincewa da yankunan.
Takunkuman sun hada da bankunan Rasha da kuma damar da Rasha ke da ita ta shiga kasuwar Taryyar Turai.
EU ta ce tana duba yiwuwar daukar karin mataki a kan Belarus wadda ke bayar da hadin kai ga Rasha.
Wata Babbar Kotun Tarayya a Abujan Najeriya ta ba wa hukumar yaƙi da miyagun ƙwayoyi NDLEA damar ci gaba da tsare ɗan sanda DCP Abba Kyari bayan ta kama shi kan zargin safarar hodar ibilis wato koken.
Mai Shari'a Zainab Dimka Abubakar ce ta ba da umarnin bayan wata buƙata da hukumar ta shigar da zimmar neman ci gaba da tsare DCP Kyari da wasu mutum shida tsawon mako biyu.
Waɗanda za a ci gaba da tsarewar su ne: DCP Abba Kyari, ACP Sunday J. Ubia, ASP James Bawa, Sufeto Simon Agirigba, Sufeto John Nuhu; Chibunna Patrick Umeibe, Emeka Alfonsus Ezenwanne.
Sanarwar da NDLEA ta fitar a yau Talata ta ce wanda ake zargi da safarar koken ɗin na 6 da na 7 (Umeibe da Ezenwanne) sun amsa laifinsu cewa sun shigar da ita Najeriya ne daga Ethiopia.
Ta ƙara da cewa su kuma waɗanda ake zargi na 1 zuwa na 5 ((Kyari, Ubia, Bawa, Agirigba, Nuhu) 'yan sanda ne da suka kama na 6 da na 7 kuma suka kai su NDLEA don yin bincike.
"Saboda binciken da NDLEA ta gudanar ya nuna cewa na 1 zuwa na 5 sun ci amanar aiki kuma sun shiga an dama da su wajen safarar miyagun ƙwayoyi da kuma saka hannu wajen lalata hujja a kan masu laifi ta mua'amala da koken," a cewar sanarwar.
Shugaban Amurka Joe Biden ya fara jawabin da ake yaɗawa kai-tsaye yanzu haka.
Shugaban ya tambaya cewa "wane ne ya ba shi [Putin] damar ayyana yankunan maƙota a matsayin ƙasashe?".
Wannan "karya dokokimn ƙasa da ƙasa ne ƙarara," a cewarsa.
Jamus ta dakatar da aikin wani bututun iskar gas da Rasha ke gina mata bayan Shugaba Putin ya ba da umarnin tura sojoji cikin Ukraine.
A jiya Litinin ne shugban na Rasha ya amince da 'yancin kai na wasu yankunan Ukraine bayan sun ayyana ɓallewa daga ƙasar sannan ya umarci dakaru su shiga yankunan.
Ƙasashen Yamma na kallon yunƙurin a matsayin wani shiri na afka wa Ukraine.
A martaninta, Jamus ta tsayar da aikin bututun na Nord Stream 2 sannan wasu ƙasashen Turan sun saka mata takunkumi.
Aikin bututun na samun goyon bayan Jamus duk da adawar da ƙasashen Amurka da Birtaniya da Ukraine ke nunawa.
Za a kashe yuro biliyan 10 a aikin wanda Rasha da sauran kamfanonin makamashi na Turai za suke ɗaukar nauyi.
Babbar ƙungiyar ɗalibai a Najeriya National Association of Nigeria Students ta ce za ta fara gudanar da zanga-zangar ƙasa baki ɗaya idan malaman jami'a ba su sasanta da gwamnatin ƙasar ba don janye yajin aikin da suka shiga na wata ɗaya.
Mataimakin Shugaban NANS Yazeed Tanko Muhammad ya faɗa wa BBC Hausa cewa za su rufe dukkan titunan da ke shiga birnin Abuja daga ranar Litinin mai zuwa idan ba a janye yajin aikin ba.
"Zanga-zanga ce da idan muka fara ta ba za mu daina ba har sai malamai sun dawo bakin aiki, har sai mun samu mafita," in ji shi.
"Muna kira ga shugaban ƙasa da shi ma ya nuna mana goyon baya ya zauna a gida, kar ya je aiki ranar Litinin ɗin."
A farkon makon da ya gabata ne ƙungiyar ASUU ta malaman jami'ar ta fara yajin aikin gargaɗi na wata ɗaya bayan ta zargi gwamnatin tarayya da rashin mutunta yarjejeniyar da suka ƙulla tun a 2009 da kuma sabuwa a 2020.
Rundunar sojan Najeriya ta ce wasu iyalan mayaƙan ƙungiyar Boko Haram 41 sun miƙa wuya ga dakarunta a jiya Litinin.
Wata sanarwa da rundunar ta fitar a yau Talata ta ce mutanen sun ƙunshi maza 11 da mata 22 da yara takwas.
Ta ƙara da cewa dakarunta na Bataliya ta 144 ne da ke garin Dissa na Jihar Borno suka karɓe su.
Hukumomi a Najeriya sun ce wata fashewa ta yi sanadin ajalin jami’ai huɗu a jihar Neja da ke tsakiyar ƙasar.
Motar jami’an tsaro na Civil Defence ta taka nakiya ne a lokaci suke sintiri a yankin Galadiman Kogo a ranar Litinin.
Maia magana da yawun rundunar Odumosu Olusola ya ce direban motan ne kawai ya tsira, amma kuma yana cikin mawuyacin hali.
Mayaƙa da ake tunanin ƴan Boko Haram ne sun sha kai hare-hare a yankin.
Mazauna yankin sun ce an dasa nakiyar ne da nufin hana jami’an tsaro shiga yankin da ke fuskantar hare-hare.
Jihar Neja na cikin yankunan da ke fama hare-haren ƴan bindiga masu satar mutane domin kuɗin fansa.
Hukumar ƙwallon ƙafa ta Turai Uefa na duba yiwuwar sauya wurin da za a buga wasan ƙarshe na gasar Zakarun Turai ta Champions League daga birnin St Petersburg sakamakon fargaba da ake da ita kan rikicin Ukraine da Rasha.
Rasha ta tura dakaru zuwa yankuna biyu na Ukraine da suka ayyana 'yancin kansu kuma ana fargabar Rashar za ta afka wa Ukraine ɗin.
Wannan dalilin ne ya sa ake ganin Uefa ba za ta bari a buga wasan ƙarshen ba a ƙasar.
Da yake magana ranar Talata, Firaministan Birtaniya Boris Johnson ya ce "ba zai yiwu a buga wasan ƙwallo ba a ƙasar da ke afka wa ƙasashe masu 'yanci".
A gefe guda kuma, tsohon Ministan Wasanni na Birtaniya Tracey Crouch ya faɗa wa BBC cewa ya kamata Uefa ta ɗauke wasan daga Rasha "da gaggawa".
BBC ta fahimci cewa ba za a sauya ranar da za a buga wasan ba a 28 ga watan Mayun 2022 duk da cewa ana sa ran Uefa za ta yanke hukunci bayan tattaunawa kan wani filin wasan.
Wata babbar kotun tarayya da ke Jos, babban birnin jihar Filato, a Najeriya ta yanke wa Sarah Ochekpe, tsohuwar ministar albarkatun ruwa hukuncin daurin shekara shida a gidan yari.
Ochekpe ta kasance minista a gwamnatin tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan.
An gurfanar da ita ne tare da wasu mutane biyu da Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (EFCC) ta gurfanar a shekarar 2018 bisa zargin karbar Naira miliyan 450 daga hannun Diezani Alison-Madueke, tsohuwar ministar albarkatun man fetur a shekarar 2015.
Raymond Dabo, tsohon shugaban riko na PDP a Filato, da Leo Jatau, jagoran yakin neman zaben Goodluck Johnathan a jihar a shekarar 2015, su ne sauran mutane biyun da aka yanke wa hukuncin.
Wata kotu a Pakistan ta ɗaure wani mutum wata shida a gidan yari saboda ya ƙara aure ba tare da amincewar matarsa ta farko ba.
Kotun da ke Lahore ta yi watsi da ikirarin mutumin mai suna Saqib cewa addininsa ya ba shi ƴanci a matsayinsa na musulmi.
Matarsa Ayesha Bibi, ta yi nasara a kotun, bayan ta yi iƙirarin cewa ƙarin auren ba tare da amincewarta ba ya saɓa wa dokar iyali ta Pakistan.
Kotun ta ci tarar mijin dala dubu biyu.
Masu fafutikar kare haƙƙin mata, sun ce hukuncin zai karya guiwar mazan da ke da niyyar ƙarin aure, kuma zai buɗe wa mata ƙofar kai mazajensu kotu.
A Pakistan maza na auren fiye da mata ɗaya, amma dole sai namiji ya nemi amincewar matarsa ta farko kafin ya auri ta biyu.
Yanzu Saqib na da damar ɗaukaka ƙara kan hukuncin kotun.
An daɗe majalisar harakokin addinin Islama a Pakistan na ƙalubalantar dokar iyali ta Pakistan tare da ba gwamnati shawarwari da suka shafi harakokin addini.
Wata babbar kotun tarayya a Najeriya ta amince da matakin da rundunar ƴan sandan ƙasar ta ɗauka na korar wata jami'ar da ta ɗauki ciki a shekarar da ta gabata.
Mai shari’a Inyang Ekwo ya ce bai ga wani ƙwaƙƙwaran dalili ba na “haifar da ruɗani ga tsarin rundunar ba”.
Ya ƙara da cewa "Duk wanda da ya shiga rundunar dole ne ya kiyaye dokokinta ko kuma kada ya shiga rundunar saboda babu tilas game da zama mambanta."
Ƙungiyar lauyoyin Najeriya ce ta shigar da ƙarar bayan korar wata jami’ar ƴan sanda ta yi ciki ba ta da aure a watan Janairun 2021.
Sanata Rabiu Musa Kwankwaso na jagorantar wani gagrumin taro na wasu manyan siyasar Najeriya karkashin wani yunkuri mai suna The National Movement TNM.
Fitattun mutane da ƴan siyasa da suka halarcitaron sun haɗa da Alhaji Tanko Yakasai da Capt Idris Wadatsohon gwamnan Kogi da Rufai Alkali da Aminu Ibrahim Ringim tsohon dan takarar gwamna a jihar Jigawa da kuma Inijiniya Buba Galadima.
A jawabin Kwankwaso ya ce wasu ƴan Najeriya ne da suka damu da abin da ke faruwar suka haɗa kai don ceto ƙasar daga mawuyacin halin da ta shiga.
Ya ce yunƙuri ne na ƴan Najeriya masu kishi da suke zaune a gida da kasashen waje.
A cewarsa za su duƙufa wajen farfaɗo da tattalin arzikin kasar da inganta rayuwar ƴan kasa a birni da karkara
Ya ce sun shirya tsaf domin tunkarar matsalar tsaro da ta addabi Najeriya.
Fiye da shafukan intanet 30 a Mozambique - ciki har da na ma'aikatar tsaro – suka durƙushe a ranar Litinin bayan harin da masu kutse suka kai.
“Hacked by Yemeni hackers” shi ne sakon da ake ganin a shafukan na intanet, tare da hoton wani mutum sanye da mayafi kuma yana harba bindiga.
Hukumomin Mozambique sun tabbatar da harin na intanet tare da cewa sun shawo kan matsalar.
Daga cikin wadanda harin ya rutsa da su sun hada da shafukan kula da bala'o'i na kasa da masu kula da tituna da hukumomin ruwa, da ma'aikatar tsaro da cibiyar kula da sufurin kasa.
Hukumomin sun ce babu wata asarar bayanai ko fallasar bayanan sirrin ƴan kasar da aka samu - yayin da wannan shi ne hari na farko mafi girma da aka taba kai wa kasar.
Masharhanta sun yi kira ga gwamnati da ta ƙarfafa matakan tsaro na intanet saboda fargabar cewa mayaka masu ikirarin jihadi ne suka kai harin.
Ma’aikatan Nagarta Rediyo da ke Kaduna sun rufe tashar sakamakon abin da suka kira rashin biyansu albashi na tsawon wata biyar.
Ma’aikatan sun fito suna zanga-zanga domin neman haƙƙinsu tare da nuna adawa da shugabanninin gidan rediyon.
Tashar rediyon mallakin Janar Aliyu Gusau ce da ke a matsakaicin zango. Ma’aikatan sun yi kiran da a diba bukatunsu.
Barazanar yaƙi da kuma takunkuman da aka ƙaƙaba wa Rasha sun sa darajar hannayen jarin turai ta faɗi da kuma haifar tsadar farashin ɗanyen mai a duniya
An bayyana cewa sun yi cirawar da ba su taɓa yi ba tsawon shekara bakwai.
Katsewar fitar da man daga Rasha, ne ya haifar da ƙaruwar farashin ɗanyen mai zuwa dala 98 duk ganga.
Rasha ce ta biyu da ta fi fitar da ɗanyen mai a duniya bayan Saudiyya, inda Rasha ke samar da kusan kaso 40 na gas ga kasuwar turai.
Darajar hannayen jarin turai da Asia sun faɗi, haka ma hannayen jarin Rasha da suka faɗi da kusan kashi takwas.
Al'ummar garin 'Yar Katsina a jihar Zamfara mai fama da rikicin 'yan fashin daji, sun yi kira ga hukumomi su kai musu ɗauki don kuɓutar da gomman mata da ƙananan yaransu da aka sace tsawon kwana 18.
Bayanai sun ce ƴan fashin daji sun kai hari yankin na ƙaramar hukumar Bungudu ne tare da sace mata da yara fiye da 100 a ranar 5 ga wannan wata, kafin sako ƙalilan cikinsu daga bisani.
Rundunar 'yan sandan jihar Zamfara ta ce ko da yake, ba ta da tabbaci kan adadin matan da aka sace daga garin na 'Yar Katsina, amma tana yin duk mai yiwuwa wajen ganin ta kuɓutar da duk mutanen da ke hannun 'yan fashin daji a faɗin jihar.
Ku saurari bayanin da wani mutumin garin ya yi wa BBC.
Majalisar dokokin Mali da galibin ƴan majalisar sojoji ne, sun kaɗa ƙuri'ar amincewa da bai wa sojoji damar ci gaba da mulkin kasar har nan da shekaru biyar.
Bayan juyin mulkin da suka yi watanni 18 da suka gabata, da farko sojojin sun yi alkawalin gudanar da zaɓe a farkon wannan shekara, kafin soke alƙawarin daga bisani.
Matakin ya sa kungiyar ECOWAS ta ƙaƙabawa kasar takunkumin kasuwanci da na tattalin arziki, kuma a makon da ya gabata, Faransa ta sanar da janye sojojinta da ta girke a kasar domin yaƙar ƙungiyoyin masu ikirarin jihadi.
A makon da ya gabata ne Faransa ta sanar da janye sojojinta daga Mali da ke yaƙar masu iƙirarin jihadi.
Kudirin dokar bai ambaci sunan shugaban sojin ƙasar ba Kanar Assimi Goita, inda ake ganin zai iya tsayawa takara idan har ya sauka kafin gudanar da zaɓe.
A ranar Alhamis ake sa ran mai shiga tsakani na Ecowas tsohon shugaban Najeroiya Goodluck Jonathan zai tafi Mali.
Bayanai na cewa mutane akalla 55 sun mutu, sakamakon fashewar wani abu a wata mahaƙar zinari.
Ma’aikatan asibitin da jami’an yankin sun ce wata guguwa mai karfin gaske ce ta fara tashi a wurin da keGomgombiro a kudu maso yammacin kasar.
Karin mutane 50 sun jikkata ciki har da mata da kananan yara.
Hukumomin gundumar Poni da fashewar ta afku sun kaddamar da bincike.
Ana yawan samun hadari irin wannan a wuraren hakar ma'adinai na bayan fage a wasu kasashen Afirka.
Babban jami’in ‘yan sandan Najeriya da aka dakatar ya musanta zargin alakanta shi da kungiyar masu safarar miyagun ƙwayoyi ta ƙasa da ƙasa.
An kama Abba Kyari ne a makon da ya gabata bayan da hukumar yaki da fataucin miyagun kwayoyi ta kasar NDLEA ta zarge shi da alaƙa da wata kungiyar masu safarar miyagun ƙwayoyi da ke aiki tsakanin Najeriya da Habasha da kuma Brazil.
Sai dai a ranar Litinin ya shaidawa wata kotu a Abuja babban birnin kasar ta hannun lauyoyinsa cewa ƙirƙirar zargin aka yi.
Hukumar NDLEA ta yi zargin cewa Mista Kyari ya yi yunkurin bai wa jami’anta cin hanci don kilo 25 na hodar ibilis da jami’ansa suka kama sannan suka raba.
Amma ya musanta zargin.
Ya ce jami’an hukumar NDLEA ne suka masa gadar zare bayan ya nace sai an bayar da lada ga wanda ya bayar da labarin da ya kai ga kama waɗanda ake ake zargi da safarar miyagun kwayoyi kamar yadda suka amince da farko.
Ɗaya daga cikin lauyoyinsa Hamza Nuhu Dantani, ya shaida wa BBC cewa sun kuma gabatar da bukatar neman belinsa.
Ya ce saboda an ci gaba da tsare shi sama da sa’a 24 ba tare da gabatar da shi kotu ba kan zargin da ake masa, wanda ya saɓa ƴancinsa na ɗan adam.
A ranar Alhamis kotu za ta saurari buƙatar da lauyoyinsa suka shigar na neman beli.