Rufewa
Masu bibiyarmu a wannan shafin a nan muka zo ƙarshen kawo muku labarai da rahotanni kai tsaye, sai kuma gobe Litinin idan Allah Ya kai mu za mu ci gaba da kawo muku wasu labaran.
Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Wannan shafi na kawo muku abubuwan da ke faruwa a sassan duniya kai-tsaye, musamman a Najeriya da Nijar maƙotansu.
Awwal Ahmad Janyau
Masu bibiyarmu a wannan shafin a nan muka zo ƙarshen kawo muku labarai da rahotanni kai tsaye, sai kuma gobe Litinin idan Allah Ya kai mu za mu ci gaba da kawo muku wasu labaran.
Barcelona ta casa Valencia 4-1 har gida, wanda hakan ya ba ta damar komawa ta hudu a teburin La Liga da maki 42.
Pierre-Emerick Aubameyang ne ya ci kwallo biyu, yayin da Frenkie De Jong da Pedri suka ci daya kowannen su.
A yanzu Barca na kan-kan-kan da Atletico Madrid da ita ma ke da maki 42, amma kuma kungiyar da ke Camp Nou na da kwanton wasa daya.
Valencia kuwa na zaune ne na 12 a tebur, bayan kasa cin wasa ko daya a cikin biyar, inda ta yi rashin nasara uku da kunnen doki biyu.
A daya wasan na ranar Lahadi Sevilla wadda ke na biyu a tebur ta yi kunnen doki 1-1 a gidan Espanyol, kuma hakan na nufin Real Madrid ta ba ta tazarar maki shida bayan wasanni 25.
Rasha da Belarus sun tsawaita atisayen haɗin gwiwa na sojojin kasashensu a kusa da kan iyaka da Ukraine, yayin da shugabannin kasashen yamma ke ci gaba da gargaɗi kan yiwuwar mamayar Ukraine.
Ma'aikatar tsaron Belarus ta ce an ɗauki matakin ne saboda abin da ta kira halin da ake ciki ya ƙara tsananta a gabashin Ukraine.
Wakilin BBC a Kyiv ya ce wannan wata alama ce mai ƙarfi da ke nuna cewa Rasha ba ta shirya ja da baya ba.
Masu aikin kashe gobara a Portugal sun ce har yanzu ba su iya kashe gobarar da ta tashi ba a wani makeken jirgin ruwa da ke ɗauke da dubban motocin alfarma wanda ke tafiya a cikin Tekun Atlantika.
Jirigin mai suna Felicity Ace, na ɗauke da kusan motoci dubu huɗu da suka haɗa da motoci ƙirar Porsche da Audi da Bentley waɗanda ake hanyar kai su Amurka daga Jamus a ranar Laraba.
Tuni aka ceto ma'aikatan jirgin ruwan 22. Sai dai wani ma'aikaci a tashar ruwa da ke wani tsibiri ya bayana cewa ruwan da ke cikin batiran wasu motocin ne ya sa wutar ke ci gaba da ci.
Ya ce wutar ba ta kai ga tankin mai na jirgin ba. Haka kuma ya bayyana cewa kashe irin wannan wutar na buƙatar kayan aiki na musamman sakamakon ruwan kashe gobara na gargajiya ba zai iya kashe wutar da ruwan batir ya zama makamashinta ba.
Shugaban kwamitin wasannin Olympic na kasa da kasa, Thomas Bach ya sanar da rufe gasar wasannin Olympics na hunturu da aka yi a Beijing bayan makonni biyu da aka shafe ana samun nasarori da ce-ce-ku-ce a fannin wasanni.
A bikin rufe wasannin da aka yi a filin wasa na Bird Nest, Mista Bach ya nuna godiya ga yan China da suka shirya gasar yana mai cewa sun yi wani aiki na musamman.
Kasar Norway ce ta zo kan gaba a teburin lambobin yabo
Isra'ila za ta buɗe iyakokinta ga duka masu yawon buɗe ido har waɗanda ma ba su yi riga-kafin korona ba daga wata mai kamawa.
Firaiministan ƙasar Naftali Bennett ne ya sanar da hakan inda ya ce an ɗauki wannan matakin ne sakamakon raguwar da ake samu na masu kamuwa da cutar.
Sai dai ya ce gwamnatin ƙasar za ta yi sauri ta ɗauki mataki da zarar an samu sabon nau'i na cutar.
Duk da buɗe iyakokin da za a yi, amma dole ne baƙi su nuna shaidar gwajin korona kafin su shiga jirgi su je ƙasar da kuma idan sun isa.
Adadin masu yawon buɗe ido ya ƙaru a ƴan kwanakin nan sai dai kwata-kwata bai kai adadin da ake samu ba kafin ɓullar annobar.
Hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta Najeriya wato NAFDAC ta kama tan 120 na ganda mai ɗauke da sinadarai wadda aka shiga da ita ƙasar.
A wani labari da hukumar ta fitar a shafinta na Twitter ranar Lahadi, ta bayyana cewa an kama gandar a wurare shida a Legas.
Shugabar hukumar ta NAFDAC, Farfesa Mojisola Adeyeye ta bayyana cewa mutum bakwai da ake zargi da wannan lamarin ana gudanar da bincike a kansu.
Ta bayyana cewa tuni aka ɗauki samfarin gandar domin kai ta ɗakin gwaji domin gano ingancinta.
Ta kuma bayyana cewa an yi ƙiyasin farashin gandar kan kusan naira miliyan 23.
Majalisar dokokin Iran ta fitar da wasu sharuɗɗan da ta ce sai an amince da su kafin komawa kan yarjejeniyar nukiliya ta 2015 da ƙasashen yammaci.
Kamfanin dillacin labarai na IRNA a ranar Lahadi ya ce ƴan majalisa 250 cikin 290 ne suka sanya hannu kan sanarwar
'Yan majalisar 250 sun bayyana cewa Amurka da Turai sai sun ba da tabbacin ba za su fita daga yarjejeniyar da aka farfado ba kuma ba za su yi uwa makarbiya ba a yarjejeniyar.
Sharuɗɗan sun buƙaci a ɗage dukkan takunkuman da Amurka ta kakaba wa a wani tabbataccen tsari.
Sojojin Najeriya sun yi kuskuren kashe yara bakwai tare da jikkata wasu biyar a wani harin sama da suka kai a yankin Maradi na Jamhuriyyar Nijar, kamar yadda gwamman yankin ya shaida wa kamfanin dillacin labaran Faransa.
Gwamnan Maradi Chaibou Aboubacar, ya ce hare-haren sama da sojojin Najeriya suka kai ya rutsa da yara a ƙauyen Nachade a ranar Juma’a.
Gwamnan ya ce suna tunanin sojojin Najeriya sun yi kuskuren kisan yaran ne a ƙoƙarin kai wa ‘yan bindiga a yankunan kan iyaka hari.
Babu dai wata sanarwa daga rundunar sojin Najeriya game da al’amarin.
Gwamnan Maradi ya ce lamarin ya shafi yara ne guda 12, kuma bakwai daga cikin sun mutu yayin da biyar ska jikkata.
A cewar gwamnan, harin ya rutsa da yaran ne suna cikin wasa yayin da iyayensu ke hidimar biki.
Hukumar yaƙi da sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta NDLEA a Najeriya ta ce jami’anta sun kama makudan daloli na jabu a Abuja.
Sanarwar da hukumar ta fitar ta ce an yi yunƙurin sace kusan dala biliyan 2.7 na tattalin arzikin Najeriya ta hanyar tura kuɗaɗen na jabu a kasuwa da suka kai sama da dala miliyan 4.7.
Hukumar ta ce jami’anta sun kama kuɗaɗen a yankin Abaji da aka ɗauko daga Legas zuwa Abuja.
Wannan an kama wanda ake zargi da fataucin kuɗin mai suna Abdulmumini Maikasuwa.
Hukumar ta ce shugabanta Birgediya Janar Buba Marwa ya bayar da umarnin a miƙa kuɗaɗen da wanda ake zargi ga hannun hukumar EFCC domin ci gaba da bincike.
Sarauniya Elizabeth ta Ingila ta kamu da cutar korona, kamar yadda fadar Buckingham ta sanar.
Fadar ta bayyana cewa sarauniya na tattare da alamun sanyi amma ana sa ran za ta ci gaba da gudanar da ayyukanta sama-sama a Windsor a mako mai zuwa.
Rahotanni a Najeriya sun ce sojojin Najeriya sun halaka wasu kwamandojin Iswap a Sambisa ciki har da wanda ake kira Amir Buba Danfulani wanda ake zargin ya shigar da fulani makiyaya ƙungiyar.
A cikin rahoton da ta fitar, jaridar PRNigeria da ke da kusanci da rundunar sojin Najeriya ta ce an yi wa mayaƙan ne luguden wuta ta sama a wasu sansanoninsu da kuma dajin Sambisa a arewa maso gabashin Najeriya, kamar yadda majiyoyin soji suka tabbatar.
Sai dai babu wata sanarwa kawo yanzu daga rundunar sojin Najeriya da ke tabbatar da al’amarin.
Rahotannin sun ce an yi wa mayaƙan ne ruwan rokoki a Tumbun Kaiyowa da kuma Tumbun Allura, tare da kashe mayaƙan.
An kuma yi wa mayaƙan ruwan wuta ta sama a dajin Sambisa. Kwamandojin Iswap da aka kashe sun hada da Musa Amir Jaish da Mahd Maluma da Abu-Ubaida da Abu-Hamza da kuma Abu-Nura umarun Leni, a cewar PRNigeria.
Habasha ta ce a karon farko ta fara samar da lantarki daga Kogin Nilu da ake taƙaddama akansa, kamar yadda kafar talabijin ɗin ƙasar ta sanar.
Kogin wanda aka kashe wa dala biliyan 4.2 a yammacin yankin Benishangul-Gumuz, ya janyo taƙaddama tsakanin kasashen Habasha da Masar da Sudan tun bayan fara aikin gina shi a shekarar 2011.
Sudan da Masar na fargabar wannan aikin na iya rage kason ruwan da suke samu na ruwan Nilu.
Habasha ta dage cewa madatsar ruwa shi ne hanyar ci gabanta.
Aikin kogin da ake kira Grand Ethiopian Renaissance Damshi ne aikin samar da wutar lantarki mafi girma a Afirka kawo yanzu.
Ana sa ran Gerd zai samar da wutar lantarki sama da megawatt 5,000, wanda zai ninka yawan wutar da al'ummar asar ke samu idan an kammala.
Wani rahoton Majalisar Dinkin Duniya ya nuna cewa Najeriya ta shige gaba, wajen yawan yaran da ba su zuwa makaranta a faɗin Najeriya, da adadin yara miliyan 13 da ke zaune a gida, ko suke gararamba a gari.
An mayar wa masarautar Benina Najeriya tagulla biyu, fiye da karniɗaya da sojojin Birtaniya suka yi awon gaba da su, matakin da ake ganin zai buɗe ƙofar dawo da dubban kayayyakin tarihi zuwa asalinsu.
Kayayyakin da sojojin Birtaniya suka sace a 1897, yawancinsu suna gidajen tarihin ƙasashen yammaci da kuma wasu gidajen tarihin masu zaman kansu.
Masu bincike da ƴan mulkin mallaka ne yawanci suka sace kayayyakin tarihin.
Tagullan Benin - da dubban kayan ƙere-ƙere na al'adu da mutum-mutumi da hauren giwa - sun kasance alamu da ake zargi na rashin adalci. Asalinsu daga yankin da ake kira jihar Edo ne a yanzu a kudancin Najeriya.
An yi ƙasaitaccen biki na tarbon tagullan guda biyu da aka dawo da su a masarautar Benin.
Akwai wasu da dama da ake tunanin an adana su a New Zealand da Amurka da kuma Japan.
Tun a watan Oktoba Jami’ar Aberdeen ta miƙa tagullan guda biyu ga ofishin jekadancin Najeriya.
Ana tunanin akwai kashi 90 na kayayyakin tarihi na Afirka da ke gidan tarihin Turai a Faransa da kuma gidan tarihin Birtaniya na London.
Gidan tarihin Birtaniya, da ke da kayan tarihin Benin 950, ya sha suka musamman saboda ƙin amincewa ya dawo da su, amma yana ɗaya daga cikin gidajen tarihin da ke ƙoƙarin tabbatar kayayyakinsa a bisa doka.
Rundunar ƴan sandan jihar Bauchi ta tabbatar da mutuwar wani yaro matashi ɗan shekara 14 wanda ya kashe kansa a ƙaramar hukumar Ningi.
Mai magana da yawun rundunar ƴan sandan jihar Bauchi Ahmed Wakil wanda ya tabbatar wa BBC da faruwar al’amarin ya ce yaron ya kashe kansa ne ta hanyar rataye kansa a wani kangon ɗaki.
Mahaifin yaron ne ya sanar da ƴan sanda game da makomar ɗansa. Kuma ya ce yaron yana fama da rashin lafiyar ƙwaƙwalwa.
“Bayan sanar da ƴan sanda nan take jami'anmu suka inda al’amarin ya faru kuma aka ɗauki yaron zuwa babbar asibitin Ningi amma aka tabbatar da ya mutu.”
Rundunar ƴan sandan Bauchi ta ce ta ƙaddamar da bincike domin gano dalilin da ya sa yaron ya kashe kansa.
Firaministan Birtaniya Boris Johnson, ya ce shaidu daga Rasha da Ukraine na nuna alamun cewa Shugaba Vladimir Putin na kitsa wani mummunan shiri da ka iya haifar da yaƙi mafi girma a Turai tun 1945.
Da yake magana da BBC a gefen taron tsaro na da ke gudana a birnin Munich, Mista Johnson ya ce “dukkan alamu sun nuna cewa shugaban naRasha, ya fara kaddamar da aniyar ta sa.”
Ya ce idan har shugaba Putin na tunanin cewa da wannan mataki ne zai iya yi wa NATO baraza, zai gane cewa ya yi kuskure.
Masu sa ido na kasa da kasa a yankin Donbas da ke gabashin Ukraine sun ce an shafe kwana na uku ana gwabza fada tsakanin sojojin Ukraine da 'yan awaren da ke samun goyon bayan Rasha.
An kashe sojojin Ukraine biyu a ranar Asabar yayin da aka garzaya da ministan harkokin cikin gida na kasar da ke rangadi a fagen yaƙi zuwa wata mafakar karkashin kasa.
'Yan aware a Donetsk da Luhansk sun ba da umarnin gudanar da cikakken shirin soji, sai dai wakilin BBC a Kyiv ya ce mutane da dama na ganin cewa Rasha ce ke daukar abun da zafi.
Muna maku maraba da kasancewa da mu a wannan shafin inda za mu kawo maku labarai da rahotanni kai tsaye kan abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.
Sai ku kasance da mu.