Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Hedikwatar APC ta danka wa bangaren Ganduje takardar shaidar shugabanci

Wannan shafi na kawo muku abubuwan da ke faruwa a sassan duniya kai-tsaye, musamman a Najeriya da Nijar maƙotansu.

Rahoto kai-tsaye

Umar Mikail

  1. 'Abubuwan da aka gano kan cancantar malaman firamare a Borno na da tayar da hankali'

    Gwamna Babagana Zulum na Jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya ya bayyana abubuwan da aka gano a rahoton da aka mika masa kan jarrabar da aka yi wa malaman firamare na jihar da cewa abin tsoro ne matuka.

    Farfesa Zulum ya bayyana hakan ne Alhamis din nan bayan da kwamitin da aka dora wa aikin yi wa malaman firamaren 17,229 na kananan hukumomin jihar 27 jarrabawar rubutu da karatu da kuma lissafi.

    Binciken ya gano cewa daga cikin malaman 17,229 a fadin jihar 5,439 ne, wato kashi 31.6 cikin dari ne kawai suka cancanci koyarwa.

    3,815, kashi 22.1 cikin dari ba su cancanci koyarwa ba kuma ma ba za a iya musu horo su iya aikin ba, kamar yadda rahoton ya nuna.

    Sai dai kuma malamai 7,975 wato kashi 46.3 cikin dari ba su cancanci aikin ba sosai amma kuma za a iya horad da su su kware.

    Kwamishinan Ilimi na jihar, Lawan Abba Wakilbe, shi ne ya gabatar da rahoton.

    Akwai kuma kamar yadda rahoton ya nuna malamai 2, 389, kashi 13.9 cikin dari, wadanda suke koyarwa ba tare da wata takarda ta karatu ba sam-sam daga kowace makaranta ba.

    Sai dai gwamnan na Jihar Borno ya bayar da tabbacin cewa duk da matsalolin da aka gano ba zai kori wadanda ba za su iya koyarwar ba, amma bisa shawarar kwamitin zai duba yuwuwar mayar da su wuraren da za su iya wasu ayyukan.

  2. Gwamnatin Jihar Oyo za ta yi zaman sulhu da kungiyoyin bata-gari

    Gwamnatin Jihar Oyo da ke kudu maso gabashin Najeriya ta ce za ta yi zaman tattaunawa da matasa ‘yan bata-gari da kungiyoyin matsafa a jihar domin wanzar da zaman lafiya.

    Kwamishinan Yada Labarai da Al’adu da Yawon bude idanu Dakta Wasiu Olatunbosun shi ne ya bayyana haka Alhamis din nan, bayan ganawar sirri da wakilan kungiyoyin kamar yadda jaridar Punch ta Najeriyar ta ruwaito.

    Daga cikin wadanda aka yi ganawar da su a Ibadan har da kungiyar OPC da ta ‘yan sintiri ta Najeriya (Vigilante Group of Nigeria) da sauransu.

    A wata sanarwa in ji jaridar an ruwaito Kwamishinan yana cewa gwamnatin jihar da hadin guiwar dukkanin kungiyoyin matasamasu amfani da makamai ta kuduri aniyar kawo karshen tashe-tashen hankalin da ake yi da zubar da jinni tsakanin matasa ‘yan unguwa da kungiyoyin matsafa.

  3. Hedikwatar APC ta danka wa bangaren Ganduje takardar shaidar shugabanci

    Hedikwatar jam’iyyar APC mai mulki a Najeriya, ta mika takardar shedar shugabancin jam’iyyar ga bangaren gwamnan jihar Kano, wanda ya zabi Abdullahi Abbas a matsayin sabon shugaba.

    A dazun nan ne Sakataren rikon jam’iyyar na kasa Mista John Akpanudoedehe, ya mika takardar ga Abdullahi Abbas, wanda yake tare da Gwamna Ganduje da dan Majalisar Tarayya Alhassan Ado Doguwa da Kwamishinan kananan hukumomi Murtala Sulen Garo.

    Bayar da takardar shedar ta biyo bayan hukuncin da Kotun Daukaka Kara ta kasar ta yi ne inda ta soke hukuncin babbar kotun da a baya ta ba bangaren tsohon gwamnan jihar Mallam Ibrahim Shekarau nasara a shari’ar shugabancin.

    Ɓangaren Shekarau din wanda ke da Ahmadu Haruna Zago a matsayin shugaban jami’iyyar ya ce zai ɗaukaka ƙara kan hukuncin kotun da ya ce shugabancin ɓangaren gwamna ne halastacce.

    Ahmadu Haruna Zago, ya faɗa wa BBC Hausa cewa za su yi biyayya ga hukuncin amma za su ɗaukaka ƙara.

    "Za mu ɗaukaka ƙara mana, ai bin umarnin daban kuma ɗaukaka ƙara daban," in ji shi. "Lauyoyinmu na nazari kan hukuncin kotun."

    Hakan na nufin Kotun Ƙoli ce za ta raba gardama idan suka ɗaukaka ƙarar, kasancewar Kotun Ɗaukaka Ƙara ce ta yi hukuncin na yanzu.

    A zaman da ta yi yau Alhamis a Abuja, Kotun Ɗaukaka Ƙarar ta ce Babbar Kotun Abuja ba ta da hurumin yin hukunci kan rikicin sannan kuma ta ce shugabancin Abdullahi Abbas ne halastacce - ba na Haruna Zago ba.

    A makon da ya gabata ne bangaren Shekarau ya yi watsi da wani yunƙurin sulhu da jam'iyyar ta ƙasa ta yi, inda ta naɗa Gwamna Ganduje a matsayin jagoran kwamatin sasanta rikicin da suke yi.

  4. Tsohon shugaban rikon-kwarya na Liberia Amos Sawyer ya rasu

    Tsohon shugaban rikon-kwarya na Liberia Farfesa Amos Sawyer ya rasu yana da shekara 76.

    Yana daga cikin fitattun ‘yan siyasar kasar wanda ya zama shugaban rikon-kwarya a shekarun 1990, a wani yunkuri na kawo karshen mummunan yakin kasar wanda tsohon shugaban kasar wanda kotun duniya ta daure a yanzu Charles Taylor ya haddasa.

    Taylor da shi da kungiyarsa ta ‘yan tawaye NPFL ba su amince da shugabancin Sawyer ba, saboda haka suka hana shi fita daga babban birnin kasar Monrovia duk tsawon shekara hudu ta mulkinsa na rikon-kwarya.

    Bayan kawo karshen yakin kasar, Sawyer, wanda malamin jami’a ne a fannin kimiyyar siyasa, ya yi aiki a matsayin shugaban hukumar kula da mulki ta Liberia.

  5. Rasha ta ce za ta mayar wa Amurka martanin soji kan Ukraine

    Rasha ta yi barazanar mayar da martanin da ta kira na dabarun soji idan Amurka ba ta biya mata bukatunta na tsaro ba, wadanda suka hada da janyewar dukkanin dakarun Amurkar daga gabashi da tsakiyar Turai.

    Gargadin na a matsayin martini ne ga wata wasika ta Amurka wadda a ciki Amurkar ta yi watsi da kiran da Rasha ta yi da a ba ta tabbacin cewa ba za a taba bari Ukraine ta zama mamba a kungiyar tsaro ta Nato ba.

    Haka kuma Rashar ta gaya wa kasashen Yamma da su daina tura makamai zuwa Ukraine sannan a janye masu bayar da shawara da bayar da horo na Yamma daga Ukraine din.

    Can a Washington, Shugaba Biden ya ce barazanar Rasha ta mamayar Ukraine har yanzu tana nan sosai, kuma za ta iya kasancewa cikin ‘yan kwanaki – amma dai har yanzu yana da kwarin guiwar sasanta rikicin ta hanyar diflomasiyya.

    A yau Rashar ta kori mataimakin jakadan Amurka daga Moscow Bart Gorman, abin da Amurkar ta ce ya saba hankali, kuma za ta mayar da martani a kai.

  6. Birtaniya ta yi gargaɗi kan zuwan mahaukaciyar guguwa a tsibiran British Isles

    Ofishin da ke hasashen yanayi na Birtaniya, ya fitar da wata sanarwa wadda a cikinta yake gargadi ga mazauna tsibiran British Isles cewa wata mahaukaciyar guguwa da aka lakaba wa suna Storm Eunice za ta isa tsibiran ranar Juma'a.

    Ofishin ya ce ana sa ran guguwar na tafe da iskar da ke tafiyar kilomita 160 cikin kowace sa'a, kuma akwai yiwuwar za ta yi mummunar barna ga mutane.

    Ana kuma sa ran za ta yi wa turakan lantarki da gine-gine ɓarna, wanda zai tilasta a dauke hasken lantarki.

    Baya ga guguwar akwai yiwuwar ambaliyar ruwa za ta shafi wani bangare na Ingila.

  7. Nan gaba kaɗan wahalar fetur za ta zo ƙarshe - NNPC

    Shugaban kamfanin mai na Najeriya NNPC, Mele Kyari, ya ba da tabbacin cewa wahalar da 'yan ƙasar ke sha sakamakon ƙarancin fetur za ta zo ƙarshe nan gaba kaɗan.

    Mele Kyari ya bayyana hakan ne ranar Laraba yayin da yake amsa gayyatar kwamatin Majalisar Wakilai da ke bincike kan yadda aka shigar da gurɓataccen man fetur Najeriya.

    "Game da matsalar nan, bari na ba ku tabbaci cewa mun ɗauki dukkan matakan da suka dace wajen dawo da shigo da mai ƙasar nan. Mun ba da oda mai yawan gaske da za ta ba mu damar kai wa cikin watan Maris, yayin da muke da lita biliyan 2.1 a yanzu," in ji shi.

    "Matsalar da kuke gani, ina tabbatar muku cewa za ta zo ƙarshe nan da mako mai zuwa. Idan komai ya tafi lafiya, saboda matsalolin da ba za mu iya magancewa ba ciki har da jigilar mai a manyan motoci, ba don haka ba, muna da ingantaccen tsari na rarraba mai da zimmar fita daga wannan yanayin."

  8. Faransa za ta fara janye dakarunta daga Mali

    Faransa da ƙawayenta sun ce za su janye sojojinsu daga Mali, kasar da suka shafe shekara 10 suna yakar mayaka masu ikirarin jihadi.

    Cikin wata sanarwa ta hadin gwiwa da suka fitar (wadda ta hada da kawayenta na Turai da kasar Kanada), Faransa ta ce matakan da gwamnatin Mali take dauka sun tilasta musu ficewa daga kasar.

    Shugaba Macky Sall na Senegal wanda ke tare da Shugaba Macron yayin da yake wannan sanarwar, ya ce "Idan aka yi la'akari da halin da ake ciki a Mali, mun fahimci dalilan da suka sa kasashen Turai da Faransa suka dauki matakan da suka dauka a kasar, ganin cewa al'amarin ya haifar da juyin mulki har sau biyu".

    Shugaba Emmanuel Macron na Faransa ya musanta cewa Faransa ta gaza a ayyukan tabbatar da tsaro da ta yi a Mali.

  9. Ana aikin ceto yaro mai shekara 9 da ya shafe kwana uku a rijiya

    Ana ci gaba da aikin ceto a gabashin Afghanistan da zimmar zaƙulo wani yaro ɗan shekara tara da ya maƙale a rijiya tsawon kwana uku.

    Wani bidiyo da aka yaɗa a shafukan sada zumunta ya nuna yadda Haidar ke rakuye a cikin rijiyar amma yana iya motsa hannayensa da kansa.

    Yanzu rahotanni na cewa ya sake faɗa wa ƙasan rijiyar.

    Lamarin ya yi kama da wanda ya faru a Moroko a farkon watan nan, inda Rayan mai shekara biyar ya maƙale a rijiya wanda sai gawarsa aka ciro.

  10. Labarai da dumi-dumi, Rikicin APC a Kano: Ɓangaren Shekarau zai ɗaukaka ƙara

    Ɓangaren jam'iyyar APC a Jihar Kano da ke rikici da na Gwamna Abdullahi Ganduje ya ce zai ɗaukaka ƙara kan hukuncin kotu da ya ce shugabancin ɓangaren gwamna ne halastacce.

    Shugaban tsagin, Ahmadu Haruna Zago, wanda ke samun goyon bayan tsohon Gwamna Sanata Ibrahim Shekarau, ya faɗa wa BBC Hausa cewa za su yi biyayya ga hukuncin amma za su ɗaukaka ƙara.

    "Za mu ɗaukaka ƙara mana, ai bin umarnin daban kuma ɗaukaka ƙara daban," in ji shi. "Lauyoyinmu na nazari kan hukuncin kotun."

    Hakan na nufin Kotun Ƙoli ce za ta raba gardama idan suka ɗaukaka ƙarar, kasancewar Kotun Ɗaukaka Ƙara ce ta yi hukuncin na yanzu.

    A zaman da ta yi yau Alhamis a Abuja, Kotun Ɗaukaka Ƙara ta ce Babbar Kotun Abuja ba ta da hurumin yin hukunci kan rikicin sannan kuma ta ce shugabancin Abdullahi Abbas ne halastacce - ba na Haruna Zago ba.

    A makon da ya gabata ne tsagin Shekarau ya yi watsi da wani yunƙurin sulhu da jam'iyyar ta ƙasa ta yi, inda ta naɗa Gwamna Ganduje a matsayin jagoran kwamatin sasanta rikicin da suke yi.

  11. Bidiyon matan da aka yaɗa hotunan tsiraicinsu ta Telegram

    Wani binciken BBC ya gano cewa ana yada hotunan tsiraicin mata masu tarin yawa a manahajar sada zumunta na Telegram don cin zarafinsu, da ci da ceto da kunyatar da su.

    Cikin 'yan dakikoki bayan da Sara ta gano cewa an yada hoton tsiraicinta a Telegram, rayuwarta ta sauya.

    An kuma kara da shafukanta na Instagram da Facebook da kuma lambar wayarta.

    Ba tare da ɓata lokaci ba kuma wasu mutune da ba ta san ko su wanene ba suka tuntubeta suna neman karin wasu hotunan.

    "Sun saka ni jin kamar ni karuwa ce saboda [sun yi amanna] ni ce na yada hotunan tsiraici na, Hakan na nufin ba ni da wata daraja a matsayina na mace," ta ce.

  12. Labarai da dumi-dumi, Rikcin APC a Kano: Ɓangaren Ganduje ya yi nasara a kotun ɗaukaka ƙara

    Ɓangaren Gwamna Abudllahi Umar Ganduje ya yi nasara a ƙarar da ya shigar yana ƙalubalantar nasarar da wata kotun ta bai wa ɓangaren tshohon Gwamna Ibrahim Shekarau a rikicin jam'iyyar APC mai mulkin Jihar Kano.

    A zaman da ta yi yau Alhamis a Abuja, Kotun Ɗaukaka Ƙara ta ce hukuncin da Babbar Kotun Abuja ta yi ba daidai ba ne sannan ta tabbatar da cewa shugabannin da ɓangaren Ganduje ya zaɓa su ne halastattu.

    Hukuncin kotun na yau ya bai wa ɓangaren Ganduje nasara a duka ɓangarori ukun da suka ɗaukaka ƙarar a kan su, kamar yadda Barista Abdullahi Adamu Fagge ya shaida BBC Hausa - ɗaya daga cikin lauyoyin ɓangaren gwamna.

    Tun farko, ɓangaren da Shekarau ke jagoranta ya shigar da uwar jam'iyyar ƙara da kwamatin shugbancinta na ƙasa da kuma sakatarenta a ɓangare ɗaya, sannan suka shigar da shugabancin APC na Kano a ɗaya ɓangaren, da kuma kwamatin da ya shirya zaɓen shugabancin jam'iyyar a Kano a wani ɓangaren daban.

    A zaɓen da aka gudanar mai cike da rarrabuwar kai a watan Nuwamban 2021, ɓangaren Shekarau ya zaɓi Ahmadu Haruna Zago a matsayin shugaban APC na jiha yayin tsagin Ganduje ya zaɓi Abdullahi Abbas.

    A makon da ya gabata ne tsagin Shekarau ya yi watsi da wani yunƙurin sulhu da jam'iyyar ta ƙasa ta yi, inda ta naɗa Gwamna Ganduje a matsayin jagoran kwamatin sasanta rikicin da suke yi.

    Sai dai ya yi wuri a iya bayyana abin da hukuncin ke nufi ga APC a jam'iyyance musamman ganin yadda ake tunkarar babban zaɓe na 2023.

    • APC Maslaha: Wasu ƴan APC sun kafa sabuwar ƙungiya a Kano
    • Ra'ayin 'yan APC ya bambanta kan ɓangaren da zai karɓi mulkin Najeriya a 2023
  13. Mutum 13 sun faɗa rijiya ana tsaka da shagalin biki

    Akalla mutum 13 ne suka rasa rayukansu bayan sun faa cikin wata rijiya yayin wani biki da ake yi a jihar Utter Pradesh da ke yammacin Indiya.

    Yan sanda sun ce wadanda abin ya ritsa da su - duka mata ne da yara - na zaune kan murfin da aka rufe rijiyar da shi a lokacin da ya rufta saboda nauyin mutanen da ke kansa.

    Lamarin ya faru ne ranar Laraba da yamma a lokacin bikin gargajiya na “haldi”, inda ‘yan uwa suke shafa wa ango da amarya ruwan kurkur a fuska a matsayin alamar samun wadata.

    Wasu karin mutum biyu sun jikkata a hatsarin, wanda ya faru a gundumar Kushinagar.

    Firaminista Narendra Modi ya bayyana mutuwar tasu a matsayin "mai sosa zuciya".

    Lokacin da murfin ya karye, sauran baki sun ruga don ceto mutanen, inda suka kai su wani asibiti da ke kusa. Yayin da aka sanar da mutuwar mutum 11 nan take, wasu biyu kuma sun mutu a asibit, in ji ‘yan sanda.

    Babban Ministan Utter Pradesh Yogi Adityanath ya nemi shugabannin ananan hukumomi da su taimaka wa iyalan mutanen da abin ya ritsa da su.

  14. An tara wa Haiti dala miliyan 600 bayan girgizar ƙasarta

    Babban taron da Majalisar Dinkin Duniya ta yi da nufin tara kudaden tallafin taimaka wa kasar Haiti da ta fuskanci mummunar girgizar kasa a shekarar da ta gabata, ya tara dala miliyan 600.

    Fira Ministan Haiti, Ariel Henry, ya gabatar da shirin sake gina kasar da zai dauki shekara 4.

    Yayin da ta ke jawabi a taron tara kudin tallafin, mataimakiyar magatakardar MDD Amina Muhammad, ta jaddada muhimmancin taimakawa Haiti.

    Ta ce yanzu ba lokacin karaya ba ne, na farko saboda al'ummar Haiti ba su karaya ba, lokuta daban-daban suna kunshe kansu tare da kukan abubuwan da suka rasa, daga na sai su kara mikewa lallai suna buƙatar taimakonmu.

  15. Luguden wutar da jiragen yaƙin Isra'ila ke yi sun faɗa wani gari a Syria

    Kungiyar da ke sa ido a yaƙin da ake yi a Syria, ta ce luguden wuta ta sama da jiragen yaƙin Isra'ila ke yi, sun faɗa wani gari da ke kudancin birnin Damascus.

    Kungiyar The Syrian Observatory for Human Rights, ta ƙara da cewa an yi nufin kai harin ne inda sojoji ke zaune.

    Ita ma kafar yada labaran gwamnatin Syria, ta ce an kaddamar da hare-hare daban daga tuddan Golan da kuma yankin garin Zakiya da ke kusa.

    Babu dai wanda aka sanar da lamarin ya shafa ko jikkata ko kuma asarar rai, sai barnar da ba za a rasa ba.

  16. Lokaci ya yi da Amurkawa za su koma rayuwarsu irin ta baya kafin korona - Fauci

    Babban jami'in lafiya da ke bai wa shugaban Amurka Joe Biden shawara kan cutar korona, Dr Anthony Fauci, ya ce lokaci ya yi da Amurkawa za su fara komawa gudanar da rayuwarsu kamar yadda suka saba a baya.

    A wata hira da kamfanin dillancin labarai na Reuters, Dr Fauci ya ce duk da cewa har yanzu cutar nan ba ta yi ƙaura ba, amma babu yadda za a ci gaba da rayuwa a haka.

    Farfesa Anne Rimoin jami'a a fannin kiwon lafiya a Jami'ar California, ta yi ƙarin haske kan abin da Dr Fauci ke nufi.

    Ta ce abin da ya ke nufi shi ne mu koyi yadda za mu koma rayuwarmu a baya amma cikin taka tsantsan, saboda ganin sabbin nau'in korona da ke fitowa nan da can.

  17. Gwamnatin Abiya ta ce mutum takwas 'yan bindiga suka kashe a kasuwar shanu

    Mutum aƙalla takwas ne 'yan bindiga suka kashe a kasuwar shanu ta Jihar Abiya da ke kudu maso kudancin Najeriya ranar Talata, kamar yadda gwamnatin jihar ta tabbatar.

    Jaridar Punch ta ruwaito Kwamashinan Yaɗa Labarai da Tsare-Tsare Eze Chikamnayo yana cewa an kai harin ne da misalin ƙarfe 11:35 na dare.

    sai dai wasu mazauna yankin da BBC Hausa ta tattauna da su sun ce mutum 11 ne suka mutu a harin.

    "A ranar Talata 15 ga watan Fabarairu da misalin ƙarfe 11:35 na dare, wasu 'ya bindiga da ba a san ko su wane ne ba suka afka wa 'yan kasuwa a Sabuwar Kasuwar Shanu ta Omumauzor da ke Ƙaramar Hukumar Ukwa ta Gabas," in ji shi cikin wata sanarwa.

    An kai harin ne kwana ɗaya kafin komawar jagoran ƙungiyar 'yan tawaye ta Indigenous People of Biafra (IPOB), Nnamdi Kanu, gaban kotu don fuskantar tuhuma game da zargin ta'addanci a Abuja babban birnin ƙasar.

    Hukumomi a ƙasar na zargin ɓangaren 'yan bindiga na IPOB mai suna Eastern Security Network (ESN) da kai ire-iren waɗannan hare-hare.

  18. Ambaliyar ruwa ta kashe mutum kusan 100 a Brazil

    Ambaliyar ruwa da zaftarewar ƙasa a birnin Petropolis na Brazil sun halaka kusan mutaum 100, inda yawancin mutane kuma suka rasa muhallansu.

    Guguwar da aka yi da ruwan saman da aka sheka kamar-da-bakin-kwarya cikin awowi ƙalilan sun sa taɓo ya binne gidaje.

    Matan Henrique na daga cikin wadanda suka tsira. Ya ce: "Yawancin mutane sun rasa duk abin da suka mallaka, ba su da komai, babu wurin kwanciya, babu abinci, komai kankantar abu zai faranta musu rai. wasu na bukatar wanda zai rungume su cikin tausayawa da ba da kwarin gwiwa."

    Tuni jihohi makota suka fara aika kayan agaji da injinan da za su taimaka a kwashe taɓo da bishiyoyin da suka kakkarye tare da rufe hanyoyi.

    Tun da fari, a jiya Laraba Magajin Garin Petropolis ya ayyana dokar ta-baci a birnin.

  19. Barka

    Mun sake haɗewa a shafin labarai kai-tsaye, wanda a ciki Umar Mikail zai kawo muku rahotanni na abubuwan da ke faruwa a sassan duniya a wannan hantsi na Alhamis.

    Rahotannin za su fi mayar da hankali kan Najeriya da Nijar da makotansu.

    Mu je zuwa!